← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 133

Sashe 67

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ta ya aka yi ta san gidan in ba kai ka faɗa mata ba? Bata taɓa zuwa Jeddah ba balle ace daman ta san gidan. Gata nan ta zo zata chaja min kai."

"Malam ka daina yi min faÉ—a, ba budurwar ka bace, dan ta zo sai me? Na ga daman kuna zama kai da ita a london ko?."

"This is not london, saudia ne."

"Kai ka sani kuma, kai ka saba mata da hakan, da kana yin abinda nake cewa da hakan bai faru ba ai. Sai ka kore ta ko ta ta ya ka zama."

Rehaan Ya dafe kansa cikin takaici ya kashe wayarsa.

A lokacin Alma ta shigo ɗakin, ya lumshe ido ya buɗe, ya ɗago ido yana jifanta da wani irin kallo, kallon kaɗai ya saka ta tsaya cak bata ƙarasa ba, sai kuma ta koma sa baya ta fita bata ce komai ba. Ya ja tsaki ya ɗauki spoon zai ci macorni salad ɗin sai kuma ya fasa, ya yi fatali da tray ɗin ya kufe a wajan ya tsallake ya shiga bathroom.

    Alma hankalin ta ya tashi, yadda ta so ya karɓe ta ya yi rawar jiki in ya ganta bai yi hakan ba. Ta fara zagaye ɗakin da ta yiwa kanta a gidan, cikin damuwa da neman mafita. Ko ba ya so a wannan lokacin sai ta yi abinda take so, zata yi masa video sannan kuma zata same shi.

Wajan handbag ɗinta ta ƙarasa, ta ɗauko ɗauko wani tab tana kallon maganin. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "dole na yi amfani da wannan, na ga alama a london ya fi kirki, a nan bashi da kirki dole a haɗa da tab."

Ta mayar da maganin ta zauna a gefen gado tana huci, bata so yin amfani da maganin wajan cimma burinta ba, so take ta same shi a hayyacinsa ba tare da ta bugar dashi ba, so take ta same shi cikin soyayya ba tare da wani abu ya taimaka mata ba. Amma ta ga alama ya zo da taurin kai, dole ta koya msa hankali.

Washe gari Islaha da safe da ta farka bata je gidan ba, aikin gidan suka gama ita da Sunaira sannan ta yi nufin zuwa. Sai kuma ta tuna zata yi sabon content, ta yi creating topic da kanta ta ta saka hijjab ta zauna ta saka camera a gaba ta É—an yi magana mai É—auke da ilimi sannan ta yi posting.

Tun kafin ta fira take ta ganin comments yana zuwa espacilly a tiktok da ig. Ta yi murmushi ta ta miƙe ta fita zuwa gidan Rehaan. Falon babu kamar ko yaushe, ta shiga kitchen sai kuma ta tuna da bowl ɗin jiya yana sama, ta san bai saulo dashi ba, ita kuma bata so sai ta gama zata fita ace ta je ta ɗauko wani abun, hakan ya saka ta hau sama.

A hankali take takawa har ta ƙarasa ciki, falon babu kowa dan babu haske ma a falon sai kaɗan. Sai ta ja ta tsaya tana tunanin yana nan ko ba ya nan, duk da bata ga mota ba amma bata yi tunani ba ko bata nan.

A hankali take tafiya har ta ƙarasa ɗakin ta murɗa handle ɗakin ta shiga da sallama, side ɗaya gadon yana yamutse alamun an kwanta a kai, dan ɗaya side ɗin yana nan normal ko pillow sa bai nuna alamun an kwanta ba.

Ta kalli ƙasa ta ga macroni ɗin da ya ɓarar a kan carpet, ta kalli ko ina ta ga babu kowa alamun dai ba ya nan.

Ta ja dogon tsaki ta ce, "ji wani abu don Allah, ji yadda ya zubar da abu akan carpet. Kwashe kayan zan yi shara ba aikina bans, ya je ya samu ya san abinda zai yi."

Ta sunkuya ta É—auko bowl É—in, ta É—auke tray da tea É—in ta ajjiye. Tsaki ta yi tana ganin yadda salad É—in duk ya bushe, ta harari wajan harda murguÉ—a baki. Kamar wasa ta ga an buÉ—e an shigo, ta É—aga kai ta kalle sa suka haÉ—a ido ta É—auke kai daga kallonsa. Shima É—auke kai É—in ya yi, ya wuce ya É—auki wayarsa da take kan bedside.

Islaha ta bisa da kallo ta ce, "aikin banza, ji wani abu kamar ƙaramin yaro, sai ka nemo wanda zai gyara maka wajen, ni dai bazan iya ba."

Rehaan ya waiwayo ya kalle ta, ta maze kamar ba ita ta yi magana ba, dan ta san bai ji abinda take faÉ—a ba. Rehaan ya ce, "cleaner zasu gyara wajan."

Ta harare sa ta ce, "ai ko baka ce ba, ni ba gyarawa zan yi ba wallahi, ai ba ƙaramin yaro bane ba kai." Shi dai bai tanka mata ba, ya ɗauki wayarsa ya fita.

Itama downstairs É—in ta sakko ta dafa tea, ta juye a mini kettle, wacce yake da mug guda huÉ—u madaidaita. A lokacin Alma ta shigo, ta bi Islaha da kallo kallo ta ce, "he is calling you."

"Ubana ne yake kira na?." Alma bata ce komai ba dan ba ji tayi ba ta ja ta tsaya ita kuma Islaha ta fita.

Islaha tana fita ta ɗauko tab ɗin ta ƙarasa gaban tea ɗin tana marmasawa a ciki.

Daidai na Islaha ta dawo ta ga tana juya tea É—in da tea spoon, ta tsaya cak tana kallon ta tana girgiza kai cikin mamaki.

A hankalinIslaha ta ce, "kai! Me matar nan ta zuba a tea?."

Ta yi shiru tana kallon Alma sannan ta ce, "in fa ya sha wani abun ya same shi ko ya mutu ni za a É—orawa alhakkin hakan, ni za a kama a kulle ban ji ban gani ba. Dole na san abinda zan yi, bazai sha wannan tea É—in ba wallahi."

Tana ganin Alma ɗauke da tea ɗin, Islaha ta yi saurin hawa sama, gab da zata ƙarasa falon sa ta tsaya tana hangosa a zaune. Ta ƙarasa ta hau saman tana ganin Alma ta taho sai ta yi kamar zata koma ta sakka downstairs, sai da Alma tazo daidai da ita, Islaha ta bangaje ta tea ɗin ya zube a ƙasa, mug ɗin ya fashe.

"Ouchhh! You burned me with the tea" Alma ta faɗa da ƙarfi wanda hakan ta ja hankalin Rehaan ya kalle su.

Islaha a ruÉ—e kamar da gaske ta ce, "I'm sorry, it was an accident."

"To hell with the accident! Can't you see how you burned me with the tea?."

"I'm sorry Madam."

Rehaan daman ciki yake da Alma, ya ƙaraso cikin fushi ya ce, "Alma Pack your things and leave Jeddah immediately!."

Ta bi sa da kallon mamaki ta ce, "I'm Alma."

"That's exactly why I told you to leave. I don't want to see you here."

"I'm not going anywhere until you promise to marry me."

"I'm not marrying you, i don't feel that way about you. You're just my schoolmate, stop this drama and leave Jeddah now!"

"I'm not going anywhere!" Ta faɗa da ƙarfi tana tsallke tea ɗin sa ya zube ta wuce.

Islaha ta bi Ray da kallo dan bata taɓa ji ya yi doguwar magana haka ba, gabanta ya faɗi tana tunanin daman wai ba matarsa ba ce ba ko me?.

Ya kalli Islaha da take kallonsa ya ce, "go down." Bata motsa ba kallonsa take yi dan yadda yake magana cikin faÉ—a ya bata mamaki sosai.

Ya buÉ—e idanunsa a kanta ya ce, "Ba ki ji me nace miki ba?."

Islaha ta wani kalle sa jin da hausa ya yi magana, kuma hausar ta fita alamun ba koya yake yi ba ya iya, suna haÉ—a ido ya nuna mata stairs ya ce, "na ce ki sauka!"

Ya faÉ—a yana kallon ta, wanda hakan ya saka numfashinta ya tsaya cak, ta buÉ—e ido tana kallonsa cike da mamakin yaren da ya yi magana.

Rehaan yana jin ku duk rashin m din da kk yi masa🤣🤣🤣
[7/9, 11:24 AM] KRBBK: RDB2P47
Nana Haleema.

Islaha ta tsaya cak tana kallonsa cikin mamakin da ya kusa kashe ta. Ta kasa matsawa daga inda take, ta tsaya cak ta zuba masa ido jin yana magana da yaren da take tunanin ba ya ji.

GabaÉ—aya bata É—auka yana jin fulatanci ba balle hausa, kwata kwata bai yi kama dasu ba balle ta yi tunanin ya iya. A hankali ta É—auke ido sdaga kansa, jikinta ya yi sanyi tana tuna irin maganar da ta dinga faÉ—a masa tun daga kan zaman Yola har nan É—in.

Riƙo hannunta ta ji ya yi ya ya jawo ta baya, sannan ta kalle sa ta ga yana nuna mata pieces ɗin mug ɗin da suke ƙasa, Islaha ta kalli wajen dan da tuni ta taka.

Ya matsa daga wajan ya ce, "ki kawo min coffee." Ta gyaÉ—a kai ta sauka a sanyaye cikin yanayin sanyin jiki.

Tana shiga kitchen É—in ta tsaya tana mamaki, a bayyane ta ce, "daman yana jin yaren da nake ji? Wallahi na É—auka bature ne kwata kwata ba ya jin fulatanci balle hausa. Gaskiya na kwafsa, ashe daman share ni kawai yake yi, ya É—auke ni kamar mahaukaciya. Sai na ji kunya" ta faÉ—a tana dafe kai kafin ta É—ora ta yi making black coffee kamar yadda ya ce.

Da ta gama ta hau saman bata same sa a falon ba, ta ƙarasa ɗakin ta ɗan yi knocking kaɗan ta ji ya ce, "yes."

Ta tura a hankali ta gansa a zaune yana danna waya, ta ƙarasa ta ajjiye masa coffee ɗin. Bai kalle ta ba sai wayarsa da yake dannawa, dan ya rasa meyasa indai zai kalle ta to maganar Ubaid yake tunawa, wani lokacin har image ɗin su yake gani a idonsa, bai san meyasa ya damu haka ba, bai san meyasa in ya kalle ta yake jin haushi in ya tuna yarinyar Ubaid ce ba, mata nawa ya sani wanda Ubaid yake mu'amala dasu ba ya damuwa? Amma ita bai san dalilin da ya saka yake jin haushi ba, ko dan ƴar nigeria ce kuma ƴar yola oho, shiyasa ya yanke shawarar daina kallon ta.

Ta juya zata koma ya ce, "serve." Ta dawo ta zuba tana hararar sa ƙasa ƙasa, bai ma san tana yi ba ta ajjiye ta juya ta fita.
Chapter 67 · 0% Book details