← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 133

Sashe 93

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bayyane ya ce, "da wannan yarinyar zata zauna zuwa wani lokaci da ba ƙaramin kuɗi zata haɗa ba, kalli yadda take ba da riyal dubu takwas ba tare da ta ji komai ba. Lallai an jiƙata, ta zama shalelen mutanen jeedah. Ko wata uku basu cika ba ace har ta samu waɗanann uban kuɗin?."

A lokacin ya hango ta tana tahowa, ta ƙaraso da takarda ta bashi ya saka hannu ta saka hannu, sannan ta yiwa takardar hoto sannan ta bashi kuɗin.

Ya lissafa ya ga sun cika cif, ya bita da kallo ya ce, "na tambaye ki?."

"Ina ji."

"A ina ki ka samu waɗanan kuɗin? A kuɗin albashi dai bai kai ki tara wannan kuɗin ba, kuma ba ki yi kama da mai bin maza ba, amma waɗanann kuɗin da na gani a hannunki sun bani mamaki. Ba ku cika wata uku a ƙasar nan ba har yanzu, amma kin tara wannan kuɗin mai uban yawa."

Ta É—aure fuska ta ce, "tunda na biya ai shikenan. Mun rabu lafiya, ni zan koma nigeria a cikin kwanakin nan."

Ya bita da kllo ya ce, "ke kuwa kina samun wannan kuÉ—in me za ki koma nigeria ki yi?."

Bata ce komai ba, yana ta jinjina kuÉ—in sai ta kalle sa ta ce, "don Allah nawa zan samu ticket É—in Abuja?."

Ya kalle ta ya ce, "Zai kai riyal dubu É—aya da wani abun, kin ga lokacin umrah ne yanzu, ana ta shigowa dole ticket ya yi tsada. Amma za ki samu, musamman in ki ka nemi jirgin saudia."

Ta gyaÉ—a kai ta ce, "in zan siya a ina zan je na siya?."

Alhaji Musa ya buÉ—e baki ya ce, "wai da gaske ki ke?."

Ta sauke numfashi ta ce, "da gaske nake."

Ya gyaÉ—a kai ya ce, "ni kuwa na ba ki shawara mana Islaha?.."

Ta sake haÉ—e rai ta ce, "ina ji."

"Me zai hana baza ki je umrah ba, tunda visa ki bata ƙare ba, kuma kina da kuɗi. Ki je ki yi umra sannan sai ki koma gida."

Ta É—an jim alamun tunani sannan ta ce, "ni dai ka amsa min kawai."

"Kamfaninsu kawai za ki je, daga nan in ki ka tambaya za a kai ki."

Bata jira mai zai ce ba ta ce, "na gode" ta faÉ—a tana juyawa ta koma ciki.

Tun kafin ya fita ya kira Mama a waya, tana É—auka ta ce, "Alhajin Allah, tunda na ga kiran ka na san ta samu."

Ya gyaÉ—a kai ya ce, "ta samu kuwa. Wacce yarinya ki ka samu mai zafin hannu haka?."

Mama ta ce, "kamar ya kenan?."

"Cikin Æ´an matan da aka kawo mana, wacece wannan mai sa'a haka?."

Mama ta ti dariya ta ce, "ai Æ´ata ce ta cikina."

Ya gyara tsayuwa ya ce, "ke ki ka haife ta?."

"Eh mana."

"Amma za ki bari ta yi mana asarar dukiya? Tana matsayin ƴarki za ki bari ta dawo gida duk da maƙudan kuɗin da take samu?."

Mama da mamaki sosai  ta ce, "ta dawo gida kuma, Yaushe kenan?."

"Ga shi ina faÉ—a miki, kin ganni a tsaye a gidan da take aiki, ta kira ni ta bani kuÉ—in da aka kashe wajan kawo ta. Kin gansu riyal dubu takwas, naira miliyan uku ta É—auko ta bani. Yarinyar nan babu wani É—ar ta lissafa ta bani, kuma tana zancen zata siyi ticket ta dawo gida, in ki ka bari hakan ya faru ba ki kyauta mana ba Zulai."

Mama cikin firgici ta ce, "ban sani ba, kuma da muka yi waya É—azu bata faÉ—a min ba."

"To maza maza ki kira ta, ta canja sahwarar dawowa gidan nan. A cikin wata biyu da kwanaki ta haÉ—a waÉ—annan kuÉ—in, ina ga an sake kwana biyu?."

"Yanzun nan ma kuwa alhajin Allah, yanzu zan kira ta."

"Ki yi maza ki kira ta" yana faÉ—a ya yanke wayar.

Islaha kuwa da ta shiga sai ta fara tunani, sai take ji ko dai ta shiga makka ta yi umran ne kamar yadda ya faɗa mata? Tunda gashi tana ƙasar kuma ba wani kuɗi zata kashe ba, an ce babu nisa daga Jeedah zuwa Makka.

Ta sauke numfashi a bayyne ta ce, "To amma hotel fa? Zan je na dinga zama a masallaci ne?."

_Kuma in ki ka je da kuÉ—in Rehaan ki ka je, gwara ki bari Allah ya kawo ki daga baya._

Ta runtse ido jin shawarar zuciyarta, ta dafe kai dan Allah ya sani Alhaji Musa ya saka mata kwaÉ—ayin hakan, amma kuma zuciyarta gaskiya take faÉ—a mata, da kuÉ—in Rehaan zata je Umra, ita kuma bata so.

Ta zauna tana sauke numfashi, ta dafe kai cikin rashin mafita. Gashi bata so a san zata dawo balle ta kira Safeera ta yi shawara ta je umrar ko kar ta je, bata so kowa ya san da zuwanta sai dai kawai su ganta.

Cikin tunani ta kwanta, tana tunanin zuwa umrah da kuÉ—in Rehaan. Sai tunanin zagin da ya yi mata, da cikin Labiba da kuma Zainab. A haka ta kwanta ba dan tana jin baccin ba.

    Mama kuwa tana kashe wayar ta kira Labiba, Labiba tana zaune ita da Aysha, ta ga kiran Mama. Ta ɗan lumshe ido ta ce, "Mama ce."

Aysha ta ce, "Allah ya sa ba yarinyar nan ce ta faÉ—awa Mama abinda ya faru ba."

Labiba ta girgiza kai ta ce, "Islaha baza ta faÉ—a mata ba, sai dai in wani abun ne."

Ta É—auki wayar ta saka a kunne ta ce, "Mama ina yini."

Mama ta ce, "lafiya. Ya na ji maganar ki kamar mara lafiya?."

Labiba ta ce, "mura nake fama da ita."

Mama ta ce, "Na ji maganar wai za ki dawo gida, akan me?."

Labiba da mamaki ta ce, "zan dawo gida kuma? In ji wa?."

Mama ta ce, "ban gane in ji wa ba, ba yanzu Ale Musa ya bar wajan ki ba?."

Labiba ta ce, "ni bai zo inda nake ba, rabon da na gan sa tun ranar ya zo ya karɓi kuɗin nan."

Mama ta ce, "Yanzu muka gama waya dashi fa, ya ce min har riyar dubu takwas ki ka bashi, wai kin gama biyan kamfani kuÉ—in da suka kashe miki."

Labiba ta ce, "Kuma ni ya ce miki?."

"to wacece Æ´ata in ba ke ba?."

"Ki ka sani ko Islaha yake nufi?."

Mama ta yi É—if tunawa da hakan da Islaha, dan ko kaÉ—an bata yi tunanin ta ba. Labiba ta ce, "Itace ma, ko tantama bana yi Islaha ce."

Mama ta ce, "Islaha! A ina zata samu kuÉ—i kamar wannan? Ko kin haÉ—a ta da mai gidan naki ne?."

"aa Mama, ni bai sake yi min maganar ta ba ma, dan a cikin kwanakin nan ma baya nan ya yi tafiya, bai jimawa da dawowa ba."

Mama ta ce, "taɓɗijam! A ina yarinyar nan ta samu kuɗi irin wanann? Kin ji yadda yake faɗa min kuɗin da ta samu?."

Labiba ta ce, "Mama in ta so babu abinda bazata samu a nan ba. Nima dan kina yi min addu'a, da yanzu na fi haka."

"Lallai yarinyar nan tantiriya ce, ki ce yawon ta zubar É—inta kawai take yi."

Labiba bata ce komai ba, Mama ta ce, "Na yi mamaki wallahi."

Labiba ta ce, "Mama kaina ciwo yake, sai anjima" ta faÉ—a tana kashe wayar.

Nana Haleema.
[7/20, 10:26 AM] KRBBK: RDB2P68
Nana Haleema.

Bayan Labiba ta kashe wayar Aysha ta kalli Labiba ta ce, "Lafiya dai?."

Labiba ta ce, "yarinyar nan da muka haÉ—u ranar nan, wacce ta raka ni asibiti. Wai itace zata koma nigeria, har ta gama biyan kuÉ—in da aka kawo ta."

Aysha ta buÉ—e ido ta ce, "a cikin wata biyu har ta biya kuÉ—in shekara guda?."

Ta É—aga kai Aysha ta ce, "lallai yarinyar tantiriya ce, ki ce har ta fi mu iya harka."

Labiba ta ce, "ni ba wannan ba. Aysha tsoro nake ji, kar na sake yin ciki."

Aysha ta ce, "me zai kai ki sake yin ciki kuma? Wancan É—in ma kuskure aka samu, amma yanzu ai na san baza ki sake bari ki yi ciki ba."

Labiba ta ce, "ta ya kenan? Mutumin nan ba ya barina na huta, ni wallahi gabaÉ—aya na fara gajiya."

Aysha ta ce, "kin gaji da kuÉ—in?."

Ta É—ago ido ta kalle ta ta ce, "Ba haka bane, kawai ban ji daÉ—i da na yi ciki ya zube ba."

"Au so ki ka yi ki haife sa?."

"A'a."

"To ai murna za ki yi da ya fita da kansa, ba ke ki ka zubar dashi ba ai."

Labiba ta yi shiru bata ce komai ba. Aysha ta ce, "kin ga."

Ta faÉ—a tana nuna mata wasu pills a hannunta. Labiba ta kalle ta ta ce, "na meye?."

"Hana É—aukar ciki, babu ruwan ki da fargabar za ki sake yin ciki nan gaba."

Labiba ta zubawa maganin ido sannan ta ce, "ni bazan sha magani ba."

Aysha ta ce, "meyasa baza ki sha ba? Kina so ki dinga É—aukar ciki ne?."

"Bana so, amma bazan iya shan maganin tsarin iyali ba. Kar na lalata mahaifata tun ban yi aure ba."

Sai ta bawa Aysha dariya, ta yi dariya son ranta sannan ta ajjiye mata maganin ta ce, "yadda ki ka gani, gashi nan in kin ga za ki sha daidai ne, in baza ki sha ba ma duk ɗaya." Ta miƙe ta fita daga ɗakin ta bar Labiba cikin tunani.

     Washe gari Maleek da matarsa suka dawo, bayan sun huta suna zaune, su Islaha gama gabatar musu da abinci. Bayan sun kammala Islaha ta zauna ta ce, "ina da maganar da zan yi."

Maleek ya ce, "ina jin ki."

Ta sauke numfashi ta ce, "ina so zan bar aikin nan, zan koma nigeria."

Maryam ta ce, "Meyasa za ki koma?."

Islaha ta ce, "ina da wani abu da zan je na yi a can, zamana a nan ya ƙare."

Maleek ya ce, "Kin tabbatar babu abinda aka yi miki?."

Ta É—aga kai alamun eh. Maleek ya ce, "yaushe za ki tafi?."

"Cikin satin nan."

Ya É—aga kai ya ce, "shikenan, in za ki tafi ki faÉ—a min zan nemar miki ticket."
Chapter 93 · 0% Book details