← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 133

Sashe 127

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gidansu Ray shagali bikin kawai ake yi, masu henna ma daga india suka zo aka yiwa amarya da ƙawayenta ds iyayen amarya. A ranar suke yin indian night kamar yadda suka saka shi a cikin jerin event ɗin da zasu gabatar.

Ango da amarya sun sha kwalliya a cikin kayan india, kowa ya kalli Riyya ya san jininsu ce, shima Jay da yake yana da haske da kyau sai ya zama kamar É—an india É—in. Kowa in ya kalle su sai ya sake kallo saboda kyau, ita kanta Mamy É—in shigar india ta yi, kowa na wajan shigar india ya yi dan kyauta aka raba kayan.

Mama da Umma ne suka ce baza su saka ba, sai suka saka lafaya kawai amma basu naÉ—a sari kamar sauran mutane ba. Rehaan ma kayan india ya saka, irin rigar nan tasu mai É—an tsaho har guiwa.

Yana zaune a kame a wajan, har ya fi amarya da angon farin jini dan shi kaɗai ake haskawa. Cikin lokaci kaɗan hotuna da video suka zaga duniya, ana ta yaba kyau da tsarin bikin dan ya ƙayatar sosai.

Umma da Mama sai taɓe baki suke yi, suna ganin yadda ake ɓarin kuɗi a wajan dan dukkansu da kuɗin india suke liƙi ba naira ba.

Lokacin da Riyya ta je ta riƙo hannun Yayanta ya shigo kan stage wajan ya ɗauki ihu, iya Mamy ne dasu a kan stage ɗin sai Jazy da ya zama ɗan family Mmay shima.

Gently Mamy take taka rawar india, shi dai yana tsaye yana murmushi yana riƙe da hannun Banisha da take kusa dashi. Sai daga baya ya fara yiwa Mamy liƙi da kuɗin da bai san adadinsu ba, Mamy ta ruungume su aka yi musu hoto.

Daga nan aka kira mawaƙin daga gayyata tun daga ƙasar india har nigeria. Mawaƙin da india take ji dashi, mawaƙin da india suke mararinsa, mawaƙin da bollywood take ji dashi, mawaƙin da mu kan mu ƴan nigeria waƙoƙinsa suke burge, wato arijit sight. Aka chase aka raba abubuwa masu yawa, sai ƙarfe ɗaya na dare aka tashi kowa ya tafi.

Mama da Umma suna zaune basu tashi ba, duk da sun gaji amma sun ƙi tafiya, amma saboda gulma suna zaune sai sun ga ƙarshen abin.

Mama ta ce, "Abu babu tsari, wai indian night. An cuci ahlimu da aka É—auko mana wannan."

Umma ta ce, "ni ba wannan ba, wai ina matar Rehaan É—in ne? Ita meyasa ba a yi bikin da ita ba?."

Mama ta ce, "ƙyale jinin matsafa, kin san da yake ba son auren yake yi ba, bazai bari ayi biki dashi ba. Ni kuma wallahi sai na tabbatar da auren nan saboda cikar burina."

Umma ta ce, "Haushin yaron nan nake ji, da ace mutuwa a hannuna take da yanzu na kashe shi kowa ya huta. Komai ace Rehaan, komai shi? Yaran mu sun zama koma baya, ba a yin komai dasu sai shi?. In ki ka ɗauki waya ki ka duba kafafen yaɗa labarai, gabaɗaya akansa ake magana yau. Shirme!" Ta faɗa tana miƙewa ta fita.

Mama ta bita da kallo tana murmushi ta girgiza kai ta ce, "duk yadda zan yi na mallake yarinyar nan ta zama yar ɗakina sai na yi, ba a banza na tsaya kai da fata a aurota ba, ina da shiri na musamaman akan hakan. Zan riƙe ta da kyau, zan jawo ta a jiki, zan nuna mata ƙauna, yadda duk abinda na ce tayi akan Rehaan zata yi, duk wani sirrinsa zai zama yana tafin hannuna."

Ta sake yin dariya ta ce, "Mu je zuwa, yanzu ne za a fara kafcen, da ba a yi komai ba."

Washe gari.

Saheer tunda ya ji labarin za a kawo kuÉ—in fansarsa sai jikinsa ya yi sanyi, duk sai ya damu yana tunanin in ya tafi wa zai bar wa amanar sa Sudais ya bar masa? Kuma Allah ya sani ba ya so su Black su yi nasara akanta, ba ya so wani abu ya shiga tsakaninta da mai garkuwa da mutane da sunan mijinta. Duk da mijinta ne na aure, an É—aura aure da sadaki da shaidu, amma rashin mafita ce ta saka aka amince dashi.

Kwana biyu ta É—an sa ki jiki, duk bata magana har lokacin amma in suka bashi abinci suka ya bata tana ci kaÉ—an, kuma shi kaÉ—ai ne yake yi mata magana ta ji. GabaÉ—aya sai ya ji ya damu, ba dan ba ya son komawa gida ba, sai dan bai san ya rayuwarta zata kasance a wajen ba.

Ƙarar machine ɗin Arɗo da ya ji ya saka shi ya ɗago ya kalli Arɗo da ya sauka daga kan machine ɗin, ya zauna a inda ya saba zama yana kallon su ɗaya bayan ɗaya ya ce, "Ban kawo ku nan na ajjiye ku ba, ban kawo ku nan dan mata su dinga dafa mu ku abinci kuna ci ba. Duk wanda ƴan uwansu baza su kawo kuɗi ba za mu daina ganin ku, ƴan uwanku kamar ba sa son ku."

Kowa ya yi shiru babu wanda yake magana, ya kalli Saheer ya ce, "Kai yau mu ka yi zasu kawo kuÉ—in ka, ga shi akwai inda zan je na dawo. Sai dai in sun kawo su tafi, ka bi bayansu daga baya."

Saheer dai ba shi da bakin magana, wannan kashe kashe da yake yi kamar suna kashe sauro bazai bar ka ka yi magana ba. A take ya saka aka fito da mazan ciki, suka yi musu dukan tsiya aka yi video aka turawa Æ´an uwa, shi kuma ya tashi ya fita.

Kamar yadda Sadik ya shirya haka shirya kuÉ—i ya ta fi dajin da kwantance da suka dinga yi masa, su da kansu suka faÉ—a masa inda zai tsaya, ya je wajen ya tsaya, suka ce masa zai ga mai jar riga kawai ya bi bayansa, haka aka yi yana ganin mai jar riga ya bi sa, daga nan aka hau machine aka tafi sansaninsu.

Islaha da Safeera ne kaÉ—ai suka san an tafi kai kuÉ—i, ko su Baffa basu san me yake faruwa ba, ba a so su sani saboda kar su tambayi a ina aka samo kuÉ—in.

Islaha tunda Sadik ya tafi gabaɗaya bata da nutsuwa, duk ta ruɗe saboda tashin hankali har rama ta yi, tunda Sadik ya tafi bata iya zama ba kai kawo take yi. In ta gaji ta huta ta kuma miƙewa tana cigaba da tunani.

A ranar gidan su Rehaan a ranar aka haɗawa Riyya grand kamu, babu yadda Jafar bai yi da Rehaan ba amma ya ƙi zuwa.

An shirya kamu a babban ɗakin taron da ake ji dashi a garin Yola, an kashe kuɗi masu nauyi, anyi harkar gold, social media ta san ana bikin ƙanwar Rehaan Yola. Amarya ta yi kyau, ta samu gift ma su yawa marasa adadi.

Gidan su Rehaan suna can suna shagali, islaha kuma tana tunani, har dare babu Sadik babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, ko abinci ranar bata ci ba, gani take kamar Sadik É—in bazai dawo ba.

Nana Haleema.
[7/30, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P96
Nana Haleema.

Sai sha É—aya na dare sannan ta ga Sadik yana yi mata waya, ai ko hijjab bata tsaya sakawa ba ta fita a guje ta gansa a harabar gidan a tsaye.

Ta tsaya tana kallonsa ganinsa shi kaɗai, shima ya gaji kuma wahala ta bayyana a tare dashi sosai. Ta ƙaraso ta ce, "Hamma Sadik ya ake ciki, Ina Hamman nawa?."

Sadik ya kalle ta kamar yadda take kallonsa, ita kuma gani ta yi duk ya firgice, ruɗewa da tsoro sun bayyana ƙarara akan fuskarsa. Sadik Ya ce, "sun ce sai gobe ko jibi za su sako shi."

"Kamar ya? Daman in aka ba da kuÉ—i ba ranar mutum yake dawowa ba?."

"Ban sani ba Islaha, ban taɓa zuwa inda suke ba sai yanzu. Daji ne Islaha, ban taɓa shiga daji ba sai yau, wajen kamar ba a duniya yake ba."

"Ka ga Hamma Saheer?."

Ya É—aga kai ya ce, "na gan shi."

Hawaye ya sakko daga idonta, ta saka hannu ta rufe bakinta ta ce, "basu kashe sa ba?."

Ya É—aga mata kai yana murmushi ya ce, "yana nan da rai, kuma zai zo ya ganki. Wai shugaban nasu ne ba ya nan, shiyasa baza a ba da shi ba. Duk yawan kuÉ—in nan sai da na irgasu, a haka ma ban gama ba kawai na ce musu na gama ne."

Islaha ta zube a wajan ta yi sujjud shukur tana farin ciki da murnar Hamma yana da rai, sai ta miƙe ta ce, "Yanzu sai gobe ko jibi?."

Ya ɗaga kai ta dafe kai ta ce, "meyasa basu ƙyalesa yau ba? Kar su karɓi kuɗi su hana mu shi."

"Za su bayar in sha Allah."

"Ya Hamma yake, Ya rame ko?."

Sadik ya yi murmushi yana kallonta ya ce, "Samun mace mai ƙaunar mutum tsakani da Allah kamar ki za a jima, ƙarnin irin ku ya jima da ƙarewa, waɗanda suke saka rayuwarsu a hatsari saboda wanɗanda suke so ya jima da shuɗewa. Har abada Saheer bazai samu wacce take sonsa kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu masoyiya kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu mai ƙaunarsa da zuciya ɗaya kamar ke ba. Na jinjina miki sosai, kin sadaukar da farin cikin ki da rayuwarki gabaɗaya saboda shi, Allah ya bar ƙaunaa."

Ta yi murmushi tana goge hawaye ta ce, "Hamma ya wuce komai a wajena, Hamma ya yi min abinda babu wanda ya yi min shi a duniyata. Ya ɗauko ni kuma ya riƙe ni, ya taimake ni ya kaini matakin da ban yi tunanin zuwa ba. Duk ahinda  zan yi masa ban faɗi ba, kuma ban saka masa ba."

Ya É—aga kai ya ce, "Gaskiya ne wannan. Ina so na faÉ—awa Baffa saboda kar ya yi asarar da kadararsa ya siyar, amma ban san me zan ce ba."

Islaha ta ce, "Ka samu dabarar da zai daina cewa zai siyar É—in."

Ya É—aga kai ya ce, "zan san abinda zan yi in Allah yarda, Baffa yana nan?."

"Yana ciki."

"bara na je na same sa, shi da Maman." Islaha bata ce komai ba, ya wuce ya shiga ciki itama ta bi bayansa.
Chapter 127 · 0% Book details