← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 133

Sashe 42

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga harabar gidan ya burge ta sosai, gida ne mai cike da shuke-shuke da parking space mai matuƙar girma da tsari, komai na gidan ya burge ta sosai, kana kallon gidan ka san gidan larabawa ne saboda yadda aka tsara shi kuma babu hayaniya.

A hankali suka ƙarasa har bakin wata babbar ƙofa mai girma da faɗi. Ya danna door bell suka ɗan tsaya na wani lokaci kafin a buɗe ƙofar.

Da kyakywan balarabe suka yi tozali, fari ne tass mai madaidaicin jiki, ko a cikin larabawan yana daga cikin kyawawa, dan in ka kalle shi sai ka so ka kuma kallo saboda baiwar da yake da ita.

Maleek ya bisu da kallo, cikin harshen larabci ya ce, "daga ina?."

Cikin ƙaramin lokaci Oga Musa ya canja yare zuwa larabci ya ce, "barka ranka ya daɗe, itace mai aikin gidan da aka ce za a kawo." Ya faɗa yana nuna Iskaha da kanta yake ƙasa bata ɗago ba.

Maleek ya bi islaha da kallo kafin ya dawo da kallon sa ga shi ya ce, "haka nace maka ina da buƙata ne? Waye ya ce a kawo min?."

"Matar gidan nan ce ranka ya daÉ—e."

Maleek ya yi tsaki kaÉ—an ya ce, "ni ban ce a kawo min kowa ba, zaku iya komawa."

Har zai rufe ƙofa sai kuma ya kalli Oga musa ya ce, "daga Nigeria ku ke?."

Da sauri ya É—aga kai ya ce, "eh, shigowar mu kenan."

Ya É—an kalli Islaha da har lokacin bata É—ago ta kalle shi ba ya ce, "itace mai aikin?."

Ya É—aga kai, ya kalli Islaha ya ce, "ki gaishe sa."

A hankali ta É—aga ido ta kalle sa suka haÉ—a ido dashi, a sanyaye cikin english ta ce, "ina yini."

Sai ya É—an yi murmushi ba tare da ya amsa ba, ya kalli Oga Musa ya ce, "tana jin turanci?."

"Eh ranka ya daÉ—e, ta iya sosai."

Maleek ya ɗan basu hanya ya ce, "ku shigo." Daɗi ya mamaye zuciyar Oga Musa, dan da ya ce su koma bai san inda zai kai Islaha ba, kaya zata zamar masa tunda babu aikin a ƙasa, suka shiga Maleek ya rufe ƙofar.

Islaha tana saka ƙafarta falon wani shegen sanyi ya ratsa ta, da sauri ta ɗaga facemask ɗinta ta mayar hancin ta, ga wani ƙhamshi da wajan yake yi kamar kar ka daina shaƙa saboda daɗi.

Suka zauna Maleek ma ya zauna ya ce, "Nawa ta ce zata bata salary?."

Oga Musa ya ce, "ta ce za a bada riyal dubu É—aya da É—ari biyar."

Ya É—an É—aga kai ya ce, "Okay ya yi kyau. Za a bata kuÉ—in. Ka bani katin ka."

Oga Musa hannu yana rawa ya É—auko compliment card É—insa ya bawa Maleek, shi kuma ya ajjiye a gefe ya ce, "zan neme ka."

Musa ya É—aga kai ya kalle ta ya ce, "Islaha zamu yi waya, kome ake ciki zamu tattauna." Ta É—aga kai tana jin faÉ—uwar gaba mai yawa har ya fita.

Falon ya yi shiru gabanta yana faÉ—uwa sosai, ta É—aga ido ta kalle sa taga ba ita yake kallo ba waya yake dannawa, kafin ta ji ya fara magana cikin larabci.

Sai da ya gama wayar sannan ya kalle ta ya ce, "ga É—aki nan, ki je ki zauna."

A sanyaye ta miƙe da jakarta ta nufi ɗakin da ya nuna mata da hannunsa.

Tana buÉ—e É—akin ta tsaya tana kallon É—akin tana mamakin girma da kyaun É—akin, komai yana shirye tsaf kamar daman an san da zuwan ta.

Wata irin gajiya take ji a jikinta, ta ɗan sauke numfashi tana kallon kanta a ƙaton madubin ɗakin. Ji take yi kamar ba ita ba, jin ta take yi kamar a mafarki, wai itace a wata ƙasa ba nigeria ba, kuma wai aiki tazo yi aikin da ta fi kowa tsana.

Ƙofa ta gani daga gefe, ta taka a hankali ta buɗe, girman banɗaki sai ya bata tsoro, ta tsaya tana ƙare masa kallo ganin babu abinda babu a ciki, harda kayan wanka da komai a ajjiye.

Ta zauna a gefen gado a sanyaye, ta ɗauki wayarta ta kunna data amma data ta ƙi ta yi. Ta sauke numfashi sai ta ga wata takarda da scan ɗin wifi, ta ɗauka ta juya sai kuma ta yi scaning sai ga wifi ya kama a wayarta.

Message É—in da ta tura Safeera ta duba taga bata buÉ—e ba, ta É—an dafe kai ta danna vn ta ce, "Bestie ya ki ke, ya ciwon kan?. Bestie ina jeedah, har an bani gidan da zan yi aiki."

Har zata tura sai ta goge, ta yi tsaki ta sake yin wani ta kuma gogewa, daƙyar ta yi wani ta tura mata ta ɗan kwanta a kan gadon tana sauke numfashi.

Sai kuma ta miƙe a gajiye ta warware rolling ɗin kanta, ta kwance gashinta ya sauka har bayanta, ta fara ɓalle maɓallan abayar jikinta kenan taji an buɗe ƙofar ɗakin.

Da hanzari ta kalli ƙofar suka haɗa ido da Maleek, maimakon ta ga ya koma saboda ganin tana cire kaya, sai ta ga ya shigo yana binta da kallo.

Maleek ya ce, "Za ki iya haÉ—a min Coffee?."

Islaha gabanta ya faÉ—i sosai, ta gyara rigarta sannan ta É—aga kai alamun eh zata iya.

Ya É—aga kai ya buÉ—e closet É—in wajan ya nuna mata uniforms na masu aiki ya ce, "You can take your size." Ta kalli wajan ta kalle sa ta É—aga kai bata ce komai ba.

A hankali ya juya ya fita, da gudu miƙe ta sakawa ƙofar lock tana sauke nunfashi hannunta yana dafe da ƙirjinta har lokacin zuciyarta bugawa take yi.

A bayyane ta ce, "Bai damu dan ya shigo ina cire kaya ba, shi ko a jikinsa bai nuna alamun rashin kyautawa ba. Na shiga uku ni Islaha, ina na kawo kaina?."

Sai kuma ta wara ido tunawa da yace yana son coffee ta ce, "wai bazan huta ba kenan, daga zuwana sai na fara bauta?."

Tunawa babu mai bata amsa sai ta yi sauri ta shiga wanka, da ruwa mai zafi ta yi wanka ta fito ya kalli agogo a ƙarfe tara na safe.

Ta sauke numfashi tana jin bacci yana fizgarta, gajiya ta yi mata yawa tana buƙatar yin bacci, tana so ta kwanta amma babu dama.

Ta ƙarasa wajan closet ɗin tana kallon uniforms ɗin da ya nuna mata, farar riga ce da baƙin siket mai faɗi, sai mayafi baƙi da aka haɗa dashi. Ta ɗauko tana warwarewa, sai ta ga kala biyu ne akwai doguwar riga mai yanayin apron, daga sama take fara, daga ƙasa kuma baƙa ce. Sai ta ga gwara ta saka doguwar rigar, ta saka a jikinta ta ga ta zauna sosai kamar dan ita aka ajjiye.

Ta É—auki ribbon ta saka a gashinta, ta saka É—an mayafin da ake yafawa ta rufe gashinta, ta saka room slippera kalar kayan tana tunanin ta yadda zata fita.

Kallon kanta take yi, kayan sam basu kamata jikin ba amma sun yi mata kyau sosai, ta fito sak a Æ´ar aiki.

Ta lock key ɗin da ta sakawa ƙofar, ta fito a hankali tana takawa a hankali kamar bata.

Falon da suka bari ta ƙaraso, sai ta ga babu kowa sai a.c da take aikinta. Islaha sai ta tuna da yanayinta, tana buƙatar saka facemask gudun samun matsala. Ta juya zata ɗauko facemask suka yi karo da mutum.

Islaha ta tsorata sosai, ya bita da kallo ganin ta shirya cikin kayan kamar yadda ya ce, kafin ya yi murmusui ya ce, "where are you going?."

Muryarta tana rawa, "I'm going to get my face mask."

Ya girgiza kai ya ce, "You don't have to wear it, you're very beautiful" ya faÉ—a yana shafa kumatunta.

Da hanzari taja baya gabanta yana faɗuwa sosai, ta ce, "I have asthma, so I need it because of the cold" ta faɗa muryarta tana cracking ganin yana ta kallon ta. Ya ɗan bata hanya alamun ta wuce, a guje ta koma ɗaki ta rufe ƙifar tana sauke nunfashi.

Sai kuma ta É—ora hannu a kanta ta ce, "na shiga uku!."

Knocking ƙofar taji ana yi, da hanzari ta ɗauki face mask ɗin ta saka, tana buɗe ƙofar suka haɗa ido da balarabiya fara kyakykawa sanye da uniform irin nata.

Islaha bata san ta yiajiyar zuciyar ba, dan a tunaninta Maleek ɗin ne ya dawo yana ƙwanƙwasa ƙofar.

Cikin larabci ta miƙawa Islaha hannu ta ce, "barka da zuwa Jeddah. Sunana Sunaira."

Islaha kwata-kwata bata ji me tace ba, ta dai ji ta ce Sunaira. Sunaira ganin Islaha bata gane ba sai ta kuma miƙo mata hannu.

Islaha ta bata hannu suka gaisa ta ce, "Islaha."

Ta yi murmushi ta ce, "ki zo zan nuna miki kitchen."

Islaha bata ji me tace ba ya saka ta ce, "i'm sorry, no arabic."

Itama ta ɗan yi murmushi cikin ƙaramin ingilishinta ta ce, "No english." Islaha ta ɗan murmusa suka fito tare.

A falon farko a nan kitchen É—in yake, suka shiga ita dai Islaha kallon kitchen É—in take yi saboda girmansa. Daga nan ta nuna mata É—akin wanki wanda aka tanadi komai na wanki a cikinsa.

Suka dawo kitchen É—in Sunaira ta É—auki wayarta ta shiga google ta yi rubutun arabic to english ta haskawa Islaha wayar. Islaha ta karanta ta É—aga kai suka fara haÉ—a coffee.

Islaha ce ta É—auki tray É—in zuwa falon da tayi mata kwantancen nan zata kai.

Da sallama ta tura glass door ɗin ta shiga, daga ciki taji ya amsa sallamar, ta ƙarasa tana kallon ƙasa har ta ajjiye masa a kan table bata kalle sa ba.

Maleek ya ajjiye wayar hannunsa ya kalle ta ya ce, "what is your name?."

Islaha tana daga tsaye ta ce, "Islaha."

Maleek ya bita da kallo jin sunan mai daÉ—i, kafin ya maimaita ya ce, "Islaha!."

Ta É—aga kai alamum eh, ya murmusa ya ce, "from which state in Nigeria?."

Islaha ta ce, "Adamawa state."

Ya É—an bita da kallo kafin ya ce, "Fulani?." Da mamaki ta kalle sa suka haÉ—a ido, sai ta É—aga kai alamun eh.

"Wow! I have a friend from Adamawa state, but his skin color is not the same as yours. Why do you look like this?."
Chapter 42 · 0% Book details