← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 133

Sashe 3

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya yi murmushi yana ɗaga kai bai ce komai ba. Duk da ya saba da faɗar i love you ga ƙannensa da iyayen sa, but Ikram ya ga alamun ba irin love ɗin su Riyya take so ba, tana daban yake daga yanayin yadda take faɗa zaka san nata is different, shi kuma baya son causing wani abun shiyasa bai ce komai ba.

Cikin shagwaɓa ta ce, "you can't say you love me too?."

"i love you, shikenan?."

Daɗi ya mamaye mata zuciya, ta ɗaga masa kai tana jin daɗi, sai ta ji babu wanda ya iya furta Ikram da kuma kalmar i love you. Rehaan ya shiga mota tana ɗaga masa hannu suka fita daga gidan. Ta yi ajiyar zuciya tana jin ƙhamshin turarensa yana mamaye ta kayan jikinta. Zama in ya yi a waje sai ka san ya zauna, balle ita da ta yi hugging ɗinsa.

Ta yi murmushi tana shaƙar ƙhamshisa, tana jin ƙaunarsa tana sake shiga zuciyarta, ƙauna ba irin ta Yaya da ƙanwa ba, ƙauna ta masoya wanda suke burin aure...

Da alama an samo zaɓin Mamy🤭🤣

Nana Haleema
09030398006.
[6/15, 12:45 PM] KRBBK: RDB02P02
Arewapen@nanahaleema11

Tunda suka fizgeta suke tsula gudu akan titi, Islaha kawai jinta ta yi a cikin motar, bata san ta ya aka yi hakan ta kasance ba. Ta kalle su ganinsu su biyu ne kawai a ciki, sai mai tuƙa motar na uku, kana kallonsu ka san mutane ne ƙarfafa wanda suka yi kama da bouncers.

Islaha ta buÉ—e baki zata yi magana É—aya daga cikinsu ya É—ora hannunsa akan lips É—insa, ya buÉ—e idanu ya ce, "shii! Kar ki ce komai."

Islaha bata ji kashedin da suka yi mata ba, duk da tana cikin tsoro haka ta daure ta ce, "kamar ya kar na ce komai? Ina za ku kaini, su waye ku?."

Ɗaya ya kalle sa ya yi masa alama da kansa, kafin ta yi zato an saka mata baƙar hula, an kulle mata fuska.

Islaha ta kurma ihuu tana fizge-fizge, duk da sun É—aure mata iya hannu, amma sai fizge-fizge take yi ta ce, "su waye ku? Ina zaku kaini, me na yi muku ku ka É—auko ni?."

Suka yi shiru babu wanda yace mata komai a motar, dan van ɗin a kulle take, babu wanda zai ji abinda take faɗa. Ga glass ɗin baƙi, babu wanda zai hango ta duk haukan da zata yi. Islaaha ta fara dukan glass ɗin motar da hannunta tana faɗin, "A taimake ni, an sace ni! Wayyo Allah, ku taimaka min!"

Ta faÉ—a tana ihuu sosai tana cigaba da dukan glass É—in.

ÆŠaya daga cikinsu ya fusata, cikin tsawa ya ce, "ke! In ba ki yi mana shiru ba sai na dalla miki mari!."

Islaha bata yi shiru ba sai ihu take yi kamar ba warning aka yi mata ba.

ÆŠayan ma ya kalle ta ya ce, "baza ki yi shiru ba?."

Bata daina ba sai ma sake ƙara ƙarfin ihun da take yi. Wanda ya fara magana a farko 
ya ce, "zan cilla ta window yarinyar nan wallahi."

"A'a, kar ka yi haka. Yi haƙuri mu ƙarasa."

Ya yi ƙaramin tsaki suka cigaba da tafiya tana fizge-fizge tana kuka.

Ita dai ta ji an tsaya, sai sautin buɗe mota da ta ji, kafin ta ji an yi mata ɗaukar kaza. Wannan ya riƙe kafaɗarta ɗaya, ɗaya ma ya riƙe kafaɗarta ɗaya, ana tafiya da ita bata san inda zasu je ba, dan an rufe mata fuska.

Ajjiye ta ta ji an yi, sannan suka kunce mata hannunta, kafin su cire mata abin suka rufe mata fuskar ta cire da kanta, a lokacin har sun fita sun kulle ƙofar. Islaha sai da ta ɗan jira, idanunta ya dawo daidai saboda duhu, ta bi inda suka ajjiye ta da kallo ƙirjinta yana bugawa da ƙarfi.

Babban katafaren luxury parlor ne mai kyau da haske, duk inda ake neman haɗaɗɗen falo da kyau da girma yake ya kai. Ya haɗu sosai, ga sanyi da ƙhamshi da yake yi kamar gidan amarya.

Islaha ganin wannan falo sai ta kuma firgita, ta nufi ƙofar a guje tana jijjiga ƙofar amma kamar babu kowa, ta ƙarasa wajan window ta janye lalube, ta buɗe glass ɗin window tana faɗin, "ku su waye? Ina ne nan ku ka kawo ni? Don Allah ku zo ku barni na tafi. Babana bashi da lafiya, yana asibiti, don Allah ku buɗe ni!."

Tistt kamar babu kowa, dan ko mota É—aya babu a ajjiye a wajan, kamar ba yanzu aka ajjiye ba. Ta sake buÉ—e murya ta ce, "Kuna ina!." Nan ma shiru babu motsin komai.

Islaha ta dafe kai cikin rashin sanin abinda zata yi, ta sake kallon falon tana tunanin ina ne nan kuma? Ina aka kawo ta, waye ya ƙwamuso ta aka ajjiye ta a nan?.

Kamar an tuna mata, sai ta fara duba aljihun jikinta, a nan ta jiyo wayarta tana nan. Hannu yana rawa ta É—auko ta shiga kiran wayar Sadik amma network error. Ta saka wayar a flightmode ta cire, amma abinda service É—in yake nuna mata no service.

Islaha ta dafe kai ta zube a wajan ta rasa abinda zata yi, kuka take yi dan bata san abinda zata yi ba in ba kukan ba. Sai ta kuma zabura ta miƙe, ta sake komawa window tana ihuuu tana hawaye, amma babu wanda ta gani balle aji maganarta.

Ta koma ta zauna ta rasa tunanim me zata yi, hankalinta ya tashi ta rasa abinda yake yi mata daɗi. Falon shiru babu motsin komai, sai sautin ac kaɗan, sai ƙhamshi da yake yi a hankali.

Ta kalli agogo ta ga ƙarfe tara na dare, ta sake duba waya ta ga no service, ta cillar da wayar ta sake fashewa da kuka mai sauti.

Kuka ta yi mai isar ta lokaci É—aya kanta ya rike, ya yi mata nauyi, tana ji kamar zai cire saboda nauyin da take ji ya yi mata.

Ta sake miƙewa ta koma wajan window, murya a dashe ta ce, "babu kowa ne! Don Allah ku buɗe min, Babana bashi da lafiya, ina so in je in gan shi, ku taimaka min!."

Nan ma shiru babu alamun kowa, sai haske a compound ɗin gidan kamar hasken rana, da wata ƙaramar mage da take yawo a wajan.

Takaici ya mamaye mata zuciya ta buga kanta a jikin bango tana kuka, tana ji kamar ta samu wuƙa ta dinga cakawa kanta har sai ta mutu, ga waya a hannunta amma ta zama babu amfani, gata a gidan da babu kowa amma bazata iya fita ba.

A wajan ta zame ta kwanta tana kukan rashin mafita, sanyin falon ya fara yi mata yawa, ta cure a waje É—aya ta haÉ—e kanta da guiwa tana kuka mai tsuma zuciya. Tun tana kukan cikin daÉ—in rai har ta gaza, ta koma sauke numfashi, tana sake curewa waje É—aya saboda sanyin da yake ratsa ko ina na jikinta.

Ta miƙe ta sake kallon window ta ga gidan shiru babu motsin kowa. Gabanta ya faɗi, ta tafi tunanin yanzu ita kaɗai ce a gidan mai uban girma?. Hawaye ya sakko mata, ta koma ta zauna ta rasa abinda yake yi ma daɗi.

Bata san adadin lokacin da ta É—auka a wajan ba, duk da sanyin da take ji haka take zaune a wajan, tsoro da tashin hankali ya cika mata zuciya, tunanin waÉ—anda suka sace ta ya hanata sukuni. Bata san lokacin da bacci ya É—auke ta ba.

            Washe gari.

"Yauwa Hanan, don Allah turo min Islaha in kin shiga gida."

Hanan ta kalli Sadik ta ce, "Islaha bata kwana a gidan nan ba."

Ya kalle ta da mamaki ya ce, "kamar ya bata kwana a gidan ba?."

Hanan ta ce, "eh, jiya kwata-kwata bata dawo gidan nan ba, ni na yi tunanin ma a asibiti ta kwana."

Sadik ya zuba mata ido yana kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya ce, "ni ban gane ba, kina nufin bata dawo gida ba gabaÉ—aya?."

Hanan ta ce, "na faÉ—a maka na yi tunanin tana asibiti tare da Mama."

Sadik ya ce, "wataƙila tana can ɗin, na kira wayar ta bata shiga kwata-kwata. Bara na je na duba."

Zai kunna motar kenan sai ya ji Hannan ta ce, "to ai ga Maman ma."

Ya dakata yana kallon Mama da ta sauka daga napep,  ya tsaya yana jira ta ƙaraso ya ji ko Islahan tana can. Mama tana zuwa wajen ta ce," Sadik ka ganni ko? Na dawo gida na ɗan kimtsa sai in koma, na bar Sa'ida a can. Ya batun kuɗin aikin, An samu kuwa?. Nima yanzu zan ɗan tattaro wani abun sai a haɗa dashi."

Sadik ya ce, "ana kan haÉ—awa Mama. Islaha tana can ne?."

Mama ta ce, "Islaha bata je ba, na yi tunanin tare za ku tafi da ita."

Hanan ta ce, "ba a asibitin ta kwana ba?."

Mama ta ce, "tun jiya da daddare da ta bar asibiti bata koma ba har na fito."

Hanan ta ce, "to wallahi ba a gida ta kwana ba, dan kwata-kwata Islaha bata dawo gidan nan ba."

Mama ta kalli Hanan ta ce, "to wajan ƙawarta fa? Wataƙila ai tana can ko?."

Jin hakan sai Sadik ya É—aga kai yana ajiyar zuciya ya ce, "eh gaskiya ne, bara na aika gidansu Safeeran."

Mama bata ce komai ba ta shiga ciki shi kuma ya ƙarasa ƙofar gidansu Safeera Hanan ta bi bayan sa.

Kafin Hanan ta ƙaraso Safeera ta fito, ganinsa sai ta yi murmushi ta ce, "Hamma Sadik barka da zuwa."

Ya ce, "Barka dai Safeera. Ya gida?."

"Lafiya lau, ya mai jiki?."

"Da sauƙi. Ina ƙawar taki?."

"Yanzu zan tambaye ka na ce tana ina, na ga ban gan ku tare ba."

Sadik gabansa ya faÉ—i ya ce, "kina so ki ce ba tare ku ka kwana ba?."

Safeera ta girgiza kai ta ce, "ni rabona da ita tun a wajan aiki, da ta tashi ta ce min ta wuce asibiti. Na kira wayar ta jiya wajan tara na dare amma wayar bata shiga ko kaÉ—an."

Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!."

Safeera ta firgita ta ce, "me ya faru? Ina Islahan take?."
Chapter 3 · 0% Book details