Sashe 15
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zan kira Saheer na faɗa masa, ka kawo kuɗin da ya tara a haɗa a ga abinda za a yi. Daman ni da Islaha muka ce zamu karɓi loan a bank, to bamu kai ga karɓar bashin ba aka neme ta aka rasa."
Mama ta ce, "ba kace za a ba da jinginar gida ba?."
"Wallahi Mama an rasa wanda zai karɓa ya bamu kuɗin. Abin ne sai a hankali, mutane babu yarda a lamarinsu. Amma zamu yi magana da mai gidan mu ni da Saheer, ko gidan ne ya karɓa ya bamu kuɗin, tunda har aka fara haka gwara ayi aikin a huta kawai."
Adda ta ce, "Ta ya miliyoyin kuÉ—i zasu fito a wanann lokacin?."
"Mu cigaba da addu'a Allah zai dafa mana."
Mama ta ce, "Duk da haka Sadik, sai mun nema sannan Allah zai dafa mana. Baza mu zauna mu naɗe ƙafa mu ce Allah ya kawo mana wannan kuɗin ba, dole sai mun fita mu nema."
Sadik ya yi ajiyar zuciya, sun kasa gane ruɗanin da yake ciki ya ce, "In Allah ya yarda za a san yadda za a yi, tunda muka shigo nan ai baza mu fita ba, iya kuɗin wankin ƙodar da ake yi masa ma zaman kansa yake yi, dole mu biya su kafin mu tafi." Suka yi shiru kowa yana tunani, ya bar wajen ya tafi wajen Saleeem da yake yi masa waya.
Yana zuwa ya same shi a compound ɗin asibitin, ya ƙarasa ya ce, "Saleem ya ake ciki akan maganar Islaha?."
Saleem ya ce, "Wallahi babu wani update, har yanzu shiru, babu wanda ya kira ni a waya yace an ga mai kama da ita balle ita. Zuciyata tana faÉ—a min anya ba yan garkuwa da mutane ne suka É—auke ta ba?."
"Wallahi tunanina kenan nima, bana so na gasgata ne. Ga Baffa, ana neman kuɗin aikinsa daga nan zuwa gobe. Daman Islahan ce mai taimakmin akan neman kuɗin, gashi ta ɓace bamu san inda take ba. Abin ya yi min yawa, na rasa wanne irin tunani zan yi. Mama ta kira ni, Adda ta kira ni, dangin Baffa su kira ni, Saheer ya kira ni, gabaɗaya na ruɗe."
"Gaskiya ne, kana cikin ruÉ—ani mai yawa. Allah dai ya bayyana mana Islaaha, ya ba da ikon samo kuÉ—in nan."
"Amin. Amma tun farko mun san asibitin nan ya fi ƙarfin mu, ƙarfin zuciya da karanbani ne ya saka muka kai har yanzu a cikinsa."
Saleem ya ce, "to ya za a yi? Haka Allah ya rubuta zai faru."
Wayar Sadik ta fara ƙara, ya ɗauko wayar ta ga baƙuwar lamba ce, a yanayin da suke ciki na jiran waya ko yaushe baya ƙin ɗauka, ya ɗauka ya saka a speaker ya ce, "Hello."
Daga cikin wayar aka ce, "Muna magana da Sadik, abokin Saheer, saurayin Islaha?."
Gabansa ya faÉ—i sosai, ya kalli Saleem da yake sauraren wayar ya ce, "eh ni ne."
"Islaha tana hannun mu, mu ne muka É—auke ta."
Gaban Sadik ya faɗi matuƙa, cikin wani irin yanayi ya haɗɗiye yawu ya kasa magana.
Daga wayar aka ce, "Muna buƙatar kuɗin fansar ta naira miliyan ashirin, ko a bayar ko kuma mu kashe ta!."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Sadik ya faÉ—a cikin firgici yana saurare su.
"Kai kawo ta su ji muryar ta, dan su tabbatar da ita É—in ce a hannun mu."
Sadik ya nutsu yana so ya ji maganar Islaha, sai kuwa ga muryar ta ta ce, "Sadik!."
Gabansu ya faɗi sosai, tashin hankalin da bai taɓa ji ba yana ratsa shi, kafin su yi magana ya ce, "In an shirya kuɗin zamu faɗa muku yadda za a yi dashi. In ku ka saka hukuma a cikin maganar wallahi sai mun kashe ta!" Yana gama faɗa ya kashe wayar........
[6/19, 10:26 AM] KRBBK: RDB2P10
NanaHaleema.
Sadik da Saleem baki a buɗe suka bi wayar da kallo dukkansu cikin ruɗani da tashin hankalin da basu taɓa shiga irinsa ba. Ko a mafarki basu taɓa tunanin za a yi musu irin wannan wayar ba, sai gashi ta faru a lokacin da suke tsaka da tashin hankali.
Suka yi shiru na wani lokaci kafin Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Saleem kaji abinda suka ce fa."
Saleem ya sauke numfashi mai nauyi ya ce, "na rasa abinda zance ne Sadik, abin ya É—aure min kai. Muna jin irin wannan kalaman a wani waje, yau gashi yazo kan mu. Yanzu ya za a yi?."
"Mu je mu samu Dpo mu faÉ—a masa, babu zancen kar mu saka hukuma a maganar, dole mu saka su saboda mafita mu ke nema."
"Amma sun ce in aka saka Æ´an sanda zasu kashe ta, bai kamata mu saka hukuma a ciki ba."
"To Saleem muna da kuÉ—in da zamu basu ne? Da kuÉ—in fansar ta zamu ji ko da kuÉ—in aikin Baffa? Yanzu na faÉ—a maka halin da ake ciki akan aikin, gidana da nake ginawa, dana Saheer da yake yi zamu siyar a samu ayi abinda ya kamata akan lafiyar Baffa. Ban san taustsayin da ya kawo mu asibitin nan ba wallahi."
Saleem ya ce, "to mu je mu samu Dpo, Allah yasa bai tashi ba, dan dare ya yi."
Har Sadik ya ɗaga ƙafa zai fara tafiya ya ji wayar sa tana ƙara, yana dubawa ya ga Saheer ne, ya dafe kai ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Saheer ka yi haƙuri bazan iya ɗauka ba" ya faɗa yana kashe power wayar.
Ya kalli Saleem ya ce, "Saheer indai akan Islaha ne baya fahimtar komai, ba ya ji baya gani. In ya samu mummunan labarin nan yau bazai iya bacci ba, jininsa zai iya hawa wallahi."
Saleem ya ce, "mu daina ɓata lokaci, mu je mu samu Dpo." Bai musa ba suka fita aka shiga motar Saleem zuwa police station.
A can suka same shi yana niyar tafiya gida, ganin su da yayanayinsu ya saka ya zauna, suka zauna Sadik ya ce, "Ranka ya daÉ—e an kira mu a waya É—azu, yanzu haka mun tabbatar da garkuwa aka yi da Islaha, dan sun kira mu suna neman kuÉ—in fansa."
Dpo ya gyaÉ—a kai ya ce, "mu ga lambar."
Sadik ya ba shi lambar ya saka a wayarsa, sannan ya yi danne-danne ya saka a kunne ya ce, "Na turo maka wannan lamba, a bibiye ta yanzu nan" ya faÉ—a yana kashe wayar. Ya kalli Sadik ya ce, "ya ku ka yi dasu?."
Saleem ya ce, "sun tabbatar mana da tana hannunsu, dan har maganar ta mun ji, sannan sun ce in mu ka saka ku a ciki sai sun kashe ta."
Ya É—aga kai ya ce, "na san zasu ce muku haka daman, zasu faÉ—a muku abinda zaku ji taoro lokaci É—aya. Nawa suka nema?."
Sadik ya ce, "miliyan ashirin."
Cikin mamaki Dpo ya ce, "miliyan ashirin!?."
Sadik ya É—aga kai ya ce, "eh, miliyan ashirin. Sun ce zasu kira su faÉ—i inda za a kai kuÉ—in."
"Sun taɓa kiranka ne kafin yau?."
"Basu taɓa ba."
"Kuma kai tsaye suka nemi miliyan ashirin?."
"Haka ne."
Ya É—an yi shiru yana tunani kafin ya ce, "sun kira ka a yau kiran farko, kuma har sun faÉ—i kuÉ—in da suke so, naira miliyan ashirin bayan sun saka maka muryar Islaha. Sannan ya ce zai kira ya faÉ—i inda za a kai kuÉ—in, duk a yau..." ya faÉ—a cikin nazarin abun daki-daki.
Sai ya ɗan daki table ya ce, "ƴan garkuwa da mutane basa taɓa neman kuɗi ƙasa da naira miliyan ɗari, kai tsaye suna iya cewa suna neman naira miliyan ɗari biyu ko ɗari huɗu. Kuma basa fara faɗar kuɗin kai tsaye a kiran farko, suna kira su tabbatar maka mutum yana hannunsu, sannan daga baya su kira su faɗi adadin kuɗi....."
"Amma waɗannan kai tsaye sun neme naira miliyan ashiri kacal! A kiran farko, ba tare da ɓata lokaci ba."
Ya É—an kwanta akan kujera yana tunani kafin ya ce, "ba Æ´an garkuwa da mutane ne suka É—auke ta ba, tabbas an yi garkuwa da Islaha, amma ba garkuwa irin wacce aka saba ba a Nigeria ba. Wannan shirya ta aka yi, tsarawa aka yi kuma ba a yi tsarin yadda ya kamata ba."
Sadik ya ce, "amma ranka ya daÉ—e sune da kansu suka kira ni."
"Na sani Sadik, na faÉ—a maka an yi garkuwa da ita, amma ba Æ´an garkuwa da mutane bane. Tsarawa aka yi, ana sane aka sace ta. In ka tuna ta yadda aka sace ta zaka tabbatar da wannan plan ne."
Saleem cikin damuwa ya ce, "yanzu ranka ya daÉ—e me ake ciki?."
"In sun kuma kira ku cigaba da magana dasu, da zarar sun kira ku É—aya ya kira ni a waya a tura min lambar, ni kuma a lokacin zan bibiyi kiran dan na tabbatar da abinda nake zargi. Tabbas in ba yarinyar Ummi ce ta saka aka sace ta ba, akwai wasu a gefe da suka sace Islaha. Ko kuma wasu sun amfani sace ta É—in da aka ce an yi, suka kira ku suna neman kuÉ—i. Tunda maganar sace ta ta yaÉ—u, tsaf wasu zasu yi amfani da wannan dama su cika aljihunsu."
Sadik ya ce, "amma ranka ya daÉ—e naji muryar ta fa."
Ya É—an yi shiru ya ce, "kaima kamar ba É—an zamani ba? Ake haÉ—a hotununan mutane su yi motsi balle kuma murya?. Ko da yake, koma meye zamu binciko shi. Yanzu ku je gida, a daren nan zan samo matsaya akan case É—in nan."
Saleem ya ce, "kuma har yanzu ba a samu wayar ta ta shiga ba?."
"Wayar ta tana inda babu services, sannan an yi ƙoƙarin lalata duk wata hanya da zamu same ta. Wataƙila wayar bata tare da ita, garin a ɗauke ta wayar ta faɗi. In kuma wayar tana tare da ita ba ƙaramin expact ne ya ɗauke ta ba, dan sai mai ilimi da nazari ne zai yi ƙoƙarin kashe hanyoyin sadawar wayar ta."
Sadik ya sauke numfashi a sanyaye ya ce, "shikenan ranka ya daÉ—e, sai mun ji ka." Suka gaisa daga nan suka fita suka shiga motaa.