← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 133

Sashe 46

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadik ya bita da harara ya ce, "Safeera kar ki mayar damu ƙananun yara mana, kar ki mayar damu shashashai waɗanda basu san abinda suke yi ba, ki faɗa maganar da kanmu zai ɗauka, ki daina yi mana magana ta rainin hankali. Mu ba mahaukata bane da zamu yarda da wannan shirmen."

Saleem ya jinjina kai ya ce, "ya sace ta, ya ajjiye ta a gidansa bai yi mata komai ba, kuma ya saka aka dawo da ita. Ita kuma saboda ƙarfin hali, tana hannun wanda ya sace ta bata kuɓuta ba, shine harda ɗauko masa kuɗi?. Bayan ta dawo kuma ta ɓoye mana, ta dinga ɓoye-ɓoye a kan case ɗin. Yanzu kuma ta shirya tafiya ta bar ƙasar, duk babu wanda sani ba."

Ya ɗan girgiza kai ya ce, "Safeera hankali bazai ɗauki maganar nan taki mai kama da wasan yara ba, nima ban yarda ba balle Sadik, balle kuma aje kan uwa uba Saheer. Kuna ɓoye mana wani abun ke da ƙawar ki."

Kamar Sadik jira yake yi ya fara bala'i ya ce, "mu zata mayar shashashai ƴan iska? Mu za a tsaya ana tsarawa ƙarairayi kamar wasu marasa hankali?."

Safeera ta ce, "wallahil azim ban ɓoye muku komai ba, wallahi Allah abinda ya faru kenan. Islaha ta tafi dan ta nemi kuɗin da zata biya wancan bashin sa da taci, ko nace ta je neman kuɗin da zata mayar masa a inda ta ɗauke. Wallahi duk wani tunani mara kyau da kuke yi ba haka ba, Islaha bata canja ba, tana nan yadda take. Don Allah ku daina zarginta da mummunan abu, Islaha mace ce ta gari"

Sadik ya ce, "Naji mace ce ta gari. Yanzu in taje ta samo kuÉ—in ta dawo, a ina zata samu mutumin ta ba sa kuÉ—i? Ko daman ta san shi daman tun farko?

"Wallahi bata san shi ba, ta ce min zata neme sa."

"Ƙarya ne, wannan ƙarya ne wallahi!. Ta tafi yin wani abinda daban a ƙasar waje kawai, amma ba wannan tatsuniyar ba."

"Wallahi ba tatsuniya bace, gaskiya ce maganar nan ba ƙarya ba. Wannan dalilin da na faɗa muku shine ya saka ta tafiya."

Saleem ya ce, "Shikenan munji haka ne, ta ya zata biya shi in bata san shi ba?."

Safeera ta ce, "wallahi bata san shi ba."

Sadik ya ɗaga mata hannu ya ce, "Ki daina yin rantsuwa Safeera, rantsuwa akan ƙarya bata kamace ki ba. Abu ne guda biyu, ko ke da ƙawar ki kuna raina mana hankali, ko kuma ƙawar ki ta haɗa har ke ta rainawa hankali. Wannan maganar ƙarya ce wallahi, babu ta yadda za a yi mu amince da wannan wasan kwaikwayon. Sau nawa Mama tana yiwa Islaha tayin aikin tana avoiding, tafi kowa tsanar tafiya aikatau ɗin nan. Kwanaki har progeam ta fara akan hakan, ko Saleem?."

Saleem ya ce, "shine abinda ya ɗaure min kai, nida ita muka fara wayar da kai akan tafiyar nan a kafofin sada labarai, meyasa ita ta yi bayan itace mai so ta yaƙi abin?

"Ni ban yarda da wannan shirmen ba, akwai abinda aka ɓoye wanda ba a so mu sani."

Safeera ta ce, "Hamma Sadik ba a ɓoye mu ku komai ba, gaskiyar kenan."

Sadik ya ce, "to kema ta ɓoye miki, kema bata faɗa miki gaskiyar abinda yake faruwa ba, ta haɗa damu dake ta raina mana hankali tana so ta ɓoye laifinta. Bazan taɓa yarda da wannan ƙaryar ba Safeera, Islaha ta ɓoye miki gaskiyar lamarin nan, dan na tabbatar akwai wani abun bayan hakan."

Safeera zata yi magana aka kira wayar Sadik, ya kalli wayar ya kalle su ya ce, "Saheer ne, yanzu me zance masa don Allah?. Wannan tatsuniyar da Safeera ta faÉ—a mana zan faÉ—a masa, ko wani abun daban?!."

Nana Haleema✍🏻❤️
[7/2, 10:40 AM] KRBBK: RDB2P32
Nana Haleema..

Saleem ya bi Sadik da kallo ya ce, "ka ɗauki wayar ka faɗa masa gaskiya, wannan ba maganar sace ta bace balle ace a bari kar a faɗa masa daga baya. Magana ake na ta bata ƙasar gabaɗaya, dawowar ta yanzu bazai yu ba."

Sadik ya dafe kai cikin wani irin takaici da ɓacin rai ya ce, "Islaha tana bani wuta wallahi, komai ni take sakawa a ciki."

Kiran da ya sake shigowa wayarsa ne ya saka ya ɗauka, ya saka wayar a speaker, Saheer daga can ɓangaren ya ce, "ina ta kiran ka baka ɗauka. Kuna tare da Islaha ko tana wajan aiki? Tunda na tafi sau ɗaya muka yi magana da ita, yanzu ina kiranta amma bana samunta. Kuna tare ko na kira Safeera?."

Sadik ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "muna tare da Safeera da Saleem, amma babu Islaha."

Saheer ya ce, "tana ina ita? Ko ta tafi wajen aiki ko taje orphanage?."

Sadik ya ce, "kana ina yanzu?."

Saheer ya ce, "ina gida, ka bani amsa."

"In a tsaye ka ke ka samu waje ka zauna Saheer."

"Meyasa kenan? Wani abun ne ya sake faruwa?."

"Eh wani abu mai girma ya faru, shiyasa na ce ka samu waje ka zauna."

"Sadik me ya faru, wani abun ne ya sake samun Islaha? Ka yi mana, ka faɗa min abinda ya same ta bana son ɓoye ɓoye, ka faɗa min!."

Sadik ya ce, "Islaha dai bata ƙasar nan."

Saheer muryarsa har rawa take yi ya ce, "ban gane ba, tana wacce ƙasar?."

Sadik ya ce, "sun ɓoye mana komai ita da ƙawar ta, sai yanzu muke jin labari a bakin Safeera. Islaha tana ƙasar Saudia, ta biyewa Mama ta tafi aikatau."

"Ka ga Malam ka yi maganar da zan fahimta, kamar ya ta tafi aiki? Aikin jaridar ne ya kai ta saudia ko wani abun ne, ni ban gane ba?."

Sadik ya bashi labari irin wanda Safeera ta faɗa musu, sannan ya ce, "a lokacin da aka sace ta daman ni ban yarda da ita ba wallahi, dan a lokacin ta saka na ɓoye maka itace ta biya kuɗin aikin Baffa. Tana dawowa daga wajen wanda ya ɗauke ta muka je asibiti, a lokacin na ga rafar dala ɗari a hannunta. Dana tambaye ta sai ta ƙi faɗa min, ta wuce wajen biyan kuɗi ta biya kuɗin aikin Baffa. Da nayi converting dala zuwa naira, a lokacin da kuɗin hannunta naira miliyan sha bakwai kenan. Nayi nayi ta faɗa min inda ta samo kuɗin nan amma Islaha taƙi faɗa, daga ƙarshe sai ta ce min don Allah kar na faɗa maka, wallahi ba ta hanyar banza ta same su ba, ta dinga haɗa ni da Allah har na amince bazan faɗa maka ba. Yanzu kuma dan ta raina mana hankali, ta ɓullo da wannan maganar mai kama da wasan yara."

Saheer ya yi shiru ya kasa magana, kansa ya kulle ya rasa abinda zai ce. Bakinsa ya yi nauyi, bakinsa ya ɗaure matuƙa ya rasa abinda zai ce.

Daƙyar ya buɗe baki ya ce, "da gaske ka ke Islaha ta bar ƙasar nan?."

"Wallahi da gaske bata ƙasar nan Saheer."

"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Meyasa ka ɓoye min maganar kuɗin da ta zo dasu tun farko?."

"itace ta dinga roƙona akan don Allah kar ka sani, shiyasa na yi shiru ban faɗa maka ba."

"An sace ta, sannan ta dawo da bandle na dala ɗari har ta biya kuɗin aiki. Taƙi faɗar wanda ya sace ta, ta dage akan sai an rufe case ɗin sace ta da aka yi, ta koma zama cikin yanayin damuwa, ko walwala bata yi. Kenan daman saboda wannan kuɗin ne ya saka take so a kulle case ɗin?."

Sadik ya ce, "ko kuma saboda ba sace ta ɗin aka yi ba, ni fa zuciyata tana faɗa min tana sane duk abinda ya faru tsarinta ne. Haka kawai mutum zai sace ta ya ajjiye ta bai yi mata komai ba, kuma saboda ƙarfin hali irin nata da ta tashi dawowa har ta samu guts ɗin sato masa kuɗi?....Babu ta inda hankali zai ɗauki wannan maganar, babu ta inda za a faɗi maganar nan ace tayi kama da gaskiya. Ni na fi zargin kawai a wajansa ta samo kuɗin, ta damu da rashi lafiyar Baffa ne shiyasa ta tafi, amma ba sace ta aka yi ba."

"Me ka ke nufi?."

"ina nufin ta yadda mata suke samun kuÉ—i mana, su bayar a basu."

"Kana nufin Æ´ar iska ta koma?."

"Ga amsa a bayyane."

"Kar ka sake jifan Islaha da wannan kalma mara daÉ—i, tun muna shaida juna da kai ka iya harahenka akanta!."

Sai ya kuma cewa, "Duk abinda ya faru ba laifin ka bane? Da ka kula da amanar da na bar maka ai da hakan bai faru ba."

Sadik cikin takaici da haushin Islaha ya ce, "duk ƙoƙarin da nake yi a kanta baka gani ba kenan?."

Saheer ya ɗan sauke numfashi cikin yanayin damuwa ya ce, "Safeera meyasa za a haɗa kai dake a yi min haka? Meyasa zaki ɓoye min wannan magana mai girma, meyasa zaki bata goyan bayan wannan ɗanyen aikin?."

Safeera ta ce, "Hamma Saheer ni kaina ban sani ba sai da ta gama yin komai sannan ta faÉ—a min, ta san in na sani zan dinga kushe abin har ya fita daga ranta, shiyasa ta yi min shiru ban sani ba har sai da aka gama yin komai."

Saheer cikin rauni da sanyin murya mai cike da damuwa ya ce, "ƙawar ki bata kyauta min ba Safeera, ƙawar ki ta bani mamaki mai yawa, ta karya min zuciya, ta yi abinda ban yi tunani ba. Islaha bata kyauta min ba, isla....." sai ya kasa maganar ya kashe wayar.

Sadik ya ja tsaki ya ce, "bayan duk abinda ta aikata, wai har yanzu ya yarda da ita, har yanzu akwai sauran yarda a tsakaninsu. Mtsww! Wallahi Islaha ta fita daga raina gabaɗaya, duk wani girma da ƙimarta da nake gani ya riga ya zube ya bi rariya, ta bani mamaki mai matuƙar yawa."

Safeera ta fito da waya tana kallon number Islaha ta buÉ—e voice note É—in. Duk suka ji muryar Islaha tana magana a sanyaye.
Chapter 46 · 0% Book details