← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 133

Sashe 26

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juyo ya kalli Islaha ya ce, "malama Islaha na dawo kanki. Ki bamu bayanai da abubuwan da za ki iya tunawa, wanda zasu bamu makama akan nemo waÉ—annan mugaye mutane."

Ta É—an sauke numfashi tana jin idon Hamma a kanta yana yawo, ta É—ago ta kalle sa a sanyaye ta ce, "bazan iya tuna komai ba, abu É—aya na sani, shi ba bahaushe bane, kuma lokacin da aka É—auke ni rufe min ido suka yi ban san ta inda muka bi ba."

"Na faÉ—a miki indai za ki iya faÉ—a mana kammaninsa, zamu iya sakawa a zana mana shi."

"Ko yaushe yana saka facemask bazan bambamce ba gaskiya" ta samu kanta da yin ƙarya dan ta ɓoye gaskiya.

"Lambar mota, katin shaida, lambar gida babu abinda za ki iya tunawa?." Ta É—aga kai alamun eh.

Ya sauke numfashi ya kalli Saheer ya ce, "baza mu iya yin komai a case É—in nan ba, indai bata faÉ—a mana wata makama ko hujja da zamu yi bincike a kai ba. A lokacin da motar ta É—auke ta, cctv asibitin Rehaan Yola ta yanke, sannan mai napep É—in da ya ce mana yaga lokacin da aka É—auke ta, shima ya ce bai ga lambar mota ba, itama kuma sun rufe mata fuska bata ga inda aka ajjiye ta ba. Babu hoto ko wani abu da zai taimaka mana mu binciko abiinda muke son bincikowa."

Islaha ta É—an yi shiru kafin ta ce, "mai napep! Kuna nufin yazo nan?."

Dpo ya kalle ta ya ce, "kin gan shi ne?."

Ta ɗaga kai ta ce, "lokacin da nake a tsorace akan hanyar, yazo zai wuce sai na tare shi, har muka yi ciniki zan shiga ya kai ni gida, sai zuciya ta bata amince dashi ba, domin ya saka facemask da baƙin glasses bana gane yanayinsa. Sai nace yaje na fasa hawa, sai naga ya fito ya biyo ni, nayi sauri na gudu, ya kamo ni yana buɗe wata kwalba da take a hannunsa, wacce ya riƙe ta da baƙin abu."

"Ban san meye a cikin kwalbar ba, amma yana ƙoƙarin watsa min a fuskata. Yana gama buɗewa sai naji an jani da ƙarfi cikin mota, daga nan ban sake buɗe ido ba sai a wannan gida."

Dpo ya zuba mata ido har ta gama ya ce, "shima mai napep É—in ya yi nufin cutar dake kenan?."

"Ƙwarai kuwa, duk da ban san meye a cikin kwalbar ba, amma tabbas abin cutarwa."

Saheer cikin tashin hankali ya ce, "meye za a yi ƙoƙarin zuba mata? Meye a cikim kwalbar?."

Dpo ya ce, "probably acid ne, hydrocloric acid!. Babu abinda za a yi ƙoƙarin zuba mata a fuska in ba shi ba."

Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta dafe ƙirji tana buɗe cikin firgici ta ce, "Acid!."

Sadik ya ce, "Sai a nemo Muslim ya nemo mana shi, daman tare suka zo." Ya É—aga kai kafin ya É—auki waya ya kira, ba jimawa wani ya shigo yana sara masa.

Ya ce, "a je gidan tv toron giwa azo min da Muslim." Ya amsa ya fita.

Dpo ya ce, "Mai keke napep, waɗanda suka sace ki, Ummi, waɗanda suka yi waya suna neman kuɗin fansa. Mutane huɗu suna cikin case ɗin nan, kuma ko wanne a cikin su abin zargi ne. Musamman mai keke napep, zuciyata bata amince dashi ba ko kaɗan. Su kuma waɗanda suka yi waya amfani suka yi da ɓacewar ki dan su samu kuɗi. Amma su waye suka ɗauke ki? Da zamu san su bincken zai zo mana da sauƙi" Ya faɗa yana zuba mata ido yana karantar yanayinta.

Islaha ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bata so ta yi wani motsi da zai saka ya zargi bata da gaskiya.

Saheer ya ce, "Officer ni ina ganin ko sun tsorata ne shiyasa ta ƙi magana? Duk da na san Islaha bata da tsoro, amma yanayin abinda bata saba gani ba zai sakawa ta ji tsoron yin magana. Na santa da wayo, kuma tana riƙe abu komai ƙanƙantarsa, amma a wannan gaɓar tace bata riƙe komai ba."

Officer ya ɗaga kai ya ce, "Islaha ke da ƙawar ki kuje ku jira mu daga waje."

Ta miƙe a sanyaye ita da Safeera, har zata fita daga office ɗin sai ta juyo ta kalle su, a hankali da sanyin murya ta ce, "A nemo mai napep ya faɗi waɗanda suka saka ya zuba min acid, sannan a nemo waɗanda suka kira waya suna neman kuɗin fansa ta. Amma batun waɗanda suka sace ni don Allah a bar maganar, a rufe case ɗin, wallahi bana so a dinga tayar da maganar ko kaɗan. Ni aka sace, kuma nace bana so a yi bincike, kawai a bar maganar tunda na dawo lafiya" tana gama faɗa ta buɗe ta fita ita da Safeera.

Safeera ta ƙarasa inda ta zauna, itama ta zauna ta ce, "Islaha meyesa ki ke so a rufe case ɗin nan? Kina ganin anyi ƙoƙarin zuba miki acid fa."

Ta sauke numfashi zata yi magana sai ta fasa, ta riƙe hannun Safeera suka fita daga harabar station ɗin gabaɗaya, suka tsaya a jikin motar Sadik da take waje.  Islaha ta ɗan yi tsaki tana kalle-kalle ta ce, "ban gamsu da wajan nan ba, ki jira mu koma gida zan faɗa miki wani abu, amma..."

Sai ta fasa faɗa ganin Hamma da Sadik sun fito, gabanta ya yanke ya faɗi ganin harara da banzan kallon da Hamma yake binta dashi. Ta san baya fushi da ita, kafin ya yi fushi da ita za a jima sosai, ko da itace babu gaskiya yana sharewa ya cigaba da rarrashin ta. Amma in ya yi fushin sai ta gwammaci duk kwanakin baya da yake sharewa ya yi fushin ta huta, dan in ya ɗaura ɗammarar fushi baya ji baya gani. Daga ganin yadda yake hararar ta ta san ransa a ɓace yake sosai, kuma sai dai ya yi haƙuri, dan baza ta faɗa masa ba gaskiya.

Nana Haleema.
[6/24, 11:32 AM] KRBBK: RDB2P18
Nana Haleema

Tunda suka tafi babu wanda yake magana a cikinsu, ta san ran Hamma ya ɓaci sosai, shiyasa tayi shiru kawai bata ce komai ba, ta zubawa window ido ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi saboda fargabar haɗuwa da Hamma. Bata san me zata ce masa ba, kuma tasan bazai yarda da dalilinta va

Ƙarar da wayar ta ta tu ya saka ta kalli wayar, ganin sunan Zainab ne sai ta ɗauka, daga can ɓangaren Zainab ta ce, "Adda Islaha yaushe ki ka dawo? Shine baki neme ni ba, na damu da rashin ki, kullum sai na yi kuka."

Ta yi murmushi ta ce, "ki yi haƙuri Zainab. Ya ki ke?."

"Lafiya lau Adda. Allah ya tsare gaba ya cigaba da kiyaye ki."

"Amin Zainab. Ina Hafsa?."

"Adda ina son magana dake da gaggawa."

Islaha ta ce, "kina ina yanzu?."

"Ina gida, amma zan fito gobe sai mu haÉ—u."

Islsha ta ce, "shikenan sai kin zo."

Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar tana sauke numfashi mai nauyi. Sadik yana tsayar da motar Saheer ya fita daga ciki cikin ɓacin rai.

Sadik ya kalli Islaha ya ce, "Islaha na kasa gane miki, sai abubuwa ki ke yi wanda bamu san shi dake ba. Yanzu da Saheer ya san labarin maƙudan kuɗin da na gani a wajan ki me zai yi zargi don Allah?."

Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce, "ka rufa wannan asirin don Allah, na faÉ—a maka ni ban aikata komai ba wallahi. Ban yi abinda ku ke zargi ba, ban yi abinda zuciyar ka take zato ba. Ka bar maganar tsakanin mu, da kaina zan faÉ—a masa in sha Allah" ta faÉ—a tana buÉ—e motar ta fita Safeera ma ta bi bayanta.

Suna shiga gidan Saheer ya fito, kafin ta ƙarasa ciku shi ya ƙaraso, suka tsaya a compound ɗin gidan ya ce, "faɗa min dalilin ki na so a kulle case ɗin nan Islaha, faɗa min abinda ya saka kika ce a bar maganar, har ki ke cewa bakya so ki ji ana maganar case ɗin. Ina jinki."

Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya faɗi sosai, magana yake cikin fushi da ɓacin rai. Ba haka suka saba magana ba, sai ta ji hakan baƙo har ya haifar mata da faɗuwar gaba.

Ta buɗe baki zata yi magana ya ce, "wallahi in baki bani hujja mai ƙarfi ba zan iya marin ki, In kin san baki da hujja ki yi min shiru kawai."

Islaha ta buɗe baki cike da mamaki tana kallonsa, yau Hamma ne yake cewa zai mare ta? Lallai ta ɓata masa rai matuƙa. Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba.

Ya gyaÉ—a kai yana kallon ta ya ce, "da haÉ—in bakin ki aka É—auke ki kenan ko?."

Ta girgiza kai ta ce, "a'a."

"FaÉ—a min su waye."

"Na faÉ—a maka wallahi ban san su ba."

"Shikenan Islaha, ki yi yadda ki ke so" ya faÉ—a yana fita daga gidan a fusace.

Ta zauna a wajan cikin damuwa mai yawa, Safeera ta ce, "tashi mu shiga ciki, lokacin sallah ya yi." Bata musa ba suka shiga ciki, gidan babu kowa suka shiga É—akin Islaha suka yi sallah.

Bayan sun idar safeera ta ce, "Nima kin neman jefa zuciya ta a cikin zargi, wanne kuÉ—i aka gani a hannun ki, sannan meyasa bakya so a yi bincike akan case É—in nan?."

Ta kalli Safeera ta ce, "Safeera wanda ya sace ni babban mutum ne, duk da ba yaren mu bane, amma kina ganinsa kin san yana da kuɗi sosai. Gidan da aka ajjiye ni ban taɓa ganin gida kamar sa ba, komai na gidan na daban ne da wanda ban saba gani. Ga masu tsaron sa a gidan da yawa, hakan ya tabbatar min da baza mu iya case dashi."

Safeera ta yi dariya tana girgiza kai ta ce, "hakan da ki ka faɗa ya sake saka min zargin wani abu a zuciyata. Kin manta kece mai iƙirarin ko wa waye zaki iya shari'a dashi indai akan gaskiyar ki? Ko kin manta kece wacce kuɗi ko matsayi baya baki tsoro?."

Islaha tayi ajiyar zuciya tana kallon ta ta ce, "Zan faÉ—a miki komai, amma don Allah kar ki faÉ—awa kowa."

Safeera ta ce, "ina jin ki."
Chapter 26 · 0% Book details