Sashe 89
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta saka lambar ta kalli Islaha ta ce, "a ina za ki kwana? Ko yau za ki koma?."
"Sai gobe, ina so na shiga masallaci annabi. A can zan kwana, ance min zan iya zamana a can, har na yi wanka na shirya duk a ciki."
"Ki yi min addu'a in kin je, ina so na je amma babu dama, ko kuÉ—in mota ma bani dashi. Albashina na farko ma a magani suka tafi, saboda mura da tari."
Islaha ta sauke jakar bayanta, ta ɗauko kuɗi ta ce, "ki riƙe wannan Umma."
Umma ta kalli kuÉ—in, ta kalli Islaha ta ce, "Islaha a ina ki ka samu wannan kuÉ—in?."
Islaha ta ce, "na faÉ—a miki kyautarsu da ake yi min, ranar farko riyar dubu bakwai ya bani."
Umma bata karɓi kuɗin ba, ta zuba mata ido ta ce, "Islaha kar fa ki ɓata rayuwar ki a ƙasar nsn, na lura in ka ja mutuncin ka zaka zauna lafiya, amma in ka watsar ya watse."
Islsha ta sakawa Umma kuÉ—in ta ce, "Wallahi Umma babu abinda nake aikatawa, ki yarda dani, kyauta aka bani."
Umma ta kalli kuÉ—in ta ga riyal dubu biyu ne, ta sauke numfashi ta ce, "na gode, Allah ya albarkaci rayuwar ki, ki yafe min."
Islaha ta murmusa ta ce, "Amin Umma. Ina tunanin komawa Nigeria a kwanakin nan, wannan kuÉ—in da aka yi min kyauta dasu zan biya su Mama kawai na wuce gida."
Umma ta É—aga kai ta ce, "Hakan ya fi miki, Allah ya saka mu a danshin ki."ta amsa da amin a sanyaye.
Umma ta ce, "Labiba fa?."
Islaha ta ce, "sau ɗaya na taɓa ganinta, har yanzu ban sake ganinta."
Umma bata ce komai ba, Islaha ta sha ruwan sannan ta miƙe ta ce, "Umma ni zan tafi."
Umma ta miƙe ta riƙe hannunta ta ce, "Allah ya kai ki lafiya, na gode miki, in ba ke ba waye zai yi min abinda ki ka yi? Allah ya albarkaci rayuwar ki."
"Amin Umma. In sha Allah sai na zama silar barin ki gidan nan."
"Allah ya sa Islaha."
Tare suka fito, Islaha ta bi falon da kallo ganin kamar ba yanzu Umma ta gyara sa ba, anyi kaca kaca dashi da abinci.
Umma ta ce, "kin gani ko, ga shara ga wanke wanke, ga wankin kayansu, sannan ga kula da yaran. Kullum a haka nake."
Islaha tausayim Umma ya sake kamata, a lokacin matar ta fito ta fara yiwa Umma masifa.
Umam ta fusata ta ce, "bazan yi aikin ba, ki dake ni. Haifata ki ka yi da za ki dinga yi min faɗa? Dan ina aiki a ƙarƙashin ki sai ki dinga ɗaga min murya?. Wallahi ba ki isa ba, na daina ɗaukat wulaƙancin ki!."
Sak matar ta yi, duk da ba ji take yi ba amma Umma ya bata tsoro, ta ja baya ganin Umma tana yi mata faÉ—a sosai, sai ta bar wajan bata ce komai ba.
Islaha ta ce, "Yauwa Umma, haka za ki dinga yi musu, duk da ba ji suke yi ba amma zasu yi shakkar ki, ki dinga ƙunduma musu ashariya."
Umma ta ce, "Na gaji islaha, mu je na raka ki." Tare suka fito Umma ta raka ta har kan titic ta tari taxi ta hau Umma ta koma ciki cikin kewa.
Islaha tunda suka É—auki hanya ta yi lamo a jikin kujera tana kallon titi, tunanin halin da ta ssmu Umma take yi da abinda take faÉ—a mata.
Ta sauke numfashi tana tunanin ita kam Allah ya tarfawa garin ta nono, Allah ya kai ta hannu na gari, basu taɓa ƙoƙarin cutar da ita ko neman ta da wani sharri ba, ga kuɗi da take sami hankali kwance ba tare da ta ba da kanta ba. Tabbas Allah ne ya ga zuciyarta ya haɗata da mutanen kirki masu farar zuciya, in itace a halin da Umma take ciki bata san wanne mataki zata ajjiye abinda zai faru ba.
Kallon titi take yi ganin ko ina mai kyau da É—aukar hankali, ta girgiza kai tana tabbatar da an yiwa nigeria nisa ta ko wanne fanni.
Sun É—an jima suna tafiya kafin ya tsaya, a nan take hango gate É—in masallacin, ga mutane ana ta shige da fice dan a idar da sallar la'asar lokacin. Cikin zumuÉ—i da sanyin jiki ta fito, ta bashi kuÉ—in da suka yi sannan ta taka a hankali tana nufar gate É—in.
Tafiya take yi tana kalle kalle, ta san duk wanda ya ganta ya san faron zuwa masallacin ce, amma sai ta ga babu mai kallon ta kowa harkokinsa yake yi.
A sanyaye take takawa tana sake kallon ko ina, sai yanzu ta san ta shiga madina, dan Umma a ƙauyen Madina take. A haka ta riski inda banɗaki yake, ta ga mata yadda suke hawa excletor yana sauka da su banɗakin, itama ta bisu ta yi alwala ta fito ta yi sallah a harabar masallacin.
Babu inda ta sani, bata san kuma me zata yi a gaba ba. Tana zaune tana kalle kalle, sai kuma ta tashi ta shiga cikin mata ganin ana ahiga cikin masallaci. Shiga ta yi ta zauna ganin mata a zaune wasu suna addu'a wasu suna karanta alkur'ani. Ta zauna ta ɗauki alkur'ani tana karantawa har aka yi sallar i'sha tana ciki, yunwa take ji, amma saboda bata son fita haka ta maƙale a ciki gani take ksmar in ta fita bazata dawo ba.
Jin yunwar ta dame ta ya saka ta fito, ta si yi abinci ta koma harabar masallacin ta ci ta sha ruwa. Sai kuma ta miƙe tana zaga ko ina dan in ba haka ta yi ba bazata rage dare ba.
Tun daga farkon masallacin sai da ta kai ƙarshe, nan ta ga mata sun hau layi ita dai bata san me za a yi ba itama ta hau. Sai gashi ta shiga rauda wothout nusik permit, ita bata san ma rauda za a shiga ba, sai da aka shiga ɗin wannan ta ji hakan a zuciyarta.
Bayan sun fito ta dinga jin farin ciki yana ratsata, tunda ta zo ƙasar bata taɓa jin daɗi da alfaharin zuwa kamar lokacin ba.
Ta dinga yawace yawace, ta shiga binwood, ta shiga movepick har taba da wayar ta ayi mata hotuna.
Haka ta raba dare tana zaga ko ina, in ta ga wani hotel da ya yi mata kyau kawai ta shiga ta gama yawo da É—aukar hoto sannan ta fito.
Sai biyu na dare ta koma cikin msallacin, a nan bacci ya É—auke ta bata farka ba sai kiran farko na asuba. Duk da baccin da take ji haka ta fita ta yi alawa ta dawo ta fara sallah tana addu'a.
Sai bayan sallar asuba sannsn ta fito ta shiga banÉ—aki ta yi wankanta, ta canja kaya ta saka wasu kayan a cikin jakar. Ta so komawa Jeddah da safe, amma da ta tuna juma'a ce sai ta fasa, ta yi niyar sai bayan juma'a sai ta tafi.
Sai bayan an idar da juma'a sannan ta fara shirin tafiya, sai take ji kamar kar ta tafi, ta dinga jin zuciyarta babu daÉ—i kamar ta koma.
Ta ji daÉ—in zaman kamar ta cigaba da kwana kar ta koma, dan ita kam ko shekara zata iya yi a haka; ta kwana a masallaci abinta.
Har zata tafi sai ta fasa, ta sake komawa ta kwana asabar, ta saka sabuwar rigar da ta siya sannan ta fara shirin tafiya saboda marar ta da ta ji tana É—aurewa alamun period zata yi.
Duk sai hankalin ta ya tashi kar ciwo ya riske ta a haka, a station É—in ta si yi tucket na daidai kuÉ—in wancan, ta shiga ta zauna a seat number ta.
Idonta a rufe yake ruf, ta jingina da kujera tana jin yadda mararrta take É—aurewa tana rutse ido.
Ƙhamshin turaren wanda yake kusa da ita ya mamaye hancinta, sai ta ja facemask ta rufe hancinta, ta saka hannu ta kashe a.c inda take saboda sanyi, ta ja labule ta rufe window ɗin.
Babu jimawa sai ta ji an kunna ac, ta É—ago jajayen idanunta ta kalli wanda yake zaune a gefenta, a lokacin jirgi ya fara tafiya...........
Nana Haleema.
[7/19, 10:59 AM] KRBBK: RDB2P65
Nana Haleema.
Kansa yana ƙasa yana danna waya kamar bai san abinda ya yi ba, Islaha ta ɗauke kai ta sake kashe a.c, dan yadda kansa yake a duƙe kuma ya saka glasses bata gane waye a kusa da ita ba.
Ta sake komawa ta kwanta tana runtse ido cikin ciwon da ya fara takura mata. A lokacin train staff suka fara raba musu abin sha, Islaha idonta yana rufe bata sani ba, sai magana ta dinga ji a kanta sama-sama.
Sanyin ta sake ji ya dame ta, ta É—aga kai ta ga an sake kunna ac, ta waiwayo ta kalle sa a lokacin ya É—ago kai yana magana da wani da yake É—aya side É—in.
Yana juyowa suka haɗa ido, dan ya cire glasses ɗin idanunsa. Islaha gabanta ya yanke ya faɗi, ta yi saurin ɗauke kanta tana mamakin wacce irin ƙaddara ce take haɗasu ko yaushe? Ita ba wata danginsa ba, amma ko yaushe sai su haɗu. Bata ce komai ba, tacure a waje ɗaya, ta kifa kanta a jikinta tana kuka mai sauti.
Rehaan yana jinta, duk da ta rufe rabin fuskarta da face mask amma ya gane ta, haushinta ya sake mamaye masa zuciya. Ya ja tsaki ya ɗauke kai yana jin kukanta a kunensa, bai san ƙaddara da ta saka shi siyan ticket na kusa da ita ba, ji yake kamar ya miƙe ya koma wani wajan saboda takaici.
Kuka take yi sosai, sanyin ya yi mata yawa ga ciwon da yake damunta. Ta yi shiru bata ce komai ba, bata cikin yanayin masifa dan tana kan ciwo, sauƙi take nema, amma bata san inda zata same shi ba. Ga sanyi, ga ciwo, gashi bata da mai taimaka mata.
Muryar ta a sarƙe ta ce, "Don Allah ka kashe ac, zan mutu."
Banza ya yi mata kamar bai ji ba, bai ma motsa ba balle ta fahimci ya ji har ya kashe É—in.