← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 133

Sashe 16

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saleem ya ce, "wato ban san haka ƴan sanda suke da saurin fahimta ba sai yau. Sadik wannan ɗan sanda kansa yana tafiya, kansa yana ja matuƙa, ya san aikinsa sosai. Sai da ya faɗa sannan nayi noticing, sace islaha bai yi kama da satar masu garkuwa da mutane ba, tabbas tsarawa aka yi, kuma Ummi nake zargi."

Sadik ya ce, "wallahi nima na raina aikin ƴan sanda, saboda sai naga kamar ba wani abin kirki suke yi ba, ashe su ɗin mutane ne na musamman. Tabbas kuɗi ake so a karɓa a hannunmu, Islaha tana hannunsu amma ba wajan ƴan garkuwa da mutane ba, tabbas akwai abinda aka tsara kuma aka shirya ake son gabatar dashi."

Saheer ya sake kiran wayar Sadik, Sadik ya dafe kansa bai É—auka ba. Saleem ya yi dariya ya ce, "ka É—auka mana, in baka É—auka ba hankalin sa bazai kwanta ba."

Ya lalle sa ya ce, "baka san Saheer ba ne, damuwar sa kaÉ—ai yawa ce da ita, musamman in akace abu ya shafi Islaha ai ba zaman lafiya" ya faÉ—a yana É—aukar wayar ya saka a speaker.

Saheer ya ce, "Tun ɗazu ina yi maka waya ka ƙi ka ɗauka, ka san a yanayin da nake ciki zaka dinga share calls ɗina kamar wani yaron ka?."

Sadik ya ce, "ina gaban dpo ne shiyasa ban É—auka ba, ya aka yi?."

"Kai zan tambaya, ya batun Islaha?."

"Ka fara tambayar batun kuÉ—in aikin Baffa kafin ka tambaye ta ko?."

"Baffa ko yau za a iya samun kuɗin aikinsa, ita kuwa fa? Malam ka faɗa min halin da ake ciki akan maganar matata. In ba dan ƙasar nan ta kulle dani ba ka isa na tsaya ina sauraren ka? Ai da yanzu na dawo ina nemanta da jikina da aljihuna. Har ma na dinga kiran ka ƙi ɗauka?."

Sadik ya ɗan murmusa ya ce, "babu wani cigaba a maganar ta. Amma ɗazu wasu sun kira mu suna neman kuɗin fansa, kuma sun saka mana muryar Islaha mun ji. Sun ce mana suna buƙatar naira miliyan ashirin, in ba a bayar ba zasu kashe ta."

Saheer cikin wani yanayi ya ce, "kafin a kashe ta, ni ka ke so ka kashe Sadik, meyasa baza ka aiko da mutane su harbe ni a nan kawai na huta ba?...." Ya cigaba da magana ya ce, "Yanzu ka san da irin wannan maganar ka yi min shiru? Ka san hakan ya faru ka ƙi ɗaukar wayata? A ina ka ke so na saka raina, ka san a yanayin da nake zaune a ƙasar nan kuwa?."

Sadik bai ce komai ba ya yi masa shiru, Saheer ya yi shiru yana salati, muryarsa ta yi sanyi sosai kafin ya ce, "yanzu ya ake ciki?."

Sadik jin muryar Saheer ɗin ta yi ƙasa kamar mai kuka sai ya ce, "kuka ka ke yi?."

"Ban cancanci na yi kukan bane? Sadik mahaifina yana kwace babu lafiya, ga matata an sace ta, gashi ana batun kuɗin fansa alamun garkuwa aka yi da ita. Ni kuma ina nan wata ƙasa a kulle an hana shiga da fita, wallahi Sadik ji nake kamar zuciyata zata buga saboda tashin hankali, ni kaɗai na san irin abinda nake ji a raina. Baza ka taɓa hasashen yanayina ba tunda ba kai ne a cikinsa ba. Gani a raye amma na zama bani da amfani, gani da lafiya amma babu amfanin da zata yi min. Matata tana wani wajen da ban san ina ne ba, ni ina nan a kulle babu shiga babu fita."

Ya sauke numfashi, cikin rauni ya ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. Sadik a daji suke ajjiye mutane, Islaha tana da asthma, a wanne yanayi zata kasance? A cikin bishiya suke ajjiye su, ga iska, ga ƙura, ga sanyi, a wanne hali take ciki yanzu?."

Sadik da Saleem suka kalli juna jin yadda yake magana cikin rauni, sai ya basu tausayi matuƙa, ko waye a yanayin da yake ciki dole ya shiga wani hali.

Sadik ya tausasa murya ya ce, "ka yi haƙuri, ka cigaba da addu'a, in sha Allah komai zai wuce. Mun yi magana da dpo ya tabbatar mana da za a nemo mafita a cikin daren nan, dan shi bai amince ƴan garkuwa da mutane ne suka ɗauke ta ba, abin ya fi kama da plan aka haɗa mata."

Saheer ya yi shiru kafin ya ce, "za a iya, ana jin haushinta sosai musamman akan case ɗin wasu yara da ta dinga yayatawa, ni kaina sai da na yi mata magana amma ta ce aikinta yake yi. Allah ka fito min da Islaha cikin ƙoshin lafiya."

Suka amsa da amin Sadik ya ce, "duk abinda ake ciki zan faÉ—a maka" Daga haka suka kashe wayar dukkansu jikinsu a sanyaye yake.

Saleem ya ce, "Allah ya bayyana Islaha cikin aminci, Allah ya sa Islaha tana hannu na gari." Sadik ya amsa da amin suka ja motar suka bar wajan.

****

Zainab damuwa ta yi mata yawa, ta nemi Islaha sau babu adadi ta rasa, gashi akwai maganganu a bakin ta wanda take son sanar da ita, amma bata samu dama ba.

Tana zaune ta yi shiru ita kaɗai aka turo tazo in ji Mama. Bata ce komai ta miƙe ta nufi office, ta tarar da Mama a zaune ita da wata baƙuwa. Zainab ta zauna ta ce, "Mama gani."

Mama ta bita da kallo ta ce, "ke yanzu bakya yiwa kan ki faÉ—a Zainab? Bakya so rayuwar ki ta inganta kamar ta sauran mutanen gidan nan?."

Zainab ta yi shiru bata ce komai ba, Mama ta sauke numfashi ta nuna mata wacce take zaune ta ce, "Za ki bita gidanta, za ku dawo nan da kwana biyu."

Zainab ta É—aga kai ta kalli yadda matar ta zuba mata ido, ta É—auke kai ta kalli Mama ta ce, "Mama me zanyi a can har kwana biyu? Kitso za a yi mata?."

Mama zata yi magana matar ta ɗaga mata hannu, ta miƙe tsaye ta ce, "kar ki damu, ku gama magana gabaɗaya sai komai ya biyo baya."

Mama ta É—aga mata kai ta ce, "shikenan sai mun yi waya."

Matar ta fita Kama ta kalli Zainab ta ce, "ke ko sha'awar rayuwar Hafsa bakya yi? Hafsa an canja mata makaranta ta koma makarantar kuɗi, sana'ar ƙunshin da take yi yanzu tafi ƙarfinta. Wayar hannun Hafsa itace wayar da ake yayi yanzu, ke kuwa kina nan kina fama da wayar da ko dubu hamsin bata kai ba. Meyasa baza ki yiwa kanki faɗa ba?."

Zainab ta É—ago kai ta ce, "Mama ni ban gane me ki ke nufi ba."

"Da kin bita na kwana biyun zaki gane mai nake nufi, baza ki dawo gidan nan ba sai da manyan kuɗaɗe masu matuƙar yawa. Ni na rasa irin ki wallahi."

A lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo, ganin Fadwa ce sai Mama bata dakata da maganar ba ta kalli Zainab ta ce, "yanzu haka ki ke so a tsaya Zainab?."

Zainab ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba. Fadwa ta ce, "Zainab jeki ɗaki." Zainab ta miƙe ta fita dan so ta ke ta bar wajan.

Tana fita Mama ta daki table ta ce, "Yarinyar nan tana neman tarwatsa min tunani, tana neman neman yi min asarar da ban taɓa yin irinta ba. Ina zainab ta samo taurin kai ne?."

Fadwa ta yi tsaki ta ce, "rainon Islaha ce fa, kin manta Hafsa da Zainab su ne ƙannen da tafi ji dasu a gidan nan?."

Mama ta girgiza kai ta ce, "dole na samu nasara akan Zainab, ban ga dalilin da zai saka ta yi min asara ina ji ina gani ba."

Fadwa ta ce, "Wallahi in ki ka zuba ido itama irin Islaha zata zama, muna ji muna gani komai zai dinga tsallake mu yana zuwa wajan wasu."

Mama ta girgiza kai ta ce, "bata isa ba wallahi, in kin ga hakan ya faru to ki rubuta a zuciyar ki bani da rai, matuƙar ina da rai hakan bazai taɓa faruwa ba wallahi. Ko haukata Islaaha zan iya yi, indai zan yi nasara a kanta."

Fadwa ta ce, "Daman na zo na faɗa miki zan je na dawo." Hannu kawai ta ɗaga mata dan Zainab ta chaja mata kao matuƙa.

Tana fita aka kira wayar Mama, ta É—auka ta saka a kunne ta ce, "meye kuma?."

Daga can ɓangaren ya ce, "Hajiya naira duba ɗari biyu zaki ƙara mana, kuɗin hannunmu ya ƙare."

Da mamaki ta ce, "kai dakata! Wai me kuke yi da kuÉ—i har haka?."

"Ciyar da ita mu ke yi."

"Islahan wacece da take cin wannan kuÉ—in a cikin kwana biyu kawai? Kawai akan abinci ta ake kashe waÉ—annan kuÉ—aÉ—en?."

"Muna yi mata kiwo mai kyau ne shiyasa."

"Bazan ba da wannan kuɗin ba, zan tura muku dubu hamsin, daga shi bazan sake ƙara muku komai ba wallahi."

"Shikenan ki turo" ta yi tsaki ta ajjiye wayar ta ce, "Islaha har yanzu baki fita daga rayuwata ba, amma zan yi maganin ki. Zan sadaukar da komai dan ganin bayan ki" ta faÉ—a tana sauke numfashi cikin wani irin yanayi.

Nana Haleema.
[6/19, 10:27 AM] KRBBK: RDB2P11
Nana Haleema.

A firgice ta buɗe ido ƙirjinta yana bugawa, yadda ta buɗe ido a firgice tana zare ido zai tabbatar da ba ƙaramin tsoro da firgici take ciki ba. Duk da ac da take falon amma zufa take yi, ƙirjinta sai sama da ƙasa yake yi saboda tsoro da tashin hankali.

Ta dafe ƙirji tana kallon falon tana tuna abinda ta gani a cikin mafarkin ta.

A hankali ta fara sauke ajiyar zuciya, tana tunawa ba gaskiya bane mafarki ta yi, ba a gaske ya faru ba mafarki ne. Taja numfashi mai ƙarfi tana lumshe idonta cikon wani yanayin faɗuwar gaba mara misaltuwa.

Mafarki tayi wai Baffa ya mutu, sannna taga Hammanta cikin wani irin yanayi mara daÉ—i, duk ya birkice yana ta kuka yana kiran sunanta. Ita kuma ga wani abu ya yi mata katanga dashi, tana so ta fito amma ta kasa.
Chapter 16 · 0% Book details