Sashe 14
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya buɗe baki kamar baya son magana ya ce, "So......you can't say sorry for your mistake?."
Anya Islaha zata ce sorry ɗin nan?🤣🤣🤣
Nana Haleema.
[6/18, 10:05 AM] KRBBK: RDB2P09
Nana Haleema.
Kamar a sama haka ta ji maganar, ta ɗago da sauri ta kalle sa sai ta ga kamar ba shine ya yi maganar ba, dan tunda ya sato ta bai taɓa yi mata magana ba sai yanzu.
Da ta ji yadda ya furta maganar da english sai ta tabbatar da ba bahaushe bane, dan ko kaÉ—an turancin sa bai yi kama da irin na wanda ya koya ba, kana jin yadda english É—in yake fita ka dan yaren sa ne, kuma british english yake yi.
Ta ɗan kalle sa kallon up and down, da ta tabbatar baya jin hausa, sai ta taɓe baki ta ce, "Ji shi don Allah, wai jira yake na bashi haƙuri daman? To me na yi masa da zan basa haƙuri?" Ta faɗa ƙasa-ƙasa cike da mamaki ba tare da ta san ya ji ba.
Rehaan ya ɗan ɗago ya kalle ta suka haɗa ido, ta ɗauke ido dan ba ji yake yi ba. Ta mayar da idanunta gefw ta ce, "ji shi yana kallona, kamar ji me nake faɗa. Ni dai bazan ba da haƙuri ba, sai dai ya kashe ni."
Rehaan ya girgiza kansa yana mamakin wannan yarinya mai kama da aljanu, ya É—auke kai bai ce komai ba.
Ta ce, "Ni ban yi laifin da zan bada haƙuri ba, kaine ka yi min laifukan da zaka bani haƙuri ba ni ba. Ka zuba min tea a hotel, ka kalle ni ka share kamar baka sanni ba. Ka fasa min wayata a asibiti, amma ka share ko sannu baka ce min ba, yanzu kuma ka sato ni ka kawo ni nan, kuma duk jira ka ke na baka haƙuri?. Lallai sannu Malam bature...Ko zan iya sanin sunanka?" Ta faɗa tana kallonsa.
Bai motsa ba baice mata komai ba, ta É—an girgiza kai zata yi magana aka kira wayar sa. Ya kalli wayar sai ya É—auke kai bai É—auka ba ta cigaba da rining har ta katse.
Islaha ta ce, "kai! Daman waya tana aiki a gidan nan? Kenan ni aka kashewa services?" Ta faÉ—a a hankali tana kallo wayarsa da waya ta kuma shigowa.
Wayarta ta gani a ajjiye a akan table, ta kalle sa ta ga kamar ya manta da ita a wajen a zaune, harda lumshe idanunsa kamar mai jin bacci.
Islaha ta ce, "bawan Allah baka ce komai ba, ka bar ni na tafi yanzu, duk abinda ka ke ji dashi a kaina daga baya sai mu tattauna."
Bai kalle ta ba dan bazai sake yi mata magana ba, ko me zata ce ya gama da ita, shi dai bazai yi magana ba. Ya miƙe zaune sosai yana sauke ƙafa daga kan table ya ɗauki wayarsa yana dannawa.
Hawaye ya sakko daga idon Islaha, ta tsani wulaƙanci a rayuwarta, musamman ta yi magana an jita kuma a share, yana daga cikin abinda yake tunzurata sosai, yanzu zata fusata ta birkice ta hau bala'i. Ta bi sa da kallo zuciyar ta tana tafasa sosai ta ce, "ka kashe ni mana kawai ka huta."
Bai ko kalle ta ba ya cigaba da abinda yake yi, sai daga baya ya kalle ta, ya ga ta zuba masa ido, ƙiris take jira ta shaƙe shi saboda takaici. Bai ce komai ba ya miƙe ya hau sama ya bar mata wajan bai sake kallon inda take ba.
Isaha ta bisa da kallo bata motsa daga inda take ba, yana ɓacewa ta ƙarasa ta ɗauki wayarta ta danna taga tana yadda take, ta kalli saman wayarta amma har lokacin no services.
Abin ya bata mamaki, ganin shi gashi har waya tana shigowa wayarsa amma ita wayarta babu services. Inda ya tashi ta kalla, ta ga rafar dala ɗari ne guda biyu a ajjiye, ta ɗauke kai ta nemi waje ta zauna dan bazata fita ba, so take ayi ta ta ƙare kawai, in zai barta ta tafi ya barta, in bazai barta ba ya faɗa mata me yake nema da ita,
Shi kuwa yana hawa sama Shams ya kira a waya, yana É—auka ya ce, "Da gaske tana da mara lafiya?."
Shams ya ce, "yes Sir. Wanda yake riƙon ta za a yiwa dashen ƙoda."
"Meyasa baka faÉ—a min ba?."
Shams ya yi shiru dan bai san me zai ce ba, lokacin da ya yi niyar faɗa masa shine ya dakatar dashi daga faɗar, amma a yanzu ya san halin ogan nasu bazai taɓa karɓar uzurinsa ba.
Rehaan ya ce, "Is okay " daga haka ya kashe wayar ya zubawa madubi ido yana kallon kansa kamar mai son gano wani abun.
So yake ya ajjiye ta tayi shekara ɗaya a gidan bata je ko ina ba, so yake ya nuna mata waye shi ta tabbatar yana da ikon da zai iya ɓatar da ita daga duniyar babu abinda aka isa ayi masa.
So yake ya saka ta saduda, bakin tsiwar ya mutu, so yake ta zube tana bashi haƙuri tana roƙan ya haƙura ya fitar da ita daga gidan. Bai ɗauko ta don ya azabtar da ita ba, ko dan ya yi mata wani abun ba. Kawai iko yake so ya nuna mata, ta san waye shi.
Ya sauke nunfashi yana kallon kansa, saboda mara lafiyar da aka ce dole zai yi haƙuri ya ƙyale ta, tunda har aka ce babanta ne, kuma yana da matsalar kidney ba abin wasa babe, babbar damuwa ce da ya kamata ya haƙura ya janye ƙudurinsa. Ya san daɗin iyaye, ya san ya ake ji in basu da lafiya. Ba dan ta isa ba, sai dan girma da darajar iyaye, in ba dan haka ba sai ta shekara a gidan ko compound baza ta fito ba, sai ya nuna mata iko da matsayin da yake dashi.
Ya yi tsaki a bayyane ya ce, "amma bata bani haƙuri ba, sannan...." Sai ya yi shiru yana cigaba da kallon kansa kamar mai son gano wani abun a fuskarsa ko jikinsa.
Ya furzar da iska a bayyane, ya lumshe ido ya buÉ—e, ya shafa gashin kansa yana É—an girgiza kai ya ce, "is okay Rehaan, stop this drama please, allow her to go, saboda lafiyar babanta. Allow her Rehaan."
Ya faɗa yana rarrashin kansa, dan so yake ya nuna mata shima babban mai taurin kai ne da kafiya, duk rashin jinta ya fita, ba ita kaɗai ta iya taurin kai ba, shima ya iya, ba ita ce mara kunya ba, shima ya iya. So yake kawai ta tabbatar ba kowa ake ɗagawa murya a kwana lafiya ba, shiyasa yake rarrashin kansa akan ya barta ta tafi, rashin lafiya tana gaba da ƙudurinsa.
Bakin gado ya koma ya zauna, ya ɗauki wayarsa ya shiga camera falon da aka ajjiye ta yana ganin lokacin da suka yi magana da Shams da abinda take faɗa masa. Ya ajjiye wayar ya rufe ido yana fatan bacci ya ɗauke shi, amma da ya rufe ido sai ya tuna da ita, zuciyarsa tana faɗa masa yanzu in ya bari ta tafi ta yiwa banza kenan. Ya ja numfashi da ƙarfi, ya sake rufe ido ya rasa abinda ya kamata ya yi.
Islaha kamar mayya ta ƙi barin falon, tana zaune akan kujera, daga ƙarshe ta zame ta zauna a ƙasa ta kwantar da kanta akan kujerar tana rufe ido cikin tunani kala kala da ya tokare mata zuciya.
Ta yi alwashin babu inda zata je, a wajan zata zauna sai da in ya dawo ya saka a kashe ta, ta gaji da rainin hankalinsa.
******
"Yauwa Malam Sadik. Tun É—azu nake neman ku. Na ga sanarwa an sace Islaha?" Dr Isma'il ya faÉ—a yana kallon Sadik cikin damuwa.
Sadik ya ce, "Wallahi an sace ta, mun yi iya abinda zamu yi ba a ganta ba. An yi cigiya a inda aka san tana zuwa ba a same ta ba. Daga ƙarshe wani mai napep yazo ya ce a gabansa aka ɗauke ta."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kuma an kai repost wajen Æ´an sanda?."
"An kai Dr. A gaban Æ´an sandan ake faÉ—ar an ga lokacin da aka sace ta. Ana ta bincike a kan hakan."
"Allah ya bayyanata cikim aminci, Allah ya sa ba garkuwa aka yi da ita ba."
"Amin ya Allah."
Dr ya ce, "Akan maganar aikin mahaifin ku ne."
Sadik gabansa ya faÉ—i, amma bai nuna ba ya ce, "Ina ji Dr."
"ya kamata a haɗa kuɗin aikin nan a kawo, sai kuɗi yazo sannan zamu saka file ɗin ku a layin waɗanda za a yiwa aiki. Duk da na faɗawa wanda muke saka ran zai yi aikin, kuma ya amsa zai yi ɗin. Shine mai asibitin gabaɗaya, na faɗa masa zancen aikin ya ce na tuna masa ranar lahadi. Aikin mahaifin ku shine kaɗai dashen ƙoda da za a yi a ranar, dan haka dole ya kasance an shirya komai yadda ta kamata. Inda kuɗin a hannun ku aje a biya yanzu, in aka biya zasu tura file ɗin, in ya ga komai ya tafi yadda ya kamata sai ya fi mayar da hankali akan aikin."
Sadik ya ja numfashi ya ce, "zuwa yaushe kenan?."
"Gobe ko jibi, ya kasance an biya kuÉ—in. In aka biya kuÉ—in ma kafin ranar, in ya san da maganar za a iya yin aikin a wuce wajen."
Sadik ya gyaÉ—a kai ya ce, "in sha Allah za mu san abinda ya kamata mu yi, za a haÉ—a kuÉ—in kafin lokacin."
Dr ya ce, "Haka ya kamata ayi. In ka biya kuÉ—in ka faÉ—a min, duk da zasu tura min amma ka faÉ—a min ta yarda zan sanar da Dr É—in."
"Shikenan Dr, na gode" ya faɗa yana miƙewa ya fito jikinsa a sanyaye.
Yana ƙarasowa reception ya ga su Mama suna jiran ya ƙaraso. Ya ƙarasa suke ya ce, "Akan maganar kuɗin aikin ne Adda, an ce ana so a biya kuɗin daga gobe zuwa jibi. Kuma ni wallahi tunda Islaha ta ɓace hankalina ya rabu biyu, har yanzu bazan ce ga abinda aka samu ba."
Adda ta ce, "ai dole hankali ya rabu biyu, ga aiki ga kuma ɓatan Islaha. Yanzu ya zamu yi?."