← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 133

Sashe 43

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi shiru bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, "You look so beautiful. Why do you look even better than him?."

Islaha nan ma ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata ce komai ba, wannan iyayin nasa ya fara isar ta wallahi. Maleek ya É—an É—aga kai ya ce, "well, you looks so beautiful. I like your skin type."

Islaha a gajiye take hakan ya saka ta ce, "thank you."

Ya nuna mata hanya ya ce, "you can go."

Kamar an saka ta a aljanna haka taji, ta yi saurin barin wajan ta koma É—akin da aka ajjiye ta. Uniform É—in ta fincike ta canja kaya ta kwanta tana ji kamar ana sassara jikinta saboda gajiya.

Labiba suna shiga É—akin da aka ajjiye ta taga tangamemen É—aki mai kyau da tsari kamar ba na mai aiki ba, ta buÉ—e ido tana juyi a É—akin ta ce, "sabuwar duniya."

Matar da take bayanta ta yi darita ta ce, "ki ka shigo cikinta."

Da hanzari ta juyo tana kallonta jin tana hausa, Labiba da mamaki ta ce, "Daman kina jin hausa har haka?."

Tayi dariya ta ce, "Sunan Aisha, kefa?."

"Labiba sunana. Amma na yi mamaki da na ji kina hausa a ƙasar nan."

"Ni Æ´ar Niger ce, kuma na yi zaman nigeria."

"Kai amma na ji daÉ—in haÉ—uwa dake a gidan nan sosai. Naji daÉ—i dana samu wacce take jin hausa."

Aisha ta yi murmushi ta ce, "nima na samu ƙawa. Ki shiga kiyi wanka ki fito ki shirya, kin san gidaje irin wannan ba a zama haka. Sai kin jure, zaki sha wahalar aiki, dan wallahi ba a hutawa."

Labiba ta ce, "daman shi ya kawo ni ai, kuÉ—i nazo nema, dan haka ko meye bazai dame ni ba."

Aisha ta yi dariya ta ce, "da alama kan ki a waye yake Labiba, da wuri zaki tara kuÉ—i a gidan nan. Ki shiga kiyi wankan zan jira ki."

Aisha ta fasawa Labiba kai jin ta ce a waye take, cikin iyayi ta ƙarasa banɗaki ana yanga ita lallai wayayayyi.

Aisha ta bita da kallo tana murmushi, ta girgiza kai ta ce, "Sannu da zuwa gidan Ubaid, gidan kuɗi kuma gidan jin daɗi, gidan nasara kuma gidan rashinta, gidan fantamawa gidan morewa." Ta yi yar ƙaramar dariya ta juya ta fita ta bar mata ɗakin.

Labiba bata jima ba ta fito, taga an ajjiye nata uniform irin na jikin Aisha, ta É—auka ta saka tana kallon kanta dan ita kanta ta san ta yi kyau.

A lokacin Aisha ta dawo ta bita da kallo tana murmusji ta ce, "kim yi kyau sosai. Kin karanta tsarin gidan nan dai ko?."

Labiba ta ce, "ni saka hannu kawai na yi, ban wani duba soaai ba."

"Lallai kam sannun ki. To babu sata, babu gulma, babu yawo waje barkatai. In ki ka saɓa kaɗan daga cikin rules ɗin gidan nan za a iya kama ki. In mun fita zan baki takardar ki sake dubawa dan ki kiyaye dakyau. Mu je na nuna miki inda ya kamata, sannan sai kizo ki ɗan huta na ɗan lokaci."

Tare suka fito daga ɗakin tana nuna mata duk inda ya kamata ta sani, zuciyar Labina fari ƙal ganin gida irin wanda take mafarki, gida kamar ba a duniya ba, ga abokiyar aiki ƴar nigeria.

Ta kusa da Ubaid da yake zaune yana danna laptop suka zo wucewa, ya É—aga ido ya kalli Labiba ya ganta ta yi kyau a cikin shigar da ta yi, ta yi kyau cikin kayan kamar ka sace ta ka gudu.

Da hannu ya yi musu alamun da suzo, suka nutsu suka ƙarasiɓo wajen suka tsaya cikin girmamawa..

Suna zuwa ya bi Labiba da shegen kallon up and down ya ce, "ya sunan ki?."

Labiba ta ce, "Labiba."

Ya É—an yi jim ya ce, "Habiba?."

Ta girgiza kai ta ce, "Labiba."

Ya É—an É—aga kai ya ce, "from nigeri, right?." Ta É—aga masa kai alamun eh tana kallonsa.

Da hannu ya yi mata alamun ta tafi, ta miƙe tana tafiya ya bita da kallo yana shafa kansa, ya girgiza kai don tayi daidai da tsarinsa sosai.

••••••

Tunda ya dawo daga wajan aiki yana tsaye ransa a ɓace, ya tsani ya dawo daga wajan aiki kuma ya tsaya neman wani abun da zai sha da kansa, yafi son da ya dawo a kawo masa komai baya son ɓata lokaci.

Ya sauke numfashi, dan cikin kwana biyu cleaners ya ke É—aukowa su zo su gyara masa gidan, dan shi baya so a haÉ—a shara da girki, ya fi son chef daban cleaners daban.

Ya ja tsaki ya É—auki waya ya kira Jazy, yana É—auka ya ce, "Jazy meyasa wai ka sallami housemaids É—in gidan nan? Kana neman haukata ni, ina zan saka raina ne?."

Jin Rehaam yana faÉ—a abinda ba sabon sa ba sai ya bawa Jazy mamaki ya ce, "me ya faru?."

"Na dawo daga aiki, ina buƙatar sha tea amma babu kowa a gidan nan. Waye zai bani?."

"Ka yi order ko ka fita kasha"

"baka da hankali Jafar, ki fi kowa sanin ina son abu bana son ɓata lokaci ko?."

Jafar ya ce, "yanzu ya zan yi maka? Ni ka ke so na zama maid nazo ina yi maka aiki, ko kuma daga nan zan turo maka mai aikin gida?. Ina cleaners É—in da suke zuwa yi maka aikin gidan?."

"Cleaner chef ne?."

Jazy ya É—an yi shiru kafin ya ce, "Okay ka yiwa Maleek ko Ubaid magana mana, na san akwai housemaids a gidansu sosai, sai a baka É—aya."

Ya É—an girgiza kai ya ce, "mun yi magana da Maleek, but bai ce min komai ba har yanzu. Kuma ni permanent nake so, bana son sharing chef, bana so na dawo ina son wani abun ace sai na jira."

"Mr Rehaan samu housemaids ko chef a Jeddah bazai yi maka wahala ba, ka bincika zaka samu. Gidan Maleek ko Ubaid mata ne, kai kuma ka fi son maza."

"Ina son matan, indai za a samu."

"Lallai ka ji uwar bari, sai ka san yadda zaka yi."

Ray ya ja tsaki ya kashe wayar cike da takaicin Jazy.

Ya dafe kai, shi babu abinda ya iya dafawa balle ya ce zai je dafa, tea kwai ya iya shima a dafa ruwa zafi a saka lipton da sugar shine abinda ya iya. Komai yi masa ake yi, ta ya zai juri ko yaushe in ya dawo shi zai dafa abinda zai ci ko sai ya tsaya a hanya, ko sai ya jira rider ya kawo masa?."

A Englaand suna da housemaid ɗin da yake musu girki ko yaushe, cleaner kuma kullum ana zuwa sau uku ko huɗu ana gyara inda suka ɓata shiyasa bai iya yin komai ba.

Daman Jazy ne mai ƙoƙarin girki, da yana nan da bashi da matsalar abinci ko matsalar abin sha ko wani abun.

Ya É—an yi tsaki yana neman number Maleek, dan ba kasafai ya cika sakewa da Ubaid ba, rawar kan Ubaid ya yi yawa, ya fi son shiri da Maleek dan yana da nutsuwa akan Ubaid.

Ya kira number Maleek yana fatan Allah ya sa a samu housemaid ɗin da za a tura masa a take su zo su fara yi masa aiki, bai damu da mace ko namiji ba, ko ma waye yana maraba dasu. Tunda nema yake bashi da zaɓi, amma da a gida ne baya haɗa hanya da housemaid mata, ya fi son maza su yi masa komai.

Kuna Maleek zai ba da Islaha kuwa?
Ina labarin Hajiya Umma?
Labiba fa?

Mu je zuwa🤭💃🏻
[7/1, 1:08 PM] KRBBK: RD2P30
Nana Haleema.

*MADINA*
*AL KHALIDIYYAH AREA.*

Umma tunda aka gama gabatar da ita ga mutanen gidan take a gantale a falon gidan, tana kallon falon sanyin a.c yana ratsa ƙasusuwanta. Dan sanyin ba ɗan kaɗan bane, sanyi ne mai yawa wanda ya fi ƙarfinta.

Falon yana da girma da manyan kujeru masu girma, ga wani ƙaton dining table mai guda ashirin, alamun iyalai gidan suna da yawa ba na yara ba.

Ga wasu ƙofofi a falon wanda bata san na meye ba, ga ƙatuwar tv, komai na falon ya yi yadda ya kamata.

Umma dai tana zaune ga yunwa ga gajiya, sanyin duk ya dame ta kuma ba a bata wajan zama ba balle ta shiga ta zauna.

Wata balarabiyar budurwa ce ta fito daga ɗaki, ta bi Umma da kallo kafin ta ƙwalawa Mamanta kira cikin harshensu ta ce, "Mama Wannan baƙuwar a ina zata zauna?."

Daga ciki ta ji muryar babar cikin harshen su uwar ta ce, "ki raka ta ɗakin baƙi ta ajjiye kayanta."

Ta kalli Mama ta ce, "Mu je."

Umma bata fahimta ba, ita dai taga tana kallon ta kuma tana yi mata magana, amma bata san me take faɗa ba. Yarinyar ta yiwa Umma nuni, hakan ya saka ta miƙe ta ta bi bayanta tana sake kallon ko ina na falon.

ÆŠaki ne madaidaici da komai a cikin sa, Umma ta shiga tana ajjiye kayanta gana kallon É—akin cikin wani irin yanayi mara daÉ—i.

Umma ta zauna a gefen gado tana kallon ɗakin, sai kuma ta miƙe tana kallon ƙofar tana tunanin banɗaki ne, ta buɗe tana kallon banɗakin kafin ta shiga ta yi wanka.

Tana fitowa taga yarinyar nan a tsaye a É—akin tana kallon É—akin. Umma tana fitowa ta bita da kallo kafin ta yi mata alama da tazo da hannunta.

Umma ta canja kaya a gajiye, ta yi tunanin za a barta ta huta amma sai ta ga akasin haka. Ta fito tana takawa a hankali dan ta gaji sosai ma kuwa.

Tana fitowa ta ga mutane harr a falon manya da yara, kowa ya zuba mata ido yana ƙare mata kallo kamar sun ga wata mujiya.

Iyayen gidan tana kallonsu ta san sune iyaye, uwa da uban suna zaune a waje É—aya, sai sauran yaran duk mata ne da namiji É—aya, suna zaune sun yi kaca-kaca da wajan suna ciye ciye kamar ba manya ba.

Umma tana fitowa matar ta kalle ta tayi mata nuni da ta kwashe kayan wajan. Umma a sanyaye ta duƙa ta fara kwashe kayan, aka nuna mata kitchen ta kai ta ajjiye.
Chapter 43 · 0% Book details