← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 133

Sashe 31

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta bi sa da kallo tana girgiza kai cike da mugunta. Dan an kama ta akan Islaha ba hakan yana nufin ta yi sanyi ba, a lokacin ta ɗaura ɗammarar yaƙi da Islaha.

         ••••••

Bayan kwana biyu.

Islaha ta cigaba da harkokin aikinta, dan cikin kwanakin bata samun zama duk wani É—aukar rahoto ita ce take zuwa, fuskarta ta sake fita musamman a shafukan yaÉ—a labarai. Ta sake sama cele a idanun al'ammu, ta sake yin farin jini, saboda kyaun fuskar ta da iya aiki da kuma farin cikin da take dashi.

Bayan ta tashi daga waje aiki asibiti ta wuce, a nan ta tarar da Saheer da Mama a wajan Baffa da ya fara samun sauƙi. Ta shiga da sallama aka amsa, Baffa ya kalle ta cikin ƙarfin hali ya ce, "Islaha kin dawo?."

Ta ɗaga kai ta ce, "na dawo Baffa, ya ƙarfin jikin?."

"Alhamdu lillah."

"Allah ya ƙara lafiya."

"Amin. Allah ya yi miki albarka."

"Amin Baffa."

Mama ta yi tsaki ta ce, "waÉ—anda ka haifa kuma Allah ya kwashe musu tasu albarkar kenan ko me?." Baffa dai bai kulata ba dan ta lafiyarsa yake yi ba ta surutan banza ba.

Islaha ta ce, "na shiga wajan Kawu yana bacci."

Baffa dai kallon ta yake yana murmushi, yana jin alfahari a ransa, yana ji ina ma shine ya haife ta. Adda ta bashi labarin wahalar da tayi a kansa, ta faɗa masa komai da faɗi tashin da ta dinga yi akan nemo kuɗin aikinsa. Ta yi abinda ƴaƴansa na cikinsa basu yi masa ba, ta yi masa abinda bazai taɓa mantawa dashi ba har abada.

Islaha bata jima a asibitin ba ta fito ta tsaya a ƙofar ɗakin ba tare da tana yin komai ba, babu jimawa Saheer ya fito yana kallon ta ya ce, "mu tafi gida ko ba yanzu zaki tafi ba?."

Ta gyaÉ—a kai a sanyaye ta ce, "yanzu zan tafi, na gaji sosai."

"Sannu" ya furta yana kafe ta da idanunsa. Ta sunkuyar da kai, ta É—aga kai bata ce komai ba ya yi gaba ta bi bayansa.

Suna fara tafiya a motar da ta zama kamar tasa ya ce, "kin ce na baki kwana biyu zaki faÉ—a min, kwana biyu ta wuce har ina shirin komawa inda na fito, har yanzu baki faÉ—a min dalilin da ki ka ce zaki faÉ—a min ba. Wato kin yi min wayo ko? Tunda gashi an bar batun case É—in gabaÉ—aya."

Ta É—an dafe kanta ta ce, "Ba wayo nayi maka ba Hamma, zan faÉ—a maka."

"Ina jin ki."

"Hamma Saurin me ka ke yi? Na ce zan faÉ—a maka. Kuma yanzu kaina ciwo yake min wallahi" ta faÉ—a yana dafe kai tana lumshe idonta dan kar ya sake maganar.

Ya yi shiru bai ce komai ba har suka je gida, amma zuciyarsa sai saƙe-saƙe take yi masa akan case ɗin, yana kawarwa ne saboda zargi. Islaha ta fita ta ahiga gida, shi kuma sai ya nemo mata maganin ciwon kai ya bata sannan ya shiga ya kwanta dan shima ya gaji.

Da daddare Mama ta dawo, tana zaune a ɗaki ita da Hajiya Karima tana amsa waya Islaha ta shiga a hankali ta zauna a kusa da ƙafarta tana jira ta gama wayar.

Mama da take waya ta ce, "ai visa ta fito, ko gobe za a iya siyan tikiti su tafi, a filin jirgi zasu haÉ—a su da Oga Musa ya rarrabasu inda ya kamata."

Mama ta kuma cewa, "Ai gani ga Kariman fa, babu wani abun zai faru sai alkhairi." Mama ta sake yin shiru kafin ta kashe wayar.

Mama ta kalli aminiyar ta da take kallon ta, suna mamakin ganin Islaha a É—akin a zaune, ta kalli Islaha cikin mamakin abinda ya kawo ta ta ce, "Islaha lafiya?."

Islaha ta gyara zama, cikin sanyin murya ta ce, "Mama alfarma nazo nema a wajan ki in zan samu."

Mama ta ce, "ina jin ki, faÉ—i in zan iya."

Islaha ta buɗe ledar hannunta ta miƙawa Mama ahinda yake ciki.

Mama da Karima suka kalli juna, kafin Mama ta saka hannu ta karɓa tana juya abinda ta kawo mata a hannunta ta ce, "faskon tafiya wata ƙasa nake gani, na waye?" Ta faɗa tana buɗewa sai ga hotom Islaha da sunanta.

Mama ta kalle ta cikin mamakinta ce, "Fasko É—in ki ne ai, yaushe ki ka yi?."

Islaha ta ce, "ranar litinin na yi Mama."

Karima ta ce, "ƙasar waje zaki je kenan?."

Islaha ta girgiza kai, ta sunkuyar da kai a sanyaye ta ce, "ina so a tafi dani aikin da za a je yi Saudia, daman naji ana neman mai irin kamannina, na shirya indai akwai dama."

Mama da Karima suka kalli juna cike da mamaki da tsoro, Mama ta ajjiye passport É—in a kusa da ita ta ce, "ban gane ba, yi min bayani yadda zan gane Hajiya Islaha."

"A asibitin fa Baffa yake na ji kuna cewa akwai gidan da aka samu amma babu mai zuwa. Shine na je nayi komai na kawo miki, indai ba a samu mai zuwa gidan ba nima ina so naje nayi aikin, ina da buƙatar kuɗin a halin yanzu."

Karima ta yi dariya cikin jin daɗi ta ce, "Amma kin kyautawa kan ki Islaha, yadda ki ke da kyaun nan, da kala mai kyau rububin ɗaukar ki aiki za a yi. Wallahi baki taɓa burge ni ba sai yau, ban yarda ke wayayyiya bace sai yanzu."

Mama da mamakin Islaha ya kusa kashe ta ta ce, "wai kina nufin kema saudian zaki tafi?."

Islaha ta É—aga kai kamar mara jini saboda sanyin jiki ta ce, "indai akwai dama ina so na je."

Mama ta yi dariyar jin daÉ—i ta ce, "dama mai kyau ma Islaha, akwai damar da zaki je ki yi aiki ki samu kuÉ—i masu kauri."

Mama ta saki fuska ta dafa Islaha ta ce, "Ko ke fa, da irin haka ki ke yi ai da bamu dinga samun saɓani dake ba. Kar ki damu, aiki kamar kin tafi kin gama wallahi. Bara ma kiga, ai ba a bori da sanyin jiki" Mama ta faɗa tana ɗaga waya.

Mama ta ce, "Ga data page nan zan turo, a buga mata visa. Itama da ita za a yi tafiyar, cikon ta ukun ce" tana faÉ—a tana kashewa, ta É—auki hoton fasko É—in Islsha ta tura.

Mama tana murmushi tans kallon Islaha ta ce, "kin taki sa'a, yanzu visa tana saurin samuwa, da an tura suke bayarwa babu wata wahala yadda ya kamata, muna zaune a nan za a iya turo visa ki. Kuma akwai aiki mai kyau a ƙasa, ina tabbatar miki da a cikin wata biyar zaki iya haɗa naira miliyan goma. Aiki da larabawa ba ƙaramin kuɗi yake kawowa ba, kin san su akwai kyautar girma ta ban mamaki, haka kawai zasu iya baki kyautar miliyan guda ban da albashin ki."

Islaha ta sauke numfashi, tana ji a ranta lokacin sauke nauyin bashin da taci yazo ta ce, "yaushe ne tafiyar?."

Hajiya Karima ta ce, "an samu visa mutane biyu, zamu jira taki ta fito, na tabbatar zuwa gobe za a samu takin ma. Dan yanzu ma yamma ta yi ne, da za a iya nemo visa ki. Ana samun visa nan da jibi ma za a siyi tikiti ku wuce, daman ku uku ne, keda Labiba da babar ƙawar ki."

Islaha ta É—aga kai ta ce, "Allah ya kaimu."

"Amin. Ki zauna cikin shiri, ga jakar tafiya a can ki zo ki É—auka ki haÉ—a kayan ki da abinda zaki yi amfani dasu."

Islsha a sanyaye ta ce, "Amma ni bana so aikin ya wuce shekara É—aya, iya na lokacin da nake so zan yi na dawo gida."

Mama ta yi dariya tana yi mata kallon baki da hankali ta ce, "kar ki samu damuwa, Allah ya kaimu."

Islaha ta É—an yi shiru sannan tace, "Mama don Allah bana so Hamma ya sani, tunda ya ce tafiya zai yi a bar tafiyar sai Hamma ya bar garin nan. Daman ga Baffa yana asibiti, shima bazai san mun tafi ba. In na je can zan san yadda zan yi da Hamma, amma don Allah koda wasa bana so ya san da tafiya Mama."

Mama ta sake dafata ta ce, "nima bazan bari ya sani ba, na san halin Saheer zai iya kifar da burin ki. Jeki abin ki, na san abinda zan yi babu abinda zai faru."

"Na gode" Islaha ta faɗa tana miƙewa a sanyaye ta fita daga ɗakin.

Tana fita Mama ta yi shewa suka tafa da Karima, Mama ta ce, "ke ki ga ikon Allah, ashe arzuƙin wannan gida da ake yi mata talla a Jeddah ta tabbata daga hannunmu za a ci sa. Ki duba Islaha dai, yarinya fitsararriya da muka yiwa tayin zuwa ta watsa mana ƙasa a ido, yau gata wai itace da kanta ta kashe kuɗi ta yi fasko har ta kawo a tafi da ita. Kai lamarin nan ya yi min daɗi sosai."

Hajiya Karima ta ce, "nima ya buge ni, na yi mamaki sosai da ta sakko cikin sauƙi haka. Kin ga wannan gidan, da kuɗin aikin sai yadda muka yi dashi."

"Ga mai gidan daman babu lafiya, har islaha ta tafi ba sani zai yi ba balle ya ɗaga min hankali. Ssheer ma barin gari zai yi, su je can su ƙarata ni na tura ta inda zan samu."

"Amma fa lamarin nan ya É—aure min kai, meye sakko da ita haka?."

Cikin rashin damuwa Mama ta ce, "koma meye wannan ita ta ga zata iya, ni dai taje ta samo min kuÉ—i kawai shine burina."

Karima ta ce, "Kai amma za a yi rububin yarinyar nan, dan Oga Musa ya faÉ—a min akwai fararen fatar da suke son mata irin Islaha, dan gidan da yake magana a kai yace mai gidan irin fatar Islaha yake so, da ta je zai É—auka. Yarinya ga shegen kyau da gashi, ga kalar fatar ta abin kallo ko baka yi niya ba...."

Hajiya Karima ta yi dariya ta ce, "Inda zata bi ƙananun hanyoyin da ake da wuri zata zama Hajiya wallahi."
Chapter 31 · 0% Book details