Sashe 63
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma cikin kuka ta ce, "Na gaji Atika, gida nake son dawowa. Na gaji da zama a nan, aikin ya fita daga raina, ina so nazo na riƙe ƴaƴana. Wahala nake sha, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Na gaji wallahi."
Atika ta ce, "da wuri haka? GabaÉ—aya kwanan ku nawa da tafiya da ki ke son dawowa? Ko har kin tara da yawa ne?."
"Wallahi babu abinda na tara, hasalima bani da ko sisi a hannuna. Ɗazu layin waya na je siya, sai ranta min kuɗin aka yi dan bani da komai. Na gaji Atika, Ki ta ya ni da addu'a, Allah ya kuɓutar dani daga hannunsu."
"Kin san dawowar ki yanzu bazai yu ba ko? Dole sai kin gama biyan waÉ—anda suka kai ki kuÉ—insu ko?."
Kukan Umma ya ƙaru ta ce, "na sani, shiyasa na ce ki taya ni da addu'a."
Atika ta ce, "ki yi haƙuri, zaki saba a hankali."
"baza ki gane halin da nake ciki ba. Ga wahala, ga fargaba, ga tsawa, ga aiki, ga raini. Haka kawai zan buÉ—e ido na ga magidanci tsirarara a gabana. Ya zan yi?."
Atika ta ce, "haƙuri zaka yi, a hankali komai zai zama labari."
Umma ta ja numfashi ta ce, "Safeera har yanzu fushi take yi dani, ki bata haƙuri ki ce ko sau ɗaya ne ta yi magana dani."
Atika ta ce, "zan yi mata magana in na shiga gidan. Ki cigaba da haƙuri, ki ta addu'a, Allah ya kare ki daga sharrin shaiɗanin can."
Umma ta ɗaga kai kamar tana gabanta ta ce, "ki ta ya ni, ki saka su Rukayya su ta ya ni. Ina so na nemi afuwar su Yayan Katsina ban san ta ya zan fara ba."
Atika ta ce, "Allah zai kawo mafita, ki cigaba da haƙuri." Umma ta amsa suka yi sallama zuciyarta cike da abubuwa kala kala......
Nana Haleema.
[7/7, 6:25 PM] KRBBK: RDB2P43
Nana Haleema.
_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L
••••••••••••
*YOLA.*
"Ummi meyasa bakwa yin aiki yadda ya kamata ne? Har yanzu Æ´an kallo complain suke yi akan rashin Islaha, mun rasa mabiya da yawa saboda rashin ta. Da Saleem ya duba shafin mu na tiktok mutane sama da dubu uku sun yi unfllowing É—inmu saboda rashin fuskar Islaha. In mu ka yi posting a ko yaushe magana É—aya ce, su dai a dawo da Islaha ko su daina bibiyarmu. Shirin Rayuwatatalkshow views sun ragu sosai, lokacin da Islaha tana nan sai a samu masu kallo sama da dubu É—ari biyar, amma tun bayan tafiyar ta ba a wuce dubu hamsin, wani har dubu ashirin. Me yake faruwa ne?."
Tunda ya fara magana Ummi da Jamila suka yi shiru, sai da ya gama sannan Jamila ta ce, "Chairman tsakani da Allah sun fi son fuskar Islaha, saboda son da masu kallo suke yi mata ya saka ta sama permanent a ɓangaren interview da talkshow, sai ta ƙure ake canja ta a ɓangaren. Ba laifin bane, mun iya aiki daidai ƙarfinmu, kawai zuciyarsu tana tare da Islaha ne shiyasa ake samun matsala. Kuma baza mu maye gurbinta ba, sai dai mu yi abinda zamu iya."
Chairman ya ce, "Yanzu haka za a cigaba da zama kenan? Muna samun masu kallo dubu ɗari uku zuwa ɗari mun dawo dubu ashirin?. Ko interview ɗin da Muslim ya yi da minister tsaro akan satar yaran nan, har yafi interview ɗin Ummi views. Asara mu ke ta tafkawa, kwata-kwata bata yi sati uku da tafiya ba, amma muna ta samun naƙasu akan harkokin mu."
Ummi ranta ɓaci yake yi, baƙin ciki da hassadarta suka sake ninkuwa fiye da baya, hassada ta ɗaure mata harshe ta kasa cewa komai balle ta yi magana.
Chairman ya ce, "ina magana Ummi kin yi yi shiru."
Daƙyar ta buɗe baki ta ce, "To Chairman na rasa me zan ce ba, gani ka ke kamar ba ma yin ƙoƙari a aikin nan, ka manta tun kafin Islaha mu ne muke tafiyar da komai yadda ya kamata, zuwan ta ne ta asirici kowa ya zama babu mai son fuskar mu sai fuskar ta."
"Ke Ummi bana son shirme, wanne irin asiri kuma?."
Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, shi kuma ya ce, "baza ki iya bakin ki ba? Baki daddara da abinda ya faru ba ko?."
"Chairman ai ba wani abun na ce ba, gaskiya ce ba wani abun ba."
Chairman ya ce, "ke ki ka sani kuma, ni dai in aka cigaba da samun akasi wallahi zan canja ku gabaÉ—aya na zuba wasu. Bazai yu na dinga asara saboda ku ba."
Jamila a tausashe ta ce, "ka yi haƙuri Chairman."
Ya ja tsaki ya ce, "ku je. Sannan ku aiko min da Safeera."Basu jima da fita ba Sfeera ta shiga da sallama.
Ta ce, "Chairman gani."
Chairman ya ce, "Safeera ban tabbatar rashin ƙawarki zai taɓa mu har haka ba sai yanzu da mu ke ta samun raguwar mabiya. In ki ka duba comments section zancen Islaha ne, in bamu dawo da ita ba su dai zasu daina bibiyar mu."
Safeera ta ce, "ina lura da komai Chaairman."
"babu batun dawowar ƙawar ki nan kusa Safeera? Kina gani bata rufe sati uku ba har yanzu, amma mun rasa mutane masu yawa. Ya ki ke ganin abinda zai kasance in ta sake kwanaki bata nan?."
Safeera ta ce, "In sha Allah baza a sake rasawa ba, zan tambaye ta in na koma na ji yaushe zata dawo, in sha Allah zata dawo a cigaba da komai kamar yadda aka sa ba."
"Don Allah ki tambayar mana ita, rashinta zai iya sakawa mu rasa abubuwa da yawa. Guest uku muka kaiwa katin gayyata amma sun bamu uzuri, abinda bai taɓa faruwa damu ba kenan. Da zarar Islaha ta kaiwa mutum iv yake saka mana lokaci, wani ma shi zai ce ta saka lokacin da ya yi mata. Don Allah ku yi magana da ita."
Safeera ta ce, "in Allah ya yarda zamu yi magana, zata dawo komai zai dawo."
Chairman ya ce, "na gode Safeera, ki je ku cigaba da aiki."
Lokacin da ta fito office ta koma, tana shiga Saleem yan shigowa ta kalle sa ta ce, "Chairman ne ya yi min magana akan rashin Islaha, ba ka gani ba kamar ya yi kuka. Da yana da iko da ya yi fuffuke ya je ya É—auko Islaha ta dawo, ta É—ora daga inda ta tsaya."
Ya yi murmushi ya ce, "Rashin ta ya taɓa gidan gabaɗaya, har bana son buɗe tiktok saboda yadda za ki ga ana wulaƙanci dan ba ita bace."
Safeera ta yi dariya ta ce, "Hajiya Ummi uwar hassada, tana murna ta rabu da targaÉ—e sai ga karaya ta samu. Bata rabu da bukar ba an haifi Habu."
Saleem ya yi dariya ya ce, "Ai na san ji zata yi kamar ta kashe Islaha ta huta."
"Ai da tana da dama wallahi zata iya. A haka zata ƙare, babu abinda ta isa ta yiwa Islaha wallahi. Bara na koma gida na kira ta na bata labari." Saleem ya yi murmuahi suka cigaba da hirar su.
  Ummi tana barin office ɗin Chairman office ɗin Muslim ta nufa, yadda ta shigo ya fahimci akwai damuwa, kuma daman ya san zata zo saboda irin cin kashin da ƴan comments section suke yi mata. Kamar sun fi tsanar Ummi akan kowa, har gwara shi in ya yi ba a cewa a canjasa, amma in Ummi ce yanzu za a cika comments section da magana.
Ummi a firgice ta ce, "babu yadda za a yi a kashe Islaha ne? Babu wanda zamu biya ya kai ta har a shafe labarin ta daga duniya gabaÉ—aya?."
Muslim bai ce komai ba, sai da ya miƙe ya buɗe office ɗin ya leƙa dama da haggu ya ga babu kowa sannan ya dawo ya saka mukulli ya ce, "me yake damun ki? Wannan ɗaga muryar da ki ke yi na meye? In wani ya ji abinda ki ke faɗa fa?."
Ummi cikin ƙunar zuciya ta ce, "Islaha! Ta tafi ɗin ma ban daina ƙunsar baƙin ciki saboda ita ba, bata garin nan, bata cikin gidan nan amma tana bakin kowa, harda masu kallon mu. Ka kalli wulaƙancin da aka yi min a hirar jiya? Ka kalli yadda ake saka hoton Islaha a commets section ana cewa in ba ita ba an daina kallon mu?."
Muslim ya ce, "na gani."
"Haukacewa ake so na yi ne? So ake na kashe kaina saboda baƙin cikin Islaha?. Chairman ne ya kira mu yanzu, wai faɗa mana yake yi in aka cigaba da samun low views sai canja wasu presenters ɗin. Ya manta kafin Islaha ni ce highest presnter da ta fi kowa na gidan nan farin jini da samun views, ya manta ni na fara aiki a nam kafin ita?. Tunda ta zo na koma baya, yanzu akan rashinta yake cewa zai canja mu, ni Ummi ni za a canja na koma bayan camera saboda ita!. Wallahi bazan bar yarinyar nan ba, bazan ƙyale ta ba, sai na yi mata abinda har ta mutu bazata manta dani ba."
Muslim a tausashe ya ce, "kwantar da hankalin ki, mafita ya kamata mu samu akan hakan ba wannan É—aga muryar ba. Ki zauna mu yi magana."
Ta zauna kamar zata farka kujerar, sai jan numfashin mugunta take yi hassada da baƙin ciki suna nuƙurƙusar zuciyata.
Muslim ya bita da kallo ya ce, "a hankali zamu yi maganinta, yadda ta bar aikin nan baza ta sake dawowa ba. Baƙin fenti ya kamata mu shafa mata, yadda ƴan kallon ma zasu dinga son ganin fuskar ta ba balle har su ce suna son ganinta."
"Me zamu yi? Ni a ganina batun acid É—in nan ya kamata a dawo dashi, da zarar ta dawo a lalata fuskar shegiya, sai na ga wacce fuskar za a dinga gani ana yabawa."