Sashe 30
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*JEDDAH, SAUDI ARBIA*
*AL HAMRA, CORNICHE RESIDENCES.*
Unguwa ce mai kyau da tsari, unguwa ce mai ɗaukar hankali tun daga kallon farko zaka san ko a cikin ƙasar saudia ba ƙananun mutane ne suke zaune a cikin ta ba. Unguwa ce mai cike da tsafta, da tsaro na musamman.
Ko ina na kan titin unguwar al hamra cike yake da cameras saboda tsaro, unguwa ce da take kusaa da ƙaton tekun Corniches, babban ocean da yake ɗaya daga cikin manya manyan ruwan da ake ji dasu a garin Jeddah. Unguwa ce da take ɗauke da gidaje masu kamar hotel, wanɗanda ake yi musu laƙabi da hotel style. To ko wanne ɓangare unguwar Hamra ta yi.
Rehaan yana tsaye daga cikin apartment ɗinsa, yana tsaye a bedroom ɗinsa ya yaye labule yana kallon ƙaton ocean ɗin da ya mamaye bayan ɗakinsa.
Hannunsa riƙe da mug yana shan tea a nutse, hannunsa ɗaya yana cikin aljihun wandonsa yana kallon yadda mutane suke hutawa a wajan, suna kai kawo ana shan drink. Ya sauke numfashi yana lumshe idanunsa, haka kawai fuskar Islaha ta zo idanunsa, ya ɗan runtse ido yana cize bakinsa, irin ka tuna abinda baka so ka tuna ɗin nan. Ya yi ƙoƙarin kawar da hotonta daga idanunsa, ya cigaba da shan tea ɗin amma still ita yake gani tana harararsa.
Kalamanta ya tuna, sai ya murmusa ya girgiza kai yana taɓe bakinsa. Shi bai taɓa ganin yarinya mara hankali kamar ta ba, da zai san danginta da ya basu shawarar a kai ta asibiti a dubu lafiyar ta, dan tana da matsalar ƙwaƙwalwa.
Door bell ɗin da aka danna ya katse masa tunani,ya fito daga ɗakin a nutse, ya sauka downstairs ya ƙaraso ya buɗe ƙofar falon.
Ubaid da Maleek ya gani, maƙotansa mafi kusa, wanda gidansu yake kusa da na juna. Apartment ɗin Rehaan shine a tsakiya, sai na Ubaid a ɓangaren dama, sai Maleek a ɓangaren haggu. Ubaid likita ne shima, sun taɓa aiki a asibiti ɗaya shi da Rehaan, ta dalilin haka suka saba dashi.
Sun saba da juna sosai, tare suke haÉ—uwa a buga ball, a É—an sha tea, a yi hira. Dukkansu larabawa ne, Maleek balaraben Saudiya ne haihuwar Riyad, Ubaid kuma balaraben Egypt ne. Maleek yana da aure, Ubaid kuma bashi da aure.
Rehaan da ya buɗe ƙofa ya gansu sai ya yi murmushi yana kallon su kamar yadda suke kallonsa suna murmushi.
Cikin turanci harshen Maleek ya ce, "Rehaan barka da zuwa." Gaisawa suka yi, suka shiga falon suka zauna.
Rehaan ya zauna shima ya ce, "ya aiki?."
"Alhamdu lillah. Baka faÉ—a mana zaka zo ba, da mun shirya maka abubuwa na musamman."
Ya É—an murmusa ya ce, "na zo aiki ne, bazan jima ba zan koma."
Ubaid ya ce, "ina Jafar?."
Rehaan ya ce, "Yana Englaand."
Maleek ya ce, "kai kaÉ—ai zaka zauna?."
Rehaan ya É—aga musu kai yana É—an murmushi bai ce komai ba. Sai kuma Rehaan ya ce, "yauwa ina son house maid, ku tura min maid daga wajan ku, zan dinga biyansu in sha Allah."
Ubaid ya ce, "Bani da House maid, amma za a kawo min daga Nigeria. Ka san na fi son aiki da yan ƙasar ku, musamman mata."
Rehaan ya bisa da harara cikin takaicin wanann É—abi'a ta Ubaid. Ubaid ya yi dariya ya ce, "da gaske nake, za a kawo min house maid daga can. In sun zo sai mu dinga sharing, is normal."
Rehaan ya yi masa banza, dan in akwai abinda yake jin haushi bai wuce matan ƙasar sa da suke barin ƙasarsu su taho aikin gidajen larabawa ba, abin yana yi masa ciwo matuƙa, dan bashi da damar da zai hanawa ne, amma wallahi da sai ya hana ɗan nigeria zuwa Saudia aiki a gidan larabawa.
Ƙasa mai girma da daraja kamar Nigeria, amma matan cikin ta sun saka ƙasa suna tuntsurar da mutuncinta. Da ace aiki ne mai tsafta da tsari da sauƙi, to yawancin wannan aikin da shirme da watsewa yake ƙarewa. Duk da ba duka ne ɗaya ba, amma majority haka ce take faruwa.
Ya san kalar rayuwar da suke yi a ƙasar, ya san babu abinda larabawa suka raina a yanzu kamar ƴan Nigeria, saboda ƙasƙantar da kansu da suke yi a ƙasar da sunan aikatau. Yana zama cikin larabawa, yana jin yadda suka mayar da matan nigeria kamar toys, wasu matan sune suke kawo musu kansu dan su samu kuɗin abinci.
Ya san halin Ubaid sosai, mayen ƴan mata ne lamba ɗaya, duk macen da ta yi aiki a gidansa sai dai Allah ya kyauta kawai, dan yana da kuɗin da yake sakar musu, lokaci ɗaya mata suke rikicewa, su ruɗe duk abinda yake so zasu yi masa shi. Shiyasa har rige rigen kawo masa ƴan mata ake yi daga nigeria. Dan wanda ya kawo ma zai samu, itama in ta bada kanta babu abinda bazai yi ba, baya jin ƙyashin kashewa ƴan mata kuɗi, ƴan matan ma na Nigeria, musamman baƙar fata. In aka ce mace baƙa ce ta shiga uku a wajen Ubaid, ya dinga nacewa mace kenan har sai ta amince masa, dan yana da kyau da kuɗi, da wuri suks faɗawa.
Shi kuma Rehaan haushin hakan shiyasa basu cika shiri da Ubaid ba, Maleek ne mai halin kirki, sun fi shiri dashi sosai akan Ubaid. Bai shiga shiga harkar Ubaid ba, dan ya tsani É—abi'unsa sosai.
Maleek ganin yadda Rehaan yake hararar Ubaid sai ya yi dariya ya ce,"Kar ka damu Dr, zan turo maka housemaid daga gidana, duk da nima babu sosai, amma za a kawo. Matsalar suna jin tsoron cheetah da ka ke kiwo ne fa."
Ya ɗan yi murmusui yan shafa kansa, sai a lokacin ya tuna bai ma je ya ɗauko ajiyarsa ba, daman Jafar ne yake takura masa akan a ɗauke su, amma shi kam yana son kiwo, musmaman kiwo irin na su Cheetah wanda ba a ko ina ake yin su ba sai a gidajen larabawa. Kiwon damisa ko zaki a manyan gidajen larabawa ba komai bane, sun saba yi sosai. Ya so ya yi a gida Nigeria Abba ya hana, sai da ƙananun abubuwa irinsu ɗawisu.
Ya ce, "in anjima zan je na ɗauko ta, kuma baza ta yi musu komai ba. Ƙarama ce sosai, bata cutarwa."
Maleek ya ce, "nima tsoron gidan nan naka nake ji indai har suna nan."
Ya sake yin dariya kaÉ—an, kafin ya tashi da niyar kawo musu black tea, sai da ya shiga kitchen É—in ya yi tsaki, dan shi ya tsani aiki, yafi so komai ayi masa.
A kawo masa tea kuma a ɗauke cup ɗin, inda dama a bashi a baki hakan yafi masa daɗi. Ya tsani sai ya dawo daga aiki ya dafa tea, shiyasa yake tsaywa a cafe ya siya, yana tuƙa mota yana sha. Gabaɗaya ya sangarce, babu abinda ya iya sai dafa tea ɗin kawai, shima daga ruwa sai lipton da sugar, bayan hakan babu abinda ya iya sakawa. Shiyasa ya damu da rashin housemaid ɗin, sai danasani yake da bai taho da chef ba.
Yana dafa ruwa a kettle yana tsaki, yana ji ransa yana ɓaci, yana jin dole ma a samu masu aiki, dan shi bazai iya wata wahala ba, daman Jazy ne ya sallame, gashi ya rasa yadda zai yi. A haka ya kawo musu suna sha suna ƴar hira kaɗan kaɗan.
Nana Haleema.
[6/25, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P021
Nana Haleema.
Ummi ta bi Muslim da kallo lokacin da ya shiga office ɗinta, bayan ya zauna ta miƙe ta rufe ƙofar ta jingina da ƙofar ta ce, "meye plan na gaba?."
Ya bita da kallon mamaki da tsoro ya ce, "kina nufin baki zubar da makamanki ba duk abinda ya faru?."
Ta sauke numfashi tare da harɗe hannu a ƙirji ta ce, "Yanzu aka fara wallahi, dan an kama ni an kai ni gaban hukuma ba hakan yana nufin zan ja da baya ba."
Muslim ya girgiza kai ya ce, "kina bani tsoro Ummi, har yanzu akwai zargi a kan ki fa"
"Sai me?."
"Hmmm! Na É—auka kin yi sanyi ai."
"Har abada wallahi, sai na ga bayan Islaha."
"Dakyau! Kin san in aka kama mai keken nan akwai damuwa ko?."
"Yana ina yanzu haka?."
"Na ce ya ɓuya, kar ya sake ya fito inda mutane zasu ganshi, in aka kama sa kema kin san mu ma nun kamu."
Ta dafe kai ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Ni so nake na ji ka shirya wani abu akan Islaha, so nake na ji ka haɗa gagarumin plan ɗin da zai tarwatsata ita da rayuwarta gabaɗaya."
Muslim ya ce, "ɗaukar mataki a kanta ba abu ne mai wahala ba, amma zamu ɗan jinkirta saboda idon mutane da yake kanta a yanzu. Duk wani motsinta an saka hukuma tana bibiya, samun galaba a kanta a wannan lokacin abu ne mai wahalar yuwa. Amma akwai babban shirin da zan yi a kanta, farin jinin da take dashi a duniya nake so na lalata, ta yi baƙi a idanun al'ammu, a daina ganin farin ta ko kaɗan."
Ummi ta ce, "da zarar an ga fuskarta a dinga bad comments, sannan a dinga cewa ba a buƙatar fuskarta."
"Haka nake so na yi Ummi. Ina so na samu wani abun da zan yi posting wanda zai tarwatsa rayuwar ta gabaÉ—aya."
"Me zai hana baza muyi amfani da AI ba?."
"Kusan kowa ya gano AI yanzu, ana gani za a iya fahimtar sa ba tare da dogon nazari ba. Ita da kanta nake da buƙata ta aikata ba AI ba."
Ummi ta yi shiru tana tunani kafin ta ce, "to ya za a yi yanzu?."
Ya sauke numfashi ya ce, "ni na san abinda ya kamata nayi, tunda acid bai yi aiki ba, wani abun zai yi mana amfani. Ke dai ki zama cikin shiri, ko yaushe zaki iya jin labari akan Islaha."
Ta yi dariya ta ce, "ko yaushe a shirye nake, indai akan ganin bayan Islaha ne, na É—aura É—ammara."
Ya yi mata jinjina ya ce, "dakyau mace mai kamar maza, ina zuwa" ya faɗa yana miƙewa ya fita.