← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 133

Sashe 34

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safeera ta ce, "babu gaskiya, duk hanyar da zaki bi ki samu maƙudan kuɗi kamar wannan a lokaci ɗaya ba hanya ce mai ɓullewa ba. Sata, iskanci, fashi, damfara da sauransu. Sune zasu kawo miki kuɗi masu yawan wannan lokaci guda. In kuwa ta hanyar halak ne dole sai kin jira, a hankali a hankali in kin tara sai ki biya."

Ta ja nunfashi mai ƙarfi ta ce, "Yaushe kenan? Yaushe zan tara wannan kuɗi masu yawa?. Shekara goma ko ashirin?."

"To gashi nan dai."

"Safeera ni dai na samo mafita, kuma in Allah ya yarda a shekara ɗaya zan haɗa masa kuɗinsa. Zan neme sa a duk inda yake na damƙa masa koda zai saka a kama ni."

Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "wacce mafita ce wannan?."

Islaha ta ɗan yi shiru tana kallon ƙasa, ta ɗago ta kalli Safeera da take kallon ta tana jin nauyin faɗar abinda yake bakin ta.

"FaÉ—i mana Islaha, kin saka ni a tunani fa."

"Na shiga cikin waÉ—anda Mama zata kai Saudia aiki a wannan lokacin, tafiyar baza ta wuce nan da kwana biyu ba."

Safeera ta zabura ta miƙe tsaye cikin mamaki da kiɗima haɗi da tashin hankali. Islaha ta riƙo hannunta ta ce, "ki zauna mana."

Safeera ta ce, "ban gane me ki ke nufi ba, maimaita na ji da kyau" ta faÉ—a tana komawa ta zauna.

Islaha a sanyaye cikin rauni da rashin mafita ta ce, "cewa nayi zan tafi aiki ƙasar larabawa, a can nake tunanin zan iya haɗa kuɗin...."

Safeera ta dakatar da ita ta ce, "kina cikin hankalin ki kuwa Islaha, kin san abinda ki ke faÉ—a min?."

"Na sani mana, ni da kaina nake faÉ—a miki abinda na yanke."

"Gaskiya ban yarda kina cikin hankalin ki ba Islaha, ban yarda kin san abinda ki ke faɗa ba wallahi. Anya a inda aka sace ki basu gurɓata miki tunani ba? Anya basu masu baki kayan maye kin sha tunanin ki ya gushe ba?."

Islaha ta runtse ido, ta san dole Safeera tana shiga ruɗani akan hakan, tunda sune masu yaƙi da son kawo ƙarshen matsalar. Dole zata firgita in ta ji ita da kanta zata je.

Cikin sanyin murya ta ce, "Safeera! Wallahi ina cikin hankali da nutsuwa, abinda nake faÉ—a miki shine asalin gaskiya ta. Har nayi international passport na bawa Mama, É—azu da safe Mama take sanar dani da har an yi min visa."

"Innallilahi wa'inna ilaihir raji'un, Islaha!" Sai ta kasa faÉ—a ta zubawa Islaha ido bata ce komai ba.

Islaha ta ce, "babu yadda zan yi Safeera, ina da buƙatar sauke nauyin da yake kaina shiyasa na yanke hukunci ban faɗa miki ba. Wallahil azim ni kaɗai na san nauyin da ƙirjina yake yi min, ni na kaɗai na san zafin da nake ji akan abinda na aikata. Ke kin san wacece ni, kin kowa sanin halina, ban taɓa ɗaukar zaren wani ba balle naira biyar. Dole hankalina ya tashi, dole na rasa nutsuwata. Mafarkai nake yi marasa kyau, har mafarki nayi na mutu kuɗin sun hana ni kwanciya a kabarina."

Safeera ta ce, "Akan wannan zaki dakusar da rayuwar ki, akan wannan zaki kashe kanki ki lalata tarbiyyar ki Islaha?. Meyasa baza ki bi wata hanyar ba, meyasa baza mu neme sa mu ba sa haƙuri akan hakan ba?."

Islaha ta goge hawayen idanunta ta ce, "Yanzun nan kika faÉ—a min hanyoyin da suke kawo kuÉ—i, a cikin wanda ki ka faÉ—a wanne zan É—auka?."

"To meyasa baza ki sauke tsiwa da girman kai mu je a basa haƙuri? Meye a cikin ido ban da ruwa? In ka san ka yi laifi baka ɗaga kanka sama kace kai baza ka ƙasƙantar da kai ba. Wacece ke da ki ka ɗorawa ranki girman kai? Meye a cikin kalmar haƙuri Islaha?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai, Safeera ta ce, "rashin ba da haƙurin nan, da wannan maganar, sun saka na ji kamar komai da ya faru ke ki ka tsara."

Ta É—an murmusa ta ce, "Safeera kamar baki sanni ba?."

"Meyasa za ki yanke wannan hukuncin ba tare da na sani ba?."

Islaha ta ce, "Na san zaki hanani ne, shiyasa na je na yi duk abinda ya kamata ban faÉ—a miki ba."

Safeera ta dafata ta ce, "ni da ke muke so mu yaƙi yawan fitar da yara da ake yi ƙasar waje da sunan aiki, yara nawa muka tattauna dasu waɗanda aka fita dasu? Mata nawa ne suka bamu labarin yadda rayuwarsu take juyewa sama ta dawo ƙasa saboda hakan?. Kin manta ina zaki je ne? Kin manta irin abubuwan da aka faɗa mana suna faruwa a can Islaha?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Safeera ta ce, "wannan ba tarbiyyar ki ba ce, tafiya ki bar ƙasa ba daidai yake da tarbiyyar ki ba. Ni da ke muka zauna a kan case ɗin Umma, mu ka yi magana dake akan zamu je Katsina wajen iyayenta don a hanata zuwa. Meyasa ki ke son tafiya bayan wannan ƙaramar matsala ce?."

"Safeera dole ce ta saka, kuma wannan matsalar ba ƙarama bace Safeera."

"Ƙaramar matsala ce mana, in mu ka neme mutumin nan muka bashi haƙuri komai wucewa zai yi. A yadda ki ke ba da labarinsa na tabbatar yafi ƙarfin naira miliyan goma sha bakwai, yadda ki ke faɗarsa dan ya ce ya bar miki abu ne mai sauƙi a wajansa. Meyasa baza mu bi hakan ba, sai ta hanyar tafiya wata ƙasa aiki?."

Islaaha ta yi shiru bata ce komai ba, Safeera ta ja tsaki cikin takaicin taurin kan Islaha ta ce, "baza ki iya ba sa haƙuri ba ko?."

Islaha ta ce, "kema kin san bazai yu ba."

"Wallahi Islaha ji nake kamar na tsinke ki da mari, wannan girman kan da ki ka ɗorawa kan ki babu inda zai kai ki sai danasani. Yanzu kin zaɓi ki bar ƙasar ki ki tafi wata ƙasar aiki a gidajen fararen fata ko?. Kin yarda ki watsar da tarbiyyar ki akan titi akan ki furta kalmar haƙuri a wajan wanda ki ka yiwa laifi?."

"To ina zan gan shi balle na ba sa haƙurin?."

"In ki ka nemo kuÉ—in a ina zaki gan shi ki ba shi?."

"Neman sa zan yi duk inda zan gan shi."

"Wannan ma sai ki neme sa ki basa haƙuri, ai ba aljani bane balle ace ya ɓace daga duniyar da muke ciki."

"Safeera ni ya yi laifi fa, kuma bayan ya yi min laifin ya sace ni. Kuma haka ki ke so na basa haƙuri?."

Safeera ta ja tsaki ta miƙe tsaye, Islaha ma ta miƙe ta riƙe ta ta ce, "Safeera kema kin san bazan iya ba, shiyasa na nemo mafita a gare ni da rayuwata. Ki yi haƙuri, na san kece mutum na biyu da baza ki ji daɗin hukuncina ba, bazan iya ɓoye miki ba shiyasa na faɗa miki, amma tafiya babu fashi. Na yi miki alƙwararin bazan watsar da kaina ba, na yi miki alƙwarain iya albashina kawai zan karɓa bazan karɓi kuɗi ta wata hanya mara kyau ba. Ko a wata ɗaya na tara kuɗin zaki ganni na dawo, bazan ɓata lokaci a can ba. Ba neman kuɗi naje yi ba, neman kuɗin da zan biya bashi zan je nayi."

Safeera ta kalle ta ganin da gaske take magana, ga rauni ya bayyana a tare da ita.

Safeera hawaye suka sakko daga idanunta ta ce, "Islaha ta ya zaki tara wannan kuɗi a wata ɗaya da iya albashi? Kuma in ki ka tafi baza ki dawo ba sai kin gama biyan su Mama kuɗin da suka kashe suka kai ki, sai kin biya kamfani kafin ki fara morar kuɗin. Kina ganin duk zaki iya hakan a ƙaramin lokaci?."

Islaha ma kuka take yi a hankali ta ce, "in sha Allah zan iya, zan nemi halak ba haram ba. Ki yarda dani, bazan yi komai da zai lalata tarbiyyata ba."

Safeer ta goge idonta ta ce, "na yarda dake bestie, ni na san wacece ke. Amma ina so ki sani daga ranar da ki ka tafi duk mai yi miki kallon mai mutunci zai daina, an riga an yiwa tafiyar nan kuÉ—in goro, ko da iya halak É—inki ki ke nema a can, an lalata hakan a idanun mutanenmu na nan. Shaida mai kyau daga bakin kuma mutune rahama ce, bana so a fara yi miki wani zargi mara daÉ—i."

"Duk wanda ya zarge ni shi da Allah, duk wanda ya yi min ƙazafi akwai ranar tsayuwa Safeera."

Safeera ta ce, "na ji. Ya zaki yi da Saheer? Na san ko za a sake yaƙin duniya bazai taɓa amincewa da tafiyar nan ba. Ya zaki yi dashi? Ya zaki yi da su Zainab da abinda ki ke bincike a gidan? Kina so ki ce min ƙudurin ki ya danne na gidan marayu? Tafiyar ki ta fi bincike akan zargin lalata yaran da ake yi mahimmaci?....."

See you on monday guys😍
[6/29, 11:53 AM] KRBBK: RDB2P24
Nana Haleema

Islaha ta ja numfashi mai tsaho ta sauke, ta ɗan yi shiru kafin ta lumshe ido ta buɗe ta kalli Safeera ta ce, “Na san Hamma bazan taɓa ɗaukar maganar nan ba, shiyasa nake fatan Allah yasa tafiyar ta kai jibi, kin ga gobe ya ce min zai koma Niger, in dai ya tafi shikenan.”

Safeera ta bita da kallon tausayi ta ce, “nufin ki ko ya dawo bazai sani ba?.”

“Dole zai sani, da kaina zan faɗa masa amma sai na tabbatar bana nan. Indai har na tafi damuwar ba mai yawa bace, kafin na tafi ne wallahi bazai taɓa bari ba. Faɗa zai ta yi, ya kuma takura min sai na faɗa masa dalilina na tafiyar.”

Safeera ta ce, “yanzu ya za a yi kenan?.”

“Sadik zan yiwa waya, zance masa ina so mu haɗu, sai na faɗa masa komai da komai. Na san da wahala ya fahimce ni, amma zan roƙesa sosai, zance don Allah kar ya faɗa masa har sai na tafi.”
Chapter 34 · 0% Book details