Sashe 94
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi murmushi tare da godiya ta tashi ta koma É—aki. Duk sai ta ke jin babu daÉ—i a ranta, amma komawar gidan ya fi mata alkhairi akan zaman.
Da yamma ta je Mall ta É—an yiwa mutane masu mahimmaci a gare ta tsaraba madaidaiciya ba mai yawa ba, tana ta shirin tafiya gida a hankali har lokacin babu wanda ta faÉ—awa.
Bayan ta dawo tana shirya kayan Mama ta kira ta, ta É—auka kafin ta yi magana Mama ta ce, "har kin samu dama da saken da za ki biya kuÉ—i gabaÉ—aya baki faÉ—a min ba ko?."
Islaha maimakon ta bata amsa sai ta ce, "Ina yini Mama?."
"ai da ban yini ba da ba ki ji mi ba. Waye ya ce ki ce za ki dawo gida ba tare da na sani ba?."
"Mama na gama abinda ya kawo ni, dawowa gidan...."
"Me ki ka gama da ya kai ki? Me ki ka gama da ya kai ki ƙasar?. Yawon watsewar ki ka gama?."
"Mama ni bana yawon watsewa, waÉ—anda suke yi dai suna yi, amma ni babu."
"Kan uba! Ni ki ke faÉ—awa wannan maganar?."
Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, dan ranta a ɓace yake sosai.
Mama ta ce, "in ba wayon banzan ba a ki ka samu waÉ—annan kuÉ—aÉ—en masu yawa? Ale Musa ya faÉ—a min duk abinda yake faruwa, ya faÉ—a min duk abinda ki ka bashi da abinda ki ka ce masa."
"Ni gida zan dawo."
"to ki nemi wani gidan, gidana ba gidan ubanki bane balle ki ce za ki dawo ki zauna. Ki san inda za li samu ki zauna, amma ba dai zama a gidana ba wallahi."
Islaha tana sane ta kashe wayar, dan in ta cigaba da jin maganar Mama zata iya zaginta bata san ta yi ba.
Rehaan yana zaune hankalinsa gabaɗaya yana kan aiki, ya yi busy sosai, yana ta aiki ko motsin kirki ba ya yi. Gabaɗaya abin ya yi masa yawa, ya samu saƙo daga kamfaninsa na Englaand, ya samu saƙo daga asibiti, ya samu daga mall da sauran kasuwancinsa.
Ya cillar da wayar jin kansa ya É—au chaji, ya hargitsa gashin kansa yana ji kiran waya yana shigowa amma bai iya É—auka ba, dan bai san me zai ce ba. Dan lokacin rufe ko ina ya kusa, dan ayi lissafi a fitar da zakka.
"Ya dai Mr Busy" Jafar ya faÉ—a yana zama a kusa dashi.
Ray ya É—ago ya kalle sa yana lumshe ido, sai kuma ya ce, "Uk, yaushe zaka koma?."
Jazy ya taɓe baki kaɗan ya ce, "Sai bayan aurena, na gama tattara komai nawa na can yana gida, ni da sake zuwa wata ƙasar sai na je honeymoon."
Ray ya ce, "ka taimaka ka je don Allah, abubuwa sun yi yawa a can."
Ya girgiza kai ya ce, "meye amfanin Alex? Na ga shine yake riƙe da komai a can ko?."
"amma ba kamar kana can ba, ban san me zan ce ba."
Jazy ya ce, "Daga nan ka wuce can, dan ni dai bazan shiga ba gaskiya, ni da Uk sai zamu tafi da Riyya."
Ray ya sauke numfaahi mai tsaho bai ce komai ba. Jazy ya ce, "lokacin lissafin ka ya yi."
A fisace ya ce, "ba shiyasa na ce ka je ba, dame zan ji? Da waÉ—anda suke Yola, ko dana Uk?."
"Ka tuna da partnership É—in kamfanin nan na France, shima zai shiga lissafi."
Ray ya ji kamar ya shaƙo wayan Jazy ya matse sai ya daina numfashi, amma sai ya daure ya shafa kansa yana girgiza kai cikin takaici. Ya san yana cikin yanayi na cakuɗewar tunani, amma ya dinga tuna masa da abinda ya manta dashi, yana sane yake tsokanarsa, dan kawai ya fusata shi.
Jazy ya murmusa ya ce, "My billionaire, yanzu dai ka zama mai saurin fusata, da ba haka ka ke ba wallahi. Yanzu da an yi magana sai faÉ—a, ka dinga sassautawa kan ka."
Ya sake yin dariya sannan ya ce, "Haka za ka yi haƙuri, ai daman masu kuɗi irin ka kullum a haka suke, ba sa samun lokacin kansu yadda ya kamata. Kullum sune tunani, lissafi da chajawar kai. Kai ka gode Allah, abubuwa suna zuwar maka da sauƙi, baka cika rasa lokacin kan ka ba."
Ray ya yi masa banza, yana ji ana yi masa waya bai amsa ba. Jaxy ya ce, "ni na san wannan shekarar ma sai dai ka kimanta kawai ka fitar. Ribar da ta shigo kamfaninka wannan shekarar ta fi ta last year...."
"Hmm dole ƴan uwanka su dinga cewa ka yi ƙanƙanta da samun irin wannan kuɗin, gabaɗayanka nawa ka ke? Amma kana da abinda ko Abba sai dai ya kalle ka. Yana da kyau ace ka yi aure, ka fasai ka ɗora matarka akan wani abun daban, yadda za ka dinga samun sauƙin wasu abubuwan."
Ray jin Jazy ya koma maganar hankali sai sauke numfashi ya ce, "Alhamdu lillah!. Amma fa is not easy, kwana biyu gabaÉ—aya kaina a rufe yake. Na shiga Dubai, daga na shiga Madina na dawo nan. Ni shiyasa nake sso ka yi auren ka tafi da Riyya can, sai ta taimaka min da wani abun."
Jazy ya kalle shi yana harararsa ya ce, "baza ka wahalar min da mata ba."
Ya harare sa sai kuma ya ja tsaki ya ce, "dole ta yi, min, bazai yu kai ba ka yi min ba, ita ka ce baza ta yi ba."
Ya yi dariya ya ce, "ina da abin yi ai, ba a ƙasan ka nake ba."
"Na fitar da kuɗi ina so na bawa mutanen gidan mu, amma bana son ƙaramar magana."
Jazy ya yi dariya ya ce, "ka san sai sun yi kuwa, ƴan gidan nan naku ko ruwa za ka faɗa sai sun ce ka zuba musu ƙasa. Amma kar ka fasa, ka yi ɗin kaine a gaba gaba dasu." Ya girgiza kai bai ce komai ba.
Jazy ya ce, "Bilal ya ce min ana ta sadaka da abinci. Na ce daÉ—ina sa Rehaan Mamy akwai hankali kaÉ—an." Ya É—an yi murmushi kawai bai ce komai ba.
Jafar ya ce, "Yauwa, ina housemaid É—in nan ta ka? Tana zuwa kuwa?."
Nan da nan annurin fuskar Rehaan ya gushe, ya É—auere fuska bai ce komai ba.
Jafar ya ce, "ina so na ganta ne."
Ya ɗago suka haɗa ido, Jazy ya ce, "Ya na ga ka ɓata rai, dan na ce ina so na ganta shine na haɗe rai haka?."
Ya sake tamke fuska ya ce, "ban taɓa jin tsanar ko wacce halitta kamar yadda nake jin tsanarta ba. Ko kaɗan bana so na tuna na taɓa ganinta."
Jazy ya zaro ido cike da mamaki, dan tunda yake da Rehaan bai taɓa ji ya ce masa ga wani ko wata da ya tsana ba, ko a film in suna kallo ba ya cewa ya tsani wani actor ko actress balle kuma a zahiri.
Jafar da ya cika da mamaki ya ce, "Meyasa? Me ta yi maka haka da ka tsane ta?."
Ya yi tsaki bai ce komai ba, yana jin tsanarta tana sake shiga jikinsa. Jazy ya ce, "kuma wallahi tana da kirki sosai, na yi binckena kanta. Ni da na ji a gidan marayu ta girma sai na ji ta bani tausayi, shiyasa ka ga na sake da ita har muna hira haka, dan rashin iyaye babu daÉ—i."
"Oh, na É—auka ka shiga jerin mazan da suke tare da ita, kamar Ubaid."
Jazy ya yi tsaki yana binsa da kallon mamaki ya ce, "ko da na shiga cikinsu ɗin bana tunanin ranka zai ɓaci kamar haka, ko da ni da ita za ka gani a ɗaki ɗaya bana tunanin ranka bazai ɓaci har haka ba Rehaan. Ni na rasa me ta yi maka da ke ke ɓata rai saboda ita, kai ta faɗa kamar wata mata mahimmaci a gare ka. Kuma ta faɗa min ta zo ƙasar nan saboda kai, lokacin da ka sace ta akwai kuɗin ka da ta ɗauka, ta ce ka duba cctv zaka gani. Wannan kuɗin shine ya kawo ta nan dan ta biya ka. Ni kuma nace maya ta koma gida, zan biya ka kuɗin ka, kuma already na tura Bilal kuɗin."
Rehaan ya É—ago ya kalle shi, sai kuma ya ja tsaki ya ce, "wani lokacin wannan É—abi'ar ta ka ta saurin sakewa da kowa haushi yake bani, a haka kamar namiji amma banza ne kai."
Kafin ya yi magana ya ce, "Kawai saboda ba ka san zafin nema bane, shiyasa ka ke abinda ka ke so da kuÉ—in Daddy, shiyasa fitar da kuÉ—i ba ya yi maka wahala. Ni da na san zafinsu ai bazan yi ba."
"Dallah can, har ka faÉ—awa wani kashe kuÉ—i?. Naira miliyan sha bakwai ne fa ba wani abu ba."
"Oh! seventeen millions ka ke cewa ba wani abu ba? Baka zafin nema ba Jazy."
Ya yi dariya ya ce, "dan kana keeping malice da ita ns ya saka ka ce cewa haka, amma ban kama ƙafarka a kashe kuɗi ba. Kuma na biya bashin da ya saka ta baro gida dominsa."
Ray ya ce, "ƙarya take yi fa, ta saka ka yi asarar kuɗin ka, dan na rantse da Allah baza a dawo maka dasu ba."
Jazy ya ce, "ka ji na ce a dawo dasu ne? Ni dai na biya mata na sauke mata nauyin da take ganin ta É—orawa kanta."
Ray ya taɓe baki ya ce, "Lokacin da na ganta a diamond hotel, ina ranar da aka ce anyi sata an gudu, har ka ke bani labari?."
Jazy ya ce, "wani É—an siyasa ko?."
"To itace ta yi, a kan idona ta fito daga É—akin, shima ya fito yana cewa ta manta face mask É—inta."
Jazy ya zuba masa ido yana kallonsa kafin ya ce, "da gaske ka ke?."
"Ita ɗin banza na yi mata ƙarya? Tun daga nan na santa, nima kuma gashi ta faɗa maka ta yi min sata. Na haɗu da ita a train da zan dawo daga Madina, har na taimaka mata ganin bata da lafiya, ashe miscarrige ta yi."
Jazy ya zaro ido ya ce, "miscarrige?."