← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 133

Sashe 129

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta saka hannu ta karɓa tana kallon kuɗin ganinsu sa yawa. Baffa yana murmushi ya ce, "kin san meye wannan a hannun ki?."

Islaha ta ce, "A'a Baffa."

Baffa ya murmusa cikin jin daÉ—i ya ce, "sadakin auren ki ne."

Gaban Islaha ya faɗi, ta buɗe ido waje ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi. Ta kalli kuɗin ta kalli Baffa da yake kallonta, ta sake ɗauke kai tana jin wani iri a jininta, ga wani irin yanayi da take ji yana manaye ko ina a jikinta.

Mama ta yi tsaki ta ce, "Sadakin auren mahaukacin har wani abin murna ne? Mahaukaci ne fa wanda aka bata, sai meye dan ya aure ta?. A banza zai kashe ta kuma ya kashe banza, babu abinda aka isa ayi ranta ya tafi a banza. Ni tunda dai bata auri ɗana ba ko waye ta aura bai dame ni ba, Saheer dai ya fi ƙarfinta wallahi."

Baffa bai kulata ba ya ce, "Islaha kin yi shiru."

Gabanta faɗuwa yake yi, da farko bata yi tuannin zata ji irin wanna faɗuwar gaban ba tunda ta san a yadda aka gina auren, amma sai ta ji tsoro yana mamaye mata ƙirjinta, fargaba da sanyin jiki suna yi mata dirar mikiya lokaci ɗaya.

Cikin sanyin murya ta ce, "Har an yi auren?."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "An É—aura. Yanzu ke matarsa ce halak malak, sun ce min gobe zasu turo da motoci a É—auke ki, tunda babu bikin da za ki yi sai ki tare a gidan ki gobe."

Ta wara ido tana kallon Baffa jikinta har rawa yake yi ta ce, "Baffa gobe kuma?."

"Ko kina da shirin da za ki yi ne?."

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Baffa ya ce, "na riga na amsa musu, amma in akwai abinda za ki yi sai a faÉ—a musu."

"Shikenan Baffa."

"Na faÉ—awa Yayar ki, za a zo ayi miki ado irin na amare, bai kamata a kai ki a haka ba."

Islaha ta ce, "ba sai ta zo ba Baffa."

Baffa ya ce, "Haka za a yi auren na ki babu kwalliyar amare?."

Ta yi shiru bata amsa ba dan gaskiya babu abinda zata yi. Baffa ganin haka sai ya ce, "Shikenan, ki je ki haɗa komai na ki, yau Allah ya ɗaga darajar ki daga ƙasa zuwa sama. Waɗanda suke ganin ki a wulaƙance zasu fahimci sun tafka kuskure, zasu gane sune a wulaƙance ba ke ba."

Islaha ganin Baffa zai fita sai ta ce, "Baffa kuÉ—in."

Ya kalli kuɗin ya ce, "Sadakinki ne, ke za ki riƙe."

Ta bi kuÉ—in hannunta da kallo ta sake kallon Baffa ta ce, "Baffa ka bar su a wajan ka."

Ya yi murmushi ya ce, "Haƙƙinki ne Islaha." Daga haka ta fita ita kuma ta sauke numfashi tana kallon kuɗin.

Ta kalli Mama da take tsaye tana kallon ta, ta ɗauke kai tana miƙewa tsaye. Mama ta bita da kallo ta ce, "Amaryar mahaukaci! Yau Allah ya yi zan rabu da alaƙaƙai daga cikin gidana, sai a je can a ƙarata. Ko banza za ki dinga kwana a ac kina cin kaji."

Islaha ta haɗɗiye yawu bata ce komai ba ta raɓa gefen Mama zata wuce Mama ta ce, "daman na rantse, babu ke babu Saheer, kuma rantsuwata bata faɗi a ƙasa ba. Ki je ki ƙarata da mahaukacin ki, a bi wani sarkin, Saheer kam ya fi ƙarfin ki wallahi." Bata tanka ba ta shiga ɗaki, ta rufe ƙofar tana jingina da bango ta lumshe ido.

Ta buÉ—e idanunta ta kalli kuÉ—in hannunta, tana ayyana sadakin aurenta ne a hannunta, aurenta kuma ba da Hamma, da wanda ta fi tsana a duk duniya. Ta juya kuÉ—in a hannunta, tana tuna wanda ta aura a zuciyar ta.

Ta yi tsaki a bayyane ta ce, "igiya uku ta aurensa ta hau kaina." Ta dafe kai cikin takaicin da ta ji yana mamaye ta, ta cize bakinta tana ji kamar ta zane kanta saboda takaicin da ya cika mata zuciyarta.

"Rehaan!"

Kalaman da ya faɗa mata a ƙasar saudia suna yawo a kunnenta, ta runtse a bayyane ta ce, "na yi saboda Hamma, na yi saboda Hamma ya kuɓuta, na yi saboda rayuwar Hamma ta dawo, saboda shi ne kawai, ba dan ya isa ba. Na yi komai domin shi, kuma zan dawo gare sa in sha Allah" ta faɗa dan ta kawar da tunanin da yake damun zuciyarta.

Ƙwanƙwasa ƙofar ake yi a hankali, Islaha ta bar jikin ƙofar ta buɗe ƙofar suka haɗa ido da Safeera. Islaha ta bata hanya ta shiga, sannan ta mayar da ƙofar ta rufe. Islaha bata ce komai ba ta ƙarasa gefen gado ta zauna, ta zame ɗankwalin kanta, ta ajjiye kuɗin akan cinyarta tana ji duniyar tana juya mata.

Safeera ta ce, "ya dai?."

Ta É—ago ta nuna mata kuÉ—in ta ce, "an É—aura auren."

"Shine ya saka ki a damuwa?."

"Ina ji kamar ban kyauta ba, sai yanzu nake jin na tafka kuskure babba. Jikina yana bani kamar...." Sai ta kasa faÉ—a ta dafe kanta.

"Islaha komai ya riga ya faru, wannnan tunanin da ki ke yi duk ihu ki ke yi bayan hari. Yanzu ke matar Rehaan ce, kamata ya yi ki fara tunanin abinda zai biyo baya, ba wanda ya riga ya wuce ba."

"Ya zan yi, ina ji kamar ban kyautawa Hamma ba, ban kyautawa rayuwata gabaÉ—aya ba."

"Hmm kina son maimaita magana É—aya Islaha, ke ki ka ce za ki iya yin komai saboda shi. Yanzu kuma kin yi saboda shi É—in, meyasa ki ke damun kan ki?."

"Zan iya yin komai saboda shi" ta sake maimaitawa don Safeera ta tabbatar."

Safeera ta dafata ta ce, "ki saka a ran ki wannan É—in ma saboda shi ne."

Ta ɗago idanunta da suka fara cikowa da hawaye ta ce, "ya zan yi in Hammma ya dawo, da wacce fuska zai karɓi maganar nan?. Aure na yi fa, duk da auren contarct ne, amma kafin ya fahimce ni ni kaina na san za a sha wahala" ta girgiza kai tana ɗaga hannu sama ta ce, "Allah ka taimake ni Hamma ya fahimce ni, Allah ka sa kar ya yi min mummanar fahimta."

Safeera ta ce, "Haka za ki faɗa masa ya fahimta, komai zai yi daidai in sha Allah. Ki daina damun kan ki, komai ya riga da ya faru, danasani akan abinda ya wuce ɓata lokaci ne Islaha. Na farko baza ki dawo da abinda ya wuce ki gyara ba, sannan tunaninsa ɓata miki rai kawai zai yi, tunda ba ki da magani. Kuma auren nan na suna ne, tunda za ku zauna matsayin ma'aurata amma ba wai na gaske ba."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Baffa yana zancen gobe zan koma gidan, ni wallahi komai ya fice min daga rai" ta faÉ—a tana kwnaciya da baya cikin wani irin yanayi.

"Daman ai a can za ki zauna, tunda a matsayin matarsa ki ke yanzu."

Ta yi ƙaramin tsaki ta rufe ido ta ce, "bana son maganarsa wallahi, ban san haka na tsane sa ba sai yanzu."

Safira ta yi dariya ta ce, "taimakon ki ya yi dai, ba dan shi ba da ynzu an kashe Hamma har lahira."

Banza ta yi mata bata ce komai ba tana saƙawa da warwarewa. Itama Safieera bata ce komai ba suna zaune a wajen har aka yi sallar la'asar, a nan suka yi sallah ta sake komawa ta zauna tana buga tagumi cikin sabon yanayin da take jin jikinta.

Safeera ta katse shirun ta ce, "Amma bakya ganin Mama zata faÉ—awa Saheer kin yi aure?."

Islaha ta miƙe zaune sosai tana gyara ɗankwalin kanta ta ce, "ko shakka babu, Mama sai ta faɗa masa. Kin san halinsa da saurin ɗaukar zafi, kafin na samu ya fahimce ni ma babban aiki ne wallahi."

Safira ta ce, "dole zai birkice, tunda yana da kishi, kuma magana ake ta kin auri wani. Amma daga baya komai zai zama ya yi daidai in sha Allah. Duk inda wanda ka ke so yake, in aka ce ya yi aure dole za ka ji zafi da kishi a ranka."

Islaha bata ce komai ba suka jiyo hayaniya daga falo, da sauri suka miƙe suka fita falon suka ga Baffa ne sai su Mama da suke a tsaye.

Baffa ya ce, "Islaha an saki Saheer, yanzu haka yana asibiti tare da Sadik!."

Nana Haleema.
[7/30, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P98
Nana Haleema.

Wani irin dumm ta ji a kanta kamar an doka mata abu mai nauyi a tsakiyar kanta, sai da jinta da ganinta suka É—auke na wani lokaci, kafin ta dawo hayyacinta, jikinta ya fara rawa, ta koma da baya da hanzari ta É—auko hijjab, ta dawo ta samu Baffa da su Mama har sun fita daga falon ta rufa musu baya da sassarfa.

GabaÉ—aya suka tafi asibitin da Saheer ya ke, suna shiga suka tarar da Sadik a tsaye yana amsa waya yana faÉ—awa mutane an sa ki Saheer ya dawo.

Yana ganinsu ya kashe wayar, Baffa ya ƙarasa ya ce, "Yana ina?."

Sadik ya ce, "an yi masa allurar bacci, yana ciki ana ba shi kulawar da ta kamata."

Islaha da ta fi kowa zaƙewa ta ce, "Zan iya shiga na gansa?."

Hanan ta buÉ—e baki ta ce, "ka ji wani abu, ga mahaifiyarsa bata shiga ta gansa ba sai ke?."

Islaha bata kula Hanan ba kallon Sadik take yi tana jiran amsa. Sadik ya ce, "an ce dai kar a tashe sa, amma za a iya shiga É—aya bayan É—aya a gansa."

Hanan ta yi caraf ta ce, "Mama mu je ki gansa, babu wata bare da zata fara shiga wajansa bayan ga ki. Ke ki ka haife sa ba, ba ita ba."

Islaha ta ja gefe ta jingina da bango ta bawa Mama hanya ta wuce, Mama da Hanan suka shiga. Babu jimawa Mama ta fito tana kuka tana faɗin, "kun ga yadda ya koma? Gabaɗaya ya rame ya yi baƙi, jikinsa ya yi ƙuraje. Allah ya isa! Allah ya isa! Allah ya isa!!. Allah ka shiga tsakaninmu da waɗannan mutane, ka yi mana maganinsu cikin gaggawa.”

Bafffa ya kalli Islaha da ta ke hawaya ya ce, "ki shiga ki gan shi Islaha."
Chapter 129 · 0% Book details