← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 133

Sashe 84

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jazy kalli Islaha ya yi mata alama da ta kalli inda ya kalla, ta É—aga kai ta kalli Rehaan sannan ta kalli Jazy alamun na gani meye. Ya ce, "Rehaan AbdulAziz Yola, wanda ki ka fi sani da Ray!."

Wani irin dum Islaha ta ji a kanta da kunnenta, ta buÉ—e ido sosai ta saka É—aga kai tana kallon Rehaan da yake amasa waya yana murmushi.
Yana sanye da riga mai ƙaramin hannu, sai dogon wando, ya saka hannu a aljihun yana zagayawa daga nan zuwa nan.

Ta sake kallin Jafar alamun tana son tabbatarwa, ya É—an murmusa yana É—aga mata kai ya ce, "Ba ki yarda ba?."

Bata amsa ba dan mamaki ya kashe ta a zaune, Jazy ya É—an É—aga murya ya ce, "Rehaan!."

Rehaan ya É—an zabura ya juyo yana kallonsa, ya yi masa alamun what kafin ya bar wajan.

Ya sake kallon Islaha da ta daskare a wajan, ta kalle sa dan har lokacin bata dawo daidai ba, mamaki take yi da ya kasance shine Rehaan Yola, zuciyarta bugawa take yi, dan kwata-kwata bata taɓa wannan hasashen ba.

Ya ce, "har yanzu ba ki yarda ba? Ko dan kina ganin babu security kamar a Nigeria?."

Ta ɗan sauke numfashi ta kasa magana, dan harshen ta ya sarƙe, kamar an ɗaure sa ta kasa furta komai. Rehaan Yola kawai take maimaitawa a ranta, tana ganin abin kamar rainin hankali.

Jazy ya ɗauki wayarsa a gefe kafin ya miƙa mata, ta karɓi wayar tana kallo, ta sake jin faɗuwatr gaba mai yawa, dan ta tabbatar shine Rehaan Yola. Ta kalli Jafar tana miƙa masa wayar sa, ta koma ta zauna tana ganin abin kamar wasa.

Jazy ganin ta shiga ruɗani sosai ya ce, "Islaha nan gidan Rehaan, duk abinda ya faru ya faru tsakanin ki da Mr Ray. Shiyasa na ce kina da sa'a, babu macen da ta taɓa rayuwa dashi kamar ki. Ke kam kin zauna dashi, kun yi magana, sannan ya yiwa mahaifin ki tiyata. Ta ko ina kin shiga rayuwarsa, shima ya shiga ta ki. Itace sa'ar da nake faɗa miki, dan ni na san waye Rehaan, na san abinda zai yi da wanda bazai yi ba."

Ta É—an kalle sa ta ce, "Da gaske shine Mr Ray?."

Ya É—aga mata kai ya ce, "a gidan Mr Ray ki ke, Miss Islaha."

Islaha ta gyaɗa kai ta ce, "Ikon Allah! Wallahi ban taɓa sani ba. Ban ɗauka ma wannan yana jin hausa ba, har na gama zama a hannunsa ɗauka nake yi ba bahaushe bane, dan sau ɗaya na ji ya yi magana, kuma ban san sunansa ba. A nan ma sai akan wannan baturiyar na ji ya yi min hausa."

Ya yi murmushi ya ce, "na san ba ki sani ba, shiyasa na faÉ—a miki."

Ta sunkuyar da kai ta yi shiru bata ce komai ba, dan jikinta har rawa yake yi saboda mamaki.

Ya gyara zama ya ce, "kin san meyasa nake tambayar ki kuma nake faÉ—a miki?."

Ta girgiza kai alamun bata sani ba, ya ce, "Tunda na yi bincike a kanki sai na ji na yarda dake, sai nake ji a raina aikin nan da ki ke yi kamar bai dace dake ba. Kina da carrier mai kyau, kina da farin jini, ana son fuskar ki a duniya, meyasa za ki zo nan ki dakusar da rayuwar ki?."

Ta É—an rausayar da kai ta ce, "na faÉ—a maka ina nan saboda shi, wallahi ba dan kuÉ—in nan ba da babu abinda zai kawo ni Jeddah da sunan aiki."

"Tun farko da kin faɗa masa maganar kuɗin da ba ki tsinci kan ki a nan ba. Na faɗa miki shine ya yiwa mahaifinki tiyata, ranar da ya yi aikin ranar ya tawo nan, bai sake komawa ba har yanzu. Na tabbatar da bazai karɓi komai na ki ba."

"Haka kawai ban san mutum ba sai na roƙe sa? Ni ɗaukar da na yi ma ban san dalili ba. Kuma wallahi da na san shine Mr Rehaan, da na san shine zai yiwa Baffa aiki, da bazan ɗaga hankalina na taho nan neman kuɗin da zan bashi ba."

Jazy ya kalle ta, ta É—aga kai ta ce, "Eh, da na san shine da bazan zo ba. Na ci bashin kuÉ—insa, kuma na ba da kuÉ—in a asibitinsa. Na É—auko, kuma na mayar."

Jafar ya yi dariya yana kallon ta ya ce, "yanzu ki ajjiye batun nan, kina da asthma aiki irin wannan bai dace dake ba. Ki koma gida, ki cigaba da aikin jaridar ki, kamar zai fi miki."

Islaha ta ce, "ina son hakan, amma bazai yu ba sai na sauke nauyin da yake kaina. A nan ne zan iya haÉ—a masa kuÉ—in nan within one year, can kuwa fa?."

"Au ki ka ce baza ki biya ba."

"ai cewa na yi da san haka ne tun farko, amma ba wai na fasa biya É—in bane."

Jafar ya nuna mata kuÉ—i akan table, ta kalla ta ga kuÉ—in saudia ne masu yawa a wajan a ajjiye.

Ya ce, "tun jiya kuɗin nan suke a wajan nan, ɗabi'ar Rehaan ce ajjiye kuɗi ya manta. I'm very much sure kuɗin nan da ki ka ɗauka ya manta dasu, in dai ba ɗauka aka yi aka bashi ba shikenan sun sha ruwa. Sai dai Shams ya ɗauke ya ajjiye a wajensa, dan duk inda Rehaan zai zauna indai zai fito da kuɗi, daƙyar bai bar wasu a wajen ba."

Islaha ta kalle shi ta ce, "dan shi bai sani ba ai Allah ya gani, akwai haƙƙin hakan a kaina."

Ya gyaɗa kai ya ce, "In dai za ki koma Nigeria, na yi miki alƙawarin zan biya Rehaan kuɗinsa, Shikenan ko?."

Ta É—ago ido yana kallonsa bayan ta buÉ—e su waje, ta ce, "za ka biya sa kuma? Ni ban ce ka biya ba, zan yi aiki da kaina dan biyasa."

"Kina son zaman nan É—in kenan, in kina so fine bai dame ni ba, sai ki zauna."

Ta sunkyyar da kai ta ce, "bana son zama, ina da abubuwan yi da yawa a can. Kawai bazan amince ka biya min kuÉ—in bane Mr Jafar, na gode da niyar alkhairi, amma gwara na yi aikin na samu na biyasa."

"Ban ce zan biyasa saboda wani dalili ba, zan biyaa ne saboda na yi niya. Yanayin rayuwarki, da ciwon da ki ke dashi ne ya saka min son biya miki kuÉ—in. Dan haka kar ki damu, bazai san ma na tura masa kuÉ—in ba. A account É—in PA É—insa zan tura, ba shi ne ma zai ga alert É—in kuÉ—in ba."

Ta sauke nunfashi cikin wani irin yanayi, ta kalle sa zata yi magana ya katse ta ya ce, "Indai bakya son aikin nan da gaske, kawai ki fara shirin komawa Nigeria, in kuma kina so ban yi miki dole ba."

Ta sauke numfashi a hankali, ta É—ago ta sake kallonsa ta ce, "kamar na É—ora maka nauyi, ba ka sanni ba fa."

"Na sanki mana" ya faÉ—a yana É—aukar wayarsa da dan gaske yake zai biya mata É—in, gwara ta koma gida ta bar Jeddah

Islaha a sanyaye ta ce, "Na gode Mr Jafar, Allah ya saka maka da alkhairi..."

"Amin Miss Islaha."

Ta kalli hanyar da take jin takun tahowa, ta ga Rehaan ne yake sakkowa, ya ƙaraso ya wuce su ya fita bai ko kalle su ba.

Yana fita ta girgiza kai ta ce, "Da gaske shine Mr Ray?."

Jafar da yake jinta ya É—an murmusa ya ce, "Sai ki fara shirin interview."

Ta É—an buÉ—e ido cikin firgici ta ce, "har yanzu yana interview tana hannunka."

Ya kalle ta ya ce, "Ki faÉ—a min abinda Alma ta yi nufin yi masa please, hankalin mu ya kasa kwanciya da ita."

Ta kalle sa ta ce, "na faÉ—a maka tsakani da Allah na yi."

"nima tsakani da Allah zaki faÉ—a min."

"Na ganta a kitchen tana zuba masa tablet a tea, sai na haÉ—a accident É—in da na zubar da tea É—in."

Ya harÉ—e hannayensa yana binta da kallo ya ce, "meyasa ki ka yi abinda ki ka zubar da tea É—in?."

"Saboda in wani abun ya same sa ni za a ce, ban san me ta zuba a ciki ba, shiyasa na yi hakan."

Ya ce, "na biyun fa?."

"Ya ce na kai masa tea bedroom, na kai na fito ba jimawa na dawo na ɗauki cup ɗin, sai na ga ta fito daga ɗakin cikin murna tana cewa yanzu zai fara aiki. Sai ban yarda da ita ba na shiga ɗakin, sai na same sa kamar wanda aka yi knocking out ya riƙe kansa, daga ƙarshe ya kwanta bacci ya ɗauke sa....."

"Sai na ɗan ɓuya a ɗakin, a nan na ga ta shigo tana undressing kayan jikinta, sannan ta saka waya da light ta fara ɗaukar video. Ni kuma sai na fito, na ɗauke wayar na goge video, na ce in bata fita ba sai na kira police. Shine kawai."

Ya girgiza kai ya ce, "Thank you so much, mun gode da wannan taimakon da ki ka yi."

Ta ɗan taɓe baki ta ce, "ba dan shi na yi ba, saboda Allah na yi. Kuma na san in wani abun ya faru dashi ni za a ce, tunda ni ce housemaid a gidan."

"Mun gode."

"Kar ka faɗa masa, ka ƙyale sa kawai." Ya gyaɗa mata kai alamun to.

Ya miƙe tsaye itama ta miƙe tana yin rolling mayafin kanta ya ce, "ki koma, zuwa gobe in Allah ya kaimu ki siyi ticket ki koma Nigeria. Zamu sake haɗuwa in lokacin interview ya yi."

Ta yi murmushi ta ce, "na gode sosai." Bai ce komai ba ya fita ya biyan Rehaan dam ya san ita ya tafi.

A zaune ya same sa a cikin garden ya harÉ—e hannayensa yana girgiza kai kamar wanda aka yiwa laifi. Jazy ya zauna a kusa dashi bai ce komai ba.

Ray ya wani kalle sa ya ce, "so you found a new girlfriend, you are cheating Riyya."

Jazy ya yi dariya cikin mamaki ya ce, "girlfriend kuma?."

"Yes, awa nawa ku ka yi a zaune kai da ita? Sai wani hira ku ke yi kamar ka santa, kana ta dariya abinka."
Chapter 84 · 0% Book details