Sashe 57
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwaggo ta ce, "ai yawon dangi ba nasu bane, duk inda zasu je barin nan ne."
"To zan bar su su kaÉ—ai a gidan nan ne Gwgago?."
"Aure zaka yi kawai, tunda kana da gida da halin riƙe mace ai, meye laifi dan ka yi?."
Baba ya ɗan miƙe zaune sosai ya ce, "Gwaggo aure fa?."
Gwaggo ta ce, "Auren fa, ko akwai haramci ne?."
"Babu gwaggo. Amma sai na ga auren ya yi wuri, har yaushe Maimuna ta tafi d zan yi aure? Sai mutane su ga kamar daman jira nake ta tafi na yi aure ai."
"To sai me? Duk abinda mutane zasu ce su ce mana, na ga dai kai ka san matsalar da ka ke ciki ko? Kuma maganinta zaka yi, in zaka biyewa maganar mutane ko baka yi ba sai an yi maganar."
"Haka ne. To ni Gwaggo yanzu in na É—auko batun aure wa zan aura?."
Gwaggo ta ce, "Ga matar nan Atika, meye laifinta?. Ka san halinta ta san naka, ga gidanta da take zaune ga gidanka. Meye aibu dan ka aure ta ka haɗa da ƴar ta ka riƙe?."
Baba ya zubawa Gwaggo ido har ya gama kafin ya murmusa ya ce, "Gwaggo Atika ƙawar Maimuna ce fa, ƙawar ta ce wacce zan kira ta da aminiya, ko nace nace ta zama ƴar uwa."
Gwaggo ta ja tsaki ta ce, "ko uwa ɗaya uba ɗaya suke ƙarewar ƙawance, in baban su ɗaya uwa ɗaya tunda babu Maimuna zaka iya auren ta, balle wani ƙawance, abu indai ba haramun bane shikenan. Yadda take kula da yaranka na tabbata zaka samu kwanciyar hankali a auren ta, mai son naka ai ba abin wasa bane ba."
Baba ya yi murmushi ya ce, "Gwaggo ni gaskiya babu batun aure a gabana balle har na yi tunanin zan iya auren Atika."
Gwaggo ta ce, "ya kamata ka kawo sa kuwa, dan bazan zuba ido kana barin ƴan mata su kaɗai a gida ba. In aka fahimci baka nan hauro musu fa?. In kuwa da babba idanunsa ma makami ne babba."
Baba ya girgiza kai dan ya san gaskiya ta faÉ—a, ya ce, "zan san abinda zan yi in sha Allah, komai zai yi daidai Gwaggo."
"Daidaita komai kawai ka auri Atika, ai ba aibu a lamarin."
"Ikon Allah! Gwaggo ita an faÉ—a miki zata iya aure na ne hala?."
"Ka gwada ka gani, zan iya rantse maka akan zata amince. An ce tafi shekara sha biyar tana zawarci, wallahi kana yi mata tayi zata amsa. Ai kai ba irin wanda za a ƙi bane, ta san yanayin yadda ka ke tsayawa akan iyalanka ai."
Ya girgiza kai ya ce, "Shikenan gwaggo, zan yi tunani zan kuma yi addu'a."
Gwaggo ta ce, "ko kai fa, haka zaka ce daman. Allah ya sanya mana alkhairi" ta faɗa tana miƙewa shima ya miƙe.
Sai da ya raka ta har waje É—anta ya zo ya É—auke ta a mota ta tafi.
Ya bi motar da kallo yana murmushi, yana tunanin maganar Gwaggo yana ganin kamar ba abu ne da zai yu ba.
*JEEDAH..*
Slowly take tafiya kamar bata so, hannunta riƙe da ledar Nahdi pharmacy ta shiga gidan Maleek ta wuce ɗakin da yake nata ta cire hijjab ɗin jikinta.
Ta buÉ—e ledar ta ciro pad da panadol da pack É—in facemask da ta siya. Ta sha panadol É—in ta zauna a gefen gado ta dafe kai dan yanayin ta babu daÉ—i as usuall.
Kwana biyu Maleek ya yi tafiya, aikin ya ɗan ragu sai gidan Rehaan da take shiga, kuma har lokacin bata taɓa ganin mai gidan ba.
Yanzu ma can take niyar zuwa amma bata jin daɗin jikinta, a wannan yanayin ba kasafai ta cika son zama cikin jama'a ba, dan yanayinta ko yaushe zai iya canjawa ta fara yiwa mutane faɗa. Gashi tana ƙasar da ba nigeria ba, kar ta je ta aikata abinda zai zamar mata matsala.
Tana jin kanta cikin kaɗaici, sai ta ji tana buƙatar rarrashi ba tare da an yi mata komai ba.
Ta jima a zaune a haka, kafin ta miƙe ta shiga banɗaki ta saka pad ɗin ta fito tana jan numfashi daƙyar. Ta ji daɗin maganin da ta sha, amma duk da haka tana jin ciwo sosai.
Hijjab ɗin ta saka aka turo ƙofar aka shigo, Sunaira ta gani suka yi maganar bebayen da suka saba. Islaha ta ce mata zata shiga gidan da take zuwa, daga nan ta jawo ƙafa slowly tana takawa a hankali zuwa gidan.
Magriba ta yi lokacin, duhu ya yi amma ko ina haske kamar dare bai yi ba. Tana shiga motar cleaners tana fita, ta bisu da kallo ta ce, "ko meyesa bazai É—auko chef daga wani wajan ba oho, ba dan kuÉ—i nake nema ba da me zai kai ni aiki kamar wata baiwa?."
Sai da ta yi typing lock code ɗin ƙofar sannan ta tsaya tana jira ƙofar ta yi ƙara sannan ta buɗe, ta yi tsaki ta ce, "Aikin banza, gida kamar gidan tuba duk an bi an rufe sa da lambobi."
Sautin lock É—in ta ji alamun ta buÉ—e, ta shiga falon yana nan yadda yake kamar kullum babu kowa.
Haka kawai ta ji falon yana bata haushi, ta yi tsaki tana hararar falon ta ce, "aikin banza, kullum baya nan, ni ga Æ´ar aiki sai dai na yi masa aiki na ajjiye, yana can yana hutawa ina gaban stove zafi yana tafasa ni."
Islaha ta taka a hankali zuwa inda kitchen É—in yake. Ta kunna hasken ta ga komai yana inda yake ko cup É—in da sha tea babu.
Ta kama ƙugu ta ce, "wai yana cin abinda nake dafawa ma kuwa ko wahalar banza nake yi?." Sai kuma ta sake yin tsaki ta ƙarasa ta haɗa komai na tea ta ɗora akan stove ta kunna.
Ta rasa me zata dafa ranar, duk ranta a ɓace yake bata san me ya kamata ta yi ba. Loades fries nw ya zo ranta, hakan ya saka ta ɗauko irish potatoes irin na ƙasar manya manya, babu wahalar peeling sannan ga auki. Guda uku kacal ta gyara ta yanka yadda ake soya dankalin turawa.
A lokacin ta ji marar ta tana ɗaurewa, idanunta ya ciko da hawaye, ta fara kuka mai sauti ita kaɗai tana yi tana share hawayenta. A haka ta soya ta ajjiye, ta buɗe fridge ta ɗauko chicken breast ta yanka ƙananu ta saka spices ta zuba a fan ta ɗora akan stove ɗin.
Ta koma gefe tana jan numfashi tana jin yadda take flowing a hankali. A hankali ta ƙarasa ta kwashe kazar, ta buɗe fridge ɗin ta ɗauko mayonnaise ta zuba a ƙaramin bowl, ta zuba ketchup a kai, ta ɗauki lemon ta zuba kaɗan, ta saka chili powder da maggi ta yi mixing a haɗe.
Casrool ta ɗauka mara girma sososai, ta zuba dankalin a ƙasa sannan ta kawo wannan kaza ta zuba a sama, ta zuba cheese, sannan ta zuba cream ɗin da ta haɗa ta sake zuba cheese. Ta ɗauka ta saka a cikin oven, mintina kaɗan ta cire ta kalla ta ga loaded fries ɗin ya yi kyau sosai.
Dafa kitchen island ta yi tana jan numfashi mai ƙarfi, bata daina kuka ba har lokacin, dan ita kaɗai ta san irin abinda yake ji a jikinta. Buɗe murya ta yi tana kuka mai matuƙar sauti dan ta san babu kowa a gidan, tana kiran sunan Hamma da Safeera.
A lokacin Rehaan ya shigo gidan, yana buÉ—e falon ya ji sautin kuka har tsakiyar kansa. Gabansa ya faÉ—i lokaci É—aya, ya fara tunanin waye a gidan yake kuka haka?. A hankali ya ajjiye wayarsa akan table ya shiga ciki a hankali ya nufar inda yake jin kukan.
A tsaye ya ganta ta juya baya ta riƙe kitchen island ƙam jikinta yana rawa. Kallo ɗaya ya yi mata ya gane itace housemaid ɗin, uniform ɗin jikinta sun tabbatar masa da wacece.
"Are you Okay?."
Rehaan ya furta a tausashe yana kallonta, dan daga ganin yanayinta bata da lafiya.
Islaha ta firgita jin magana a bayanta, kuma ta san babu kowa a gidan sai ita kaɗai. Firgtar da ta yi, sai tsantsin tiles da ɓawon dankali guda biyu da suke a ƙasa, suka ja ta da ƙarfi, ta yi gaba zata faɗi da fuskar ta, Rehaan ya yi hanzarin ƙarasawa ciki, ya taro ta ta faɗo ƙirjinsa gabaɗayanta......
An haÉ—u faâ¤ï¸â€ðŸ”¥
Nana HaleemaâœðŸ»
[7/6, 9:35 AM] KRBBK: RDB2P39
Nana haleema.
_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments É—in ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link É—in ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode É—in baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S
……
Kanta yana kwance a kirjinsa, jikinta ya saki gabaɗaya, sai ƙhamshin turarensa da yake shiga hancinta yana ratsa kanta da zuciyar ta a hankali.
Rehaan sai da ya yi da gaske ya rike ta, yadda ta faɗo jikinsa gabaɗaya sai da ya kusa faɗuwa, dan bai ɗauka jikinta zai saki haka ba, sai ya ji ta sakar masa jiki tana kwantar da kanta a ƙirjinsa.
Hannunsa ɗaya yana waist dinta, ya zagaya dashi har cikinta ya rike ta yana kallon gashin kanta da yake baƙi sosai, ga kitson da ta yiwa kanta, irin na fulanin daji guda biyu kacal.
Ya ɗago ta yana kallon fuskarta, amma idanunta a rufe yake sai hawaye da yake sauka a hankali, ya ɗan zubawa fuskar ta ido na wani lokaci, sai kuma ya ɗauke kansa daga kallonta. Daga yanayin uniform ɗin jikinta ya san itace housemaid ɗin da Ubaid yace masa ya turo, ya riƙe fuskarta yana ɗan jijigawa.
Camly ya ce, "can you hear me? What's wrong with you?."
Islsha tana jinsa amma tana buƙatar kwanciya a halin da take ciki, tana jin muryarsa da ƙhamshinsa har cikin zuciyarta, amma kuma ta kasa buɗe ido ta ga waye.