← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 133

Sashe 6

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsit wajan kamar babu kowa, ta juyo tana kallon falon taga ƙaton tray a ajjiye, da mini tea flaks, sai kayan tea da plates a rufe. Sai slice bread mai girma ajjiye.

Ta É—ora hannu a kai ta fashe da kuka, a. bayyane ta ce, "kenan ana sane dani, har abinci aka kawo min. Na shiga uku!" Ta faÉ—a cikin tsananin tashin hankali.

Ta cire rolling É—in kanta ta cillar da mayafin, ta zube guiwa a wajan tana kuka mai tsuma zuciya. Idanunta suka yi mata nauyi, ga yunwa ga ciwon kai ga taurin kai, dan baza ta ci abincin ba sai dai ta mutu ta yunwa.

A fusace ta miƙe, ta yi fatali da tray ɗin ya faɗi a ƙasa komai na kai ya zube, kayan tea ɗin ne da suke gwangwani, sai flaks ɗin tea ɗin sune ba su yi komai ba, amma abinda yake cikin plate ɗin ta zubar.

Cikin ihu ta ce, "bana ci, bana son cin komai. Ku bar ni yunwa ta kashe ni, bazan ci ba!" Ta faɗa tana hakki dan numfashinta ya ɗan riƙe, ga ciwon kai.

Takaici ya saka ta rasa me zata yi, ta gaji da yin kukan, ji take kamar ta dinga dukan kanta har sai ta fitarwasa kanta jini.

Ta koma ta yi lamo tana jin zuciyarta tana bugawa sosai, tana kwance a kan carpet tana jan numfashin da ya tsaya mata a ƙirji saboda yadda numfashin nata ya tsaya.

Ta juya ta yi rigingine tana kallon sama idanunta a rufe cikin rashin sanin abinda zata yi, waye zai kuɓutar da ita daga halin da take ciki?.

******

Sadik tunda ya ga kiran wayar Saheer gabansa ya faÉ—i, ya kalli Saleem da suke zaune ya ce, "Saheer ne yake yi min waya, har bana so na É—auka wallahi."

Saleem ya ce, "É—auki, rashin É—aukar bashi da amfani."

"Na tabbatar sanarwar neman Islaha ya gani, shiyasa yake waya" ya faÉ—a yana É—aukar wayar ya saka a speaker.

Cikin fusata Saheer ya ce, "Kai Sadik me nake gani haka? Wacce Islaha ce ba a gani ba?."

Sadik ya yi shiru bai ce komai ba. Saheer ya ce, "ina magana ka yi min banza, wacce Islaha ce ba a gani ba?. Me ya kawo hoton Islaha duniya ana yaÉ—awa ana cewa ana nemanta?."

Sadik ya ce, "Saheer gaskiya ne abinda ka gani, tun daren jiya ba a ga Islaha ba, kuma...."

Cikin ɗaga murya da tashin hankali ya katse sa ya ce, "kuma me! Ka san da hakan shine ka yi min shiru baka faɗa min? Jiya me ka ce min, cewa ka yi bakwa tare ashe daman tun lokacin hakan ya faru ka ɓoye min?."

"Bana so na tayar maka da hankali ne shiyasa ban faÉ—a maka ba."

"Shirun da ka yi min yanzu kwantar min da hankali ya yi? Kamar Islaha ace tun jiya ba a ganta ba ka kasa faÉ—a min? Meye amfanina da bazan sani ba?."

"Ka yi haƙuri."

"Ina ta je? A ina aka sace ta?. Naga ana cewa ta fito daga asibiti, an duba cameras É—in da yake wajan?."

Sadik ya ce, "duk mun yi fa, amma babu wani labari wallahi. Iya fitowarta daga asibitin kawai mu ka gani."

Saheer ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Sadik amanar da na bar maka kenan, ta ya za ka bar Islaha ta fito ita kaÉ—ai cikin dare?."

"Ka san ina ta cikun cikun neman kuÉ—in aikin Baffa, lokacin da ta je asibitin bana nan

"Ya Subahanallahi! Yanzu ya ake ciki? Har yanzu babu wani wanda ya samu labarinta?."

"Babu."

Saheer ya É—an yi shiru, muryarsa tana cracking cikin damuwa ya ce, "Anya ba Æ´an kidnappers ne suka É—auke ta ba?."

Sadik jin rauni a muryar abokin nasa sai ya basa tausayi, ya tausasa murya ya ce, "bama fatan hakan in sha Allah. Kai ba ka da wani waje da ka ke tunanin zata iya zuwa?."

"Babu Sadik, duk wajen wanda zata je na tabbatar yanzu kuna tare. Ya Allah! Ina Islaha ta ke? Allah ka sa duk inda take tana cikin amininci."

"Amin."

"Sadik ana sanyi a nan ko?."

"Uhum ana yi."

"Islaha bata son sanyi da iska mai ƙarfi, kasan tana da asthma. Yanzu in tana wani wajen da ciwon ta zai tashi fa, waye zai kula da ita har ya bata taimako?" Ya faɗa cikin rauni.

Sadik ya ce, "in sha Allah tana waje na gari."

"An sanar da Æ´an sanda?."

"Duk mun yi Saheer."

"Shikenan, nima zuwa gobe zan taho nigeria."

"Amma ka faɗa min akwai abinda zai riƙe ka a can, ka faɗa min mahimmacin aikin ko?."

"Ta ya zan iya zama babu Islaha Sadik? Ta ya hankalina zai kwanta har na yi aiki ban san inda take ba?. Gwara na rasa komai na dawo mu nemo ta tare."

"Dawowar ka ba ita zata bayyana Islaha ba, ka zauna ka cigaba da neman kuɗin aikin Baffa, ka dinga ta ya mu da addu'a, itace abinda take so faga gare ka." Saheer bai ce komai ba ya kashe wayar cikin ƙunar rai.

Saleem ya girgiza kai yana jinjina ƙarfin son da Saheer yake yiwa Islaha ya ce, "gaskiya Saheer yana son Islaha, ban taɓa jin rauni a muryarsa haka ba."

Sadik ya murmusa ya ce, "A dai wannan zamanin, ni dai na jima ban ga masoyi kamar Saheer ba, itama kuma na jima ban ga mace mai riƙo da halicci da soyayya kamar ta ba."

Saleem ya ce, "Allah ya bayyana mana ita."

"Amin ya rabbi."

Kiran Saherr ne ya sake shigowa, Sadik ya É—auka Saheer ya ce, "kuna tare da Safeera ne?."

"Eh yanzu ta bar nan, muna tare har Saleem."

"yauwa, akwai wata ma'aikaciyarsu Ummi, kwanakin baya ta yiwa Islaha barazanar sai ta ga bayanta. Ka tambayi Safeera a gabanta aka yi, aje a kamata ta fito da Islaha. A jikina nake jin itace ta É—auke ta."

Sadik ya ce, "anya zata aikata haka?."

Cikin masifa ya ce, "in ba ita bace to waye? Ka je a kamata ta fito min da matata, in ba haka ba wallahi sai na saka an yi mata abinda bazata taɓa mantawa dashi ba. Ka tambayi Saleem da Safeera, su sun san case ɗin. Ranar da aka bata katin gayyatar Ray ranar abin ya faru."

Saleem ya ce, "Saheer tabbas an yi haka, ta shigo wajan Safeera tana faÉ—a mata, nima kuma ina wajan."

"Yauwa, kaima shaida ne. Don Allah aje a san abinda za a yi a kamata, ta faÉ—a mana inda ta kai Islaha, in ba haka ba mu tafi kotu."

Saleem ya ce, "in sha Allah za a yi hakan yanzu kuwa."

Saheer ya ce, "na gode" ya faÉ—a yana kashe wayar.

Sadik ya ce, "Haba Saleem, ya za ka biye masa?."

Saleem ya ce, "in abinka ya taɓa har a bakin allura nemansa za ka yi. Dole Ummi ta shigo ciki case ɗin nan saboda furucinta, dan haka ka tashi mu je kawai. Wannan babban case ne, kuma Ummi zata iya aikata komai dan ganin bayan Islaha."

Sadik ya ce,  "a kan me?."

"Saboda ta fita É—aukaka a wajan aiki mana. Tashi mu je."

Sadik ya miƙe ya ce, "Amma baza a karɓi shaidar Safeera ba, saboda ƙawar Islaha ce."

"Ba za a rasa cctv ta É—auka ba, mu je dai kawai."

Aka kira Safeera dan a tafi police station a kai report akan Ummi.

*******

Maman Orpanage tana zaune tana kallon abinda yake faruwa, tana ganin yadda duniya ta hargitse akan neman Islaha, ana ta reposting hotonta. Hotunanta sai yawo suke yi a duniya ana cigiyar inda take.

Ta yi murmushi tana kaÉ—a kai ta ce, "aiki ya yi kyau" ta faÉ—a tana É—agowa ta kalli wanda yake kallon ta.

Ya yi murmushi ya ce, "duk abinda ki ka ce shi nake yi ranki ya daÉ—e."

Ta yi dariya ta ce, "Aiki ya yi kyau sosai. Ka yi komai ta yadda babu wanda zai fahimta. Ka yi komai akan lokaci, a daidai lokacin da ake buƙatarsa. Zan ƙara maka naira dubu ɗari akan abinda mu ka yi za a baka."

Ya yi dariyar nasara da jin daÉ—i ya ce, "Godiya nake uwar É—akina, Allah ya ja da rai."

Ta kalle sa a nutse ta ce, "bana so a samu matsala, yadda aka yi wannan babu matsala ina so aikin gaba ma ya zama mara matsala. A É—auke wayar ta, a tabbatar an goge komai na kan wayar ta, ko da hotonta ne a goge ta yadda babu abinda zai dawo kai."

"Sannan kar a barta ta dawo nan kusa, ayi nisa da zamaninta kamar shekara É—aya zuwa biyu nan gaba. Ta cigaba da rayuwarta a nan, kar ku bari ta ga fuskar ku, ko ta ji wani abu daga gare ku. Tana da wayo, tana da kaifin basira, Æ´ar jarida ce, tsaf zata iya yin abin da baku yi tunani ba. Ku É—auke wayarta gabaÉ—aya, kar ku barta da waya, in ba haka ba da gidan da ku kan ku zata iya yiwa video."

Ya É—aga kai ya ce, "an gama ranki ya daÉ—e."

"Ba zancen an gama ba, Islaha ta wuce tunanaka, tana da wayo, tana da fikira tsaf zata yi abinda ba ku yi tunani ba."

"Ai ranki ya daɗe tunda ta shiga hannu zancen ya ƙare wallahi."

Ta girgiza kai ta ce, "haka nake so naji, haka nake so naji, dan na tabbatar da komai zai tafi yadda nake so. Zata iya tafiya, zaka ji alert."

"an gama ranki ya daÉ—e, amma in aka samu akasi ko ta yi taurin kai za ki ji wani labarin da ba wannan ba."

"Duk yadda ku ka yi, ku tabbatar kawai bata ganku ko ta ji sunana ba."

"An gama" ya faɗa yana buɗe ƙofa ya fita.

Ta sauke numfashi ta ce, "matsala ta ƙare!."

*****

Ƴar sanda mace, da maza biyu ne suka nufi ma'aikatar su Islaha, ana zuwa aka nemi ganin Ummi aka nuna musu offfice ɗinsu.

Aka yi knocking suka shiga akace ai tana office É—in Chairman. Suka wuce can, ya basu izinin shiga, suka shiga suka gaisa.

Officer ya ce, "Muna neman Ummi Mubarak ne."

Ummi ta bi su da kallon mamaki ta ce, "gani."
Chapter 6 · 0% Book details