← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 133

Sashe 54

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sai madarar da aka dafa, kar ya a ɗanyen maradar da ba a dafa ta ba. Sannan a dinga shan ruwa sosai, ya kasance a yini ɗaya ana shan ruwa lita 2 zuwa 3 a rana. In an dawo asibiti aka duba, in likita ya ga da yuwa a ƙara adadin ruwan za a ƙara ko a rage. A dinga kula da lafiya yadda ya kamata, a dinga zuwa asibiti duk bayan sati biyu ana ganin likita, in kuma aka samu kwanaki bayan an warke yana da kyau a dinga zuwa asibiti ana duba lafiya gabaɗaya. Yana da kyau a dinga duba yanayin yawan jini, sugar, da sauransu."

"Abinda ya kamata a gujewa gishiri, É—anÉ—ano mai yawa a abinci, barasa, É—anyen naman da bai dahu sosai ba. A guji aiki mai nauyi ko yawon da zai wahalar da jiki Baba. In dai aka kiyaye wannan, aka yi komai yadda ya kamata, ana shan magani ana zuwa checkup in sha Allah za a samu lafiya sosai."

Baba ya gyaÉ—a kai ya ce, "na gode sosai likita."

Dr ya kalli donar ya ce, "na dawo kan ka."

Kawu ya yi murmushi ya ce, "to ina ji likita."

"A yawaita shan ruwa kamar lita biyu zuwa biyu da rabi a rana. A dinga cin nama mara kitse, a dinga cin kayan lambu, ƴaƴan itaciya, madara amma ba da yawa ba. Baba a gujewa cin gishiri da sugar mai yawa, lemo mai gas, inda hali duk wani soft drink a dakatar da shansa na wani lokaci. A gujewa maganuna ba tare da umarnin likita ba, ko ciwon kai aka ji yana da kyau kafin a sha magani azo a ji me likita zai ce, maganunan hausa su ma a ajjiye su a gefe. In za a sha ruwan ya zama ana rarrabawa, kar a ɗaga kai asha ruwa mai yawa lokaci ɗay,  an fi so a sha da kaɗan kaɗan. Sannan zaka ɗan dinga jin zafi ko kasala wani lokacin, ana buƙatar ka huta sosai, aƙalla sati huɗu zuwa biyar. Baba a guji aiki mai wahala, a dinga zuwa ana duba lafiya akai akai, a dinga zuwa ana duba yanayin fitsari, da yanayin hawan jini, da sikari."

"Amfanin gujewa abu mai kitse saboda kar a ƙara ƙiba, amfanin gujewa gishiri ƙaruwar hawan jini, amfanin gujera sugar saboda ɗagawar sugar. Akwai maganin da yake ƙara sikari a cikin maganin da za a baka, shiyasa ake so a rage shan farin sikari mai yawa. A yanzu jinin ku da sugar ku duk ya yi yadda ake so, fitsari ya koma kalarsa shine jin daɗin mu."

Kawu ya ce, "in sha Allah za a kiyaye."

Dr ya ce, "Allah ya ƙara lafiya."

Suka amsa da amin Dr ya ce, "in kun gama clearing bill za a baku takardar sallama, daga nan zan iya cewa sai wani lokaci."

Sahaeer ya ce, "za a iya zuwa wanann asibitin don duba lafiya?."

Dr ya ce,  "Sosai ma, tunda suna da file a nan za a iya zuwa ko yaushe in sha Allah."

Sadik ya ce, "mun gode."

Sadik da Saheer suka fita zuwa reception dan su biya abinda ya rage.

Suna gama biyan kuÉ—in Dr ya kalli Sadik ya ce, "Sadik minti É—aya don Allah."

Sadik bai ƙu ba ya ƙarasa inda yake, Dr Isma'il ya ce, "Don Allah ina Islaha? Kwana biyu bana ganin ta."

Sadik ya É—an murmushi ya ce, "kwana biyu ta É—an yi tafiya."

"Aiki ko ƙaro karatu?."

"Duka biyun."

"Shiyasa bana ganin programs É—inta. Zan iya samun number ta don Allah?."

Sadik ya murmusa ya ce, "ba kana da social media handles É—in ta ba? Kawai ka yi mata magana, dan inda take a yanzu waya bata shiga."

Ya ɗaga kai ya ce, "na gode. Allah ya ƙara musu lafiya." Ya amsa suka yi musabaha sannan ya dawo wajan Saheer da yake ta kallonsa.

Saheer ya kasa haƙuri ya ce, "me likitan nan ya ce maka?."

Sadik ya kalle sa bayan ya haÉ—e rai ya ce, "Islaha yake nema."

"A matsayinsa na waye zai neme ta?."

"a matsayin wanda yake sonta mana, zaka hana mutane son Islaha ne?."

Saheer ya zuba masa ido yana kallo cikin kishi mai tsanani, ya kasa cewa komai ya cize baki cikin baƙin ciki.

Sadik ya ɗan taɓe baki yana kallon Saheer ya ce, "kai duk wannan kyautatawar da yake yi mana ka ɗauka a banza yake yinta?....."

Sadik ya yi Æ´ar dariya ya ce, "Wallahi son Islaha yake yi, tun ba yanzu ba na lura da hakan."

Saheer ya yi shiru bai ce komai ba zuciyarsa bugawa take yi da sauri sauri. Kishi yake ji mai tsanani, zuciyarsa tana yi masa zafi da raÉ—aÉ—i akan kamalan Sadik.

Sadik ya ce, "Yarinyar akwai farin jini, da wahala taje wani waje ba a ce ana so ba."

Saheer bai ce komai ba ya haÉ—É—iye mugun abu da ya tsaya masa, da ace Islaha tana nan babu abinda zai hana bai saka an É—aura masa aure da ita ba, daga lokacin babu wanda zai sake cewa yana sonta.

A wannan yanayin suka shiga mota aka wuce gida. Saheer har aka je gida bai ce komai ba, yana riƙe da Baffa har ɗakinsa. Bayan sun kwantar dashi shi da Sadik suka raka Kawu gidansa, bayan sun yi masa siyayya mai yawa wacce take nuni da jin daɗinsu akan abinda Kawu ya yi.

Bayan sun dawo gida suna zaune a mota Sadik ya kalle sa ya ce, "sai wani ɓata rai ka ke yi dan kawai an nemi lambar Islaha. Islahan da bata gaban idanunka a yanzu, ka san abinda take aikatawa a halin yanzu?."

Ya juyo ya kalle sa yana ɗaga masa hanmu ya ce, "Ya ishe ka, ka daina faɗar wannan maganar akanta. Bana son wannan shirmen da ka ke faɗa, na faɗa maka bana so amma ka ƙi yarda ko?."

Sadik ta ce, "gaskiya ce ai, kaima ka saukewa kanka wannan damuwa da takaicin da take ɗura maka, ka share ta ka nemi wata ka huce takaici. Nan na dinga converncing ɗinka akan ka barta a dinga tafiyar aikin nan da ita amma ka ƙi, da a cikin mu take da duk ba haka ba. Yanzu gashi tana can wata ƙasa ƙarƙashin larabawa, Allah kaɗai ya san abinda yake faruwa a can. Duk yadda ka ke wannan haukan a kanta, ita ko neman ka ma bata yi, tana can tana hutawa cikin ac tana cin kaza kullum."

Saheer ya kalle sa rai a ɓace ya ce, "kai ka san dan kaine shiyasa na tsaya kana faɗa min wannan maganar ina ƙyalewa ban fasa maka baki ba, kaima ka kusa kaini bango, in baka iya bakin ka na wallahi zan baka mamaki. Sadik ka daina yiwa Islaha wannan mummanan zaton, ko ina Islaha zata je ni na yarda da ita, baza ta taɓa aikita wani abu mara kyau ba. Na amince da ita har cikin raina, na yarda da ita ɗari bisa ɗari,  ko a cikin maza dubu zata kwana ta tashi bazan zargi Islaha ba. Kaima ka iya harshen ka, in ba haka ba wallahi sai na ɓarar da kai a wajan nan."

"Gaskiya ce baka so, kuma wannan ba mummanan zato bane gaskiya ce."

Saheer bai ce masa komai ba ya fita daga motar ya shiga cikin gida, dan in ya cigaba da sauraren sa zai iya yi masa duk abinda zai yi danasani nan gaba.

Wajan Baffa ya wuce ya tarar da Mama da Adda a zaune, yana shiga Baffa ya ce, "Saheer ina Sadik?."

Saheer ya ce, "ya tafi Baffa, yanzu muka rabu dashi bayan mun kai Kawu gida."

Baffa ya ce, "Aboki ne na gari, yana da kirki sosai. Ya yi abinda ko kai da kanka iyakacin abinda zaka yi kenan, iya abinda zaka yi kenan daga kwanciyata zuwa yanzu. Allah ya yi masa albarka, Allah ya sa ya fi haka, Allah ya sake haÉ—a kan ku." Saheer ya amsa da amin yana jin haushim Sadik a ransa.

Baffa ya ce, "in na samu lafiya zan je har gida wajan iyayensa na yi musj godiya, zan je na yi musu godiyar abinda É—ansu ya yi mana na karamci."

Mama ta ce, "ya kamata" ta faɗa a taƙaice.

Baffa ya ce, "Ina Islaha ne? Ina ta tambaya sai ku yi min shiru."

Saheer ya ɗan sauke kai ƙasa ya ce, "Baffa Islaha bata nan."

Baffa da yake kwance ya ɗan motsa kaɗan zai miƙe zaune, Saheer ya miƙe ya riƙe sa ya ce, "Ka yi hankali Baffa."

Mama ta ce, "saboda an ambaci Æ´ar gold É—in ka bata nan, shiyasa zaka hallaka kan ka."

Baffa bai kula ta ba ya ce, "ina jin ka, ina ta je?."

Saheer ya kalli Mama, ya juyo ya kalli Baffa ya ce, "Mama ta tura ta aikin ƙasar waje."

Mama ta buɗe ido cikin masifa ta ce, "kamar ya na tura ta? Kai Saheer bana son iskanci da wulaƙanci. Kamar ya na ɗauke ta na kaita ƙasar waje? Jaririya ce ita da zan goya ta a baya na kaita inda nake so?."

Baffa ya kalli Mama ya ce, "Ya isa! Saheer ka yi min bayani yadda zan gane."

"Baffa Islaha bata ƙasar nan, yau kwananta goma da tafiya. Mama ce ta...."

Mama ta katse sa cikin faɗa ta ce, "na rantse da Allah in ka sake ambatar Maman nan sai na tsinke ka da mari, ka ji min yaro da wulaƙanci. Ni na ɗauki Islaha na kai ta, ba itace ta zo ta same ni ta ce na kai ta ba?. Lokacin da na so ta je ba ƙi ta yi ba? Kuma ina zaune ta kawo min fasko ta ce min gashi ta yi in da dama na saka ta tafi a cikin wanda zasu tafi a kwanakin. Dan ka raina ni sai ka dinga cewa ninna saka ta? Ta ƙarfi na jata na kai ta ko kuma sakawa na yi aka ɗauke ta aka kai ta?."

Baffa ya É—an ja numfashi ya ce, "Ya isa haka, ki daina yi min ihu a kaina."
Chapter 54 · 0% Book details