← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 133

Sashe 22

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamy ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Zuwa yanzu ya kamata ace ka yi aure."

Ya kalli Mamy ya ce, "ba kin ce zaki zaɓa min mata ba? Na baki dama kawai, ko wacece indai tayi miki nima tayi min, amma ban da cousins."

Mamy ta girgiza kai tana ɗan murmushi ta ce, "Ga Ikram nan na faɗa maka, itace zaɓina."

"Mamy ban dasu."

"To ai gidan nan baza su yarda da zaɓina ba, kuma kakarka ta zaɓa maka matar aure."

"Wannan matar tana da mental issue fa, babu wata mata da zan aura daga wajanta Mamy. Ko an aura min sai na warware" ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Mamy ta miƙe tana dariya ta ce, "Kai da Kakarka, wallahi babu ruwana, baza ka jawo a dinga ce min ni na zuga ka ba."

Ya ɗan girgiza kai yana ɗaukar wayarsa ya ce, "matar aure indai ba daga wajan ki ba, bazan karɓa ba.....Zan kwanta Mamy."

"Okay Baby. Kwana biyu baka yin azumi litinin da alhamis, meyasa?."

Ya É—an shafa kansa ya ce, "Zan yi, sai na je Jeddah."

"Yauwa, bana so ka daina, shine garkuwar da yake kare ka."

Ya ɗaga kai ya ce, "In sha Allah" ya faɗa yana fita daga apartment ɗin ta bida sa kallon ƙauna da soyayya.

Gab da zai shiga apartment ɗinsa ya hango Salman yana tahowa inda yake, ya tsaya cak duk da wajan akwai rana amma haka ya tsaya yana kallonsa har ya ƙaraso. Yana ƙarasowa Salman ya ce, "Kai na ɗaukowa."

Ya faɗa yana miƙa masa roba ta natural tamarind drink. Rehaan ya karɓa yana murmuahi ya ce, "na gode sosai."

Shima murmushi ya yi yana kallonsa. Rehaan ya shiga ciki sai ya ga shima ya biyo bayansa. Bai hanasa ba ya bari ya ƙarasa shigowa sannan ya kulle ƙofar. Suna shiga falon aka fata ƙwanƙwasa ƙofar, Rehaan ya dawo da baya ya buɗe ƙofar ya ga Umma ce.

Ya ɗan kalle ta a taƙaice ya ce, "ina yini."

Umma ta harare sa tana tsaki ta ce, "Sai yau ka san ya na yini?..." ta kalli Salman ta ce, "Salman fito" ta faÉ—a tana shiga falon tana kallon Salman.

Salman ya ƙi kallon ta ya ce, "a nan zan zauna." Ta yi tsaki ta shiga ciki ta riƙo hannunsa ta ce, "ina magana kana daɗa gyara zama, dallah ta so."

Salman ya ƙi tasowa ya fizge hannunsa ya yi bayan Rehaan yana neman ya cece sa. Shi kuma ya rasa ya zai yi, sai ya kalli Umman a sanyaye ya ce, "Umma ki bar shi a nan ɗin."

Umma ko kulasa bata yi ba sai da ta riƙo hannun ɗanta sannan ta ce, "na bar shi ka cigaba da yi masa kallon mahaukaci ko? Har ka samu damar cewa zaka kai shi asibiti, kai ga mai kuɗi ko...?" Ta ƙarasa faɗa tana hararar sa.

Ta kalli Salman ta ce, "Mu je" ta faɗa tana jan hannunsa da ƙarfi suka fita daga falon.Ya yi ajiyar zuciya yana kallonsu har suka fita daga wajan gabaɗaya. Zai kulle ƙofar kenan ya ga kiran Abba yana zuwa wayarsa, ya ɗauka da sallaama, Abba ya amsa ya ce, "ka same ni a falo" daga haka ya kashe wayar.

Rehaan ya É—an yi jim, kafin ya mayar da wayar aljihu yana ji kamar ya yi kuka, dan bai san me Abba zai ce masa ba. Babu yadda ta iya haka ya fito daga falon ya nufi wajan Abba.

A falo ya samu Abba da Mama a zaune, ya shiga da sallama suka amsa ya zauna, ya É—an kalli Mama ya ce, "ina yini."

Ta wani kalle sa kallon rainin wayo ta ce, "daman ina so na yi maka magana, wato nuna mana ka ke yi Nadira ce kaÉ—ai babar ka, mu ba iyayenka bane. Kwanan ka nawa baka gidan nan, da ka dawo ba sai ka shiga wajan kowa ka gaishe ta ba? Sai yanzu da ka ganni da Abba shine zaka wani ce ina yini? Gaisuwar ma sai a kan hanya za a yi?."

Shi dai ya yi shiru bai ce komai ba, sai Abba ne ya ce, "baka kyauta ba Rehaan."

Ya yi ƙasa da kansa bai yi magana ba, dan bai san me zai ce ba. Abba ya ce, "akan maganar matar da Daada ta zaɓa maka ne, na nemi unguwarsu kuma na ji labari akan iyayenta. Abinda ya dakatar dani an ce min mahaifinta yana asibiti bashi da lafiya, shine maganar ta dakata, da yanzu sai dai ka ji an tsayar da lokacin auren."

Rehaan ya kalli Abba cikin wani yanayi, Abba ya É—aga masa kai ya ce, "Ka cigaba da shiri kawai, ku cigaba da shirye-shiryen auren ku kai da Jafar. In kana Jeddah zaka ji labarin an saka ranar aure, kar kace ban faÉ—a maka ba. Ka fara shirye-shirye dan tare zaku angwance da Jafar......" ya faÉ—a yana kallonsa kamar yadda shima yake kallon Abban.

Another banger🔥😂😂😂

Nana Haleema.
[6/23, 11:47 AM] KRBBK: RDB2P15
Nanahaleema.

Rehaan ya ɗago yana kallon Abba jin abinda yake faɗa, ransa ya ɓaci sosai, yana ji a ransa ko me zai faru bazai taɓa auren zaɓin Daada ba sai dai ko meye ya faru.

Rehaan ya kalli Abba ya ce, "Abba ban santa ba fa."

Abba ya É—aga kai ya ce, "Na san baka santa ba, amma kafin auren ai zaka santa."

Rehaan ya ce, "Abba na faÉ—a maka bana ra'ayin auren nan, meyasa zaka biyewa Daada don Allah?."

"Saboda uwata ce Rehaan, dole na biye mata nayi abinda take so."

"Wanne irin aure ne wannan? Ban san yarinya ba, itama bata sanni ba, ace za a aura min ita?. Kuma kowa ana basa dama ya kawo wacce yake so amma ni meyasa za a yi min haka?."

"Sai haƙuri, hakan za a yi Rehaan." Ya sauke numfashi bai ce komai ba zuciyarsa cike da jin haushi da takaici mai yawa.

Mama cike da makirci ta ce, "gaskiya dai Abba a duba lamarin nan, a bashi dama kamar yadda ake bawa ko wannen su dama ya kawo wacce yake so."

Rehaan ya kalle ta ya ce, "ki faÉ—a masa please, bana son auren nan, meyasa ake so dole sai an yi min?."

Abba ya ce, "Rehaan gwara ka so auren nan, dan yin sa babu fashi, gwara ka daina ja kawai."

Ya ɗan shafa kansa bai ce komai ba, Abba ya ce, "tashi ka je, na san lokacin yin baccin ka ne yanzu. Zamu ƙarasa maganar in ka farka."

Ya gyaɗa kai ya miƙe ya fita yana ji kamar yaje ya shaƙe Daada ta mutu kowa ma ya huta, saboda haushinta ko gaishe ta bazai je ba ya yi shigewar sa apartment ɗinsa.

       ******

Cikin lokaci kaɗan labarin ganin Islaha ya zaga ko ina, ana ta yi mata addu'ar barka da dawowa da fatan Allah ya kiyaye gaba. Ita kuwa tana gida, tunda Saheer ya rakata ɗaki take baccin gajiya da baccin da ya taru a idonta. Dan ko da Safeera basu yi magana ba, ganin tana jin bacci ya saka ta ƙyale ta.

Sai bayan sallar magrib ta farka, ta yi wanka ta yi sallah ta fito falon babu kowa alamun duk basa nan. Tana gab da shiga kitchen Saheer ya shigo da sallama, ta amsa ya bita da kallo ganin kanta babu É—ankwali, gashinta ya sauka har baya, sannan gashin ya yi tudu daga sama, kamar wacce ta hargitsa shi da hannunta.

"Da daren nan ki ke yawo haka?."

Ta É—an yi murmushi ta ce, "abinci nake so na ci, sai na kira ka mu je asibiti."

Ya bita da kallo kafin ya tako inda take ya ce, "ki je ki saka É—ankwali sai kizo ga abinci na siyo miki."

Ta ɗaga kai ta juya ya bi dogon gashinta da kallo, ta sauke numfashi, yana jin shauƙi in ya tuna nan da lokaci kaɗan ba gashinta kaɗai ba, ita kanta nan gaba mallakinsa ce.

Ba jimawa ta dawo ta ɗaura ɗankwali ta zauna ya bata pack ɗin abinci, ta karɓa ta ga fried rice ce da chicken, an zuba mata sauce mai albasa sai ƙhamshi take yi. Ta ɗauki disposable spoon ta ɗebi ta fara ci.

Yadda bakinta yake moving É—aukar hankalinsa yake yi, bakinta yana daga cikin abinda yake É—aukar hankalinsa akan fuskarta. Bata san yana kallon ta ba abinci take ci, sai daga baya ta É—ago suka haÉ—a ido. Sai yaji kamar ta watsa masa wuta, yadda ta É—ago É—in ya saka ya ji sabuwar soyayyar ta a zuciyarsa.

Islaha ta ce, "Hamma baza ka ci ba?."

Ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "na ƙoshi, ke na siyawa."

Ta kalle sa ta ce, "ya na ji voice É—inka ya canja, meya faru?."

Ya kalli idonta kafin ya yi murmushi bai ce komai ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya ya ce, "ya kika kasance a cikin kwanakin da ki ka ɓace? Wacce irin rayuwa ki ka yi?."

Gabanta ya faÉ—i sosai, ta kalle sa a hankali bayan ta É—auki ruwa a cikin ledar da ya kawo mata, ta sha sannan ta ce, "kullum sai na yi kuka."

Ya É—aga kai ya ce, "na san zaki yi Islaha.....Ana kiran sallah, zan je na yi sallah, in na dawo sai mu tafi ko?."

Ta ɗaga kai ta ce, "to." Bai ce komai ba ya miƙe ya fita, itama bata jima tana cin abincin ba ta miƙe ta shiga ɗaki. Ta jima da gama shiryawa sannan ya yi mata waya ya ce ta zo su tafi, ta fita ta gan shi a mota a zaune ta shiga ta ce, "wannan motar fa Hamma? Na ga bata Hamma Sadik bace."

Ya fara jan motar sannan ya ce, "daÉ—ina dake baki da duhun kai, kina da tambaya akan abinda baki sani ba. Indai kika ga canji sai kin yi magana."

Ta yi dariya kaɗan, shi kuma ya ce, "sabuwar da Sadik ya siya ce, da ni zan siya to saboda aikin Baffa ya saka nace masa na fasa. Yanzun ma ya ce na riƙe, ni kuma bana son bashi. Daman da ba a samu kuɗin aikin Baffa ba, da ita za a siyar. Daman niyata muyi aure da sabuwar mota, sabuwar amarya, sabon gida, sabuwar mota."
Chapter 22 · 0% Book details