← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 133

Sashe 58

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har lokacin yana riƙe da ita sai dai ya raba ta da jikinsa, bai kuma magana yin ba ya riƙo ta a yana sake riƙe hannunta suna takawa a hankali suka fito falon, ya zaunar da ita yana kallon yadda take kuka har lokacin.

Coat ɗin jikinsa ya cire, ya kwance necktie ya cire, ya rage bottuns ɗin saman rigar. Ya cire tucked in ya koma kitchen, ya dauƙo ruwa mai madaidaicin sanyi ya ƙaraso ya miƙa mata ya ce, "take it."

A hankali ta fara buɗe ido tana kallon abinda ya miƙo mata, bata gani sosai yadda ya kamata, amma tana ganin mutum a tsaye yana miƙa mata ruwa amma baza ta ce waye ba.

Ta karɓi ruwan ta sha ta ajjiye, ya bar wajan ya ƙarasa ya ɗauko panadol ya dawo ya bata guda ɗaya, dan ya ga alama tana cikin radaɗi, yana kula da yadda ta riƙe kanta yasan tana buƙatar pain reliever.

A hankali ta karɓa ta sha ta koma ta jingina da kujera, gabaɗaya ƙhamshin falon ya canja ya koma ƙhamshinsa. Gashi ya kunna ac ta fara fita a hankali, sai ƙhamshin ya haɗe da sanyin ya ba da wani yanayi mai daɗi.

A hankali ta fara jin relief ta koma sauke ajiyar zuciya a hankali, ta buƙe ido ta kai kallon ta gare sa, sai ta ga ya dora ƙafa kan ƙaya yana danna waya hankalinsa kwance.

Sai kuma ta ga ya É—ora waya a kunne yana magana cikin turanci, bai jima ba ya sauke wayar.

Islaha gefen fuskarsa take gani, gashinsa ya rufe gefen fuskarsa, ta miƙe zaune sosai gabanta yana faɗuwa matuƙa. Ta miƙa hannu ta ɗauki glass cup ɗin da ya miƙa mata, ta kai bakinta zata sha kenan Rehaan ya juyo suka haɗa ido.

Gabanta ya faɗi, glass cup ɗin hannunta ya faɗi ƙasa, ruwan da ta sha ya sarƙe ta ta fara tari. Islaha kallonsa take yi tana tari kamar yadda yake kallon ta

Sai kuma ya ɗauke kansa daga kallon ta ya cigaba da abinda yake yi ita kuma ta sake firgicewa. Da sauri ta miƙe tsaye tunawa da babu ɗankwali a kanta balle hijjab ɗin da ta shigo dashi, da sauri ta koma kitchen ta saka ta fito a hankali tana kallonsa kamar bai san da ita a wajan ba.

Kallonsa take yi ƙirjinta yana bugawa, kamar bai san ta fito ba duk da yana jin motsinta kuma ba kallon ta yake yi ba.

Ita dai ta kasa banbance yanayin da take ciki, gizo yake yi mata kamar yadda take yawan ganin fuskarsa a mafarki yana tambayarta bashinsa, ko kuma shi ɗin ne dai?. Tunda ta zo Jeddah take mafarkin sa, ta san kuma saka abinda ta yi masa a ranta ne ya saka take ganinsa, amma yanzu abin ya fara bata tsoro matuƙa, tunda gashi ta fara ganinsa a zahiri.

Gab da zata wuce ya sake juyowa ya kalle ta suka sake haɗa ido, yadda ta firgita hijjab ɗinta ya taɗeta ta baya ta zube a ƙasa, kuma bata daina kallonsa ba. Sai kuma ta miƙe da sauri ta juya ta fita da sassarafa bata sake waiwayonsa ba.

Shi dai bai motsa daga inda yake ba, shi kansa yana ganin kamar ya san fuskar, kawai bazai tsaya ya tsaurara tunani a kanta ba ne, bashi da wannan lokacin. Sai ya yi tsaki tunawa da maganar Ubaid, ya sake kallon inda ta zauna yana tuna duk abinda Ubaid ya faÉ—a a kanta.

Ya yi ƙaramin tsaki ya miƙe yana tuna yanayinta, ya shiga kitchen yana kallon abinda ta haɗa komai tsaf sai ɓawon dankali guda biyu da yake ƙasa.

Ya saka hannu ya ɗauke ya saka a dusbin, ya ƙaraso ya zuba tea yana buɗe casrool ɗin yana kallon abinda yake ciki. Fork ya ɗauka ya ci abinda ta yi, sai kuma ya zauna a kan dining ɗin da yake kitchen ɗin ya ci sosai, ya sha tea sannan ya miƙe da tea ɗin a hannunsa ya hau sama.

Islaha a yanayi na ruÉ—ani ta koma, ta cire hijjab É—inta ta ajjiye tana kallon kanta yana tuna fuskar wanda ta gani. Ta dafe kanta da hannu biyu a bayyane ta ce, "da gaske shine ko kuma...."

Sai kuma ta katse waccen maganar ta ce, "nan fa ba Yola bane, ya aka yi ya zo nan kuma?."

Ta ɗan runtse ido jin mararta tana murɗawa, ta buɗe idon ta ce, "Ya aka yi ya zo nan? Shine wai ko ba shi bane?" Ta faɗa da ƙarfi jin tunanin yana neman yi mata yawa.

Buɗe ƙofar ta ji anyi, ta kalli wanda ya shigo ta ga Maleek ne, ta bisa da kallom mamaki dan ta san baya nan.

Ya ƙaraso ya riƙe kafaɗarta ya ce, "Islaha are you Okay?."

Sai a lokacin ta tuna maganar da ta yi da ƙarfi ne ya ji har ya shigo, ita ta manta ma da ƙarfi take magana, a ruɗe take sosai. Ta ɗan matsa baya tana ɗaukar hular ta saka a kanta, sannan ta ɗaga kai alamun lafiya lau take.

Ya bita da kallo ya ce, "you look so stress, and why are you shouting?."

Islaha kamar zata kuka ta ce, "i'm not feeling wll."

"Okay, let me take you to the hospital."

"No, i'm feeling better."

"No, let me call my friend, he is a dr."

"No Sir, i'm Okay."

"are you sure?."

Ta É—aga kai alamun eh sannan ya ce, "don't stress yourself, ki kwanta ki huta." Ta É—aga kai shi kuma ya fita.

A hankali ta zauna tana tunanin wannan lamari, ita ta kasa banbance abinda idonta ya gani dan gani take kamar ba shi É—in bane. Ta ya zata ganshi a Jeedah bayan ta san a Yola yake? Shine ko kuma gizo yake yi mata saboda kuÉ—insa da ta É—auko? Sai ta sauke numfashi, ta jawo wayarta ta shiga lambar Hamma ta ga har lokacin bai yi unblocking É—inta ba. Ta rufe ido ta sauke nunfashi a hankali cikin kewar sa mai tsanani, kamar wasa ta ga kiransayana shigowa.

Ruɗewa ta yi, ta gigice ƙijrinta yana bugawa ta miƙe tsaye, hannunta yana rawa tana kallon sunan Hamma da yake yawo a kai, murmushi take yi tana zubar da hawaye ganin sunan masoyinta yana kiran ta.

Wayar ta katse bata É—auka ba saboda ruÉ—ewa, wani kiran ya sake shigowa, daÉ—i ya mamaye mata zuciya a bayyane ta ce, "Ya sake kirana, ya kuma kira, Hamma yana kira" ta faÉ—a hannunta yana rawa kafin ta É—auka.

Ta saka wayar a speaker ta toshe bakinta da hannunta ta kasa cewa komai, shima daga can ɓangaren kasa yi mata magana ya yi shiru yana jin saukar numfashin ta a hankali. Saheer ya murmusa har ta ji sautin murmushin.

Calmly ya ce, "Matar Hamma!."

Sai kawai ta fashe da kuka mai matuƙar sauti, ya sauke numfashi a tausashe ya ce, "na kashe wayata, na sake yin blocking ɗinki?."

Kai take girgizawa kamar yana ganinta, ta kasa magana sai kukan da ya sarƙe ta ya hanata cewa komai.

Saheer ya ce, "Islaha!."

Muryarta tana cracking ta ce, "Hamma!."

"Matar Hamma, ki bar wannan kukan mu yi magana. Kar ya sarƙe ki samu attack, ki nutsu mu yi magana."

Ta kasa cewa komai sai ya kashe wayar, sai ta ga video call yana shigowa, ta zauna sosai ta É—auka fuskar hammanta ta bayyana mai cike da annuri.

Kanta a sunkuye yake ta kasa É—agawa ta kalle sa, ya ce, "bakya so ki ganni ko?."

Ta girgiza kai ta ce, "kunyar ka nake ji Hamma, bazan iya haÉ—a ido da kai ba, ina jin nauyin kallon ka."

Ya yi murmuahi ya ce, "É—ago ki kalle ni." A

hankali ta É—aga kai ta kalle sa suka haÉ—a ido, ya ce, "filter ki ka saka ne?."

Ta girgiza kai alamun bata saka komai ba, kuma bata yi magana ba, ya ce, "fuskar ki ta kumbura kaÉ—an, sannan ta yi ja alamun kin yi kuka sosai. Baki da lafiya?."

Ta É—aga kai a hankali ya ce, "me yake damun ki?."

A sanyaye ta ce, "ciwon kai ne."

Ya girgiza kai ya ce, "kin sha magani?." Ta É—aga kai tana tuna wanda ya bata magani, tana ganin abin kamar a mafarki ya faru, kamar zata buÉ—e ido ace mafarki ne haka take hango abin a idanunta. A sanyaye ta ce, "na sha, kuma har ya fara dainawa."

"To ki je ki huta kar na dame ki, na san ku dare ya yi ko?."

Ta É—aga kai ta ce, "an yi sallar i'sha."

"to ki kwanta, gobe zamu yi magana ?" Ya faÉ—a da sigar tambaya yana kallon ta.

Ta girgiza kai tana shagwaɓa ta ce, "Ni dai kar ka kashe."

Saheer murmusa ya ce, "ina so ki huta, gobe in kin samu lokaci ki yi min magana, sai kira ki mu yi hira."

"In ka kashe baza ka kuma kira na ba."

"Zan kira ki mana."

Ta kalli idonsa ta ce, "baza ka sake ƙin kula ni ba?."

Duk da ya kula da hasken da ta yi, da ramar da ta yi bai yi mata magana ba ya ce, "bazan sake ba matar Hamma, ki huta kin ji?." Ta É—aga kai tana murmushi.

Ya bi jelar kitson ta da kallo ya ce, "da kan ki kika yi kitson?."

Ta kalli jelar kalbar sannan ta ce, "da kaina na yi...." da shagwaɓa ta ce, "na sha wahala, hannuna ya dinga ciwo. Na yi awa biyu ina yi."

Ya yi dariya ya ce, "Wannan gashin naki ai yafi ƙarfin ki daman, ke daman ba ƙwari ba."

Ta yi murmushi ta ce, "To bani da wanda zai yi min."

Ya sake yin dariya kaÉ—an ya ce, "Sai da safe."

Zata amsa kenan aka ɗan ƙwanƙwasa ƙofar, ta kalli ƙofar dan a tunaninta Sunaira ce sai ta ce, "come in."

Maleek yana shigowa gabanta ya faɗi, ta juya ta kalli Saheer da yake kallon Maleek da ya shigo, ya ƙaraso inda ta ke yana bata magani ya ce, "take this and sleep."

Ta karɓi maganin ta ce, "thank you." Ya yi murmushi ya juya ya fita.
Chapter 58 · 0% Book details