Sashe 1
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
RAGAYAR DUTSE BOOK 2
Arewapen@nanahaleema11
#The Surgery
#The working abroad
#The kidnapping
#The marriage.
A hankali yake fitowa daga bedroom ɗin Mamy zuwa parlour, jikinsa a sanyaye yake sosai, gabaɗaya baya son zaman gidansu bai san meyasa ba. In ya dawo haka yake ƙarewa da sanyin jiki, bashi da kuzari ko kaɗan.
Mamy da take zaune ta ce, "Rehaan ina zuwa?."
Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Zan je in yi wanka, ina so na je na gaida Mummy."
Mamy ta É—aga kai jin ya ce Mummy ta san babar su Jafar yake nufi ta ce, "Okay, amma kar ka tafi kai kaÉ—ai." Ya É—aga kai bai ce komai ba ya fita daga apartment É—in zuwa na sa.
Yana fitowa suka haɗa ido da Mama ta rako baƙuwa daga ɓangarenta, ya ɗan ɗauke kansa yana tafiya a hankali ya wuce zuwa ɓangarensa.
Ƙawar Mama ta bisa da kallo har ɓace ta ce, "kut! Haka ki ke fama? Ya fi ƙarfin ya gaishe ki kenan ko? Balle ni na saka ran zai ce min ina yini?."
Mama ta girgiza kai ta ce, "shegen yaro ne, magana ma sai ya ga dama yake yi min balle gaisuwa. Kaf gidan nan babu tantiri kamarsa, sai ya yi sati biyu a ƙasar nan sai ya ga dama zai ce miki ina yini."
"Kuma ki ka zauna, ki ka zuba masa ido ya raina ki har haka?. Ke ce fa uwar gida, ke ce babba a gidan nan fa."
"Kema kin san bazan zauna ba, babu abinda ban yi ba amma wani lokacin kamar aikin ba ya ci, ina kan yi É—in ma zan ce."
"Kar ki yi sanya, ki maganin sa ta ƙarfi da yaji, kar ki bari nan gaba ya sake kallon ki ya ɗauke kai, raini ne mai girma. Da a gaban ƙawayen mu ya yi miki haka ai ya cuce mu, ya gama zubar miki da ajin ki wallahi."
"Ki dakusar da ɗaukakar sa ta ƙarfi, a bazama wajen malamai su taimaka mana ya yi ƙasa. Bayan an dakushe shi, ki ɓata masa suna ta yadda bazai taɓa goguwa ba. In ba haka ba wallahi muna ji muna gani komai zai koma hannun ƴa india."
"Bari kawai. Bazan taɓa ƙyale wani ya fi ƴaƴana ba, kema kin san bazan bar hakan ta kasance ba. Ban san ya aka yi na yi baccin da Rehaan ya kai wannan matakin ba, ban san ya aka yi hakan ta faru ba. Amma yanzu na farka, hana idona bacci nake yi na je neman taimako. duk dan saboda naga bayan ɗaukakar nan ta sa. Kuma na san zan gani, dan zan iya yin komai akan hakan."
"Shegen yaro, ni kaina na tsane sa balle ke. Ki duba fa, ya wani kalle mu sheƙeƙe ya wuce."
A lokacin Salman ne ya zo wucewa, ya ƙwacewa yara alewa, ya yi dagaje-dagaje da bakinsa kamar ba babba ba. Gashi kallon farko zaka yi masa ka san ya girma, yanayinsa da halittar da Allah ya basa ka san ta manya ce sosai. Ga gashin da yake fuskarsa, gashi fari tass kyakykawaZ
Ya kalli Mama yana nuna mata alewar ya ce, "bazan baki ba."
Ta ɗan taɓe baki ta ce, "jeka ka shanye kayan ka, na gode." Ya wuce ta da gudu ya shiga wajen Umma.
Mama ta kalli ƙawarta suka ƙyalƙyale da dariya har suna tafawa. Ta ce, "wai wannan ba Salman bane, ɗan kishiyarki?."
Mama ta ce, "shine mana."
"Haka haukan nasa ya sake yin gaba? Kamar ya girmi Sameer ko?."
"Ya girmi Baba ba ma Sameer ba, Sameer fa daga shi sai Rehaan."
Matar ta É—an yi dariya ta ce, "Ikon Allah, gashi nan ya zama kamar jikanki."
"Haka ma da kyaun gani fa, wani lokacin abin tausayi."
"Haka nake so na ga Rehaan, yana yawo yara suna binsa ana kiran mahaukaci."
Mama ta yi dariya ta ce, "ke dai sai mun yi waya, akwai labari mai zafi" ta faÉ—a tana raka ta mota ta shiga ta tafi.
   Rehaan yana kallon yadda Yayansa ya wuce a guje jikokin gidan suna binsa a guje ana kokawar ƙwatar alawa daga hannunsa.
Ya sauke numfashi ya shiga ɓangarensa yana jin zuciyarsa babu daɗi akan hakan. Har ya shiga sai kuma ya dawo da baya ya shiga ɓangaren mahaifinsa da sallama. Umma ta amsa daga falon, ya ƙarasa tura ƙofar suka haɗa ido da ita.
Rehaan ya ce, "Abba yana nan?."
A daƙile ta ce, "yana wajan Daada."
Bai ce ƙala ba ya juya ya nufi wajan Daada dan yana son ayi maganar Salman.
A zaune ya samu Abba shida Baffa ƙaninsa a kusa da Daada, ya yi sallama suka amsa ya ƙarasa ya zauna.
Ya kalli ƙanin Abba ya ce, "Baffa ina yini."
Da murmushi ya ce, "lafiya lau Rehaan, ya jiki?."
"Na ji sauƙi."
"Allah ya ƙara lafiya."
"Amin."
Ya kalli Abba ya ce, "Abba wajan ka naje baka nan."
Abba ya ce, "to lafiya?."
Ya É—an kalli Daada suka haÉ—a ido, ta harare sa ta ce, "ko na baka wuri ne?."
Ya É—auke kai daga kallon ta ya ce, "daman akan maganar Hamma Salman ne, naga yanayin sa ya sake lalacewa Abba, ba kamar wancen zuwan da na yi na gansa ba. Ban ji daÉ—in yadda na gan shi yanzu ba, shiyasa na zo dan na yi maka magana a kai. Akwai likitan da na sani zai yi masa aiki, in sha Allah za a dace akan hakan."
Abba ya sauke nunfashi ya ce, "Rehaan ba yau aka saba yiwa Salman magani ba."
Rehaan ya ce, "duk da haka Abba, ba a san inda za a dace ba. Kuma ai ba a taɓa yi masa aiki ba, in aka gwada sai a dace."
Baffa ya ce, "gaskiya ne. Ba a san inda za a dace ba, magani lalube ne a cikin duhu."
Daada ta ce, "Ni kaina lamarin yaron nan yana bani tausayi matuƙa, ya koma kamar yaro ɗan shekara biyar. Ya girmi Baba, ya girmi Sameer ya girmi Muhammad amma ya zama kamar jikokin gida. Abin akwai taɓa zuciya."
Rehaan ya ce, "Daman zan je Jedda, zan saka ayi masa visa sai mu tafi dashi a duba sa."
A lokacin Salman ya shigo a guje yara suna binsa zasu ƙwace chocolate ɗin hannunsa.
Banisha ta shigo ta ce, "Hamma ka bani chocolate É—ina."
Ya noƙe kafaɗa ya ce, "bazan baki ba, ai Abba ne ya siya min."
Ta hararesa ta ce, "ba ka shanye ta ka ba, kawai ina tsaye ya ƙwace ta daga hannuna. Gaskiya ka bani." Ganin zata ƙwace sai ya gudu ta bisa zata ƙwace.
Salman ya dawo kusa da Rehaan ya ce, "kaga Banisha zata ƙwace min ko?."
Rehaan rauni ya mamaye masa zuciya, ya É—an sauke nunfashi ya ce, "Kiddo meye haka?."
Cikin shagwaɓa ta ce, "kawai na fito daga wajen Mamy ya ƙwace min. Ni ai bana kula shi, shine kawai ya ƙwace min."
"ki je É—akina ki É—auki wata."
Banisha ta harare sa, shi kuma ya yi mata gwalo yana riƙe hannun Rehaan.
Salman ya miƙawa alawar bakin Reahaan ya ce, "ka sha."
Rehaan ya girgiza kai ya ce, "na gode Hamma, bana sha."
Ya sake miƙa masa ya ce, "kai kaɗai na bawa, in ba kai ba ko Daada bazan bata ba. Ka sha da daɗi" ya faɗa yana ɗora masa masa alawar a bakinsa. Rehaan ya riƙe hannunsa alamun baya so.
Salman kamar zai yi kuka ya ce, "baza ka sha ba ko? Kaima ka ce ni ƙazami ne, kai ne kaɗai mai sona kaima baza ka sha ba?."
Rehaan ya buɗe baki a hankali Salman ya saka masa alawar yana dariya. Shima Rehaan murmushi ya yi yana kallonsa cikin tausayi da ƙaunarsa.
Ya kalli mutanen da suke kallonsu, kowa tausayin Salman ya bayyana akan fuskarsa, dan Daada kuka take yi, shi kansa Rehaan É—in ji yake zuciyarsa ta karye kamar ya yi kuka.
Abba ya sauke numfashi ya kalli Rehaan da yake kallonsa ya ce, "Rehaan yanzu ya ka ke so ayi?."
"Kawai a bari mu tafi dashi Jedda, tunda ina can zan dinga kula dashi da kaina. In kuma Umma zata je sai ta je mu zauna tare dashi. In sha Allah zai dawo lafiya."
A lokacin Umma ta shigo tana faÉ—in, "Daada sannun ku. Kai Salman kai nake nema, taso muje ka sha magani."
Ya noƙe kafaɗa yana kwanciya a kafaɗar Rehaan alamun bazai je ba. Rehaan ya kalle sa ganin fuskarsa ta cika da gashi alamun ba a gyara masa ba, ya ce, "zamu je a gyara gashinka" ya faɗa yana shafa fuskarsa a hankali.
Umma ta harari Rehaan ta ce, "ai da ba kai ka ke kai sa a yi masa ba ko? Uban ƴan iyayi. Kana can wata ƙasar kana rayuwa, sai yau zaka ce za a je a gyara masa gashi, haka aka ce maka ni bana kai shi?."
A lokacin Mama ta shigo da sallama, ta samu labarin Umma dasu Rehaan suna ɓangaren Daada, hakan ya saka ta shigo dan bata san me zai faru a ciki ba.
Abba ya ce, "ku ƙaraso ku zauna daman shawara ake nema, Rehaan ne yake da magana akan Salman."
Rehaan dai kallon Salman yake da ya lalata kayansa da alawa, shi kansa ya ɓata masa kayan jikinsa. Sai kuma ya fara ja masa gashi, Rehaan duk da yana jin zafi, bai ce komai ba kuma bai hanasa ba.
Abba ya ce, "Daman Rehaan ne yake so zai tafi da Salman Jedda a yi masa magani."
Umma ta haÉ—e rai ta ce, "wanne irin magani? Bashi da lafiya ne?."
Daada ta kalle ta cike da mamakita ce, "ke sai an ce miki bashi da lafiya ma?."
"To na ga a haka yake rayuwa ko?."
"asibiti ƙwaƙwalwa zai kai sa."
Umma ta girgiza kai ta ce, "A'a, wallahi É—ana ba mahaukaci bane. Babu asibitin mahaukatan da za a kaisa."
Abba ya ce, "asibitin ƙwaƙwalwa aka ce, ba mahaukaci aka ce masa ba."
Umma ta ce, "a duk ɗaya ne, duk wanda aka ɗauka aka ce zai ga likitan ƙwaƙwalwa kasan mahaukaci ake ɗaukarsa. Ɗana ba mahaukaci bane, babu asibitin da zai je wallahi. Ban nema ba, na gode da niya, Allah ya ba da lada, amma bazai je ba."