Sashe 41
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ga watsu mata su biyu sanye da abaya baƙa, ta rufe fuskarsu da niƙab kamar yadda suka saba ganin larabawa.
Suna ƙarasowa inda suke suka ɗaga niƙab ɗin, duk suka bita da kallon ganin hausawa ne ce kamar su, sai dai sun sha bleaching har wani yellow suke yi, kuma kana ganin su ka ga waɗanda ta waye a harkar zaman Saudia.
ÆŠaya ta bisu da kallo tana tauna chewing gum su ta ce, "Sannun ku da zuwa." Suka amsa kafin ta kalli mutumin suka canja yare zuwa larabci suna gama.
Sun jima suna magana kafin ya kalli Islaha da Labiba ya ce, "Ku zamu tafi tare daku, gidan da zaku zauna a nan gari yake ba sai an je Makka ko Madina ba. Amma Hajiya ke a Madina gidan aikin ki yake, zaku tafi da wannan zata kai ki har gidan da zaki yi aikin."
Duk da tunda suka taho Umma bata cewa Islaha komai ba amma sai jikinta Islaha ya yi sanyi, ta kalle sa ta ce, "me zai hana itama baza a barta a nan ba? nafi so a haɗa mu waje ɗaya tare."
Oga Musa kalli Islaha ya ce, "Ya sunan ki ma?."
"Islaha."
"Islaha gidajen aikin da aka samu a nan Jeddah gida biyu, kuma kamar ku ake buƙata ba mai shekarun ta ba. Inda zata je a Madina shine daidai ita, kuma gida ne da zata ji daɗinsa sosai."
Islaha ta kalli Umma da bata ce komai ba, matar tayi dariya ta ce, "Kar ki damu Islaha, duk zaku saba fa. Da kun saba dan ki ɗauki ƙafa daga Jeddah kin je Madina abu ne mai sauƙi. Kawai dai duk inda zaku je ku dinga tafiya da passport ɗinku kafin visa ta ƙare. Visa shekara ɗaya aka yi muku, zaku jima kuma zaman yanci a ƙasar nan."
"Abinda zan ja hankalin ku a akai shine, Ku ku ji sata, babu ruwansu da ba yan ƙasa bane sai an yanke muku hukunci wallahi. Ku guji abubuwa saɓawa doka, wallahi ku ka aikata a gidan yari zaku ƙare rayuwar ku, in hukuncin kisa ne ya hau kan ki kashe ku zasu yi wallahi. Gidan da za a kai ku manyan gidaje ne, sai kun yi taka tsantsan."
Suka amsa cikin gamsuwa da bayanan su.Labiba cikin iyayi ta ce, "in Allah ya yarda zamu yi komai yadda ya kamata."
Matar ta kalle ta ta ce, "da alama baza ki bamu kunya ba, na gan ki a waye kamar kin taɓa zuwa."
Labiba ta yi farr da ido jin an yabe ta, tana ta murmushi cikin jin daÉ—i.
ÆŠayar da suke tare ta ce, "Ku mu je safiya yana yi, mu da zamu É—auki hanya ma mune abin ji."
A hankali suka fara tafiya, suka iso bakin titin airport ɗin. Hajiyar ta kalle su bayan ta tsayar da mota ta ce, Mu mun wuce Madina sai kun ƙaraso."
Ta kalli Umma ta ce, "Hajiya muje."
Islaha ta kalli Umma, itama ta kalle ta Islaha ta ce, "Allah ya kiyaye Umma."
Umma ta ce, "amin." Daga haka Umma da Hajiyar suka shiga mota suka É—auki hanyar Madina.
Oga Musa suka gama magana da ɗaya matar ta tafi, shi kuma kalle su ya ce, "yanzu zamu wuce gidanjen da zamu je. Labiba da Islaha, ina sake jan kunnen ku ban da ƙazanta, ban da sata, ban da gulma." Ya faɗa yana tsayar da moyar ya faɗawa driver inda zai kai su.
Bayan sun gama ciniki, aka saka kayansu a booth, ya shiga gaba Islaha da Labiba suka shiga baya suka fara tafiya.
Duk safiya ce ko ina cike yake da haske da mutane, Islaha tunda ta kalli titi sau É—aya bata sake kallon titi ba ta sunkuyar da kai tana ji ana tafiya amma ta kasa É—ago kanta.
Tana kallom Labiba tana ta hotuna, ita kuwa ba ta wannan take ba, yanayinta gabaÉ—aya babu daÉ—i tana ji kamar zuwan bazai zama alkhairi ba.
Sai da motar su ta tsaya sannan Islaha ta É—ago a hankali tana kallon estate É—in da suke a tsaye. Ki ina na unguwar tas, gashi shiru babu alamun mutane, ga sanyi unguwar kasancewar ta a kusa da teku. Motoci kaÉ—an-kaÉ—an ne suke wucewa, ko ina ya yi tas dashi kamar kar ka daina kallo.
Oga Musa ya nuna musu gidajen ya ce, "waÉ—anan sune gidan da zaku yi aiki. Ya sunan ki ma?."
Ya faÉ—a yana kallon Labiba da ta saki bakin da hanci tana kallon gidan da ya nuna zasu shiga kamar wanda take gani a film.
Ganin bata ji ba sai ya sake cewa, "ke dake nake fa."
Labiba ta yi sauri ta ce, "Labiba sunana. Wannan gidan na tsakiya shi zamu shiga? Na gan shi mai kyau, har yafi waÉ—annan kyau."
Oga Musa bita da kallon sama da ƙasa, dan ya lura tana da rawar kai sai ya ja mata kunne ya yi mata gargaɗi zata shiga hankalinta. Ya ɗaure fuska ya ce, "ki adana wannan rawar kan na ki, ki nutsu ki san abinda ki ke yi. Wallahi ki ka aikata wani abun ba daidai ba kama ki zasu yi. Nan saudia ce, in hukuncin kisa ne ya hau kan ki kashe ki zasu yi, ba cin hanci ake basu ba balle su sake ki. Ki kula da tsarikan gidajen, zasu faɗa miki tsarikansu, kuma dole ki bi, in ba haka ba kece a ruwa."
Labiba sai ta É—an nutsu ta kalle sa ta ce, "zan kiyaye in sha Allah."
Ya ce, "ku fito." Duk suka fito aka fito da kayansu.
Ya kalli Islaha da take kallon gidajen da suka tsaya a wajen ya ce, "ki jira mu a nan, bara na fara shigar da ita na dawo na shiga dake."
Islaha ta ce, "kuma ba matsala in na tsaya a nan? Kar su kama ni."
"Kar ki damu, babu damuwa."
Ya kalli Labiba ya ce, "mu je." Ta ja jakarta suka shiga gidan da yake ɓangaren dama.
Tunda suka shiga take kallon gidan cikin burgewa, dan gidan ya tsaru, ya haɗu irin su take kallo a turkish drama, bata taɓa zaton zata shiga cikinsa ba sai gata a ciki.
Lokacin da suka shiga falon numfashinta sai da ya kusa ɗaukewa dan bata taɓa ganin gida mai kyaunsa ba, komai ya tsaru irin tsarin larabawa.
A falon baƙi suka zauna har lokacin Labiba kalle-kalle take yi cikin burgewa.
Ba su jima ba Ubaid ya fito sanye cikin ƙananun kaya yana amsa waya, suna ganinsa suka miƙe tsaye har ya ƙaraso ya zauna sannan suka zauna suma.
Bai jima yana wayar ba ya kashe, suka gaisa dashi ya nuna Labiba ya ce, "Gata nan, itace wacce aka kawo daga nigeria."
Ya bi Labiba da kallo da take murmushi, ya kalle ta cikin turanci ya ce, "What is your name?."
Labiba ta ce, "Labiba."
"daga wani gari?."
"Adamawa, Nigeria."
Ya É—aga kai yana binta da mayen kallo ya ce, "Albashin ki Riyal dubu É—aya ne duk wata kin yarda?."
Labiba ta ce, "na yarda."
"Good" ya kalli Oga musa ya ce, "Ina takardar ta?." Oga musa ya ɗauko takardar gwajin jinin da Mama ta bashi, ya ɗauko ta Labiba ya bashi ya karɓa yana dubawa.
Ya É—aga kai ya kalle ta ya ce, "Za a raka ki inda zaki zauna, gobe zaki fara aiki."
Cikin murmushi ta ce, "na gode."
Ba jimawa sai ga wata mata ta fito sanye da uniform, farar riga da baƙin siket, sai kanta da ta rufe da baƙin mayafi.
Ubaid ya nuna mata Labiba ya ce, "New housemaid."
Jikin matar har rawa yake yi ta buɗe wata drawer ta ɗaukowa Labiba wata tarkada ta miƙa mata da biro. Oga Musa ya kalli Labiba ya ce, "Ki karanta ki saka hannu."
Ita sai ta ji tsoro ganin yadda matar take rawar jiki, dan bata san me yake saka ta rawar jikin ba. Labiba ta saka hannu ba tare da ta karanta ba.
Tana saka hannun ya yi alama da takai Labiba É—aki, ta taimaka mata aka shiga da jakarta É—aki.
Ubaid ya miƙe tsaye ya yiwa Oga Musa kyauta sannan ya fita ya ce, "in tayi zan kira ka na faɗa maka, in an samu matsala zan faɗa maka. Ina fatan ka faɗa mata tsarikan mu?."
"Ta sani."
"Ya yi kyau" ya faÉ—a tana shiga ciki shi kuma ya koma wajen Islaha.
Yana fita ya samu Islaha a tsaye a inda ya bar ta, ya kalle ta ya ce, "naga ke kina da nutsuwa sosai, kuma baki da hayaniya irin Labiba, in ki ka mayar da hankali zaki samu alkhairi sosai. Suna son mace mai nutsuwa da zafin nama, da ance a yi kawai ayi kar a ɓata lokaci. Ki kula da komai yadda ya kamata, kar ki bari a aikin farko su gano kuskure kin ji?."
Islaha ta É—aga kai ta ce, "In sha Allah."
"Muje na kai ki gidan."
Haka kawai gaban Islaha ya faÉ—i, ta kalli gidan da yake tsakiya wanda taga sun tunkara, gidan babba ne sosai, gashi da kyau duk adon glass ake hangowa tun daga waje.
Ta kalli gefen gate É—in ta ga house number, daga gefe kuma an rubuta DR REHAAN da wani irin front mai kyau da É—aukar hankali. Ta yi ajiyar zuciya, ta ga Oga Musa yana niyar buÉ—e gate É—in, dan ta kula kamar su babu mai gadi, kawai buÉ—ewa ake a shiga, taga haka ya yi a gidan da aka shiga da Labiba.
Ta yi ajiyar zuciya, ta bishi da kallo gabanta yana faÉ—uwa sosai......
Nana HaleemaâœðŸ»â¤ï¸
[7/1, 1:07 PM] KRBBK: RDB2P29
Nana Haleema.
Oga Musa ya dawo da baya yana sake kallon Islaha ya ce, "ba wannan gate É—in bane, wancan ne."
Ita dai bata ce komai ba, ta kalli gate É—in tana mamakin kyaun gate É—in kamar da gold aka tsara sa, har fuskar ka kana iya gani a jiki kamar madubi, sai dai shi gold ne har É—aukar ido yake yi.
Islaha ta bi bayansa suka shiga gidan tana tafiya slowly kamar bata son shiga ciki.