← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 133

Sashe 95

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na ga record É—in ta a asibiti da komai, ta sha wrong medicine ne ya saka cikin ya zube. A ina ta samu ciki? Ko shima ni ne silar da ya saka ta yi?."

Jikin Jafar sai ya yi sanyi dan ya san bazai taɓa yi masa ƙarya akan Islaha ba. Jazy sai ya ji bai ji daɗin maganar ba, da gaske shi tausayi ta bashi shiyasa ya taimake, ta ashe ƙarya ta yi masa.

Ray ya ja tsaki ya ce, "ka daina yi min magana a kan wacce bata cikin rayuwata, a bar maganar don Allah, ka daina ɓata min rai."

Jazy ya ce, "na yi mamaki ne sosai, ban yi tunanin tana da ɓoyayyen hali ba, dan ni da zuciya ɗaya na taimaka mata." Ray ya miƙe ya bar masa wajan, dan shi ko tuna ta ma ba ya son yi ko kaɗan.

Nana Haleema.
[7/20, 10:27 AM] KRBBK: RDB2P69
Nana Haleema.

Islaha a hankali take tafiya da daddare akan titi, titin yana burge ta yadda komai yake cikin tsari, duk da akwai nisa da mall ɗin amma haka ta ke son zuwa a ƙafa saboda kawai titin yana burge ta.

Daidai wani shawarma and home of ta ga Jafar a tsaye, ta É—an yi jimm tana kallonsa dan bata so su haÉ—u, ba dan ya yi mata laifi ba sai dan É—an uwansa da take jin haushi. Ganin bai ganta ba sai ta É—auke kai tana fatan Allah ya sa kar ya ganta, dan bata san me zata ce ba.

A hankali ta ji an ce, "Miss Islaha."

Ta É—an runtse ido kafin ta juyo a hankali, ta kalle sa da murmushi ta ce, "Mr Jafar."

Ya yi murmushi yana kallon ta, ta ɗan ƙarasa kusa dashi ta ce, "ina yini."

Ya ce, "lafiya lau. Ina zuwa ke kaÉ—ai?."

Islsha ts ce, "zan je mall ne."

"Mall ɗin za ki je da ƙafa?."

"Uhum, ina son ganin gari ne kawai."

Ya É—an girgiza kai ya ce, "i through kina Nigeria."

Ta girgiza kai ta ce, "Jibi zan koma in sha Allah."

"Allah ya kaimu. Na tsayar dake, sai kin dawo, a yi min tsaraba." Ta É—an yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiya ta a hankali.

Jafar ya tsaya yana tunanin abinda Rehaan ya faɗa masa, ya san Rehaan bazai yi masa ƙarya ba, dan shi damuwar wani ba damunsa ta yi ba, ba ya shiga lamarin da bai shafe sa ba, tunda har ya faɗa ɗin ya san ta faru.

Amma Islaha bata yi kama da irin matan da yake kwantanta dasu ba, she looks very decent and neat, bata yi kama da abinda yake yawan faÉ—a a kanta. Abinda ya yarda dashi akan Islaha kawai bata da kunya, kuma tana da tsiwa, shima ba ko yaushe ba.

Lokaci na farko da ya ji bai yarda da maganar Rehaan ba, duk da ya san abinda ya faɗa masa ya faru, dan bazai yi ƙarya akan Islaha ba, amma ba a kan Islaha ba, sai dai in kuskure ko akasi aka samu a kan hakan. In itace wacce yake cewa ta yi sata a hotel da yanzu an kamata, tunda ba ɓoyayyiyar fuska ce da ita ba, tana da ɗaukakar da baza ta yiwa ɗan siyasa sata ya ƙyale ta. Kuma shi ba daga gidan Ubaid yake ganin ta ba, a gidan Maleek yake ganinta, hakan sai ya tabbatar masa da kuskure Rehaan ya yi.

Ya kawar da tunanin daga ransa, amma yana ji a ransa sai ya yanke ta a idanun Rehaan, ba dan wani abu ba, sai dan baka dan me gobe zata haifar ba. Ice cream da shawarma ya siya ya koma gida ya tarar da Rehaan yana shirin tafiya aiki, yana tsaye a gaban consool É—in falon yana gyara zaman necktie É—in wuyansa.

Ya yi kyau cikin black É—in suit, ya haÉ—e gashinsa a tsakiya, ga wani luxury watch da ya É—aura a tsintsiyar hannunsa. Jafar ya kalle sa ya É—auke kai, ya zauna a kan kujera yana waya da inda ya ba da order kayan da zai saka.

Sai da ya gama wayar Rehaan ya kalle sa ya ce, "kai kaÉ—ai ka ke siyayyar ka, ba ka faÉ—a min."

Jazy ya ce, "sau nawa ina faɗa maka kana avoiding ɗina? Shiyasa na ƙyale ka, bikina ne ba naka ba, ni ya kamata na yi duk abinda zan yi."

Ya gyaÉ—a kai ya ce, "bikin ka ne kam" ya faÉ—a yana É—aukar wayarsa.

Jay ya ce, "Kaima harda kai, tunda tare za a haÉ—a mu."

Hararar sa ya yi, hakan ya saka ya É—an yi murmushi bai ce komai ya fara cin shawarmarsa hankali kwance.

Rehaan yana sauka Mamy ta kira wayar Jafar, ganin video call ne sai ya gyara zama sosai kafin ya É—auka.

Fukar Mamy ta bayyana kan screen, ganinsa da ice cream da shawarma sai ta ce, "shan zaƙi, sanyi, ciye ciye duk ka iya Jafar."

Ya É—an yi dariya ta ce, "Ina yini Mamy."

Ta ce, "Lafiya lau Jazy, nima yau na zama Rehaan, na ce Jazy."

Ya yi murmushi Mamy ta ce, "Tunda mu ka yi magana da kai baka ce min komai ba, ya amince da zancen Ikram kuwa?."

Jazy ya ce, "Wallahi Mamy na yi masa, amma ina farawa ya ce shi baya so, Ikram ƙanwarsa ce ba zai iya auren ta ba."

Mamy da damuwa ta ce, "Jafar Rehaan ya girma fa, ga arzuƙin da Allah ya yi masa, aure ne kaɗai ya rage masa. Meyasa bazai amince ya auri Ikram ba? Duk wacce zata aure shi a yanzu dan kuɗi zata aure shi, amma ikram mun santa, mun san wacece ita."

"Mamy ko ni na faÉ—a masa, da yana zancen zai yi lissafi za a fitar da zakka nake faÉ—a masa ya kamata zuwa yanzu ya yi aure."

Mamy ta É—an yi jim kafin ta ce, "Ni na fara wani tunani Jazy."

Jafar ya ce, "na me kenan Mamy?."

"Anya yana da lafiya?."

Maimakon Mamy ta ji kunyar tambayar shine ya ji kunya, amma ganin ita ko a jikinta sai ya basar yana É—an murmushi ya ce, "waye ya sanar masa Mamy? Amma na tabbata lafiya lau yake, yana da ilimin da in bashi da lafiya zai nemi magani bazai zauna ba."

"Haka ne kam Jafar. Daman ni ya bawa damar zaɓa masa mata, kawai zan zaɓa nasa ita, koda zai zo ya ce baya so na san daga baya zai amimce. Zan yi magana da Ikram, in ta shirya aurensa za a yi bayan auren ku."

Jafar ya ce, "Mamy amma da kar a yi gaggawa,  ki bari ya amince ɗin. Kin san hali, ɗan rigima ne."

Mamy ta ce, "ƙyale ni dashi, bazan zuba masa ido haka ba. Ita wacce Daada zata aura masa bamu san wacece ba, wataƙila tana daga cikin waɗanda zasu so su ga bayansa saboda kuɗi. Ina so ya samu wacce zai samu peace of mind."

Jafar ya ce, "Shikenan Mamy, Allah ya zaɓa mana abinda ya fi alkhairi." Ta amsa da amin ta kashe wayar.

Jafar ya sauke numfashi ya ce, "za a sha rikici dashi kam, kafin ya karɓi auren nan za a jima sosai." Ya faɗa yana kiran Juwariyya, dan tunda Rehaan ya fita bashi da abokin hira, gwara ya kira ta su sha soyayya.

       ••••••

Daada tana zaune ita kaÉ—ai a falon ta, Abba ya shiga da sallama ya zauna a kan carpwt ya ce, "lokacin da ki ka aika in zo na shiga wanka, yanzu na fito."

Daada ta kalle sa ta ce, "akan maganar yarinyar nan da Muhammad zai aura, an sake komawa kuwa? Tunda ka ce min babanta yana asibiti baka sake cemin komai ba. Ka san da bikin Zuwairiyya nake so a haÉ—a, gabaÉ—aya biki yanzu bai wuce sati huÉ—u ba."

Abba ya ce, "Daada wanda take hannunsa ba mahaifinta bane."

Daada da mamaki ta ce, "waye É—in ta?."

Abba ya ce, "Yarinyar a gidan marayu ta tashi, bata san kowa nata ba, tana gidan ne a matsayin ƴar riƙo ba ƴar gida ba."

Abba sai ya ji shiru Daada bata ce komai ba, jin shirun ya yi yawa ya É—ago ya ga Daada tana hawaye.

Hankalin Abba ya tashi ya ce, "Daada lafiya,
Me ya faru haka? Na faÉ—i wani abun da ya saka ki kuka ne?."

Daada ta dakatar dashi da hannunta ta ce, "ashe shiyasa ta shiga cikin raina, shiyasa nake jin sonta har cikin jinina, ashe marainiya ce.
Allah sarki, maraya bawan Allah, Allah sarki Ishlaya, sai na sake jin sonta, sai na sake ji dole ma Muhammadu ya aure ta."

Abba ya É—an girgiza kai jin kukan ba wani mai babban dalili bane ya ce, "Zan saka a sake bincikawa in Allah ya yarda. Tunda kina so za a yi in Allah ya yarda, in mahaifin nata ya dawo daga asibitin za a je a same shi in Allah ya yarda."

Ta goge idonta ta ce, "haka nake so na ji, Allah ya nuna mana lokacin." Abba ya amsa ya tashi ya fita.

Abba yana fita ya shiga apartment ɗinsa, a zaune ya tarar da Mama tana jiransa, ya ƙarasa ya zauna ta ce, "ka dawo."

Ya É—aga kai ya ce, "Na dawo. Daada da rigima, wai batun auren Rehaan take yi da yarinyar nan. Ni da yake ban mayar da hamkali ba, tunda na saka a ka bincila sau É—aya ban sake bincikawa ba."

Mama ta ce, "Tunda ka ga ta dage akwai alkhairi a ciki, gwara ka saka albarka Allah ya sanya alkhairi."

"Maganar auren take yi a na nan da sati uku fa, Kawai sai na je na ce musu nan da sati uku zuwa huÉ—u É—ana zai auri Æ´ar ku?."

"Ai ba wani abun damuwa bane, akwai abinda za a dawata su dashi har a yi auren a wannan lokacin."

"Ba a yi binciken kirki a kanta ba, bazai yu ace daga nemo yarinya a yi aure babu bincike mai ƙarfi ba."

Mama ta ɗan ɓata fuska ta ce, "haka ne kuma" ta faɗa dan kar ta musa ya yi saurin gano ta
Chapter 95 · 0% Book details