Sashe 125
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni ba danasani nake yi ba, kawai bana so a dinga jifana da kalman da zasu yiwa Hamma ciwo. Ina yin auren nan zan koma bazawara a idanun mutane, ba kowa ne ya san ya zaman auren zai ya kasance ba. Amma tunda zai bani kuɗin a karɓo Hamma duk abinda mutane zasu ce ba komai bane."
Safeera ta ce, "Amma kina ganin zai ba da kuÉ—in nan kuwa?."
Ta gyaÉ—a kai ta ce, "zai bayar, sanin zai bayar É—in ne ya saka na amince. Zai amince saboda Babansa, ni kuma na amince saboda Hammana."
"To wai shi wanne irin kuÉ—i ne dashi haka? Miliyan hamsin fa da yawa."
"Shi ya sani, ni dai ya tura min kuÉ—in na bayar a yi fansar Hamma."
"To me za ki cewa Baffa in aka bada kuÉ—in?."
Ta É—an yi shiru sannan ta ce, "zan faÉ—awa Sadik ya faÉ—a masa kawai sun sako shi ba tare da an bada komai ba, a rufe maganar kar ya sani.....Ke ni fa da akwai yadda zan yi, da na yi dan na tabbatar Hamma bai san da maganar nan ba, da na faÉ—a masa wani abu a madadin na ce masa na yi auren yarjejeniya."
Safeera ta ce, "Gaskiya za a yi daru dashi akan auren nan, yadda yake kishin nan na ki in ya ji kin auri wani kafin shi, sai ya haÉ—É—iye zuciya ya mutu."
"Wannan shine tashin hankalina Safeera, shine kaÉ—ai abinda nake jin tsoro wallahi. Amma in sha Allah zai fahimce ni."
Safeera ta ce, "Allah ya sa."
Ta amsa da amin ta ce, "zo ki raka ni wajan Baffa na faÉ—a masa na amince da auren."
Safeera ta ce, "amma bakya so."
"Wallahi Allah bana so, Allah ya sani bana ƙaunar auren nan."
"Sai haƙuri, dan dai ki ki karɓi kuɗin nan shikenan komai ya fara." Ta yi shiru bata ce komai ba suka tafi wajen Baffa.
A zaune suka same shi dan tunda aka samu damuwar nan ta sace Saheer ya daina fita, ko ya fita da wuri yake dawowa saboda ana neman maganin damuwar da suke ciki.
Islaha ta zauna ta ce, "Baffa ina yini."
Baffa maimakon ya amsa sai ya ce, "yau ban gan ki ba."
"Eh Baffa, na É—an fita ne."
Baffa ya ce, "Na san da kina gidan nan da yanzu muna tare akan maganar Saheer."
Islaha ta ce, "Baffa akan maganar auren nan ne."Â
Baffa ya ce, "ina jin ki."
Ta haɗɗiye yawun takaici da baƙin cikin kalaman da zasu fito daga bakinta ta ce, "Ka yi haƙuri da abinda na ce maka a akan auren."
"Babu komai Islaha, kar ki damuwa, ai ba matsala bane."
Ta yi shiru bata ce komai ba tana kallon ƙasa, Baffa da yake kallon ta ya ce, "Faɗi abinda yake ranki, ina jin ki."
Islaha a sanyaye ta ce, "Daman...." Sai ta kasa magana ta kuma yin shiru.
Baffa ya ce, "ki nutsu, ina jin ki. FaÉ—i abinda yake zuciyarki, kar ki saka tsoro ko fargaba."
Islaha ta ce, "Daman cewa zan yi na amince da auren Baffa."
Baffa ya yi murmushin jin daÉ—i ya ce, "da gaske ki ke?."
Islaha ta ce, "Da gaske nake."
Baffa ya ce, "Allah ya yi miki albarka. Duk da ba ki san waye mijin ba ki ka amince da abinda na ce miki, ki ka yarda da maganata ki ka amince da kalamana. Islaha ba ƙin ki nake yi da Saheer ba, akwai abinda nake dubawa akan auren ki dashi shiyasa na soke shi da kaina."
"Islaha In sha Allah wanann auren da za ki yi baza ki yi danasani ba. Kuma daman na faÉ—a miki ni tuni na faÉ—a musu kin amince, amma tunda yanzu kin amince da kan ki kin ga faÉ—uwa ta zo daidai da zama. Allah ya yi miki albarka, Allah ya taimaka miki, Allah ya shiga lamarin ki, Allah ya sa auren nan ya zama silar farin ciki a rayuwar ki."
Islaha tana so ta amsa da amin, amma kuma addua'ar ƙarshe ce bata so ta tabbata, sai kawai ta yi shiru bata amsa ba.
Baffa ya ce, "tashi ki je, Allah ya yi miki albarka." Ta miƙe a sanyaye suka fito suka shiga wajan Mama.
Nana Haleema.
[7/29, 12:06 PM] KRBBK: RDB2P94
Nana Haleema.
Islaha suna shiga wajen Mama suka bita da kallon raini da ƙasƙanci, sai suka yi dariya ita da Hanan har suna tafawa. Irin dariyar nan ta rainin hankali, mai saka ciwo da raɗaɗi a zuciyar wanda aka yi dariya dan shi.
Mama ta ce, "Ka ga matar mahaukaci, yanzu duk wannan iyayin a auren mahaukaci za a ƙare."
Islaha bata ce komai ba ta waiwayo ta kalli Safeera da take tsaye bata ce komai ba.
Hanan ta ce, "Yayanmu dai ya fi ƙarfin wata, sai dai mahaukacin wallahi."
"To in ba mahaukacin ba ya za a yi mata tayin auren ɗan AbdulAziz Yola? Sai dai mai taɓin hankalin, shine daidai da ita, shine bazai banbance budurwa da ragowar wasu ba. Hanan ance sunansa Salman ko?."
"Eh Mama, ance haka sunansa yake, kuma in ya kashe ta ya kashe banza wallahi. Ita ba uba ba balle ya shige gaba a ƙwaci haƙƙin ranta, kuma waye yake shari'a da mahaukaci?."
Suka yi dariya suka sake tafawa kamar ba uwa da ƴa ba. Mama ta ce, "Ga idanu ga hanci, ga gashi har baya ga iyayi, ga farin jini da zaƙin murya, amma duk mallakin mahaukaci ne."
Islaha ta ja Safira suka shiga cikin É—aki, ta tsaya ta jingina da bango bata ce komai ba. A fusace Safeera ta ce, "Matar nan bata da kirki wallahi, wato mahaukaci ne zai aure ki ko? Basu san....."
Islaha ta dakatar da ta ce, "Don Allah kar ki faÉ—a, ki barsu a je a hakan, sai me?."
Sai ta É—auki waya ta kira Sadik yana É—auka ta ce, "Hamma Sadik zan iya samun account details É—in ka?."
"Me za a yi dashi?."
"KuÉ—in fansar Hamma za a saka, account É—in ka zai cire wannan kuÉ—in lokaci É—aya?."
Cike da mamaki ya ce, "Islaha a ina ki ka samu wannan kuÉ—in masu yawa haka?."
Ta ce, "zan yi maka bayani. Amma yanzu ka turo min kawai" ta faÉ—a tana yanke wayar, ta ga Safeera tana kallon ta.
Ta kalli Safeera ta ce, "meye ki ke kallona kamar na ci bashin ki?."
Safeera ta ce, "kina da sa'a wallahi." Ta yi tsaki ta shiga banÉ—aki ta bar mata wajan.....
Bata jima da shiga ba ta fito, ta ga Safeera riƙe da takardar yarjejeniya tana karantawa. Safeera ta kalli Islaha da take tsaye a wajen kayanta tana bincika kayan ta ce, "ni ban ga wani rules na ɗaga hankali a rules ɗinsa ba. Ya ce ba ya so mutane su san ya aure ki kema bakya so, ya ce babu ruwansa dake kema kin faɗa...."
Islaha ta yi tsaki bata ce komai ba, Safeera ta ce, "Amma Islaha rule ɗin nan na ki na ƙarshe anya zai yu kuwa?."
Islaha ba tare da ta juyo ba ta ce, "wanne kenan?."
"Da ki ka saka no intimacy, kina ganin zai ba ki waÉ—nanan kuÉ—in ba tare da wani abu ba?. Kuma in ki ka duba a cikin na sa rules É—in bai saka haka ba, ni sai nake ganin kamar bazai yu ba."
Islaha ta waiwayo a fusace ta harare ta ta ce, "Ita yarjerjeniya ko ɗaya bai saka rules ba indai ɗaya ya saka kuma ka saka hannu ciniki ya faɗa. Ba gwara ya hana ni aikina da fita daga gidan akan abinda ki ke faɗa ba? Na yi miki kama da wacce zata saurari wancan banza?. Na rantse da Allah Safeera kina da abin haushi, har kin ɓata min rai."
Safeera ta É—an yi dariya sannan ta ce, "Ba banza bane, tunda aurensa za ki yi."
"Auren contract ba. A cikin wata biyar ɗin nan ko hannuna ya riƙe ya karya mana rules, kuma in ya sake ya yi wannan gangancin daga ranar bazan sake zama dashi ba. Daman saboda me na yarda da auren? Saboda Hamma ne, kuma na san zuwa lokacin ya dawo, bazan tsaya ina ɓata lokacina a gidansa ba. Da gangan zan yi abinda zai karya ɗaga daga cikin rules ɗina ko da ba ya so, daga nan zan yi terminating contract ɗin kowa ya kama gabansa."
Safeera ta yi dariya ta ce, "mugunta kawai ki ka shiryawa bawan Allah. Da dai kawai ya saka hannu ne, amma ajjiye macen da ka san matar ka ce ta aure, addini da al'ada sun baka ko wacce irin dama a kanta, ka ajjiye ta har tsahon wata biyar kana kallon ta ba tare da wata alaƙa ba akwai wahala, a wannan zamanin dai kafin a samu wanda zai yi wannan jan halin za a jima."
Islaha ta ji kamar ta tsinkawa Safeera mari ta ce, "Yana rayuwa a cikin turawa, ya san girman karya rules ɗin da ka yi signing akan amincewar ka a kai. Ni mallakin Hamma ce, babu wani banza da bawa kaina matuƙar Hamma yana da rai."
"Hmmm Islaha kenan!. To kina nufin za ki cigaba da son Hamma bayan wannan yarjejeniyar?."
"Ban gane ba, da sai na ajjiye son nasa kenan?."
"eh mana, na ga matar aure ce ke, son wani ta fuskar soyayyar babban zunubi ne."
"Da yake zuciyar tawa whatsapp ce, da zan kunna data na hau lokacin da nake so na sauka lokacin da na ga dama ko?. Kuma da ki ke zancen aure, ki dinga haÉ—awa da contract."
Safeera zata yi magana ta ce, "Dallah malama ki yi min shiru, kina ɓata min rai."
Islaha ta É—auki wayarta ta ga Sadik ya turo acc details É—in. Ta É—an dafe kai tana tunanin anya abinda ta yi daidai ne kuwa? Sai yanzu abin yake damunta take ganin kamar ba daidai ta yi ba, sai yanzu take gani kamar ta dakusar da rayuwarta ta lalata carrier ta.
Ta bi account number da kallo tana tunanin turawa Jafar, ta zauna a kan gado ta ce, "Safeera ina cikin damuwa, kamar ban aikata abinda ya kamata ba. Contract marrige na yi, wayyo Allah!."