← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 133

Sashe 98

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safeera ta yi shiru tana binta kallo, Islaha jin ta yi shiru sai ta ɗago ta kalle ta ta ce, "ba ƙarya nake yi miki ba Safeera, wallahi da gaske nake. Ashe likita ne, yana aiki a ƙasar, shine wanda mai gidan da nake yiwa aiki ya ce na je na dinga dafa masa tea. Kuma babban mai kuɗi ne ko a ƙasar nan, kuma babban ma'aikaci ne. Safeera wallahi ni ban ɗauka yana jin yaren mu, dan bai yi kama da ƴan ƙasar mu ba gabaɗaya."

Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Abin ne ya É—aure min kai, maganar ta yi wani iri Islaha. Shi ya sace ki, ki ka É—auki kuÉ—insa, ki ka je Jeddah dan ki tara masa kuÉ—insa ki biya sa, sannan kuma kin fara aiki a gidan sa, kuma kin samu kuÉ—in da ki ka biyasa a gidan sa. Ta ya hankali zai É—auki wannan? Kar ki saka zuciyar mu ta yi zargin wannan plan ne, da sace ki da zuwan naki da komai da komai."

Islaha ta É—an rufe ido ta buÉ—e ta ce, "Safeera wallahi Allah da gaske nake miki, ni ban san shi bane, da farko in na shiga gidan bana ganinsa, sai ranar da nake fama da ciwon mara ne muka haÉ—u. Da ya nuna bai gane ni ba nima sai na numa ban gane sa ba, na cigaba da harkokina. Kuma in dai zan iya zuwa Jeddah, shima zai iya."

"Na ji, za ki iya zuwa, shima haka. To ta ya ki ka samu kuÉ—in da ki ka biyansa a cikin gidan?."

"Wai kin san waye shi kuwa?."

Safeera ta ce, "Ta ya zan sani bayan ba ki faÉ—a min ba?."

Islaha ta ce, "zan faÉ—a miki waye shi, amma bana so kowa ya sani don girman Allah."

"Ina jin ki."

Islaha ta yi ajiyar zuciya, ta ce, "wayar ki da data?."

Ta ɗaga mata kai alamun eh, Islaha ta ɗauki wayar Safeera ta shiga google ta yi searching sannan ta ce, "karɓi ki duba."

Safeera ta karɓa tana kallon screen ɗin, ta kalli Islaha ta ce, "Rehaan Yola nake gani."

Islaha ta ɗan zuba mata ido dan bata san ta ya zata ɗauki wannan maganar ba, ko ita aka zaunar aka faɗawa wannan shirmen baza ta yarda ba, kai tsaye zata ƙaryata mutum sai dai su yi faɗa.

Islaha ta ce, "Dashi na haÉ—u a diamond hotel a lokacin da muje can neman, ya zuba min tea a jikina na nuna masa kuskurensa. Da shi muka haÉ—u asibiti lokacin da ki ka same ni ina kuka har ya fasa min wayata....."

ta ja numfashi tana kallon irin kallon da Safeera take yi mata sannan ta ce, "shine ya sace ni, kuma shine likitan da ya yiwa Baffa tiyata, kuÉ—insa na É—auka, kuma a gidansa nake shiga aiki!."

"Mtsw!" Safeera ta ja tsaki bata ce komai ba, ko kallon Islaha bata kuma yi ba ta É—auke kanta jin ta mayar da ita kamar wata yarinyar goye.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

Nana Haleema.
[7/21, 12:04 PM] KRBBK: RDB2P72
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.🙏🏻😭_

Islaha ta yi murmushi tana kallon Safeera ta ce, "ba ki yarda ba ko?."

Safeera ta kalle ta ta ce, "kema ba ki yi abinda zan yarda ɗin ba, in ba dan ke ce b da bazan tsaya na saurari wannan shirmen ba. Rehaan Yola fa ki ke magana, kina zancen dashi ki ka haɗu ki ka yi kaza kaza kamar wani ɗan gidansu Hamma. Rehaan ya wuce tunanin ki, a ina za ki gansa balle har wannan abubuwan su faru?. Kuma kina nufin duk yadda hotunansa suka baza duniya ba ki taɓa ganinsa ba? Ke ma'aikaciya ce, kuma ƴar social media, kina nufin ba ki san fuskar Rehaan ba?...."

Ta É—an girgiza kai alamun kin raina min wayo ta ce, "Haba Islaha, ki faÉ—i abinda hankali zai É—auka, wannan hankali bazai É—auka ba."

Islaha ta yi ajiyar zuciya mai tsaho sannan ta koma koma tana cigaba da fito da kayanta sannan ta ce, "Ban yi tunanin in kowa bai amince dani ba kema za ki ƙi yarda dani, na ce miki wallahi amma ki kasa yarda."

Safeera ta ce, "Abin ne bai yi making sense ba Islaha, ta ya zan yarda da abinda ki ka faÉ—a?. Rehaan Yola fa, kina magana akan wanda ganinsa ma wahala yake yi, kuma ke kina faÉ—a min wai shine ya sace ki. Don Allah ta ya zan yarda da wannan maganar ta ki?."

Ta ɗago ta kalle ta ta ce, "Wallahi Allah da gaske nake miki, kin san ba ki isa na yi miki rantsuwa akan ƙarya ba, shima R Yolan bai isa na yi rantsuwa akan ƙarya saboda shi ba. Ban taɓa ganinsa ba, ko na taɓa ganin hotonsa ban tsaya na kalla yadda ya kamata balle har na haddace sa ba. Kin san Allah? Har na gama zama a hannunsa ban san waye ba, ban taɓa ji ya yi magana ba sai sau ɗaya, kuma ban ji wani ya kira sunansa ba. A Jeddah ma in ban da zuwa Jafar ban san waye ba, shine yake faɗa min da wanda nake tare. Ki yarda ko kar ki yarda bai dame ni ba, bazan zauna ina yi miki rantsuwa kina ƙaryata ni ba" ta faɗa tana fito da wata ledar alawa ta ajjiye.

Safeera ta girgiza kai cikin al'ajabin wannan lamari ta ce, "Na yarda Islaha, kawai abin ne yazo wani iri shiyasa."

Islaha ta yi mata banza ta cigaba da abinda ta ke yi. Sai daga baya ta ce, "ke kowa yana tambayata ya Umma amma kin kasa buɗe baki ki tambaya, na rasa a ina ki ka samo wannan baƙin halin. Kina ji har Maman su Kausar sai da ta tambaya, amma ke kin kasa cewa tana ina, bayan ita kullum cikin maganar ki take."

Safeera ta murmusa ta ce, "na san tana cikin ƙoshin lafiya."

"Ta ya ki ka sani? Waya ku ka yi da ita ta faÉ—a miki haka ko ganinta ki ka yi?. Ki daina irin wannan, uwa ce ita.."

Safeera sai ta ji zuciyarta ta karye, dauriya kawai take yi, amma ita kaÉ—ai ta san ya take jin kewar Umma.

Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Islaha kullum da tuanninta nake kwana nake tashi, kullum da kewarta da son ganinta muke kwana muke tashi. Ita fa ta haifemu, amma ta ajjiyemu, ta ajjiye aurenta ta tafi neman kuɗin da babu lallai ace ta same shi. Sai dai na nuna kamar ban damu ba saboda ƙannena, amma ni kaɗai na san yadda rashinta yake yi min illa. Duk yadda Mama zata kula damu ba kamar ita ba, kullum Khajida zaman jiran dawowarta take yi, kullum a zancenta take; so ki ke dinga nuna na damu su ma su shiga damuwa?."

Islaha ta É—an yi murmushi ta ce, "ke kenan, kin san ta ki mahaifiyar tana da rai, ni kuwa na ce me?." Safeera ta goge idonta bata ce komai ba.

Islaha ta ce, "ko ba ki nuna kin damu ba, ki dinga magana da ita hakan zai saka ta ji daÉ—i."

Safeera ta ce, "da ki ka je wajen ta ya ki ka same ta?."

"Umma tana lafiya lau, bata san zan je ba, ta so ta bani saƙo mai yawa na kawo mu ku. Amma ga wannan ta ce na kawo miki."

Safeera ta karɓi ledar alawa da yawa, gasu nan kala-kala masu kyau tun daga leda.. Islaha ta bata tsaraba ta ce, "Ga doguwar riga na siya miki."

Safeera ta karɓa tana murmushi ta ce, "Na gode sosai, hajiya Islaha mai capacity. Amma ba ki gama bani labarin ba."

Ta tattare kayan waje ɗaya ta ɗauki kayan gidan Mama sannan ta ce, "Ba yau ba. Zo ki raka ni gidan Mama, sauran kayan ki ajjiye min, duk wanda zan bawa zan karɓa." Safeera ta amsa, ta ɗauke kayan ta ajjiye a waje mai kyau, sannan ta saka hijjab suka fito zuwa gidan Mama.

A falo suka samu Mama a zaune ita da Hanan suna cin abinci. Islaha suka shigo da sallama ita da Safeera, suka amsa suna kallon su.

Hanan ta buÉ—e ido ta ce, "Islaha!."

Islaha ta É—an murmusa ta ce, "Na'am, Hanan."

Islaha ta kalli Mama ta ce, "Mama ina yini."

Mama ta sauke numfashi tana kallon ta ta ce, "da mu ka yi magana a waya mai na ce miki? Bana faÉ—a miki in kin dawo ki nemi wani gidan ba? Me ki ka zo yi min nan?."

Islaha ta É—an yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, tana tunanin shekanan kuma, ta dawo za a É—ora daga inda aka tsaya.

Mama ta ce, "kin je kin gama yawon ki, za ki ɗauko ƙafa ki zo min gida?. Kuɗin da za ki biya a shekars ɗaya, shi ki ka biya a wata biyu kacal, kuma ki samu na dawowa ƙasar nan. Kalli yadda ki ka koma, ai ana ganin ki an san ba iya abinci ne ya mayar dake haka ba, akwai wani abun a bayansa."

Islaha ta É—an runtse ido ta ce, "Mama ni ba yawo na yi ba, ban aikata komai ba, na samu dama ne shiyasa na dawo. Daman ba a son raina na tafi ba, abinda ya kaini shine ya dawo dani."

Mama ta zuba mata ido tana kallon ta, kafin ta ja ƙwafa ta ce, "to sai ki bar min gidana, ai ba da kuɗin ki aka gina gidan ba ko?."

Islaha bata ce komai ba, ta miƙawa Mama tsarabar da ta siyomata ita da Hanan ta ce, "Ga tsarabar Jeddah, babu yawa."

Hannan ta ja ledar tana buÉ—ewa ta ce, "Lallai Mama da gaskiyar ki, wanda ya je aikatau ina shi ina tsaraba? Gaskiya da walakin goro a miya."

Mama ta kalli kayan ta kalle ta ta ce, "bazan ƙi karɓar kaya ba, amma zama a gidan nan ne baza ki yi ba, ki je ki nemi wajen zama, amma ban da gidan nan."

"Wa nake gani kamar Islaha!."
Chapter 98 · 0% Book details