← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 133

Sashe 101

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi murmushi tana kallonsa, har zai tafi sai ya kasa daure abinda yake yawo a jininsa, ya dawo da baya, ya riƙe fuskar ta ya ce, "Ina ji kamar na rungume ki, ina jin kewar ki da yawa, ganin ki kaɗai bai gamsar dani ba, ina so na ji ki a jikina. Shiyasa na so kafin ki dawo an ɗaura auren mu, yadda zan nuna miki adadin kewar ki da na yi."

Islaha ta sake sunkuyar da kai ƙasa bata ce komai ba. Saheer ya yi ƙasa da murya yana kallon ta ya ce, "in rungume ki?."

Islaha ta ƙi kallonsa, sai wasa da take yi da hannunta amma ita kanta ta yi murnar ganinsa sosai ta jin daɗin haɗuwarsu.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Me ki ka saka shi gida kina yi masa ku kaɗai a gida babu kowa?.”

Nana Haleema.
[7/21, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P74
Nana Haleema.

Jin muryar Mama cikin amo duk sai suka waiwayo suna kallon ta. Mama ta ƙasaro da zafin nawa ta janye Saheer daga kusa da ita.

Ta kalli Islaha ta ce, "rungumarsa za ki yi? Na ce rungumarsa za ki yi ko sumbatarsa za ki yi?. Kin je kin saba bin maza, kin ɗanɗana fulani kin ɗanɗana larabawa, dole ki zo ji cigaba da lalata min yaro. Yaarinyar da ta gama lalacewa a ƙasar waje, in ban da masifa da bala'i me zata yi min a gidana?."

Saheer da yake ji kamar ya yi kuka saboda kalaman Mama, a sanyaye  ya ce, "Mama ki bari don Allah."

Ta harare sa ta ce, "dallah can yi min shiru, mara zuciya da kishin kai. Me za ka yi da wannan ragowar? Me za ka yi da wannan watsatstsiyar wacce ta gama raba kanta a ƙasar waje?. A cikin wata biyu ta haɗa kuɗin da aka kai ta ta biya, sannan ta siyi ticket ta dawo gida kuma harda tsaraba. Daman Labiba ta faɗa min, gida gidan larabawa take shiga, wannan ya ɗauka wannan ya ajjiye."

Islaha hawaye ya sakko daga idonta ta ce, "Wallahi Mama ni ba yawon....." ta kai mata mari Islaha ta yi saurin komawa bayan Saheer tana kuka.

Mama ta nuna ta da yatsa ta ce, "sai na tsinke ki da mari. Ni ki ke faÉ—awa haka, ni ki ke kallon idona ina faÉ—a kina musawa?. In ba watsewar ba faÉ—a min me ki ka yi?."

Bata ce komai ba sai kukan da take yi kawai, kuka mai tsuma zuciya, kukan da yake fita da wani irin sauti mai tayar da hankali.

Mama ta jawo ta daga bayansa ta ce, "bar jikinsa ko na fasa miki ba ki. Ni dai an cuce ni, an kawo min tsintacciyar mage, an haÉ—a ni da mugun iri."

Saheer ya ce, "Mama don Allah ki bari, ki daina faÉ—ar hakan babu daÉ—in ji."

Ta harare sa ta ce, "ga ka gata nan, sai ayi auren na gani" ta faÉ—a tana barin wajan.

Ya kalli Islaha da take kuka sosai, ya kasa yi mata magana ganin yadda take jan nunfashi hawaye yana sakkowa daga idonta.

Cikin sanyi jiki ya ce, "Ki yi haƙuri, je ki ɗaki ki zauna na kawo miki abincin, ki daina kuka kar ki sarƙe.”

Bata shiga É—akin ba, ta É—auki mayafinta da ta ajjiye a wajan ta fita daga falon a guje.

Da sauri ya bita yana kiran sunanta, ta tsaya ya ce, "kar ki fita Islaha, ki jira ni na kawo miki abinci."

Ta ja numfashi ta ce, "na...na ƙoshi" ta faɗa muryar tana cracking saboda kuka.

Ya ce, "sai kin ci, shiga ɓangaren Baffa na kawo miki."

Ta ƙi motsawa daga inda take, ya ƙaraso kusa da ita ya ce, "ki je ki zauna ki jira ni."

A lokacin Baffa ya shigo gidan ya ƙaraso ya ce, "Saheer me ya same ta take kuka haka?."

Saheer ya kalli Baffa ya ce, "Baffa Mama ce."

Baffa ya sauke nunfashi ya ce, "wani abu ne ya faru?."

"Ka san halin Mama Baffa, kalamai marasa daÉ—i ta dinga faÉ—a mata, shine ta É—auko mayafi zata fita."

Baffa ya ce, "Islaha mu je falona ki zauna, kai ina zaka je?."

Saheer ya ce, "abinci zan kawo mata, ta ce yunwa take ji."

Baffa ya ce, "jeka ka kawo mata, Islaha mu je ciki."

Bazata iya yiwa Baffa musu ba, ta karɓi ledar hannunsa suka cigaba da tafiya a hankali shi kuma ya fita.

Suna shiga Baffa ya ce, "Zauna Islaha." Ta zauna a kan carpet ya zauna a kan kujera.

Ya ce, "ki cigaba da haƙuri kin ji, ki cigaba da ɗauke kai ƙiris nake jira na ɗaura auren ku. Amma bara Saheer ɗin ya zo mu san abinda za a yi." Ta yi shiru tana goge hawaye, Baffa ya dinga rarrashinta cikin kalamai na kwantar da hankali.

A lokacin Saheer ya shigo da sallama, suka amsa ya ƙaraso ya zauna ya miƙa mata ledar abincin ya ce, "ga abincin nan."

Ta ja ledar kusa da ita amma bata buÉ—e ba, Baffa ya ce, "ki ci abincin ki, ina zuwa" ya faÉ—a yana tashi ya shiga É—aki dan ya bata dama ta ci.

Saheer ya bita da kallo, a sanyaye ya ce, "Islaha ki ci."

Ta buÉ—e ledar ta ga fried rice ce da chicken, ta sauke numfashi ta fara ci a hankali dan da gaske yunwa take ji. Harda ruwa da lemo a ledar, ta sha ruwan ta rufe ragowar abincin.

A lokacin Baffa ya dawo ya zauna, Saheer ya ajjiye masa tasa ledar abincin da ya siyo masa a kusa dashi.

Baffa ya kalli Saheer ya ce, "Ina so É—aurin auren ku kar ya wuce nan da sati É—aya, ka shirya?."

Cikin ƙarfin guiwa ya ɗaga kai alamun eh, sai kuma ya ce, "Baffa ina jin tsoron furuncin Mama."

Baffa ya ce, "ka bar ni da ita, kar ka damu da wannan furucin nata, babu abinda Allah zai yi maka."

Baffa ya kalli Islsha ya ce, "Ƴata Islaha kin amince da auren ku nan da kwana sha huɗu?."

Islaha sake saukar da kanta ƙasa bata ce komai ba, Baffa ya ce, "Kar ki ji kunya, na san kema kin gaji da takura da zagi da tsangwar da Zulaiha take yi miki sun ishe ki. Bana so ki dinga jin kamar dan ba ki da iyaye ne ya saka ake yi miki haka, bana so ki ji na gaza a matsayina na uba a gare ki. Ina so ki samu farin ciki da kwanciyar hankalin da nake so ki samu, ina so ki samu walwala da nutsuwa kamar kowa. Shiyasa nake so a yi auren yanzu, amma sai kin amince."

Islaha ta sake sauke kai ƙasa ta kasa cewa komai, Baffa ya ce, "ki amsa."

Kanta yana ƙasa ta ce, "Duk abinda ka yanke daidai ne."

"A'a, faÉ—a min ra'ayin ki."

"na ba ka zaɓi Baffa."

"sai kin zaɓa."

Ta kasa É—ago ido ta kalle sa ta ce, "na amince Baffa."

Baffa ya murmusa ya ce, "ki fara ƙananun shirye-shirye, daman ya ce min an gama haɗa lefen ki, ginin gidansa shima ya zo ƙarshe. Kai ko ba a gama ba, na yarda ku kama haya ku zauna, nan gaba sai ku tare a gidan na ku."

Islaha dai kanta yana ƙasa, Saheer ne yake murmushin jin daɗi, amma in ya tuna da Mama sai gabansa ya faɗi.

Saheer ya kalli Baffa a hankali yace, "Baffa ina jin tsoron Mama."

Baffa ya ce, "ka kwantar da hankalin ka, babu abinda zai faru, zata yi haukata ta gama."

Baffa ya kalli Islaha ya ce, "na yi miki alƙawarin baza ki sake sati biyu a gidan nan ba, za ki je inda za ki samu ƴancin rayuwa yadda ki ke so."

Ita dai bata ɗago ba ta dai yi murmushi, tana jin ƙaunar Baffa tana shiga zuciyarta sosai. Baffa ya ce, "ki yi zaman ki a nan, zan je na yi sallah na dawo" ya faɗa yaa  miƙewa ya fita.

Saheer ya ce, "to ya fita, sai É—ago ki kalle ni mu yi magana."

Ta É—ago a hankali tana kallonsa, Ssheer ya É—aga mata girarsa sama ya ce, "To ya dai Æ´an mata, kin shirya?."

Sai ta yi murmushi ta kuma sunkuyar da kanta bata ce komai. Ya yi murmushi shima sannan ya miƙe ya ce, "zan je na yi sallar magrib."

Itama ta miƙe ta ce, "nima sallar zan yi, amma bana son komawa can."

"Na raka ki É—akina ki yi alwalar?."

Ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "Kar Mama ta ganni. Bara na yi da ruwan nan, ya ishe ni" ta faÉ—a tana É—aukar ruwan suka fito tare.

Mama tunda ta shiga ɗaki take waya ta ce, "Karima abubuwa suna neman lalace min, wannan yarinyar da ta je ta dawo maganar auren nan tana sake tasowa fa, ni kuma wallahi bazan  bar Saheer ya aure ta ba."

Karima ta ce, "wata maganar ce ta taso kuma?."

"Za dai ta taso, dan yanzu haka tana ɓangaren Baffa ya sakata a gaba yana rarrashi. Ni dai taimako bai yi min rana ba wallahi, na ɗaukowa kaina abinda ya fi ƙarfina."

"Ai na faÉ—a miki, tun yarinyar bata kai haka ba nake ja miki kunne akan zamanta a gidan ki, amma ba ki É—auki mataki ba, yanzu gashi nan kina ji kina gani zata aure miki É—a bayan ta gama yawace yawancen ta."

"Bata isa ba wallahi, sai dai ayi ragas, mutuwar kasko."

"Lallai ma, ke da É—an cikin ki ki ke fatan ayi ragas? Ai babu batun ragas, ke ce mai nassra kawai."

"Yanzu meye abin yi? Ni ko meye zan yi akan Islaha, in kashe ta za a yi a kashe, in haukata za a yi a haukata. Duk abinda za a yi ayi, indai zata fasa auren Saheer."

Karima ta ce, "KuÉ—i za ki fito dasu, mu je mu bi hanyar da Saheer É—in da kansa zai ce bazai aure ta ba."

Mama ta ce, "yaushe za a yi hakan?."

"Gobe ma in kin shirya mu wuce, na faÉ—a miki wannan kurarin babu abinda zai yi, tsaf za a yi auren nan ba ki sani ba wallahi. Dan haka mu je a yiwa tufkar hanci tun bata warware ba."

Mama ta ce, "ƙarfe nawa goben?."
Chapter 101 · 0% Book details