← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 133

Sashe 69

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ina cikin damuwa ne Adda Safeera, an takura min akan dole sai na je wani gida wai na yi aiki, gabaÉ—aya ban yarda da matar ba, gani nake kamar akwai wata manufar da ake so a tura ni. Mama tana faÉ—a min zan samu kuÉ—i, zan samu abubuwan mure rayuwa a can. Ni na ga ji, komai sake lalalcewa yake yi. Ina jin tsoron kar a kaini inda za a lalata ni, gabaÉ—aya zuciya ta bata amincewa da gidan."

Safeera ta yi shiru kafin ta ce, "kun taɓa magana da Islaha akan haka?."

"Mun yi, har take faÉ—a in ance na je gidan na amince na je, sai na yi mata waya. Kinga yanzu bata nan, shiyasa hankalina bai kwanta da na je É—in ba."

Safeera ta girgiza kai ta ce, "Bata ce ki yi magana da Barr Suraj ba?."

"Bata ce ba. Amma na yi recording maganar mu da Mama ta yau, zan tura miki sai ki tura mata. Ni bana samun ta a waya."

"Eh ta whatsapp za ki dinga kiran ta, za ki same ta."

Zainab ta ce, "akwai masu saka min ido sosai, gwara na tura miki sai ki tura mata zai fi."

Safeera ta ce, "shikenan turo min, nima in kim turo sai ki yi delete for me saboda gudun kuskure."

Zainab ta tura mata a lokacin, sannan ta ce, "don Allah ki faÉ—a mata ta dawo, itace garkuwa a gare ni."

Safeera ta ce, "Itama ke ce a ranta, ko yaushe cikin maganar ki take, na tabbatar zata dawo ke dan ke Zainab. Ki cigaba da yi mata addu'a, Allah ya bata abinda ta je nema."

"Amin Adda Safeera, ki gaishe ta."

"Safeera ta É—aga kai daga nan Zainab ta yi mata sallama ta tafi.

Safeera ta yi ajiyar zuciya, sai yanzu take sake tabbatar da zargin Islaha gaskiya ne, amma a cikin waÉ—anda suke zagaye da Islaha akwai munafakin su Maman, waye ko wace shine basu sani ba.

        ••••••

"Kar ki ce min komai Alma, na ba ki yarda da amana amma kin kasa yin komai. Na jima ina biyan ki kuÉ—i amma kin kasa yi min abinda nake so. Daga yau na yi canceling duk wani abu da yake tsakanina dake, bazan sake ba ki aiki akan Ray ba."

Alma murya tana rawa ta ce, "i try my best, wata housemaid ce ta ce ta kira min ƴam sanda, shiyasa na dawo amma ba wai dan ina son haka ba. Ka sake bani dama ta ƙarshe."

"Lokacin ki ya ƙare, ki goge number ta, ki goge duk maganar da muka yi dake."

Jin ya kashe wayar hankalin Alma ya tashi, ba ƙaramin kuɗi take samu da mutumin nan ba, yanzu da ya daina bata aiki ta shiga uku.

A bayyane ta ce, "this housemaid! Sai na yi maganinta, sai na kashe ta, sai na tabbatar na yi mata abinda ba a taɓa yi mata irinsa ba."

Ta girgiza kai ta ce, "zan koya mata darasi mai yawa, zan tabbatar mata da ni ba sa'ar wasan ta ba ce!. Zan yi mata abinda baza ta manta dani ba, zan yi mata abinda zata dinga tuna wacece Alma."

•••••••

Rehaan bai farka ba sai azahar, ya miƙe zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi mai girma, ya jima a haka a zaune sannan ya kalli agogo.

Ganin lokaci sai ya tafi tunani, ƙarfe ɗaya na dare ko kuma ɗaya na rana shi bai gane ba. Sai da ya huta sosai, dan kansa ya yi nauyin da in ya miƙe zai iya faɗuwa, sai da ya jira kan ya saki sannan ya miƙe ya ɗaga labuble ya ga rana ce sosai.

Ya firgita harda zaro ido waje, ya rufe bakinsa da hannayensa ya ce, "What! 1pm" ya faÉ—a yana juyowa yana kallon É—akin.

Lokacin da Alma ta shigo ya ce ta fita yake tunawa, sai ya tuna lokacin yamma ce ko sallar magrib ba a yi ba, ya tuna ta zuba masa powder a fuska daga nan bai sake buɗe ido ba, sai yanzu da ya buɗe ƙarfe ɗaya na rana.

Gabansa ya yanke ya faÉ—i, tsoro da tashin hankali ya ziyarce sa, ya bi jikinsa da kallo ya ga yadda ya ke a jiyan haka yake a yanzu, babu alamun an yi undressing É—insa.

Ya dafe kai yana so ya tuna abinda ya faru amma ya kasa, da hanzari ya motsa sai ya tsaya saboda yadda kansa ya yi nauyi haka jikinsa. Ya ƙarasa a hankali ya fito falon, falon shiru ko haske babu, ya shiga ɗakin da ya ke tunani a nan Alma ta zauna amma bata nan babu ko jakar ɗinta.

"Oh my god!"

Ya furta yana fita daga É—akin, zai sauka dan down stairs ya ji kiran sallah. Da hanzari ya dawo tunawa da sallolin da suke kansa.

Ya shiga banÉ—aki da hanzari, har zai yi alwala sai ya ja ya tsaya, ya buÉ—e ido yana kallon kansa cikin tunani. Bai san me Alma ta yi masa ba, bai san me ya faru a tsakaninsu ba, san ya tunda ya yi losing control Alma zata yi iya masa komai, dama kaÉ—an take nema ta far masa, burinta a duniya bai wuce ta same sa ba, kuma ya san zata aikata komai dan hakan.

Yanzu kenan sai ya yi prepacatuon bath for that? Ya dafe kai dan ya sama confuse and lost, ban san me ya kamata ya yi ba.

Saboda kokwanto haka ya yi wankan ya yi alwala, sai da ya yi drying kansa sannan ya fito ya yi sallolin da suke kansa. Sallar ma ba a nutse ya yi ta ba saboda tunani, ƙirjinsa bugawa yake yi ba tare da ya san dalili ba. Haka kawai yake jin kansa ya zama so corwing, fargaba ta mamaye sa sosai, ya rasa me yake damun zuciyarsa, a cushe take saboda bai san abinda aka yi masa ba.

Allah ya taimake sa ya koma night duty, da bai san ya zai yi da ranar nan da ya yi skiping without reason ba.

Walkin slowly ya fito falo, ya zauna ya dafe kai cikin damuwar da bai san daga ina take ba. Ya kira wayar Alma amma baya samun ta, ya dafe kansa ya yi shiru bai san me yake damunsa ba.

A lokacin Islaha ta shigo falon, ta gansa shiru babu haske kamar ko yaushe. Kallon upstairs É—in ta yi tana tunanin ko yana nan ko baya nan bata sani ba.

Kitchen ɗin ta shiga yana nan kamar ko yaushe babu komai a cikinsa, ta dafa tea ɗin ta buɗe fridge ta ɗauki apple ta yi slicing ta a ƙaramin plate.

Sai kuma ta ce, "shi ba ya cin abinci ne sai tea? Bai damu da a bashi abinci ba sai dai ya sha tea kawai?." Ta taɓe baki irin ina ruwan nan ɗin nan, sai ta yi tunanin jiya ta bar cup a sama, ta bar kayan a wajan dan bata ɗauka yana nan ba ta hau sama.

Sai da ta je ƙarshe sannan ta ji maganar sa, dan a hankali yake magana sai da matso sosai sannan ta ji ya ce, "Ban sani ba, abinda na sani ta zuba min powder, daga nan ban san me ya faru ba. Ina jin tsoro, ban san me ta yi min ba."

Tana jin magana daga waya ya ce, "Yarinyar nan bata da mutunci amma, kuma da ka tashi ba ga alamun an yi undressing É—in ka ba?."

"Ban ga komai ba, ni dai Im afaird Jafaar" ya furta a sanyaye yana lumshe ido.

"Ni abinda nake tsoro kar mu je ta yi snapping nude É—in ka."

"Wannan shine abinda nake jin tsoro nima, ban san me zan yi yanzu ba, kaina ya kulle, na sama confuse and lost, ina jin kaina uncomfortable, kamar dai wani abu ya faru dani."

"Kuma babu cctv a bedrom balle a ce ayi checking, amma akwai a falon ko?."

"Kamar babu cameras a gidan nan."

"Oh god!."

"Help me please!."

Jazy ya ce, "calm down, zamu san abinda ya kamata a yi in sha Allah."

Ya girgiza kai ya ce, "Alma baza ta yi powdering É—ina ta bar ni ba, She knocked me out, I'm sure she did something bad to me. Ni saboda confusing sai da na yi perupacating bath sannan na yi sallah. Na rasa tunanina, na rasa me ya kamata na yi na ji daÉ—i."

Jazy ya ɗan yi dariya ya ce, "Da yake haka abin yake da sauƙi daman, da ace wani abun ya faru a tsakanin ku za ka ga alama ko ya ya take. Abinda nake tunanin ta yi maka hoto ko video, amma ni bana tunanin wani abun ya faru a tsakanin ka da ita." Rehaan ya yi ajiyar zuciya bai ce komai ba cikin damuwa.

Islaha da take tsaye sai take ji kamar ta faɗa masa gaskiyar abinda ya faru, yadda yake magana a sanyaye sai ya ɗan bata tausayi kaɗan, a haka ta ƙarasa ta yi sallama, ya juyo ya kalle ta ya amsa.

Kamar zata yi magana sai ta fasa, maimakon ta yi abinda ta yi niya sai ta juya zata koma ƙasa.

Camly ya ce, "Wait!."

Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, bai damu dan bata juyo ba ba ya ce, "have you ever seen Alma? Jiya ko yau baki ganta ba?."

A hankali ta waiwayo suka haÉ—a ido ta ce, "i did not."

Ya gyaÉ—a kai bai ce komai ba, ita kuma ta sauka bata sake magana ba. Sai ya bata tausayi sosai, yadda ya zama confuse ya saka ta ji kamar ta faÉ—a masa, amma sai ta share tana tuna shine ya sace ta baza ta faÉ—a masa ba.

Tana komawa suka yi magana da Safeera akan zuwan Zainab. Hankalinta ya tashi musamman da ta ji recording É—in.

Har zata kira Brr Suraj sai ta fasa, tana tuna yadda aka goge hotuna a wayarta kwanakin baya, baza ta faÉ—a masa ba kar hakan ya kuma faruwa.

Bata tsaya shawara ba ta kira shi ta whatsapp ya É—auka, yana É—auka ya ce, "Hajiya Islaha."

Ta yi Æ´ar dariya ta ce, "Hamma Suraj ya aiki?."
Chapter 69 · 0% Book details