Sashe 19
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da suka bar wajan sannan ta kalle sa ta ce, "ina takardar biyan kuÉ—in aikin Baffa? An samu kuÉ—in?."
Shi dai kallon ta kawai yake yi dan bata yi kama da wacce aka sace ba, duk da fuskarta a ta É—an kumbura kuma ta É—an rame, amma babu wahala a tare da ita ko kaÉ—an. Ya kamata wahala ta bayyana a kan fuskar ta ko ya ya ne, amma shi bai ga wata alama da zata nuna ta sha wahala ba.
Ganin yaƙi magana sai ta ce, "Hamma Sadik kai nake jira."
Ya É—an sauke numfashi ya ce, "Naira miliyan biyar kawai aka samu, ita ce kawai a hannuna a halin yanzu."
Islaha ta fito da kuÉ—in daga jakar ta nuna masa ta ce, "wannan zasu isa?."
Gaban Sadik ya faÉ—i ganin rafar one hundrend dollors cikakkiya a hannunta. Ya bita da kallo cikin wani irin yanayi na firgici da mamaki ya ce, "Islaha!.....A ina kika samu kuÉ—in nan? Waye ya baki rafar dollors?."
Ta dafe kanta dan bata so maganar ta yi tsaho ta ce, "ka amsa min kawai Hamma Sadik, waÉ—annan zasu isa?."
"Akan me zan amsa miki bayan ban san a inda ki ka samu ba?....Islaha meye haka ne? Me nake shirin gani a tare dake? Kin fara bani tsoro, an nemi rasa, kwatsam kin dawo da waÉ—nanan kuÉ—in a hannun ki, me yake faruwa haka?."
Islaha ta ɗan yi tsaki, ta buɗe datar wayarta messages suka fara shigowa kamar hauka, ta san daman za a samu haka, saboda ta jima bata buɗe data ba, kuma ga yanayin da ta shiga wanda kowa ya ji labari, ta san za a dinga tura mata da saƙo. Wayar ta fara hooking, amma a haka ta shiga google ta yi converting one hundrend dollor to naira.
Bayan ta ga kuÉ—in dala É—ari, sai lissafa adadin kuÉ—in hannunta gabaÉ—aya, dala É—ari-É—ari sau É—ari, ta ga kuÉ—in hannunta miliyan sha bakwai ce da wani abun a lokacin.
Ita kanta sai da gabanta ya faɗi, bata taɓa kawowa yawan kuɗin ya kai haka ba, bata yi tunanin kuɗin su kai miliyan goma ba balle sama da haka, tsoro ya mamaye mata zuciya, amma sai ta daure ta zare takardar hannunsa, ta tafi wajan payment bata kula shi ba.
Shi dai ya kasa motsi yana kallon ta tana cike form, ƙarshe ta miƙa musu rafar dalar, suka karɓa tana yi musu magana suka bata takarda bayan an yi photocopy.
Ta kusa dashi ta wuce da sauri, ta nufi inda suke ajjiye suka ta bata file É—in Baffa ta saka a ciki payment bill É—in a ciki.
Wanda ya bata file É—in ya ce, "donar É—in yazo, yau a nan zai kwana."
Ta É—aga kai ta dawo wajan Sadik ta ce, "a kira Kawu, sun ce a nan zai kwana yau." Shi dai Sadik ya zuba mata ido ya kasa motsi sai kallon ta yake yi tana ta kai kawo daga nan zuwa nan kamar ba wacce aka sace ba.
Ganin ya kasa magana sai ta tafi wajan Mama ta faɗa mata sannan ta dawo wajan Sadik ta ce, "Yauwa na gama, zamu iya zuwa inda zamu je yanzu" tana faɗa ta ƙarasa wajan Safeera da Saleem suka fita.
Sadik ya biyo bayansu jiki a sanyaye, zuciyarsa tana faÉ—a masa abubuwa marasa kyau akan islaha, a haka suka shiga mota suka tafi wajan Æ´an sanda dan a sanar dasu ta dawo.
Babu wanda iya yi mata magana har suka je, suna zuwa wajan sa suka zauna. Dpo ya kalle ta ya ce, "Islaha barka da dawowa gida cikin aminci."
Ta É—aga kai ta ce, "yauwa barka."
"Islaha zamu so mu ji waÉ—anda suka sace ki, hankalin mu ya rabu gida biyu saboda abubuwan da suka faru. Jiya mun amsa kiran da aka ce sai an bada naira miliyan ashirin za a bada fansar ki."
Islaha ta sauke numfashi ta ce, "ni ba garkuwa aka yi dani ba, sace ni aka yi, amma ba masu garkuwa da mutane bane."
"To kenan su waye suka kira mu waya?."
"Wallahi ban sani ba, amma na tabbatar a inda nake, da inda aka ajjiye ni babu wanda zai yi waya ya ce a basa kuÉ—i."
"A ina aka ajjiye ki? Waye ya sace ki kenan?."
Ta É—an yi shiru tana sauke numfashi cikin wani yanayi, ta lumshe ido ta buÉ—e ido tana tunawa da in fa ta faÉ—a zancen kuÉ—insa zai fito, gashi ba a riga an yiwa Baffa aikin ba balle ta ce taci riba. Kuma kowa zai san ta É—auko masa kuÉ—i, ita kuma ba haka take so ba.
Ta kalle sa ta ce, "ni ban san sunansa ba, abinda na sani kawai ba ɗan ƙasar nan bane, dan ko kaɗan bai yi kama damu ba. Sannan yana da kyau sosai, sannan yana da dogon gashi, kamar balarabe ko ɗan india haka. An ajjiye ni a wani estate da bazan banbance ina ne ba, sannan an kashe services ɗin wayata, da aka fahimci ina video sai aka goge komai na wayar tawa, aka mayar da camerar waya ta blank, yadda bazan iya komai ba."
"Kuma babu hannun abokiyar aikin ki Ummi a ɓatan ki?."
Islaha ta girgiza kai ta ce, "Gaskiya bata da hannu ko kaÉ—an."
Dpo ya ce, "Amma ta yi iƙararin sai taga bayanki, bakya tunanin ita ta sace ki?."
Ta girgiza kai ta ce, "dan tace sai taga bayana ba hakan yana nufin zan yi mata sharri ko na É—ora mata laifi ba, gaskiya Ummi bata da hannu a sace ni É—in da aka yi."
Dpo ya ce, "Kuma gashi kin ƙi yi mana bayanyi yadda zamu gane waye ya sace ki. Meyasa bakya so mu sani? Bakya so a yi bincike a kai ne?."
Islaha a gajiye ta ce, "kamar yadda na faɗa maka wallahi ban san sunsan ba, in na sani zan faɗa maka, kuma bazan rantse akan ƙarya ba, fuskarsa kawai na sani a idona."
"Zaki iya yi mana bayanin fuskar sa mu tura a É—auko forensic sketch artist su zana mana shi?."
Ta ɗan yi shiru tana sauke numfashi, zuciyar ta tana tuna mata da kuɗinsa da yake hannunta, tabbas in yana da laifi itama tana da laifin aron kuɗinsa ba tare da ya sani ba. Da ace tana da kuɗin da zata bashi, da ta saka an zana shi ɗin kawai ko dan a kamo shi. Dan zata iya bada bayaninsa cikakke, tana hango fuskarsa yadda ya kamata a idanunta, ƙwaƙwalwarta ta riƙe fuskarsa sosai. Kuma tana da hoton Shams, in aka kamo Shams mai gidansa ya kamu. Babbar matsalar da zata hanata magana itace kuɗinsa.
Ta ɗan yi shiru kaɗan ta ce, "Ranka ya daɗe...." Sai tayi shiru bata ƙarasa ba.
Ya ce, "Ina jin ki, faÉ—i abinda yake bakin ki."
Islaha ta É—an lumshe ido kaÉ—an ta ce, "kawai a kulle case É—in nan."
Sadik da mamaki yake kallon ta ya ce, "kamar ya kulle case É—in? Islaha sace ki aka yi fa."
Dpo ta ɗaga masa hannu alamun ya ƙyale ta, ya kalle ta ya ce, "sun yi miki bazarana kenan, sun ce in muka ji labari sai sun kashe ki ko sun cutar dake, haka ne?."
Islaha ta yi shiru bata amsa ba, bata so ta amsa ƙarya ta zama gaskiya a wajensu, dan ta san ƙarya take yi in ta amsa.
Dpo ya É—aga kai ya ce, "Sadik kuje da ita ta huta ta samu nutsuwa, in yaso sai a dawo mu tattauna."
Islaha ta girgiza kai ta ce, "A nutse nake ranka ya daɗe, ina gane komai yadda ya kamata. Kawai tunda Allah ya bayyana ni a rufe case ɗin, bani da buƙatar a yi dogon bincike a kai. Ummi kuma bata da hannu a sace ni ɗin da aka yi, sannan waɗanda suka yi waya akan kuɗin fansa wasu ne daban a gefe, sun yi amfani da ɓatan da nayi suka kira waya suna neman kuɗin fansa, amma ni ba garkuwa aka yi dani ba" ta ƙarasa faɗa cikin sanyin murya tana kallonsu.
Nana Haleema.
[6/22, 9:41 AM] KRBBK: RDB2P13
Nana Haleema.
Dpo kallon ta yake yi yana nazarin yanayinta daki-daki, ya girgiza kai ya ce, "Tunda har kin tabbatar ba Ummi bace, kuma kike da tabbacin ba waÉ—anda suka sace ki ne suka yi waya ba, hakan yana nufin kin san waÉ—anda suka sace ki."
Ta É—an dafe kai ta ce, "Officer na faÉ—a maka na sani, amma ban san sunansa ba."
Dpo ya kalli Saleem da Sadik ya ce, "ku je da ita gida ta huta, zuwa jibi sai ku dawo mu cigaba da magana. Tana cikin ruɗani ne yanzu, wataƙila sun yi mata barazana."
Zata musa ya dakatar da ita ya ce, "Ki je gida, kar ki ce komai, kawai ki je." Bata iya cewa komai ba suka tashi suka fito daga office É—in suka koma mota.
Safeera ta dafa Islaha ta ce, "ni ban gane miki ba Bestie, meyasa zaki ce a kulle case É—in nan? Sannan su waye suka sace ki?."
Sadik ya kalli Safeera ya ce, "Safeera ba wannan zaki tambaya ba, tunda har Islaha tace basu Ummi bane, sannan ta ce waÉ—anda suka yi waya suma ba su ne, kin ta tabbata ta san waÉ—anda suka É—auke ta."
"Kuma da ta tashi dawowa babu wahala a tare da ita, babu wata kama da zata nuna mana an sace ta. Kuma sai ta dawo da bandle ɗin hundred dollors, cikakkiyar rafa da ta kai miliyan sha bakwai. Ba rafar dubu ɗaya ba, rafar dala ɗari. Da nayi converting dollor to naira a wayata, a yadda dollor ta yi tsada a yanzu, naira miliyan goma sha bakwai da wani abun ne a hannunta. Tana dawowa kai tsaye ta biya kuɗin aikin Baffa......" ya ƙarasa faɗa yana kallon ta.
Ya ce, "Islaha ta ya zamu amince da wannan abubuwan da mu ka gani a tare dake? Sace ki aka yi ko kuma tafiya ki ka yi?."
Saleem ya buÉ—e ido cikin mamaki ya ce, "Rafar dala fa ka ce?."
"Wallahi da gaske nake maka, yanzu maganar da nake yi ta biya kuÉ—in aikin baffa dasu."