← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 133

Sashe 56

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adda ta ce, "to waye ya sace ta É—in?."

Ta ɗage kafaɗa ya ce, "shima taƙi faɗa, sai ta ce wai bature ne baya jin yaren mu. Ya ɗauke ta har na tsahon kwanaki, ya ajjiye ta a gidansa yana bata abinci mai kyau tana kwana a ac, ya rabu da ita ba tare da ya riƙe ko hannunta ba. Ita kuma da yake ga shugabar masu shirme, da ta tashi dawowa sai ta ɗauko masa kuɗi masu yawan da ta biya kuɗin aikin Baffa. Magana ake ta miliyan sha ba ƙananun kuɗi bane, don Allah da wanne ido zan kalli maganar nan? Da wanne kunne zan ji wannan dramar ta gamsar dani?."

Adda ta É—an yi jim kafin ta kalle sa ta ce, "kana zargin Islaha ta aikata wani abu ne ta samo wannan kuÉ—in?."

Ya girgizs kai ya ce, "ko kaɗan ban taɓa zarginta ba, itace take neman saka min zargin ta a zuciyata Adda. Ta tafi da sunan an sace ta, ta dawo da kuɗi masu yawa, taƙi faɗar wanda ya ɗauke ta, ta ƙi faɗar dalilinta, sannan ta ce a rufe maganar. Yanzu ta bar ƙasar da niyar wai zata biya bashin da ta ɗauko. Don Allah ko Ihsan ɗin ki aka faɗawa wannna maganar zata amince?."

Adda ta ce, "ni abinda nake so na ji, me ta yiwa wanda ya É—auke ta har ya saka aka sato masa ita? Sannan da ya sace ta kawai ajjiye ta ya yi yana bata abinci?."

"Hmmmm! Kema dai kya tambaya, ajjiye ta kawai ya yi yana bata abinci tana bacci, da ta tashi dawowa kuma sai ga kuÉ—i."

"Ka faÉ—a min, me ya haÉ—a su?."

"Ta ce wai faÉ—a suka yi, rashin kunya ta yi masa a hotel, lokacin da ta je neman Mr Rehaan Yola, sai kuma a asibiti. Na rasa wanne irim tunani ma ya kamata ace na yi."

Adda ta sauke numfashi ta ce, "indai da gaske baka zarginta kamar yadda kace to ya kamata ka amince da abinda ta ce, kaine mutum na farko da zaka fara b da shaidar ta, in da Islaha Æ´ar iska ce zuwa yanzu kowa ya sani, kai kanka ko zuwa yanzu in baka zama É—an iskan ba to ka rabu da ita. Ni a jikina ina ji maganar ta gaskiya ce, duk abinda ta yi ta yi ne saboda mahaifinka. Na san halin islaha da gaggawa, wani lokacin sai bayan ta aikata abu take zuwa ta yi nadamar hakan. In zuciyar ta tana son abu kawai tana aikatawa ne nan take, kar ka yanke mata hukunci cikin rashin sani, islaha bazata yi wani abu mara kyau ba."

Ya kalle ta ya ce, "kawai rashin kunya sai ya saka a sace mutum?."

"Eh mana, ai baka san wanda ta taɓo ba. Kuma ka san halin kayar ka, ba kunya ce da ita ba ko kaɗan. Tana da tsiwa mai yawa, zata aikata abinda ya fi haka ma. Kuma wani saboda haka zai iya sace ta, ba lallai sai ya yi mata komai in ya ɗauke ta ba. Ai ba ko wanne namiji ne yake ɗaukar mace dan ya yi amfani da ita ba, wataƙila shi ya ɗauke ta dan kawai ya yi mata gargaɗi."

"Kuma sai ta satowa mutum kuÉ—i?."

Adda ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Saheer zuciyar ka ta daina rawa akan Islaha, ni wallahi na amince da ita. Ka fi kowa sanin yadda bata ƙaunar aikin nan, ba tun yau ake yi mata talla tana ƙi ba, ƙaramin dalili bazai saka ta cilla kanta a cikin wannan yanayin ba. Ka tsaya ka saurare ta."

Saheer ya taɓe baki yana ajiyar zuciya ya ce, "ni na yi blocking ɗinta, bani da lokacin yin magana da ita a yanzu."

Adda ta ce, "kar ka yi haka, ka yi haƙuri ka tausaya mata don Allah."

"To ni an yi min adalci kenan? Ta bar ƙasa ban san lokacin da zata dawo ba. Me take yi a can, a hannun wa take, wacce irin rayuwa take yi duk ban sani ba. Auren ta zan yi fa, itace nake mafarkin ta zama mahaifiyar yaran da zan haifa a duniyar nan, meyasa zata yi min haka?."

Adda ta tausasa murya ta ce, "bata kyauta ba, amma ka yi haƙuri."

"In na yi haƙurin yaushe zata dawo? Ina da kuɗin da zan je na ɗauko ta ne Adda?."

Adda ta kalle sa jin muryarsa ta yi sanyi, sai ya bata tausayi, dan ta san Saheer yana son Islaha sosai. Ta É—aga masa kai ta ce, "komai warware in sha Allah, ka yi magana da ita don Allah, na tabbatar tana tare da damuwar rashin kula ta É—in da baka yi."

Ya kalli gefensa sannan ya ce, "na ce mata me? Na faÉ—a mata tsarabar da zata siyo min, ko na ce mata a ina take aiki, ko na ce mata aikin me take yi?."

Adda ta ce, "Haba Saheer, ban sanka da mita ba, ka bar maganar nan, ka je ka yi magana da ita ka ji?."

Ya kalle ta ya ce, "kin san mahaifin Safeera ya saki babarsu saboda tafiyar nan?."

Adda ta zaro iso ta ce, "ban gane saki ba, wanne irin saki?."

Ya taɓe baki ya ce, "Wallahi ya sake ta, ya faɗa mata sai babu igiyar aurensa a kanta sannan zata tafi, kuma ta tafi ɗin shi kuma ya sake ta."

"Innalillahi! Me Mama ta saka ta aikata ne haka?."

Saheer ya ce, "lamarin Mama sai addu'a kawai, amma abim yana yi min ciwo sosai. Ta raba aure guda saboda wani banzan aikin da ba duniya zaka je ka samo ba."

Adda ta ce, "ban da abin Umma meye na tafiya? Da girmanta da komai don Allah." Bai ce komai ba ya fita daga gidan ita kuma ta shiga cikim gidan.

******

     Safeera a gaggauce ta shiga gida, tana shiga ta tarar da Gwaggonsu ƙanwar Baba tana gidan.

Ta yi murmushi ta ce, "Gwaggo ina yini."

Ta yi murmushi ta ce, "lafiya lau Æ´ar jarida. Ya na ga ki a firgice haka?."

Safeera ta ce, "Baba yana azumin tsakiyar wata, zan dama masa kunu, ya ce min baya jin daɗin na Ruƙayya, shiyasa nake saur" ta faɗa yana ajjiye mayafinta.

Ruƙayya ta ce, "Adda ai Maman su Kausar ta aikowa da Baba kunu, gashi nan na kai masa ɗakinsa."

Safeera ta ji daÉ—i a ranta ta ce, "da gaske?."

"Wallahi da gaske, harda da ƙwai ta soya masa. Kuma daman na yi masa fanke mara sugar irin wanda yake so."

Safeera ta zauna tana ajiyar zuciya ta ce, "kai amma na ji daÉ—i sossi, a gagaguce na dawo wallahi saboda aikin Baba."

Gwaggo ta ce, "ai ya faɗa min zancen ƙawar Babar ku, tana da kirki sosai, bata jima da fita daga nan ba."

Safeera ta yi murmushi ta ce, "tana da kirki sosai Gwaggo, baki ga yadda take yi mana ba wallahi, tana kula damu sosai kamar sun haÉ—a jini da Umma."

"Ta kyauta, haka ake son ƙawa ko aboki su kasance na gari. Tunda ita uwar taku ta watsar daku ta tafi gantali ita ta sani." Basu ce komai ba suka yi shiru.

Gwaggo ta ce, "Baban na ku nake jira ya dawo mu gaisa sai na wuce gida."

Suna nan zauna suna ta hira sai ga Mama Atika ta shigo da sallama. Suka gaisa da Gwaggo cikin sakin fuska, ta miƙawa a Gwaggo kwano ta ce, "Tuwon alkama nayi, shine na miki."

Gwaggo ta karɓa ta ce, "kai amma na gode sosai Atika, Allah ya bar zumunci."

"Amin Gwaggo."

"Da haka ake samun ƙawaye masu kula da yaran ƙawayensu da an more wallahi, ke kam kin yi dace abin ki." Ta yi murmushi bata ce komai ba, a lokacin Baba ya shigo.

Har ƙasa Atika ta zube tana gaishe sa, ya amsa da sakin fuska ya ce, "Ya hidima Atika?."

"Alhamdu lillah, ai babu komai."

"Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa da amin tana murmushi.

Gwaggo ta ce, "ka ga kaɓakin arzuƙin da aka aiko min dashi, tuwon alkama da miyar kuɓewa harda man shanu. Bayan ta aiko maka da kunun buɗa baki, har su doya da ƙwai."

Baba ya cika da mamaki, wannan dafe-dafen abincin da Mama Atika take yi ya yi yawa, ya ce, "Atika kar na É—ora miki nauyi fa, hidimar nan ta yi yawa. Iya saurraren yaran da ki ke yi ma ya isa, dan Allah ki daina hidimar dafe dafen nan."

Ita dai murnushi take yi sannan ta ce, "Babu komai Baban Safeera, duk an zama É—aya. Kuma ina dashi ne shiyasa nake yi, da babu da bazan yi ba." Baba

ya ce, "duk da haka dai ki É—an rage, kar hidimar ta yi yawa." Bata ce komai ba sai murmushi da take yi.

Mama Atika kalli Gwaggo ta ce, "Gwaggo zan koma, na bar Kausar ita kaÉ—ai."

Gwaggo ta yi murmuahi ta ce, "To Atika, Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa da min ta miƙe ta fita daga gidan.

Baba suka gaisa da Gwaggo kafin ya shiga ciki ya yi alwala ya fito ya je masallaci, bayan an idar ya dawo ya shiga É—akinsa yana cin abinci.

Ba jimawa Gwaggo ta shiga ta same sa ya gama cin abincin yana zaune. Gwaggo ta zauna ta ce, "har ka gama buÉ—e bakin?."

Ya É—aga kai ya ce, "Na gama Gwaggo, yanzu zaki wuce?."

"eh yanzu zan wuce, jira nake É—an wajan naka ya zo ya É—auke ni. Amma kafin nan ina da wata magana."

Baba ya ce, "ina jin ki Gwaggo."

"Matar ka ta watsar da ƴaƴanta ta tafi yawon gantali, zaman yaran nan su kaɗai in baka nan akwai damuwa tunda ba namiji ne a gidan ba. Kuma ana so duk inda ƙarami yake ya kasance akwai babba a tare dashi."

"Gwaggo kullum da tunanin nan nake kwana nake tashi, yanzu haka nan da sati biyu zan yi tafiya, amma ban san ya zan yi ba. Ina ta tunanin ko na tura su Katsina sai na tuna da aikin Safeera da makaratar su Rukayya, sai na yi tunanin gidan ki sai kuma na ga kar hiidmar ta yi miki yawa. Na dai rasa inda zan aika su."
Chapter 56 · 0% Book details