Sashe 60
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana shiga kitchen ɗin ta kunna haske, ta bi ko ina da kallo kamar mai neman wani abun. Sai ta jingina da bango tana tunani, a bayyane ta ce, "Har ƙhamshin turaren iri ɗaya, bazan manta da ƙhamshin turaren nan ba tunda ya jima kafin wayata ta daina ƙhamshin. Ya aka yi nake jin ƙhamshin a nan? Shima ƙhamshin gizo yake yi min ko me?." Sai ta zame ta zauna akan tiles, ta haɗa kai da guiwa bata san asalin abinda yake damun ta ba.
Rehaan yana tare da baƙi a sama suna meeting, yana zaune ya ji wayarsa ta yi alert ɗin lock ɗin da yake haɗe da ƙofar falo, wanda duk wanda ya shigo indai yana gidan zai sani, hakan ta ba shi tabbacin an shigo gidan.
Rehaan ya miƙe tsaye ya sakko ƙasa ya shiga kitchen ɗin, dan daman ita kawai yake jira, da yana da number ta da ya kira ta, dan yana buƙatar ta a lokacin.
Bai kula da ita ba ya shiga kalle-kalle sai ya hango ta a zaune a ƙasa ta haɗe kai da guiwa. Ya bita da kallo yana mamaki, yana tunanin dalilin da ya saka ta zauna a ƙasa.
Islaha da ta ji motsi ta ɗago suka haɗa ido dashi da yake tsaye ya saka hannu aljihu yana kallon ta. Ta zuba masa ido ta ga ya haɗe gashin kansa, yana sanye da complete black suit, sai ƙhamshi yake yi. Islaha ta miƙe tsaye daƙyar tana kallonsa, ta gaji da gizon nan da yake yi mata, gwara ta yi masa warning kawai.
"Don Allah ka daina zuwa idona, don Allah ka ƙyale ni na huta da ganin ka ko yaushe. Na ganka a Yola, na ganka a Jeddah, na ganka a mafarki, na ganka a zahiri, ka bari na huta don Allah. Na san na yi laifi, kuma zan gyara kuskurena, zuwana nan ma saboda na biya bashi da na ɗauka ne. Ka ƙyale ƙwaƙwalwata ta huta, kar ka saka na haukace. Ko yaushe kai nake gani, ka rabu dani na huta, da kaina zan nemo ka duk inda ka ke, ba sai ka dinga damuna da tunani ba don Allah!" Ta ƙarasa faɗa hawaye yana sakkowa daga idanunta.
Rehaan ya bita da kallo jin tana magana ita kaɗai, sai ya kama ƙugu yana tunanin anya lafiya lau take, in ba haka wacce irin magana take yi haka kamar zautacciya?. Babban abinda ya bashi mamaki Yola da ya ji ta ambata, sannan kuma hawayen da take yi ya fi komai basa mamaki. (Ɗan rainin hankali, nufinsa ya manta Islaha😒).
Islaha ganin bai ce komai ba sai ta goge hawayen ta, tana sake tabbatarwa da kanta gizo yake yi mata bashi bane, dan da shine da yanzu ya chakumi wuyanta ya ce ina kuÉ—insa.
Ta ce, "koma meye ya faru kaine da laifi, kai ka yi min duk abinda ka yi har ka saka na aikata abinda ban taɓa yi ba. Na karɓi laifin dan daga ƙarshe na yi kuskure nima. Ka ƙyale ni, ka je can ka cigaba da zama a Yola, zan zo har inda ka ke na same ka. Ka ƙyale ni don Allah, ka daina zuwa mafarkina, ka daina yi min gizo!" Ta faɗa cikin masifa dan ita a tunaninta gizo ne ba gaskiya bane.
Yatsunsa biyu ya yi snapping a daidai fuskarta suka bada sauti mai ƙara.
Islaha ta firgita kamar wacce aka tsirawa allura, ta sake kallonsa idanunta duk hawaye. Ta ga ita yake kallo, ya zuba mata ido kawai bai ce komai ba.
Ita har lokacin bata gasgata shi ɗin bane, ta kai hannunta a hankali kamar wacce zata taɓa wuta, ta ɗan taɓa sa dan ta tabbatar na gaske ne ko kuma na bogi ne. Shi dai ya tsaya cak yana kallon ikon Allah, ya zuba ido yana so yaga a ina zata tsaya.
Hannunta ya ɗan taɓa hannunsa sa ta ji kamar jan wutar lantarki, ta ja baya da sauri tana sake kallonsa dan ta tabbatar ba gizo yake yi mata ba, shine ɗin a gabanta, a Jeddah ba a Yola.
Ya É—auke ido daga kallon ta, ya sake kallon ta ya ce, "We have seven guests, make tea for them, now......" yana gama faÉ—a mata haka ya fita ya bar ta cikin tunani da ruÉ—ani mai yawa.
Drama don start🔥ðŸ˜
_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._
https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S
Nana Haleema.âœðŸ»
[7/7, 10:21 AM] KRBBK: RDB2P41
Nana Haleema.
_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/S0HoWfmkTOI?si=vJKdn7h8rPpmDhS5
•••••••••••••
Islaha ta bisa da kallo har ya ɓace daga wajan daga wajen ta daina jin sautin takunsa, ta dafe kai cikin ruɗani da tashin hankali, a bayyane ta ce, "ta ya ya zai zama shine?."
Ta shiga zagaye kitchen ɗin, tana kai kawo kamar mai ɗawafi, sai kuma ta sake tsayawa ta ce, “amma bai nuna ya sanni ba, kuma in har shine na tabbatar zai neme ni saboda kuɗinsa....."
Ta sake yin shiru tana tunani kafin ta ce, "Amma ya aka yi na ga ya share ni, yana yi min kallon housemaid kawai ba wacce ya sani a Yola ba?." Ta safe kama ƙugu cikin son tabbatarwa.
Ta sake kallon inda ya bi, ta ja numfashi tana jin turaren yana shiga hancinta a hankali ta ce, "turaren iri ɗaya, wallahi ƙhamshin iri ɗaya ne da nasa. Na haddace ƙhamshin nan, tunda wayata ta jima kafin ta daina ƙhamshinsa. Sannan ga gashin wancan mutumin irin wannan, sannan maganar ma iri ɗaya, turancin ma irin na wancan kamar na ƴan Englaand. Iyayin da komai iri ɗaya ne."
Sai kuma ta sake jan numfashi, ta lumshe ido tana tattaro nutsuwa ta ce, "Nutsu Islaha, ba lallai shi É—in bane. Ki nutsu ki dawo hankalin ki, nan Jeddah ne ba Yola ba" ta faÉ—a tana kwantarwa da kanta hankali dan ta kasa fahimtar komai.
Sai kuma ta É—auki waya da niyar faÉ—awa Safeera, sai kuma ta fasa tana kallon wayar a bayyane ta ce, "A'a kar ki faÉ—a, in ki ka faÉ—a mata zarginsu zai iya zama gaskiya, zasu ce daman can na sanshi, kuma zasu ce da haÉ—in bakinsa na zo nan. Kenan da gaske shine?."
Sai kuma ta wara hannu ta ce, "indai har ni Islaha zan iya zuwa Jeddah shi meyesa nake ganin ba shi bane? Bayan shi mai kuÉ—i ne, zai iya zuwa duk inda ya ga dama?. Tabbas shine, ko tantama bana yi shine wanda ya sace ni."
Ta sauke ajiyar zuciya ta bi inda ya tsaya da kallo, ta taɓe baki ta ce, "yadda ya nuna bai sanni ba nima zan nuna ban sanshi ba, zan cigaba da harkata har na tara kuɗinsa na biyasa na kama gabana....."
Ta sake riƙe baki cikin mamaki ta ce, "kai!
Me gayen nan yake nufi wai, bai gane ni ba?. Lallai an yi É—an rainin sense, ya sace ni ya ajjiye a gidansa ya ce bai gane ji ba?.â€
Ta girgiza kai ta ce, “Amma mutumin nan ya yanke ni fa, abin ya firgita ni sosai. Allah mai iko, Allah ya sake haɗa mu waje ɗaya, a inda ban yi tunani zan ganshi ba sai gashi na gani" ta faɗa tana kallon stove, sai kuma ta tuna da abinda ya ce.
Ta yi tsaki ta ce, "wallahi shine, maganar ma iri ɗaya ce. Wai we have seven guests, ko shi da wa suke da baƙin oho masa. Ɗan rainin hankali mai sace mutane kawai, zaka shigo hannuna ne, bari dai na biyaka kuɗin ka, wallahi sai na yi maganin ka."
Tea É—in ta dafa kamar yadda ya ce, ta samu babban tray ta É—ora kai. Ta buÉ—e fridge ta ga akwai loaf cake a ciki, ta É—auka ta É—orawa kowa slice É—aya.
Ta cire hijjab ɗin jikinta, dan bazai barta ɗaukar trayn yadda ya kamata ba, ta gyara zama rigarta ta naɗa mayafi kamar ko yaushe. Ta ɗauki tea ɗin ta nufi upstairs a hankali saboda nauyin tea ɗin.
Stairs ɗin ma na ɗaurawa, kamar kana taka glass haka suke kana ganin fuskarka. Saman ya rabu biyu, wani ya yi gefe wani ma ya yi gefe, ta zaɓi na dama ta bi ta ƙarasa ƙatuwar balcony ɗin da in kana tsaye a jikin staircase ɗin wajan kana kallon kowa na ƙasa, hira zaka iya da mutumin da yake ƙasa shima kuma yana kallon ka.
Islaha sai da ta hau saman ta ga ashe a ƙasa ba komai take gani ba, ga asalin kallo a nan a sama, dan tunda take bata taɓa ganin lafiyayyen falo mai ɗaukar hanlali kamar sa ba. Harda BAR a gefe, wacce aka yi adogon glass cups da kwalabe kamar na giya.
Ta tsaya cak tana kallon falon dan bata san inda zata bi ba, ga dai corrior nan tana gani, amma bata san in ta bi ina zata je ba, ta ajjiye tea ɗin akan table tana sake kallon falon dan ta gaji da riƙewa. Bar ɗin take kallo, a bayyane ta ce, "Malam Bature har giya ana sha kenan, an yi asara" ta faɗa tana taɓe baki.
"Hey."
Islaha jin magana daga bayanta, sai ta juya tana kallonsa. Bature ne na asali, kana kallonsa sa ka san bai yi kama da wani jinsi ba ba sai bature.
Ta ce, "hello."
"Are you looking for meeting room?."
Ta ɗaga masa kai, ya nuna mata inda zata shiga ta ɗauki tray ɗin ta ƙarasa wajan.
Autimatic door ce a wajan, tana zuwa wajan ƙofar ta buɗe ta shiga da sallama a bakinta.