Sashe 4
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hanan ta ce, "Islaha bata kwana a gida ba, hasalima ba a san inda take ba."
Safeera ta zaro ido waje ta ce, "kamar ya ba a ganta ba, kamar ya ba a san inda take ba? Ku yi min bayani."
Sadik ya ce, "abinda ki ka ji shine gaskiya, bamu san inda Islaha take ba. Dalilin zuwan mu nan mun yi tunanin kuna tare."
"Innalillahi! To ina ta je? Ko tana orphanage?."
Sadik ya kalle ta ya ce, "tana zuwa can ta kwana ne?."
"Gaskiya tunda ta bar gidan bata taɓa kwana ba. Na shiga uku, ina Islaha ta tafi?. Bara na kira Zainab ƙanwarta ta gidan na ji ko suna tare" ta faɗa hannunta yana rawa ta kira Zainab ta saka a speaker.
Daga can ɓangaren Zainab ta ɗauka ta ce, "Adda Safeera ina kwana?."
Safeera cikin rashin nutsuwa ta ce, "lafiya. Zainab kuna tare da Islaha ne?."
Zainab ta ce, "A'a, ina ta nemanta nima, ko a waya na kasa samunta."
Safeera ta ce, "Na gode" ta faÉ—a tana kashe wayar.
Safeera ta kalli Sadik ta ce, "ina Islaha take? A ina ta kwana?" Ta faÉ—a hawaye yana sakkowa akan fuskarta.
Sadik ya ce, "kwantar da hankalin ki Safeera, zamu ganta in sha Allah."
Safeera ta fashe da kuka ta ce, "Islaha bata kwana a wani wajen sai a Hamma Sadik, bata zuwa ko ina. A ina ta zauna haka, Ina ta je?."
Ya yi ajiyar zuciya bai ce komai ba, dan abin ya ɗaure masa kai, ya rasa inda Islaha ta shiga, duk inda ake tunanin taje bata can. A lokacin Saleem ya ƙaraso wajan yana kallonsu.
Ganin yanayin da suke ciki ya saka ya ya ce, "Sadik lafiya na gan ku haka?."
Sadik ya ce, "Islaha ce ba a gani ba, tun dare jiya ba a sake samunta a waya ba. Kuma duk inda muke tunanin zata je ta kwana bata nan."
Saleem ya zaro ido ya ce, "ban gane ba, wacce Islaha kenan?."
Safeera ta ce, "Islahata, Islahata ce ba a gani ba. Ina ta shiga?" Ta faÉ—a cikin kuka mai tsanani tana kallonsa.
Saleem ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ba a san inda take ba, kuma bata faÉ—awa wani zata je wani waje ba?."
Sadik ya ce, "da zata je zata faÉ—a min, tunda yanzu ko yaushe muna tare."
Kira ya shigo wayar Sadik, ya duba ya ga Saheer ne, ya kalle su ya ce, "Ga Saheer yana waya, na tabbata ya neme ta bai same ta bane shiyasa ya kira ni."
Saheer ya É—auka ya saka a speaker, Saheer ya ce, "Sadik kuna tare da Islaha ne? Tun jiya nake kiranta bata shiga kwata-kwata. In kuna kusa haÉ—a ni da ita don Allah."
Sadik ya sauke numfashi ya ce, "Ba ma tare, amma in mun haÉ—u zan faÉ—a mata sai ta kira ka."
"Yauwa kar ka manta don Allah. In ka je asibitin ka É—auko min hoton Baffa ka turo min. Zuwa jibi zan dawo in sha Allah."
Sadik ya ce, "to, ina zuwa" ya faÉ—a yana kashe wayar.
Sadik ya kalle su ya ce, "tabbacin wani abun ne ya samu Islaha, dan da akwai inda zata je da zata faÉ—awa Saheer ko Safeera."
Saleem ya riƙe haɓa cikin tashin hankali ya ce, "abu kamar wasa, Islahan ce ba a gani ba?."
Safeera dai kuka take yi kamar ranta zai fita.
Sadik ya ce, "ba tsayawa zmau yi a nan ba, mu je mu bincika ko zamu same ta a wani waje, in ta kama mu bada cigiya."
Saleem ya ce, "gaskiya ne kam, mu je mu duba."
Safeera ta ce, "nima zan je."
Saleem ya ce, "ki koma gida, duk abinda ake ciki zan faÉ—a miki."
"A'a, ina so in je, don Allah mu tafi tare."
Suka nufi motar Sadik, Saleem ya bar tasa a wajan suka shiga suka tafi, Hanan ta shiga gida.
Hanan ta shiga ta faÉ—awa Mama abinda yake faruwa. Mama ta ce, "ban gane ba a ga Islaha ba, ina ta je?."
Hanan ta ce, "wallahi ba a sani ba. Duk inda ake tunanin zata je bata nan."
"Ikon Allah, har gidan marayun bata can? Akwai yayyenta da suka yi aure fa, duk zata iya zuwa gidansu."
"An kira iya wanda aka sani, amma bata nan."
Mama ta É—an yi shiru ta ce, "to ina yarinyar ta je? Gashi dai bata kwana a waje balle na ce harka ce ta yi kyau, duk tsiya da iskancin sai ta dawo. Gaskiya akwai alamar tambaya a lamarin nan, akwai abinda ya faru."
Hanan ta É—an yi shiru, duk da basa shiri da islaha amma ta ji babu daÉ—i akace ba a ganta ba.
   Su Saleem asibitin suka je, suka ƙarasa wajan ma'aikata suka yi musu bayani abinda ya faru, suka nemi ganin cctv amma suka hana suka ce sai an zo da hukuma. Dole haka Sadik ya koma ya kai report wajan hukuma mafi kusa, aka basu ɗan sanda ɗaya suka taho sannan suka amince aka shiga camera room ɗin.
ÆŠaki ne babba, É—aki ne mai É—auke da tv guda biyar, ko wacce da inda take haskawa. ÆŠakin kamar É—akin camera turawa, komai ana gani a tv.
Wanda yake aiki a wajan ya ce, "ina ku ke sm gani?."
Sadik ya ce, "Jiya da daddare, misalin ƙarfe takwas na dare. Wajan asibitin nan mu ke so."
Bai musa ba ya danna ya dawo da lokacin, suka fara ganin abinda yake faruwa. Sai ga fitowar Islaha daga asibitin ta miƙe hanya tana tafiya.
ÆŠan sandan ya ce, "camera ta gaba."
Ya saka ta gaba inda ta É—an tsaya cikin tsoro kafin ta cigaba da tafiya. Tana shiga wajan duhun ya kalle su ya ce, "daga iya nan cameras É—in mu suka daina aiki."
Sadik ya ce, "wayyo Allah, don Allah babu wata ma'aikata ko bank a nan kusa da zasu iya É—aukar mana abinda faru?."
Ya girgiza kai ya ce, "gaskiya babu. Asibitin nan ne kawai a wajen nan."
Kowa ya yi shiru cikin tunani, basu da yadda suka iya dole suka fito daga ɗakin. Suna fitowa wayar Saleem ta yi ƙara, ya duba ya ga Muslim ne sai ya ɗauka.
Muslim ya ce, "Saleem ba ka shigo bane? Chairman yana ta faÉ—a kai da Islaha ba ku zo ba."
Saleem a raunane ya ce, "Muslim wallahi Islaha ce ba a gani ba, yanzu haka muna kan neman inda take."
Muslim da mamaki ya ce, "kamar ya ba a ga islaha ba kamar wata tumatur? Ban gane ba."
"Abinda ka ji shi na faÉ—a, an nemi Islaha an rasa."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. A ina hakan ya faru?."
"Ganin ta na ƙarshe a nan Nadira Hospital ne, ta fito ta hau kan hanya mara haske, daga nan ba a sake ganinta ba har yanzu."
Mulsim ya cw, "subahanallahi! Wannan ai ba maganar da za a yi shiru ba ce. Bara a samu hotonta a yaÉ—a ko wani ya ganta."
Saleem ya ce, "wannan shawara ce mai kyau, mu ma mun je wajan yan sanda mun yi report."
Muslim ya katse wayar da hanzari shi kuma Saleem ya sauke ajiyar zuciya dan bai san me zai yi ba.
Sadik ya ce, "yanzu meye abin yi?."
"Cigiya zamu bayar kawai, baza mu yi sake ba, gwara mu bayar da wuri ko za a saamu wanda ya ganta."
Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allah ka nuna mana wannan baiwa ta ka, Allah ka bayyanata cikin aminci."
Saleem ne kawai ya amsa, ita kam Safeera kuka take yi kamar ranta zai fita, hawayenta yaƙi tsayawa, da ta motsa sai hawaye sharr.
A haka Adda Sa'id da ta gansu ta zo wajan, itama tana jin lamarin ta fashe da kuka cikin ruɗani da tashin hankalin da basu taɓa shiga irinsa ba.
****
Muslim yana kashe wayarsa ya shiga office wajan Ummi, ya same tana bacci akan table, ya É—an buga table É—in ya ce, "ke tashi!."
Ta É—an buÉ—e ido ta ce, "me zan yi? Ina baccina ka tashe ni."
"Dallah ki tashi ki ji."
Ta miƙe zaune tana yamutsa fuska ta ce, "meye?."
"Islaha aka nema aka rasa, tun jiya ake nemanta ba a same ta ba."
Ummi baccin da yake kanta ya wartsake ta ce, "kamar ya ba a ganta ba?."
"Wallahi ba a ganta ba, an nemi inda take a rasa."
"Kana nufin masu garkuwa da mutane ne suka kamata?."
"Waye ya sani? Yanzu Saleem yake tabbatar min da an neme ta a rasa, wayarta kuma bata shiga. Kuma bata taɓa aikata hakan ba."
Ummi ta ji wani irin daÉ—i ya mamaye mata zuciya, ta kalle sa ta ce, "kuma ba aikin ka bane?."
Ya girgizs kai ya ce, "ko É—aya, ni ai na faÉ—a miki target É—ina. To a jiyan dai na aika, kuma wanda na tura a gabnasa aka ja islaha aka saka ta a van. Abinda ya saka ban faÉ—a ba na É—auka ceton ta suka yi daga hannun mu, ashe suma da tasu manufar."
Ummi ta kasa ɓoye murnarta ta ce, "kana nufin a gaban wanda ka tura ya watsa mata acid aka ɗauke ta?."
"Wallahi kam. Ni tun jiyan na sani, so nake na ji ta inda maganar zata ɓullo."
Ummi ta miƙe tsaye cikin tsananin murna tar tana taka rawa, ta rufe fuskarta da hannunta ta ce, "wayyo Allah! Daɗi zai kashe ni Muslim. Islaha ta tafi, ta tafi kenan in Allah ya yarda."
Muslim ya ce, "dallah ki yi a hankali, yanzu ni ake jira zan faÉ—awa Chairman za a yaÉ—a hotonta ko wani ya ganta."
"Baza a yi hakan ba, kar ka yaɗa hotunanta don Allah. Ka ƙyaleta ta je can ta ƙarashe rayuwarta a inda take. Bana fatan Islaha ta dawo garin nan balle ta dawo gidan nan, bana ƙaunar ta dawo, dan haka babu wani nemanta da zaka yi."
Muslim ya ce, "hakan ya zama dole Ummi, in bamu yi ba za a zarge mu. Dole mu nuna bamu ji daɗin ɓacewarta ba, in ba haka ba za a ga kamar muna farin ciki da hakan ne."