Sashe 118
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Islaha ta fara tunane-tunane, tana tunanin ta faÉ—a ta gefe kawai, dan gwara ta faÉ—a ta window tunda bata san inda zasu kai ta ba. Ta dinga kallon gefenta tana so ta faÉ—a amma tana jin tsoro, dan motoci suna ta kai kawo a wajen.
Tana wannan tunanin suka shiga estate É—in da babu yawan mutane a cikinsa sai manyan gidaje kamar su yi magana da bakinsu.
Abin mamaki wani bababn gida ta ga an yi horn an buÉ—e sun shiga da napep, har lokacin bindigar tana gefenta bai cire ba kuma bai yi magana ba.
Suna tsayawa duk suka fita, É—aya ya kalle ya ce, "fito."
Duk da tsoron da take ji hakan bai hanata ta ce, "bazan fito ba, ina ne nan?."
Ya É—an yi murmushi dan an zana musu halayenta tsaf, duk sun san zata yi taurin kai. Ya ce, "za ki fito ko sai na fasa kan ki?."
Ta runtse ido ganin yana nuna ta da bindiga, fito daga napep É—in ba dan komai ba, sai dan bata so ta mutu bata sake ganin fuskar Hamma ba.
Ya nuna mata wata ƙofa ya ce, "ki je ki shiga wannan ƙofar yanzun nan." Bata ce komai ba ta bi wajen da ya nuna mata, dan sai take ji kamar umarni kawai yake bata.
A hankali ta shiga falon da yake da haske ko ina, ta tsaya a falon tana kallo dan bata san me zata yi ba. Gashi dai bai yi kama da sato ta da aka yi a wancan lokacin ba, amma wannan É—in ma sata ce tunda ba a son ranta aka É—auko ta ba.
A wannan lokacin Jafar ya fito daga kitchen yana amsa waya, jin maganar mutum sai ta kalli wajan suka haÉ—a ido.
Jafar ya É—an zaro ido waje cikin mamakin ganinta, ya katse wayar ya kalle ta ya ce, "Miss Islaha."
Fuskar ta babu walwala ta ce, "Mr Jafar me na yi maka ka saka aka kawo ni nan?."
Yadda ta yi maganar cikin sanyi ya saka ya ce, "ki zauna miss, amma bani na saka aka kawo ki ba."
Islaha bata zauna ba, ta kalle sa ta ce, "To waye?."
Kafin ya bata amsa aka buɗe wata ƙofa, ta kai kallonta wajan ta gan shi ya fito cikin jallabiyya brown mai kyau da ɗaukar ido.
Kwata-kwata ba inda take tsaye yake kallo ba, ita kuma shi take kallo cikin mamaki da a'aljabi haɗi da takaicin sake arba da fuskarsa a duniya. Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta take faɗa mata kenan dai shine ya sake sato ta a karo na biyu, tunda ga shi ya saka an nuna mata bindiga an kawo ta inda bata yi niya ba.
Jafar tunda ya fito yake kallonsa, sai ya yi murmushi ya kalli Islaha ganin ta zuba masa ido tana binsa da kallon mamaki da wata irin fuska ta marasa mutunci.
Ya gyara tsayuwa dan yana so ya ga yadda za a kwashe tsakanin mai girman kai da mai rashin kunya.
Kafin ya gama tunanin yadda abin zai kasance Islaha ta ce, "Wannan abin ne ya saka a É—auko ni kenan...." sai ta kalli Jafar ta ce, "akan wanne dalili zai É—auko ni? Sata ko kisan kai?."
Jafar ya yi dariya ya ce, "ban sani ba, nima na gan ki ne kawai"
"To ya saka a mayar dani inda aka É—auko ni, ina da abubuwan yi da yawa ba zaman banza nake yi ba. Meye haÉ—ina dashi da zai saka a kawo ni nan? Ko an faÉ—a masa yanzu dah da zai sace ni ya kwana lafiya?."
Jafar murmushi yake yi ya ce "ask him."
Ta juya ta kalle shi, ta ga ya zauna akan kujara kamar ma bai san dashi take magana ba. Wani irin takaici ya mamaye mata zuciya, ita ko magana dashi ma bata so balle har ta tambaye shi dalili, tunda ya ce mata ƴar iska karuwa take jin bata taɓa jin tsanar kowa kamar yadda take jin tsanarsa ba.
Ta kasa magana, ta yi shiru ba dan ta kasa ba,
sai dan takaicin da yake gangaro daga zuciyarta.
Falon ya yi shiru babu wanda yake magana a cikinsu, kowa ya yi shiru ba kamar Rehaan da ya yi banza da ita.
Islaha ta katse shirun ta ce, "Ina da wani personal agender da kai da za ka saka a kawo ni nan?."
A lokacin ya ɗago ya kalle ta suka haɗa ido, ta ƙi ɗauke idonta daga cikin nasa ta ce, "Tun muna shaida juna da kai, ka saka a mayar dani inda ka ɗauko ni, ni ba ƴar tsana bace da za ka sace a duk lokacin da ka ga dama."
Ya É—auke kai daga kanta ya yi mata banza, takaicinta da haushi da tsana ya hana shi magana, bai san haka yake ji a kanta ba sai yanzu da take tsaye a gabansa, sai ya ji a baya ba komai yake ji ba kamar abinda yake ji yanzu.
Takaici ya kusa kai Islaha lahira, ga shi bata da wani ƙarfi yadda ya kamata balle ta yi masa hauka, raunin zuciyarta ya taɓa mata gangar jikinta, ta yi sanyi sosai, ba dan haka ba da sai ta ɗauki wani abun ta fasa masa kai.
Jafar dai yana zaune yana so ya ga ta inda Rehaan zai fara, haka kawai ya ɗauko ƴar mutane shi ya fi ƙarfin ya je gidansu.
Rehaan kamar zai yi magana sai ya fasa, ya É—ago ya sake kallon Islaha yana maimaita kalmar future wife É—insa ce a tsaye a gabansa, ya É—auke kai ya gyara zama bai ce mata komai ba.
Islaha ta kalli Jafar ta ce, "don Allah ka saka a mayar dani gida, ina da abinda zan yi da yawa. Bani da lokacin wannan shirmen, bani da lokacin É—aga murya a yanzu, ko wanne second na lokacina yana da mahimmaci a gare ni."
Jafar ya yi murmushi yana jan kujerar dining ya zauna ya ce, "Bani na É—auko ki ba Islaha, shine ya saka aka É—auko ki."
"To me zai yi min da zai saka a É—auko ni?."
"Ki tambaye shi."
"Wallahi baƙin ciki da haushinsa zai iya sakawa na shaƙe shi har sai ya daina numfashi. Bana ɗaukar abinda kowa zai iya ɗauka, zuciyata daban take da ta sauran mutane, abinda nake ji daban da na sauran mutane, bazan shiga lamarinka ba, kaima kar ka shiga nawa."
Jafar da ya ga dai Rehaan ɓata mata lokaci zai yi sai ya ce, "ya ɗauko ki ne akan maganar auren ku."
Ta É—an yi jim tana kallonsa kafin ta ce, "auren mu, ban gane ba."
Jafar ya ce, "eh auren ku, kin manta za ki yi aure ranar friday?."
"Ni ban gane ba fa, kamar ya zan yi aure ranar friday?."
Jafar ya ce, "kin gane mana, ai na san kin san da auren da aka ce za a yi miki ko?."
Islaha sai ta tuna da maganar Baffa ta ce, "oh! Wai shine daman wanda ake so a liƙa min ɗin nan?."
Jafar ya girgiza kai yana dariya bai ce komai ba, yadda ta yi maganar ta bashi dariya sosai, wai wanda ake so a liƙa mata.
Ta ce, "yanzu na gane, sunan ya zo É—aya da sunan mahaifin wanda aka faÉ—a min....."
Ta yi wani murmushin rainin hankali ta ce, "To ba a faÉ—a masa cewa na ce bana yi a kai kasuwa ba? Ko faÉ—a masa aka yi na rasa masu sona ne da har za a yi min tallansa har cikin gida?."
Jafar ya É—age kafaÉ—a ya ce, "ask him Miss."
Ta kalle Rehaan da ba ita yake kallo ba ta ce, "babu wani aure a tsakanina da kai, magana ta baki ma baza ta sake haÉ—a ni da kai ba har abada balle aure. Ni ina da wanda zan aura, tallan aurenka da aka kai min kuna a kai kasuwa, ni a wajena bani da lokacin magana da kai balle auren ka....."
Ta dakata tana harɗe hannu a ƙirji ta ce, "Malam zan ce maka ko Alhaji? Ka saka a mayar dani kamar yadda ka ɗauko ni."
Sai a lokacin ya ce, "So go and tell your father to inform Abba about what you said, so the marriage can be called off."
Ta bisa da harara tana yi masa kallon up and down ta ce, "gani ga ka ai, ba sai an faɗawa kowa ba. Na ce maka bana yi, sai a haƙura ko?."
Rehaan ya lumshe ido yana jin ɗan dama dama a ransa, jin ta ce bata so kuma baza a yi auren ba ya yi masa daɗi, ko haushin rashin kunyar ma ba ya ji, tunda bata so abin ya zo da sauƙi.
Ya ce, "Kina da plan mai girma a kaina, kina shigowa rayuwata ta ko wanne ɓangare. Yanzu kuma kin zo ta ɓangarren aure...ina so na faɗa miki, ni Rehaan na fi ƙarfin ki, ki canja tunani."
"Hey Mr man! In na shiga rayuwar ka na ce na shiga rayuwar wa?...." Ta nuna sa da yatsa ta ce, "na ce na shiga rayuwar Rehaan Yola? To na samu ribar me?."
"Mr man ina so ka faɗa min da ni da kai waye ya shiga rayuwa wani, sannan ka tuna har gida aka kai min katin gayyatar auren ka, ka ga ni nake da bakin da zance nafi ƙarfin ka, tunda kai aka kawo min tallah, ba ni aka kai maka tallah ba....."
Ta yi dariyar rainin hankali ta ce, "Ai ban san arhar ta ka ta kai haka ba, ban san rashin class da ƙaryar iyayin naka a nan ya tsaya ba. Tunda aka ɗauko tallan auren ka, aka zo har gida aka samu mahaifina, ana neman na amince na taimaka na aure ka, ka dawo zero percent a idanuna..."
"Ka jira lokacin da aka kai maka tallan Islaha, daga lokacin ne ka ke da bakin cewa ta canja tunani, amma daga lokacin da aka je aka zauna da mahaifinta, aka ce an gani ana so na amince nace ina yi, na fi ƙarfin waɗannan kalaman na kan harshen ka. Ba ni da lokacin ɓatawa, ka bar maganar, dan bazai yu ba har abada!."