Sashe 104
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadik ya kuma cewa, "Allah ya kyauta kawai, amma akwai wani abun a ƙasa. Ina jin ka, meye labari mai daɗin?."
Saheer muryarsa a shaƙe ya ce, "share kawai, zuwa anjima zan wuce in sha Allah, komai normal ko?."
Sadik ya ce, "komai ya yi normal, sai mun haÉ—u" ya faÉ—a yana fita daga motar shi kuma ya ja motar ya tafi.
Islaha tunda ta shiga ake ta murnar ganinta, Chairman har office É—inta ya shiga yana ta murnar ganinta, ya zauna ya ce, "Malama Islaha, saukar yaushe?."
Ta yi dariya ta ce, "Shekaran jiya."
DaÉ—i ya mamaye ransa ya ce, "ni da ake ta cewa ga Islaha na É—auka wata muka samu daban ba ke ba, sai na yi tunanin kaf gidan nan ke kaÉ—ai ce mai irin wannan sunan, ashe ke É—in ce dai."
"Ni ce Chairman."
"Barka da sauka Islaha."
"Yauwa Chairman."
"Amma dai an dawo kenan ko? Baza ki sake guduwa ki bar mu ba? Allah in za ki sake sai dai ki nannaÉ—e toron giuwa ki tafi da ita, dan baza mu zuba ido ki saka mu watse ba."
Ta yi dariya ta ce, "na dawo in sha Allah, babu inda zan sake zuwa, muna nan tare."
Ya sauke numfashi ya ce, "har na ji daɗi wallahi, da na san kina nan ai da ke za ki yi labaran ƙarfe shida. Amma akwai na sha biyun rana ai, Allah ya nuna mna."
Ta yi murmushi ta ce, "Amin Chairman."
"Ki gode Allah Islaha, kina da sa a sosai a rayuwar ki. Kina daga inda ki ke ma É—aukakar bata bar ki ba, wannan É—an content É—in da ki ke yi ya sake farfaÉ—o damu daga doguwar suman da muka afka da bakya nan."
Ta yi dariya bata ce komai ba, Chairman ya ce, "yau yau É—in nan za a fara ganin ki, akwai labarin wasanni da za a gabatar kai tsaye, tashi ki hau camera."
Ta É—an buÉ—e ido ta ce, "Aikin Jamila da Muslim ne fa."
"Yau kema za ki É—ana, ni na san za ki iya. Taso maza maza."
"Chairman faÉ—ar sunan Æ´an ball É—in nan wani lokacin yana bani wahala, kar na kwafsa fa."
Ya kalle ta ya ce, "Sai dai in wata Islahan, ba dai ke ba, mu je." Ta dole y saka ta gabatar da shirin ba dan tana so ba.
Da yake shirin live ne a radio da tv da kafafen sada zumunta, an sha ruwan comment ana murnar sake ganin fuskar Islaha.
Shigowar Ummi kenan ta samu baƙin labari, ta nufi office ɗin Islaha dan ta ganarwa idonta. Tana shiga suka haɗu, Ummi bata ce komai ba ta juya ta bar wajan da hanzari.
Islaha ta taɓe baki, bata bi ta kanta ta wuce record office wajan Safeera, a hanya suka haɗu da Safeeran ta taho nemanta, sai suka koma office ɗin su Islahan dan su tattauna."
Safeera ta ce, "Ya dai? Na ga duk kin canja."
Islaha ta ce, "Hamma ne bai yarda da labarin da na bashi ba, wai har yana cemin ya sunan film É—in."
Safeera ta ce, "ba kowa ne zai yarda ba fa Islaha, ni kaina sai da na kai zuciya nesa sannan ya amince da maganar nan. Kowa zai yi tunanin me ya kawo Ray cikin zancen ki, da ace ƙarsmin mutum ne babu wanda zai damu, amma sunan babban mutum kamar sa ki ka ambata, iya faɗa kawai mutum zai ga kamar kin raina masa hankali ne kawai."
"amma meyasa ke ki ka yarda shi bai yarda ba? Wai har yana cewa ina rantsuwa akan ƙarya, wallahi Safeera baza ki bini bashin rantsuwa ba, bazan yi abinda zai cutar dani dan na kare kaina ba. Safeera duk abinda na faɗa miki an yi, wani abun ma ban faɗa miki ba. Meyasa Hamma bazai yarda dani ba? Shima ya fara zargina kamar Mamansa kenan?."
"ba zargi bane, kawai zai ji kamar kin mayar dashi mahaukaci ne. Amma zai amince, ki sake yi masa bayani."
Ta yi tsaki ta ce, "ai tunda ya ce na rantse a kan ƙarya babu abinda zan sake faɗa masa, in ya ga dama ya yarda, in bai ga dama ba kar ya yarda bai dame ni ba. Abu ɗaya na sani, gaskiyata na faɗa, duk wanda yake yi min wani kallo na daban shi da Allah, kuma ban yafe ba wallahi."
"Babu zancen shi ya sani, dole ki yi masa bayanin da zai gane kuma ya fahimce ki, shine wanda za ki aura fa."
Ta kalli Safeera ta ce, "to me zan ce masa? Kina ji na faÉ—a miki yadda muka yi dashi."
"Haka za ki sake faÉ—a masa har ya gane."
"Hmmmm! Ga Baffa ya ce bazan sake yin sati biyu a gidan nan ba, aurena da Hamma za a yi."
Safeera ta buÉ—e ido ta ce, "Baffa ya matsa fa, kuma na san duk saboda Mama ne."
Ta taɓe baki ta ce, "itace mana, kin ji kalaman da ta dinga faɗa min?. Ni yanzu fargaba ma nake yi wallahi, ta ya zan yi rayuwar auren da mijin da babarsa bata ƙaunata?."
Safeera ta ce, "Babban ƙalubale ne mai girma, amma kuma ai shi yana sonki."
"Na raina son da yake yi min, tunda ya kasa bani listing ears ɗinsa har yake cewa ina rantsuwa a kan ƙarya, kuma yake zargin kamar yawon banza na je na yi har na samu waɗanan kuɗin."
"Ba zargi bane, dole zuciya zata yi rawa."
"ke meyasa ki ka yarda dana faÉ—a miki?."
"Nima da farko ban yarda ba."
"yanzu fa?."
"Na yarda."
"saboda me ki ka yarda?."
"Saboda na san halinki, kuma na yarda dake."
Islaha ta ce, "kin ga kenan shi bai yarda dani ba, ga shi ke kin amince shi ya kasa amincewa. Bazan bashi tsarabar da na siyo masa ba ma, in na ba shi wani zargin ne zai sake shiga tsakani. Har Sadik É—in bazan bawa ba, zan ajjiye kayana na siyar ko na bayar. Tunda ya fara zargina in na ba shi wani zargin ne zai biyo baya."
Safeera ta yi dariya jin ta fusata sosai da Hammanta ta ce, "Ki ba shi mana, kar ki fasa alkhairin da ki ka yi iya."
Ta yi tsaki ta ce, "Bana son rainin hankali ne wallahi, bai taɓa bani haushi kamar yau ba, ya ɓata min rai sosai, da wani ne ba shi ba da sai ya raina kansa wallahi."
Sai kuma ta kalli Safeera ta ce, "Kin gama abin ki ke yi?."
Safeera ta ce, "na gama."
Islaha ta miƙe ta ce, "Mu je ki raka ni office ɗin Barr, daga nan mu je gida na ɗauki tsarabar Adda na kai mata." Safeera ta miƙe suka fito tare.
Ummi tana barin wajan office É—inMuslim ta shiga, ta same shi a zaune ta shiga a fusace ta ce, "Islaha ta dawo, ka ganta?."
Ya É—ago ya ce, "Haba Ummi, babu sallama babu neman izini?."
"Ba shi ya kawo ni ba, ka ga Islaha?."
"na ganta. Itace ta gabatar da shirin da nake gabatarwa yau."
"ka kasa yin komai a kanta, kai ka ce za ka nemo mafita kafin ta dawo, baka yi komai ba gashi har ta dawo. Na ga ji da waɗanan alƙawarin naka, ni zan yi abinda nake ganin ya dace."
Ya miƙe ya ce, "Allah ya baki sa'a, amma duk abinda ki ka aikata kar sunana ya fito, dan babu hannuna a ciki. Jeki tunda ba ki da hankali, ki je ki aikata abinda zuciyar ki take raya miki ya kamata ki yi. Ke ba ki san a hannun hukuma ki ke ba ko?" ya faɗa yana zama bai kalle ta ba."
"Ka kasa yin komai, kai ka ce baza ka bata damar dagowa ba, amma gata ta dawo, ta ya hankalina zai kwanta?."
A fusace ya ce, "an faɗa miki cikin gaggawa ake yin abun? Ko an an faɗa miki ƙaramin abu nake so na yi?. Tunda baza ki iya jira ba ki je ki yi abinda ki ka ga ya dace, amma wallahi duk abinda ki ka aikata kar ki sake sunana ya fito a ciki."
Ummi ta koma ta zauna tana jan numfashi, ya yi mata banza bai ce mata komai ba ya cigaba da abinda yake yi.
"Yi haƙuri. Hankalina ne ya tashi wallahi."
"Da sannu sannu ake yin komai, a hankali zamu É—ana tarkon da zai kama mata wuya. Program É—ina aka É—auka aka bata, ni kaÉ—ai na san abinda nake ji a raina. Dan haka ki nutsu, wallahi Allah bazan bar Islaha ba, sai na yi mata abinda baza ta iya É—aga ido ta kalli camera ba har abada."
Ummi ta ja numfashi ta ce, "yaushe?."
"Ki ƙyale ni kawai" ya faɗa yana miƙewa ya bar ta zaune.
•••••••
"Sabon labari ya bayyana, na samu labarin yarinyar nan Zainab kafin ta bar gidan nan ta bawa Yafindo ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan nan saƙo ta bawa Islaha. Har Islahan ta biyo bayan saƙon, ta dawo cikin garin nan kuma zata cigaba da tone tone. Hankalinta ya tashi tana neman ƙauyen su Yafindo dan ta a bata wannan saƙon."
Ya girgiza kai ya ce, "Yarinyar nan da gaske dai dangerous ce a gare mu. Ita Yafindon ina ne garin na su?."
"Kwata-kwata ba Æ´ar Adamawa bace."
"Duk yadda za a yi mu rigata zuwa, ko ta iska zata hau ta je wajen Yafindo, mu zamu hau guguwa mu rigata sauka, kafin ta je mu mun je mu karɓi abinda aka bata ko ta lallami ko ta ƙarfi."
Mama ta ce, "tsohuwa ce fa."
"tsohuwar fa, in ta ƙi ayi mata sbinda aka yiwa Zainab ɗin. Itama Islahan lokacin ta ya yi, dole ta rasa ɗaya daga cikin waɗnanan abubuwa guda biyu. Ko rayuwarta, ko kuma hankalinta!."
Mama ta sauke numfashi ta ce, "Mu fara da maganin Islahan, amma maganar ta tsaya iya ni da kai, kar ka faÉ—awa wani muna shirin yiwa Islaha wani abun."
Da mamaki yake kallon ta ya ce, "saboda me?."
Ta ja numfashi ta ce, "zan faɗa maka dalilin, amma dai magana ta tsaya iya ni da kai. Zan san hanyar da zan bi na yi maganinta da gaggawa, in ba haka ba zata yi mata illar da bamu taɓa zato ba."