Sashe 2
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baffa ya ce, "Haba ke kuwa, me ki ke cewa haka? Dan ance za a kai sa asibiti a duba ƙwaƙwalwarsa hakan yana nufin mahaukaci ne?."
Daada da takaicin Umma ya mamaye mata zuciya ta ce, "to meye ma in ba mahaukacin ba? Ko ba a kira Salman kai tsaye da sunan mahaukaci ba, ace mai taɓin hankali. Duk wanda za yi abinda Salman yake yi ai mahaukaci ne lamba ɗaya."
Umma ta É—aure fuska tamau bata ce komai ba, tana ta girgiza kai tana hararar Daada.
Abba ya ce, "Rehaan ya ce zai kai sa asibiti a dubasa, dan haka zasu tafi tare dashi. In za ki je sai ku tafi gabaÉ—aya."
"Tsakani da Allah sau nawa ana kai shi asibitin, sau nawa ana kai shi a duba shi? Magana É—aya ce, ko yaushe cewa ake babu komai a tare dashi. Ni gaskiya ban amince ba, babu inda zai je."
Abba zai magana Daada ta katse shi ta ce, "kin hutar da shi, daman kuɗinsa ne ai ba kuɗin ki ko na mijin ki ba. Shi ya yi niya da ra'ayi, ya ga zai yi saboda zumunci, in ya yi ba kansa zai taimaka ba ɗanki da kanki zai taimaka. Tunda bakya so kin huta, sai ki je ki cigaba da saka shi a ɗaki kuna dambe in zai saka kaya. Wata ran azo a tarar ya karya miki hannu da ƙafa."
Umma ta miƙe tsaye ta ce, "Allah zai bashi lafiya, Allah ne ya ɗora masa kuma zai yaye masa. Kuma ni ɗana ba mahaukaci bane ba wallahi, ɗa ne kamar kowa, ɗane kamar wanda kowa yake ɗa a gidan nan, lalura ce ta wani lokaci kuma zai wuce."
"Yadda za a raba a bawa mai hankali haka za a raba a bashi kasonsa. Ban nemi kowa ya kai sa asibiti ba, a riƙe kuɗin na hutar da kowa, daman ban ce ina da buƙata ba. In niyar ya yi akwai mabuƙata da yawa a waje yaje ya yi musu, sunansa zai fi ɗaukaka akan ya yi min. Ta so mu je" ta faɗa tana ƙarasowa wajan Salman da yake kallon ta.
Salman da yake kusa da Rehaan ya ce, "Umma tare da Rehaan zan zauna."
Ta zare masa idamu ta ce, "dallah malam tashi ka wuce mu je, baza ka zauna dashi ɗin ba. Ƙanin uwar ka ne?."
Salman yaƙi tashi, zata sake magana Abba ya ce, "Salamatu ki bar falon nan."
Zata yi magana ya daka matsa tsawa ya ce, "ki fita nace ko!." Ta girgiza kai ta juya ta fita cikin fusata.
Mama ta kalli Abba da Daada ta ce, "Sai haƙuri. Bata kyauta ba kam, ina laifin wanda ya ce zai taimaki naka?."
Daada ta ce, "bar shashasha, ita ai komai akan kishi yake, neman lafiyar ma kishi take yi dashi. Mtsww! Zai a bar mata shi ta jiƙa a ruwa tasha, ita ta ga zata iya."
Mama ta ce, "Allah ya kyauta" ta faɗa taa miƙewa ta fita bata sake magana ba.
Abba ya kalli Rehaan da yake ta biyewa Salman da yake ta tsokanarsaya ce, "ka ji abinda babarsa ta ce, sai ka bar maganar kawai."
Baffa ya ce, "akan me zai barta? Daman ai ba dan ita zai yi ba, dan Allah zai yi da darajar zumunci, ai bai kamata ya dakata ba."
Daada ta ce, "tunda uwarsa bata so baza ta bari ba, ku ƙyale mata shi a yadda yake."
Salman ya miƙe ya fita Rehan ya bisa da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin tausayinsa yana sake ninkuwa a zuciyarsa. Bai ce komai ba ya miƙe ya fita daga falon ya koma ɓangarensa.
   Mama tana fita daga wajan Daada wajan Umma ta wuce, ta same ta tana cika tana batsewa, a zaune tana kaɗa ƙafa cikin ƙunci da takaicin abinda ya faru.
Mama ta ce, "ki yi daidai, kin yi daidai da ki ka nunawa wancan É—an jar fatan ke ki ke da iko da Salman ba shi ba, kin yi daidai da baki amince da kai sa asibiti ba. Ki ji wata magana, daman kallon mahaukaci yake yiwa Salman É—in ko me?."
Umma ta fusata ta ce, "Rehaan ya tsaya min a rai Mama, Rehaan yana neman ya tunzura ni na aikata abinda ban taɓa tunanin aikata masa ba. Na nemasa akan ya kai Salman asibiti ne?."
"Dan ya nuna miki yana da kuÉ—i mana, ai ya nuna miki yana da kuÉ—in da É—anki bashi dashi, tunda har zai iya kai shi Jedda a yi masa magani. Shine kawai."
"kuɗinsa ɗin banza da wofi, kuɗinsa bazai taɓa ɗaga min hankali ba wallahi. Salman kuma babu asibitin da za a kai shi wallahi. Tun da ba a ce za a kai sa ba sai yanzu?. Wallahi Abba ne yake goyawa Rehaan baya, ki duba tsawar da ya yi min a gabansa."
Mama ta ce, "Ke kin san Abba duk abinda Rehaan yake so shi yake so. Tunda kin murza kambu, kin nuna babu wanda ya isa da É—anki sai ke kaÉ—ai babu mai takura miki. Ya cika iyayi, shi lallai ga bature."
Umma ta ce, "Sai ga Riyya ta kira ni a waya, wai Umma account details ɗinki ne ban gani ba, Hamma Rehaan ne ya bani kuɗi in saka miki" ta faɗa tana kwaikwayon muryar Riyya tana taɓe baki. Ta yi tsaki ta ce, "Su lallai sai sun zama lamba ɗaya a gidan nan."
"Ni ta tura min, na ga kuÉ—i masu yawa sai na kira ta, shine ta ce wai na shopping ne in ji Rehaan. Ko godiya ban yi ba na kashe wayar."
Umma ta yi tsaki ta ce, "Lokacin sa ne, ya yi gama, zai dawo tafin hannunmu wallahi."
"Nan da lokaci kaÉ—an kuwa. Ke dai kar ki yarda da batun asibitin nan wallahi, ke aka aurowa Nadira ba ni ba, kina yarda aka fita dashi ta yi nasara a kan ki."
"Ai wallahi ko Abba bazai saka na yarda ba, tunda na ce bana so a ƙyale ni, ni nake kula dashi ai ba wani ba." Mama ta ce, "gaskiya ne wannan, babu me zuwa inda yake sai ke ɗin. Bara na je na dawo" ta faɗa tana fita daga apartment ɗin ta bar Umma tana mita. Mama kuwa ta yi murmushi, ta ya zata bari a yiwa Salman magani? Ta ya zata bari Salman ya samu lafiya?. In ya samu lafiya an ƙaru kenan fa, zai shiga cikin masu riƙe da dukiyar mahaifinsu, ita kuma bata so ƴaƴanta kaɗai.
Rehaan ko da ya gama shiryawa Shams da Mansur ya kira a waya, duk da shi kaÉ—ai yake son fita amma Mamy ta ce kar ya fita shi kaÉ—ai shiyasa ya kira su. Mota ya shiga suka tafi gidan Mummy kamar yadda ya ce mata zai je.
Da sallama ya shiga falon, suka amsa suna kallonsa. Mummy cikin da farin ciki ta ce, "La la la Rehaan! Yau kai ne a gidan na mu? ." Ya yi murmushi yana ƙarasawa ciki.
Ambatar Rehaan da aka yi, ya saka wata kyakykyawar budurwa mate É—in Riyya yin tsalle ta fito daga kitchen, suna haÉ—a ido dashi ya sakar mata murmushi mai taushi, dan kallon Riyya yake yiwa Ikram ko yaushe, ta yi ihuuu ta nufesa a guje ta rungume shi tana murnar ganinsa.
Ƙiris ya rage ta kayar dashi, yadda ta ɗafe jikinsa ya saka ya yi baya zai faɗi, sai da ya yi da gaske ya tsaya ya riƙe ta ya ce, "Ikram."
Mumny ta ce, "Za ki yar dashi, kin san bashi da lafiya."
Ikram ta sake shi ta riƙe hannunsa ta ce, "My favorite bro, ya jikinka?. Da na je asibiti baka yi min magana sosai ba, har na yi tafiya na je Abuja." Tare suke tafiya tana riƙe da hannunsa har suka zauna, ta zauna a kusa dashi tana ji kamar ta shige jikinsa saboda ƙauna.
Ya bi fuskar ta da kallo yana É—an lumshe ido ya ce, "Me ake yi a Abuja?."
"Biki na je."
Ya ja hancinta ya ce, "Sarkin biki."
Mummy da take murmushi ta ce, "Sai kun gama gaisawa zamu gaisa?." Ya É—an yi dariya kaÉ—an, a lokacin Daddy ya shigo ya ce, "Ahh Rehaan, daga samun lafiya sai yawo?." Ya yi murmushi suka gaisa har Daady. Daddy ya ce, "Ya jikin?."
"Na ji sauƙi sosai."
"Allah ya ƙara lafiya, ya kiyaye gaba."
"Amin Daddy."
A lokacin ƙannen Jafar suka shigo suka gaisa suka zauna Daddy kuma ya fita.
Mummy ta ce, "gashi ka zo Jafar yana Uk."
"Wajen Mummy nazo ba wajensa ba."
Ta yi dariya ta ce, "Na gode sosai Rehaan. Ikram kawo masa abinci ya ci."
Bai musa akan kar a kawo ba, daman bai ci komai a wajen Mamy ba, Mummy kuma kamar Mamy take a wajensa.
Ikram ta miƙe ta ciko masa tray da kayan abinci ta kawo masa. Da kanta ta yi serving ɗinsa ta miƙa masa ya karɓa ya ce, "Thank you."
Mummy ta ce, "Jafar ya ce min zaka tafi Jeddah."
Ya É—aga kai ya ce, "ina da contract, zan je in gama sai na dawo."
"Allah ya taimaka Rehaan, Allah ya cigaba da kare ka."
"Amin Mummy."
"Riyya ta saka mana kuÉ—i ta ce na shopping ne, mun gode Rehaan, Allah ya albarkaci rayuwarka."
"Amin" ya amsa softly yana shan ruwa.
Sama sama suke hira da Mummy da Ikram, har ya gama ci, ya ɗan zauna kaɗan sai ya miƙe ya ce, "Mummy zan tafi."
Mummy ta ce, "To Rehaan, a gaishe da Mamy." Ya amsa suka fita shi da Ikram suna hira.
Har mota ta raka shi, tana riƙe da hannunsa ta ƙi saki kamar zai gudu. Ya ɗan kalle ta ya ce, "Ikram, ya school?."
Ta yi murmushi ta ce, "Alhamdu lillah."
"Allah ya taimaka. Ki koma gida, zan tafi."
Cikin shagwaɓa ta ce, "Ni bana so ka tafi, zan zo mu tafi Jedda."
Ya É—an murmusa ya ce, "sai kin zo Ikram" ya faÉ—a yana sakin hannunta. Har zai shiga mota Ikram ta ce, "Hamma Ray."
Ya juyo yana kallon ta kamar yadda take kallonsa, sai ƙifta idanu take yi tana kallonsa ta ce, "I love you."