← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 133

Sashe 59

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kalli Saheer da ta san jiran amsar ta yake yi, iaya kallon da yake yi mata kaÉ—ai ta san na jiran amsa ne. Islaha ta ce, "Sunansa Maleek, nan gidansa ne, a gidan nake aiki dani da wata Sunaira. Yanzu ma na yi tunanin itace shine na ce ya shigo."

"Oh! Da gidansa ne sai ya dinga shiga É—akin ki kai tsaye?."

Ta sunkuyar da kai ta ce, "ba ya shigowa, yanzu ma ni na bada dama, na É—auka Sunaira ce."

Ya yi shiru bai ce komai ba, Islaha ta ce, "Ya ga bani da lafiya shine ya kawo min magani."

Ya sake yin shiru bai amsa ba sai kallon ta da yake yi, a sanyaye ta ce, "ka yi haƙuri."

Ya girgiza kai ya ce, "ki kwanta ki huta." Ta É—aga kai ya kashe wayar...

Ta kwanta da baya tana kallon sama, cikin farin ciki tana jin daÉ—i, ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Hamma ya daina fushi dani, Allah na gode maka."

Ta juya a kan gadon ta kwanta tana murmushi, sai ta manta da batun Rehaan da ta gani, farin cikin ganin Hamma ya matar da ita wani Rehaan, daman tunanin ta gizo yake yi mata ba gaskiya bane, dan bata ga dalilin da zata ganshi a Jeddah ba. Ta miƙe ta kashe hasken ɗakin ga kwanta ta yi bacci.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._
https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S

Nana Haleema.
[7/6, 9:38 AM] KRBBK: RDB2P40
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._
https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S

••••••••••••

Bata farka ba sai ƙarfe uku na dare, ta miƙe zaune tana murza ido tana tuna mafarkin da ta yi.

A bayyane ta ce, "da gaske dai gizo ya yi min, tunda gashi na sake yin mafarki yana cewa na biyasa kuÉ—insa."

Ta sauke numfashi tana É—an runtse ido dan har lokacin tana jin ciwo kaÉ—an kaÉ—an.

Ta ɗan ja numfashi ta ce, "Allah ka bani kuɗi na biya mutumin nan kuɗinsa na huta, Allah kawo min hanyar da zan biyasa na huta da wannan bala'in. Sai mafarkinsa nake yi, fuskar da bata cancanci na ganta a mafarki ba ita nake gani. Na tsane shi, haka kawai bana son ganinsa. Bana son mutumin da ya cika alfahari" ta faɗa ta miƙewa a sanyaye dan jikinta kamar an yi mata duka, ga kasala da take ji kamar ta yi kuka haka take yi. Ta kunna hasken ɗakin ta ɗauki hular kanta ta saka, ta saka hijjab ta fito zuwa main falon.

Babu kowa a falon, ta wuce kitchen dan yunwa take ji sosai. Tana shiga ta ga babu abinci, babu komai sai da ta dafa. Takaici da baƙin cikin ya saka ta kukan da yake cin ranta, ta jingina da bango tana kuka dan bata dafa komai a halin da take ciki. So take a dafa a bata, inda hali a bata a baki. Ita ta saba, Hamma ya shagwaɓata, indai yana kusa baya bari ta yi komai, dan ya san yanayin da take ciki yana haifar mata da kasala da son jiki.

Motsin da ta ji ya saka ta kalli wajan, ta ga Maleek da shigar fita da alama dawowarsa kenan.

Ganin tana kuka sai ya ƙaraso ya ce, "Islaha are you Okay?."

Ta É—aga kai ya ce, "and why are you crying?."

Islaha ta goge idonta ta ce, "i'm so famished, and i don't want to cook."

Bai ce mata komai ba, ya ƙarasa fridge ya ɗauko mata fresh laban ya ƙaraso ya ja kujerar dinging ɗin kitchen ɗin ya ce, "have a seat please."

Haka ta ja ƙafar ta kamar mara jini, ta zauna akan kujerar, ya tsiyaya a cup ya miƙa mata. Ta karɓa sai ta ji ya yi sanyi sosai, ta ajjiye ta ce, "is too cool."

"Oh sorry" ya faÉ—a yana É—auko mara sanyi ya yi mata mix ya bata.

Islaah haka take so a duk lokacin da take cikin wannan yanayin, tana son kulawa, tana so komai ayi mata, hakan yana sakawa ta ji ta comfort bata da damuwa ko kaÉ—an.

Ta ja cup É—in tana sha a hankali, yana tsaye yana kallon ta har shanye. Maleek ya ce, "me ki ke so kuma?."

Ta girgiza kai ta ce, "nothing, i'm okay."

"Are you sure?."

Ta É—aga kai ta ce, "Thank you."

Ya murmusa ya ce, "my pleasure."

Ta sauka daga kan kujerar tana takawa a hankali ta fita shi kuma ya shiga ciki.

Washe gari da suka gama komai ita da Sunaira, yana fitowa breakfast sai da ya tambayi ya jikinta ta ce taji sauƙi.

Ya zauna akan dining É—in sanann ya ce, "za ki iya zuwa gidan Dr?."

Ta É—aga kai ta ce, "zan iya."

Ya É—aga kai ya ce, "Fine." Ya zauna ya gama cin abincinsa sannan ya fita.

Islaha tana zaune kafin ta tafi gidan Rehaan, ta yi shiru tana tunani Umma ta faɗo mata rai. Duk da Umma bata sonta amma mahaifiyar Safeera ce, baza ta iya share ta ba, kuma Safeera ta bata amanar Umma, ko lafiyar ta ya kamata ace ta kira ta ji. Ta ɗauki wayar ta ta shiga kiran wayar Umma amma bata samu, duk sai ta ji ta damu tana so ta san halin da Umma take ciki kodan saboda alƙawarin da ta yiwa Safeera.

Tunawa da Alhaji Musa ya basu lambar sa sai ta kira sa, ta yi sa a ya É—auka suka gaisa ta ce,

"Islaha ce, wacce suka zo daga Yola aka kawo su nan Jeddah."

"Okay na gane, ya aka yi?."

"Don Allah Lambar wacce ka haÉ—a Umma da ita suka tafi Madina nake so, ina ta neman Umma bana samun ta ko kaÉ—an."

Ya ce, "okay zan tura miki." Ta yi masa godiya ya kashe wayar. Tana zaune lambar ta shigo, bata yi ƙasa a guiwa ba ta kira ta.

Tana É—auka Islaha ta ce, "Barka ina yini."

Ta ce, "lafiya lau."

"Islaha ce, Æ´ar uwar wacce Alhaji Musa ya haÉ—a ki da ita ki ka kaita Madina."

"Yaushe kenan?.

"Sati biyu da suka wuce, har ni na zauna a Jeddah nida Æ´ar uwata."

"Na gane. Ya aka yi?."

"Ina nemanta a waya bana samu, don Allah ko za ki haÉ—a ni da ita?."

"Sai aka ce miki tare mu ke kwana ko me?."

"A'a ina so na san ne kawai."

Matar ta ce, "shikenan, zan tura miki da lamba Shafa sai ki yi mata magana, zata iya haÉ—a ki da ita." Bata gama maganar ba ta kashe wayar.

Islaha ta tsaya jiran lamba amma shiru, sai daga baya sai ga lambar ta shigo, Islaha ta kira kai tsaye.

Hajiya Shafa bata ɗauka, hakan ya saka Islaha ta gaji tanmiƙe ta shiga cikin ɗakinta. Ta tsaya tana kallon kanta, tana tuna abinda ya faru a gidan Rehaan wanda take ganinsa kamar a mafarki. Ta yi saurin taɓa waist ɗinta jin kamar har yanzu akwai hannun Rehaan a wajan, ta ɗan lumshe ido tana tuna ƙhamshin turarensa da sassanyar muyarsa da yake tambayarta tana lafiya.

Ta yi ajiyar zuciya, ta sake gyara kitson kanta sannan ta canja kaya zuwa sabon uniform ta saka hijjabi ta É—auki wayarta.

Sai kuma ta ya tsaya tunawa ina kuma zata je? Gidan da take zuwa ta san ba lokacin zuwan ta bane, tunda yanzu rana ta buÉ—e. Ta yi ajiyar zuciya ta fita dan sai ta ji gidan ya fita daga ranta.

Tana fitowa gidan ta ga Labiba ita da Aisha sun fito daga gidan Ubaid, suka haÉ—a ido da Labiba, sai da gaban Islaha ya faÉ—i ganin wani irin kyaun da Labiba da ta yi kamar ba ita ba. Itama

Labiban kallon Islaha take yi dan ganin ta yi kyau itama sosai, sai dai ta É—an rame kaÉ—an kuma fuskar ta ta nuna alamun rashin lafiya.

Aisha ta kalli Labiba da take kallon Islaha, kowa ya tsaya kuma babu wanda ya cewa ɗan uwansa Hii. Aisha ta ce, "wannan zuƙeƙiyar fa? Itace wacce ku ka zo tare?."

Labiba ta kalli Aisha ta ce, "itace. Tsintacciya ce a gidan mu, kuma ita Yayana zai aura."

"Kai amma tana da kyau fa, kalle ta fa, kalli skin É—inta har wani shining yake yi kamar tana shafa chocolate. Wow, gaskiya ta burge ni sosai."

Labiba ta ɓata rai ta ce, "kin ga Aisha, mu je inda zamu je."

Aisha ta ce, "ita baza ta shigo ba? Ya kamata a sako ta a sabgar nan itama ta samu, wallahi ni kaina ta burge ni balle namiji."

"Ki ka sani ko gidan da take itama irin mu ne?."

Aisha ta yi dariya ta ce, "gaskiya, daga ganin yanayinta baza a barta haka ba." Labiba ta yi dariya ta ce, "Daman ta saba, tun a gida tana yawon ta."

Islaha dai tana tsaye tana kallonsu har suka fara tafiya kafin su samu taxi su tafi.

Islaha ta yi ajiyar zuciya ta motsa daga wajan ta ƙarasa gidan Rehaan ta buɗe gate ɗin ta shiga a hankali.

Tana tafiya tana sake ƙarewa gidan kallo, ta kalli car park ɗin da yake can gefe, ta ga mota biyu a ajjiye, sai ƙaton filin da ya rage wanda zagaye ko ina da fulayoyi masu kyau da tsada.

A hankali take takawa wajan ƙofar ta saka code ɗin ƙofar ta buɗe ta shiga a hankali. Hasken falon a kunne yake saɓanin yadda ta saba tarar sa falon, sai laptop da take buɗe a ajjiye, da alama ba a jima da gama amfani da ita ba, sai mug ɗin tea da yake wajan a ajjiye.

Islaha ta bi wajan da kallo, ƙhamshin turaren Rehaan yana nan, duk inda ta gifta a falon ƙhamshinsa yake yi.
Chapter 59 · 0% Book details