← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 133

Sashe 100

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta kalle ta sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ban sani ba, amma da zan san garin su Yafindo zan je ko dan ta bani saƙon da Zainab ta bata ta bani, hankalina ya kasa kwanciya, zuciyata tana faɗa min akwai wani abun da yake faruwa."

Safeera ta ce, "gaskiya dai akwai, sai dai fatan Allah ya kiyaye."

Ta yi shiru kawai ta kwantar da kanta, tana ganin Safeera da Saleem sun kalli junansu suna kallon ta, ita dai ta lumshe ido bata ce komai ba tana tunani. Saleema wajan wankin kan ya sauke su ya tafi.

Basu jima sosai ba su fito, kai tsaye ta ce su wuce office É—in Barr Suraj.

Shima ya yi mamakin ganinta sosai, ta ƙi bashi damar yi mata tambayar yaushe ta dawo ta ce, "Hamma Suraj ba a ga Zainab ba, tun bayan wannan recording ɗin ba a kuma ganinta ba."

Barr ya ce, "dole hukuma za a saka a cikin case É—in nan, ki bar komai a hannuna, zan kai maganar gaban Æ´an sanda, za su san abinda za a yi."

"Ko yaushe sai ka ce na bar komai a hannunka, amma in na bari É—in bana ganin wani cigaba. Kwana nawa da tafiyata, na bar maka komai É—in, amma ni ban ga wani cigaba ba har yanzu."

"Islaha baza ki gane ba, wannan case ɗin ba ƙaramin case bane, ba a yi masa shigar sauri, dole sai an bi a hankali."

"Yanzu daga gidan nake, kuma an tabbatar min da bata nan, sannan akwai saƙon da ta bayar a bani, wacce aka bawa ɗin bata nan."

"Wa aka bawa?."

"Za ka iya gane Yafindo, wacce take aiki a kitchen?.."

Ya É—aga kai ya ce, "na gane ta sosai ma, Ina ta je?."

"Wai ta je ƙauye, kuma ashe ba a garin nan take ba."

Ya tallafi haɓarsa ya ce, "Amma zan so a same ta, ba mu san me ta bayar ba. Kar ki damu, tunda har ta bawa wani saƙo abin ya zo da sauƙi, za a san abinda zamu yi. Ina tare dake ko yaushe, zan san duk hanyar da zan bi na nemo Yafindo."

Islaha ta ce, "na gode, zamu yi magana anjima" ya amsa yana miƙewa suka fita.

Suna fitowa Safeera ta ce, "Islaha da kin sani ba ki faɗawa Barr maganar saƙon nan ba, kar a sake samun matsala irin wancan."

Ta kalli Safeera ta ce, "Duk da abinda ya faru ni bana zargin ko ɗaya a cikin ku, Hamma ya faɗa min na dinga ɓoye sirrin da na samo, amma bazan iya ba, dan aikin ya fi ƙarfina ni kaɗai. Ko waye yake da hannu a maganar nan, Allah zai bayyana shi da gaggawa."

"Haka ne, Allah ya ba da sa a."

"Amin."

Islaha haka ta dinga jan Safeera yawo, daga nan su je nan kuma duk akan ɓatan Zainab, sai da suka yi azahar sannan suka wuce gida.

A cikin napep É—in ma ta yi shiru tana tunani, Safeera ta ce, "ki ta addu'a lamarin nan, in sha Allah komai zai dawo daidai."

Ta gyaÉ—a kai ta ce, "ban san me zancewa Hamma akan dawowa ta ba, in na faÉ—a masa maganar Mr Rehaan Yola kina ganin zai amince?."

Safeera ta ce, "gaskiya babu lallai, kuma zai iya jin shakku a ransa. Amma kar ki ɓoye masa, kin ga kin ɓoye masa batun ɗauke ki da tafiyar ki, kuma ya ji haushi sosai kawai dan yana sonki ne yake mantawa. Yanzu kar ki ɓoye masa, ki faɗa masa gaskiya ko da zai ji haushi."

"Zai ji haushi kam, sai dan kawai faÉ—a masa É—in shine mafita. Ni kaina ina neman hanyar da zan fara yi masa bayani, shiyasa har yanzu ko waya ban yi dashi ba, dan ban san me zance ba."

"Dole ki damu ai, amma in ki ka faÉ—a masa irin abinda ki ka faÉ—a min zai ji kamar kin raina masa hankali, in ki ka canja maganar kuma daga baya ya san asalin gaskiyar bazai ji daÉ—i ba. Dole ki faÉ—a masa, tunda daman kin ce masa neman kuÉ—in biyan bashi ne ya kai ki. Abinda zai tambaye ki ta ya ki ka samu kuÉ—in a wannan lokacin, dan ko aikin gwamnati ki ke yi a can baza ki haÉ—a wannan kuÉ—in a albashin wata biyu ba. Sai dai ki faÉ—a masa É—in zai fi."

Ta sauke numfashi bata ce komai ba suka cigaba da tafiya, a daidai ƙofar gidan ta hango sa a tsaye cikin jallabiyya baƙa, Sadik yana kan mota a zaune shi kuma ya jingina da motar suna magana.

Gaban Islaha ya faÉ—i ta ce, "Safeera Hamma ya dawo."

Safeera ta kalli wajan ta gan shi a tsaye, ta kalli Islaha ta ce, "ki nutsu, kar ya ga kamar kin tsorota ya yi tunanin wani abun."

Daga can nesa suka sauka daga napep ɗin, Islaha ta biya kuɗin suka nufi wajan su Hamma ƙirjinta yana bugawa sosai.

A hankali suke nufar inda suke a nutse, Islaha ta sunkuyar da kai har suka kusa ƙaraso daf dasu. Sadik ne ya fara gano ta, ya buɗe baki cikin mamaki da ɗaure kai ya ce, "A'a, wa nake gani kamar Islaha?...itace ko gizo take yi min?."

Faɗar Islaha da ya yi sai ya ja hankalin Saheer ya kalli wajan da yake kallo, Saheer ya yi arba da bugun zuciyarsa, sai tsayar da idonsa a kanta yana kallon ta, kanta a ƙasa tana ƙarasowa har suka cin musu.

Suna ƙarasowa ta ce, "barkan ku da yamma."

Saheer ya kasa magana sai kallon ta da yake yi, zuciyarsa tana bugawa, yana so ya tantance da gaske itace ko gizo take yi masa.

Sadik ne ya diro daga kan mota ya ce, "Islaha ke ce ko kuma Æ´an biyun ki ce?."

Ta yi dariya ta ce, "Ni ce Hamma Sadik."

Ya kalli Saheer da ya zuba mata ido kamar zai cinye ta, sai kuma ya ƙaraso inda yake yana kallon ta, muryarsa a tausashe ya ce, "Matar Hamma?" Ya faɗa da sigar tambaya yana nuna da yatsa.

Islaha ƙirjinta ya buga, jin muryar masoyinta har tsakiyar kanta, ga kewar ganinsa da take addabar zuciyarta. Ta ɗago ido a hankali ta kalli idonsa, sai ta sauke kai ƙasa ta ce, "Na'am, mijin matar Hamma."

"Oh my god! Ke ce da gaske? Na kasa yarda fa."

Ta É—an yi dariya ta ce, "Ni ce fa Hamma."

Saheer ji yake kamar ya jawo hannunta ya rungume ta, sai ya tuna a ƙofar gida suke bazai iya aikata hakan ba. Amma yana so ya ji ta a jikinsa ko zai tabbatar itace ko kuma ba ita bace. Ya riƙo hannunta yana kallon bracelet ɗin daya bata ya ce, "Yaushe ki ka dawo?."

Ta sukar da idanunta ƙasa ta ce, "Jiya na dawo Hamma."

Ya wara ido ya ce, "har jiya? Kuma shine ban sani ba?."

Ta É—an kalle sa tana zame hannunta daga cikin nasa ta ce, "Mamaki nake so na baka."

Ya bita da kallon da ya mamaki ita kuma ta kalli Sadik ta ce, "Hamma Sadik ka gama mamakin ko da saura?."

Ya yi Æ´ar dariya ya ce, "Na tabbatar Islaha. Kuma ki ka sauka tun jiya babu labari?."

"Sai dare na nutsu, kuma da safe ina tashi na fita."

Sadik ya kalli Safeera ya ce, "laifin ki ne, da ba ki faÉ—a mana aminiyar ki ta dawo ba."

Ta yi dariya ta ce, "Wallahi nima ganinta kawai na yi, babu labari babu sanarwa."

Sadik ya ce, "Ma sha Allah! Tunda ta dawo lafiya ai haka mu ke fata. Gashi nan kam Jeddah ta karɓe ta."

Ta yi murmushi ta kalli Saheer da ya rungume hannunsa a ƙirji yana kallon ta ta ce, "zan shiga ciki Hamma."

Ya ɗafa mata kai ta juya zata shiga, Sadik ya ce, "sai na zo na karɓi tsarabata." Ta yi yar dariya kawai bata ce komai ba.

Safeera ta ce, "na shiga gida Islaha, zan shigo da daddare mu ƙarasa maganar mu." Ta ɗaga mata kai ta shiga cikin gida.

Sadik ya daki kafaɗar Saheer ya ce, "Saheer wallahi ƙasar Saudia ta karɓe Islaha fa, anya wani minister bazai yi maka overtaking akan yarinyar nan ba?."

Saheer ya hararesa  ya ce, "ko kunya ba ka ji, kana yabon kyaun matata a gaban idona."

Ya yi yar dariya ya ce, "Amma ya aka yi ta dawo da gaggawa haka? Ba ta yi wata uku ba fa."

Saheer ya ce, "Nima na yi mamaki sosai, kuma ban ji Mama ta ce min Labiba ta dawo ba. Amma bara na shiga na tambaye ta, dan gaskiya ina da tambayoyin da zan yi mata."

Sadik ya ce, "Ni na wuce, gobe ƙarfe nawa zaka koma?."

"sai dare zan tafi."

"Allah ya kaimu" ya faÉ—a yana shiga mota ya tafi shi kuma ya shiga gidan.

Gidan babu kowa da Mama bata nan, Baffa ma ba ya nan sai Islaha kaÉ—ai a tsaye tana tunanin abinda zata ci.

Jin motsin Hammanta sai ta juyo ta kalle sa ta ga ita yake bi da kallo, irin kallon kewa da ƙauna da kuma shauƙi.

Islaha ta É—an turo baki ta ce, "Yunwa nake ji, kuma ni bazan iya girki ba."

Saheer ya zo kusa da ita yana kallon idanunta, sai ta sauke ido ƙasa ya ce, "me za ki ci?."

Bata É—ago ba ta ce, "komai ma zan ci."

Ya sauke numfashi ya ce, "Islaha!."

Bata É—ago ta kalle shi ba, Saheer ya ce, "É—ago mana."

Ta ɗago a hankali ta kalle sa, ya ce, "ina jin kewar ki a zuciyar ki, kin yi min bazatar da ba ki taɓa yi min irinta ba."

Ta yi murmushi bata ce masa komai ba, shi kuma ya É—aga kai ya ce, "bara na samo miki abinci, na san kin saba da abinci mai daÉ—i ko?."

Ta yi dariya ta ce, "ni komai ma zan ci."

"To ki jira ni."
Chapter 100 · 0% Book details