Sashe 32
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mams ta ce, "nifa daman burina kar gidan nan na Jedda ya wuce mu, kuma tunda an samu mun gode Allah, sai a cigaba da shagali kawai."
Karima ta ce, "Ki ji fa, wai ita aikin shekara É—aya take so ta dawo. Shashasha, bata san in ta shiga sai Allah ya fito da ita ba."
Mama cikin dariya ta ce, "Ai basu san roman baka ba." Suka tafa suna dariya, suka cigaba da tattauna yadda lamarin zai kasance.
Islaha haka ta shiga ɗaki jiki a sanyaye, zuciyarta a cushe take akan abinda ta aikata, wani abu take ji ya tokare mata zuciyarta. Ta san ba daidai ta aikata ba amma hakan shine kawai mafitar ta, bata da mafita da inda zata samu kuɗi ta sauke nauyin da yake kanta sai hakan.
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ka kawo min sauƙi cikin lamarin nan, Allah ka bani abinda zan iya, Allah ka bani abinda zan iya ɗauka, dan darajar ka. Ya Allah ka bani ƙaddara mai sanyi, ka kaini hannu na gari, ka bani ikon kiyaye mutuncina a duk inda nake. Allah ka yaye min gagagwa da aikata abu a cikinta, ka bani ikon yin tunani mai zurfi kafin na aikata, amin."
Ta zauna a gefen gadon, sai kuma ta miƙe tsaye dan tana buƙatar magana da Safeera, tana so ta faɗa mata abinda yake faruwa amma bata son tayar mata da hankali, bata so ta ji labarin har an yiwa Umma visa fita ƙasar waje.
Ta tabbatar Safeera bata sani ba, dan da ace ta sani da tuni ta bata labari abubuwan da suka faru akan hakan. Ta yi ajiyar zuciya, duk da haka tana da buƙatar yin magana da Safeera da kuma Sadik, dole ta yi magana dasu ko dan abinda zai faru bayan tafiyarta, bata so Saheer ya san zata bar ƙasar sai bayan ta bari. In ta je can kome zai faru zata iya jurewa, kuma zata rarrashe shi har ya haƙura ya fahimce ta.
Ta sauke numfashi tana lumshe ido, tunda bata da iyayen da zasu saka ta ko hana ta, gwara ta yi abinda take ganin shine ya dace da halin da take ciki.
Islaha a Jeddah
Rehaan a JeddahðŸ¤â¤ï¸â€ðŸ”¥
[6/26, 12:30 PM] KRBBK: RDB2P22
Nana Haleema
Da sallama Umma ta shiga wajan Baba da yake zaune, ya amsa yana kallon ta har ta ƙaraso ta zauna. Umma ta ɗan kalli Baba ta ce, "ina son nayi magana da kai."
Baba ya É—an kalle ta sannan ya ce, "ina jin ki."
Umma ta ce, "akan batun tafiyata ƙasar waje ne, daman...." Kafin ta ƙarasa ya ɗago ya kalle ta sai ta kasa ƙarasawa ta yi shiru.
Baba bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi, ganin bai yi magana ba sai Umma ta ce, "tafiyar tana matsowa, shine na ce..." nan ma bata ƙarasa ba ya ɗaga kai ya kalle ta.
Baba ya ajjiye abinda yake hannunsa ya ce, "shine me?."
Umma ta yi shiru bata ce komai ba, duk da ƙarfin guiwar da take ji kafin tazo, yanzu da take gabansa sai ta ji tayi sanyi ta kasa magana. Sai take jin nauyin faɗa masa har an buga mata visa an yi ticket, bakinta sai ya sarƙe ta kasa faɗar abinda zata ce.
Baba ya ce, "na faɗa miki hukunci na akan maganar nan, indai ki ka amince da tafiya ƙasar waje to ki tabbatar babu aurena a kan ki."
Umma da mamaki take kallonsa ta ce, "wai da gaske zaka iya sakina? Ƴaƴa huɗu ne a tsakanina da kai, kuma dukkansu mata ne. Yanzu sai ka sake ni saboda wannan ƙaramar matsalar?."
Baba ya miƙe tsaye ya ce, "indai zaki iya tsallake su ki tafi wata ƙasa saboda neman duniya, ina so na faɗa miki nima zan iya rabuwa dake. Kuma ina kan bakata wallahi, indai ki ka zaɓi barin yaran ki nima zan zaɓi barin ki. Baza ki bar nigeria da aurena a kan ki ba, gwara ki tafi babu nauyin kowa kema zaki fi jin daɗi" yana gama faɗar haka ya mike ya fita daga falon.
Umma ta miƙe tsaye ta ce, "tabɗijam! Wallahi bazai yu ba, dole na je ƙasar nan na samo kuɗin da mata suke samowa. Da gaskiyar woman leader, indai zaka biyewa namiji zaka ƙare a wahala da takaicin rayuwa. Yanzu dubi baban Safeera, me yake tsinana min da har zai hana ni tafiya neman na kaina?. Ai wallahi tunda na yi niya sai na je, bazan zauna a nan talauci ya kashe ni ba."
Sai kuma ta sauke numfashi tana kama ƙugu ta ce, "amma bana son auren nan ya rabu, auren shekara ashirin da tara zai rabu saboda haka? Kuma sai da yara duk suka girma sannan hakan zai faru?."
Ta dafe kai cikin damuwa ta furzar da iska waje ta ɗauki waya ta kira ƙanwarta. Tana ɗauka ta ce, "Atika ina cikin matsala wallahi, Babansu Safeera ya sake tabbatar min da indai na tafi sai ya sake ni."
Daga can ɓangaren Atika ta ce, "to meye abin damuwa? In ya sake ki ai ba wani abun ne zai faru ba, ƴaƴa dai ƴaƴanki ne, kuma zaki je ki samo kuɗin aurar dasu ne tunda dukkansu mata ne. Ƴan mata uku ne a gabanki, a cire batun autar ki ita bata kai su girma ba, amma Safeera da ƙannenta duk sun isa aure. In ki ka zauna da me zaki aurar dasu?."
Umma ta ce, "shine tunanina Atika, amma bana son rabuwar auren nan wallahi. Ace aure shekara da shekaru zai rabu saboda tafiya ƙasar waje aiki? Kuma sai da yara suka girma, duk sun san meye aure da rabuwarsa sannan zai faru? Abin akwai nauyi Atika."
"meye dan ya sake ki, in ya sake ki ba sai ki sake wani auren ba?."
"Haba Atika, da tsufana, ina shirin aurar da Æ´a kuma ki ce nayi wani auren?."
"To a kan ki aka fara? Kin ga Maimuna, Kar wannan ya dakusar dake, nima harkar nake so dan bazan samu dama bane shiyasa zan yi haƙuri, amma ke tunda kin samu kar ki yi wasa da ita."
"In ya kira Yayana na Katsina ya faÉ—a masa fa?."
"To ina ruwansa? Zai hanaki abinda ki ka yi niya ne?."
Umma ta ce, "shikenan dai, ina zuwa" ta faÉ—a tana kashe wayar cikin tunani.
Baba ko da ya fita a ƙofar gida ya tsaya cike da tunani, ya san halin matarsa tsaf zata iya tsalleke auren ta tafi. In hakan ya faru bazai ji daɗi ba, bazai taɓa jin daɗi ta tafi ta bar yaranss a gantale ba tare da uwa ba. Shi mutum ne mai ɗan tafiye-tafiye neman na abinci, in ta saka ƙafa ta tafi in zai yi tafiya da wa zai bar ƴaƴansa mata?.
Ya yi ajiyar zuciya, ya saka hannu aljihu ya É—auko waya ya kira Yayanta na Katsina dan ya sanar dashi halin da ake ciki, da farko ya É—auka ta bar maganar shiyasa bai saka magabatanta a ciki ba, amma ya ga alama yanzu dole ya saka makusantata a maganar.
Basu jima suna wayar ba ya sauke wayar ya cigaba da tsayuwa a wajan har mota ta tsaya a kusa dashi.
Aka fito daga motar, mutumin ya ƙaraso kusa da Baba da fara'a Baba ya ce, "Ashe kana cikin garin na mu."
Alhaji Yakub ya ce, "na shigo garin jiya, kuma na yi niyar na shigo mu gaisa sai ga wayar ka, shine na ce ai ko ban yi niya ba ya kamata ace nazo."
Baba ya ce, "barka da zuwa."
"Barka dai. Ka yi haƙuri, ban san abinda yake fatuwa ba kenan, ai da na yiwa tufkar hanci."
"Mu ƙarasa ciki." Bai musa ba suka shiga cikin gidan da sallama.
Umma da fitowar ta tsakar gida kenan ta ji sallar tasu su ta amsa tana kallon su, gabanta ya yanke ya faÉ—i ganin Yayanta da kuma mijinta.
Cikin yaƙe da faɗuwar gaba ta ce, "Yaya Sannu da zuwa."
Ya yi murmushi ya ce, "Yauwa sannun ki." Ta nuna masa falo ta ce, "Yaya mu shiga ciki." Suka shiga shida Baba ita kuma ta dafe ƙirji tana ajiyar zuciya.
Daƙyar ta ɗauko faranti ta ɗora masa pure water guda biyu, ta koma kitchen ta ɗauko ƙaramin flakass wanda ta zuba kunu tun na safe da kofi ta shiga da sallama.
Suka amsa ta ajjiyewa Yaya ta ce, "Yaya ban san zaka zo ba, da na yi maka tanadi na musamman" ta faÉ—a tana zama da murmushi.
Yaya ya ce, "jiya nazo, daman kuma nayi niyar na shigo mu gaisa, sai yanzu Allah ya yi na ƙaraso."
Ta durƙusa har ƙasa ta ce, "Ina yini."
"Lafiya lau, ya gida ya yara?."
"Alhamdu lilah. Ya mutanen Katsina?."
"Kowa lafiya lau. Da nace musu in na zo Yola zanzo mu gaisa sun ce duk a gaishe ku."
"Muna amsawa."
"ina Safeera da ƙannenta?."
Umma ta ce, "duk suna islamiyya. Safeera kuma tana wajan aiki."
Yaya ya ce, "ma sha Allah! Allah ya taimaka."
"Amin Yaya."
"Yaushe ne bikin Safeera ne?."
"Ba a saka lokaci ba har yanzu, Yaron yana aiki ne."
"Gwara haka, gwara ya yi komai a nutse. Allah ya kaimu lokacin."
"Amin Yaya. Ga kunu na kawo maka ka sha, bara na kawo abinci" ta faɗa tana miƙewa.
Yaya ya ce, "yi zaman ki, kunun dai zan sha, abinci kam na ƙoshi."
"Ka dai ci har abincin."
Baba ma ya ce, "ya kamata dai ka ci wani abun."
Yaya ya ce, "wallahi a ƙoshe nake, zan dai sha kunun tunda daman ina sonsa." Umma ta yi murmushi bata ce komai ba, ƙirjinta yana dukan goma goma.
Yaya sai da ya sha ruwa sannan ya kalle ta ya ce, "Maimuna!."
Gaban Umma ya yanke ya faÉ—i, ta É—aga kai ta kalle sa ta ce, "Naam Yaya."
Ya gyara zama ya ce, "Meye matsalar ki? Me ki ka nema ki ka rasa a cikin gidan nan?."
Umma ta sauke numfashi kanta yana ƙasa ta ce, "babu komai."
Yaya ya ce, "A'a akwai, ki faÉ—a min abinda yake damun ki, ina ji." Umma ta yi shiru bata amsa ba, dan bata san me zata ce masa ba.
Alhaji Yakub ya haÉ—e mata rai ya ce, "magama nake yi miki, me yake damun ki?."