← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 133

Sashe 115

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jafar ne kaɗai ya amsa da amin Abba ya ce, "Sannan in sha Allah duk macen da ka gani ka ce kana so ka aura zan shige maka gaba har sai ka mallake ta. Baturiya ko ƴan india jinin babar ka, kai ko wanne yare, ko wanne ƙabila, indai ka kawo bazan ba da goyan bayan a juya maka baya ba. Kai ko ba musulma bace, indai ta yi maka za ka aure ta, tunda addini bai hana ba zan ba ka goyan baya koda kowa zai ƙi goya ma ka baya a kai. Sai na tabbatar ka samu abinda ka ke so."

Rehaan ya ce, "To Abba" ya sake faɗa a taƙaice dan bai san me zai ce ba.

Abba ya ce, "Jafar zai raka ka kaje ka ga yarinyar, daga nan sai ka dawo a É—an yi shirye shirye a kai mata da lefe da komai na al'ada, In kuma kuÉ—i za ka bata a matsayin kayan lefen sai a bayar a yi."

To kawai ya sake cewa kawai bai ce komai ba.

Abba ya ce, "ka tuna kwana tara auren ya rage, aje ayi abinda za a yi kafin lokaci ya ƙure."

Rehaan ya ce, "To Abba."

Abba ya shafa kansa ya ce, "ka cigaba da haƙuri, ɗaukakar kenan, hausawa sun ce ɗaukaka abar gudu ce kuma abar nema."

Ya kalli Jafar ya ce, "sai ka ɗora daga inda na tsaya." Jafar ya amsa sannan Abba ya miƙe ya fita.

Jafar ya kalle sa cikin tsokana ya ce, "Ango." Bai kula ba sai shan tea É—insa da yake yi kamar baya so.

Jafar ya ce, "É—an gata Abba da Daada, aure kawai za a yi maka cikin kwana tara, gaskiya kana lokacin ka." Nan ma ya yi masa banza bai ce komai.

Jafar ya ce, "ka dai yiwa Abba biyayya kawai malam."

Sai a lokacin ya kalle sa ya ce, "wai aure, sai ka ce wani toy, ni Rehaan za a yiwa haka."

"Babu mita Rehaan, kawai ka amince."

"Kamar a film, ko sanin yarinyar ban yi ba. Kamar sadakata aka bata fa."

"Na faÉ—a maka wacece?."

"Kai ka santa ne?."

"kaima ka santa."

Ya É—an zuba masa ido kafin ya É—auke kai bai ce komai ba.

Jafar ya ce, "Yarinyar nan da sace, yarinyar nan da ku ka haÉ—u a Jedda, itace dai matar ka."

Rehaan ya juyo yana kallonsa alamun ban gane ba, Jafar ya yi dariya yana ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "da gaske nake maka, wallahi itace, ka san dai bazan ce wallahi akan ƙarya ba. Abba yana faɗa min sunanta na gane ta, na saka a yi bincike a kanta a kan hakan."

Ya ajjiyd mug É—in hannunsa ya ce, "Jaazy ka daina yi min wasa."

Jazy ya ce, "ba wasa nake maka ba, wallahi da gaske nake. Itace wacce Daada take so ta haÉ—a auren ku."

Ya É—an yi shiru yana kallon waje Jazy, har Jazy ya ce, "ka zuba min ido kana kallona."

"Jazy akwai plan É—in da yarinyar nan take haÉ—awa a kaina, jikina yana bani turo ta aka yi."

Jafar ya girgiza kai cikin tabbatarwa ya ce, "Wallahi babu wanda ya turo ta, infact har yanzu bata san da batun auren ka ba, ita ta neman saurayinta da aka yi garkuwa dashi take, ta ajjiye ka a gefe kamar bata taɓa saninka a Jeddah ba."

Ya zuba masa ido ya kasa magana, yana ganin abin kamar rainin hankali. Ta ya za a ce itace matar? In ba shirya wannan abin aka yi ba ta ya hakan sai faru?.

Jafar ya ce, "ni ka daina zuba min ido, ka yi magana kawai."

Rehaan ya ce, "Kawai ina tuna irin abubuwan da suka faru ne, kai tsaye ka san plan ne wannan. Ta ya rayuwarta zata dinga haÉ—uwa da ta wa? Daga hotel sai asibiti, daga asibiti sai guest house, daga guest house sai Jeddah, daga Jeddah sai aure?. Jazy akwai abinda yarinyar nan ta shiryawa."

Jazy ya yi dariya yana girgiza kai ya ce, "na faÉ—a maka babu abinda take shiryawa, ta taimaki kakar ka akan titi, daga nan suka haÉ—u ta kawo ta gida, daga lokacin kuma Daada ta fara wannan maganar."

Rehaan ya ce, "Meyasa take shigowa rayuwata ko yaushe?."

Ya É—age kafaÉ—a ya ce, "oho, kaima kuma ka shiga rayuwarta ai."

Ya girgiza kai ya ce, "Wallahi ban yarda da yarinyar nan ba, akwai abinda take shiryawa a kaina."

Jafar ya yi dariya ya ce, "In za ka saka a bincika sau dubu, amsar itace bata da wani mugun nufi a kanka. Wallahi bata san kai zata aura ba, ta san da maganar auren amma ba ta auren take yi a yanzu ba. Duk wanda zai faɗa maka akasin abinda na faɗa maka ƙarya ce, abinda na faɗa maka a kanta shine gaskiya."

Rehaaan ya ce, "Ta ya zata dinga shogowa rayuwata ko yaushe? Da farko otel, hospital, guest house, jeddah sannan yanzu aure. Aure fa
Jazy!" Ya maimaita yana kallon Jafar.

Jazy ya ce, "ka san dai bazan yi maka ƙarya ba, ka san dai bazan faɗi abinda yake ba gaskiya ba, ka san bazan taɓa yin abinda zan cutar da kai ba, ka yarda yarinyar nan bata da nufi ko kaɗan a kan maganar nan, bata san da batun auren ka ba har yanzu."

"To ya aka yi ake zancen auren bayan bata sani ba?."

"ban sani ba, amma ita bata sani ba, amma wanda yake riƙonta ya sani."

Ya girgiza kai yana kallon Jazy ya ce, "Bazan aure ta ba Jazy, ban yarda da ita ba, bazan yarda da wannan auren ba."

"Ya kamata ka yarda."

"Bazan yarda ba, wallahi bazan yarda babu plan cikin a haÉ—uwata da yarinyar nan ba, wani ne ya turo ta cikin rayuwata."

"Daman kwai plan É—in Allah mana, kuma daman Allah ne ya turo ta rayuwarka ba wani ba."

Ya girgiza kai ya ce, "haka bazai faru ba, akwai wani abun bayan nan. Meyasa sauran mata basu shiga rayuwata ba sai ita kaÉ—ai?."

"Ni dai ban ga wani plan ba, kuma na faÉ—a maka na saka an bincika min maganar nan sosai."

Rehaan ya ce, "ta ya hakan zai faru lokaci É—aya? In ba plan bane wannan meye?."

Jazy ya taɓe baki bai ce komai ba, dan ya gaji da maimaita magana guda ɗaya.

Rehaan ya bi sa da kallon tuhuma ya ce, "anya babu haÉ—in bakinka a maganar nan? Na lura tun Jeddah kamar akwai abinda ku ke haÉ—awa kai da ita."

Jazy ya É—aga hannu sama yana murmushi ya ce, "ban sani ba, Abba ne ya bani labari."

"Amma meyasa ba ka faÉ—a masa karuwa bace!?."

Jafar ya zaro ido waje ya ce, "ni Jafar na faɗi abinda ban taɓa gani ba? so ka ke Allah ya tsayar damu ya yi mana hisabi na yi bayani da larabci?. Ba da ni ba, na san illar da take cikin yiwa mutum ƙazafi akan abinda ba ka da tabbas a kai."

Ya bisa da harara yana kallonsa amma bai ce komai ba, dan ya san yana nufin ƙazafi ya yi mata kenan. Ya ja tsaki yana ji an gama raina masa hankali a duniya, mutum kamar sa da iliminsa da komai a ace wai mata za a zaɓa masa kamar yaro ƙarami.

Ya ja tsaki mai tsaho ya ce, "Bazan amince da auren nan ba, dole a fasa shi!" Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Sai kuma ya tsaya cak jin cikinsa ya motsa, ya ɗan runtse ido yana dafe cikinsa.

Sai kuma ya fara tafiya, Jazy ya miƙe tsaye ce, "ina za ka je?."

"Zan je na faɗawa Mamy, bazan iya auren yarinyar nan ba, bazan iya auren karuwan da ta zubar da ciki ba, sannan ɓarauniyar da take yiwa ƴan siyasa sata ba."

Jafar ya ce, "Yanzu ka yiwa Abba alƙawarin za ka aure ta."

"Ni ban yi alƙawari ba!."

"Amma ka amince tunda ka ce to, kuma ka ce ka masa za ka ta ya sa yiwa mahaifiyarsa biyayya."

Ya ɗan dafe kai jin jiyoyin kansa suna harbawa, zuciyarsa tana bugawa, tsanar Islaha tana sake tasowa daga ƙasan zuciyarsa tana mamaye ko ina na jikinta.

Ya hargitsa gashin kansa ya kalli Jazy, calmly ya ce, "Jazy na tsane ta, wallahi na tsane ta bana so na ganta. Ka ji na ce wallahi ko? I mean my words."

Jafar ya ce, "To ya za ka yi? Biyayya za ka yiwa Abba."

Ya ɗago yana kallonsa, Jafar ya bishi da kallo ganin har idonsa ya canja kala zuwa jajeye, ya san ba komai ne yake canja yanayin Rehaan har haka ba, ba komai ne yake taɓa shi har ya ɓata masa rai ba. Ya yi mamaki da ya ga ransa ya ɓaci haka, ya yi mamaki da ya ga har mood ɗinsa ya canja, hakan da ya gani ya tabbatar masa da gaske ya tsani yarinyar.

Jafar a hankali ya ce, "meye na ɓata ranka haka? Ni na jima ban ga ranka ya ɓaci kamar haka ba, ka sassauta wannan ɓacin ran please."

Ray ya kalle sa ya lumshe ido ya buÉ—e ya ce, "na tsane ta, bana son ganinta ko kaÉ—an a cikin rayuwata. Ta ya za a ce zata zama matata?."

Jafar ya ce, "ni abinda nake so da kai, ka daina faÉ—ar abinda ba ka sani ba, ka daina faÉ—ar kalmar da ba ka tabbatar ba a kanta."

"Zan sake maimaitawa ,she is a prostitute….Kuma zan je na faɗawa Mamy, ni bazan aure ta."

"Kar ka faÉ—a mata."

Ya juyo ya kalle sa alamun meyasa ya ce, "hakan bai kamata ba, kuma za ka iya yin danasani nan gaba." Ya wani kalle sa yana harararsa, ya kasa cewa komai yana kallonsa jin wai zai iya yin danasani, ko danasanin me zai yi oho.

Jafar ya ce, "Just obey your father's command, ka aure ta kawai, ba ka san me hakan zai kawo ba. Wataƙila ka ga ya zama alkhairi, haƙurin da za ka yi sai ka ga ya zama riba a nan gaba."

Ganin ya yi shiru bai ce komai ba ya san mamaki yake yi akan ya ce zai yi danasani.
Chapter 115 · 0% Book details