← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 133

Sashe 128

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nan ya samu Mama a zaune suna tattaunawa akan batun siyar da kadarorin da aka saka a kasuwa. Kamar dare bai yi ba, dukkansu idanunsu biyu ana lissafa abubuwan da ya kamata a siyar.

Bayan sun gaisa Baffa ya ce, "Sadik tun É—azu nake yi maka waya."

Sadik ya ce, "ina can wajan Æ´an sanda ana maganar yadda za a fito da Saheer ba tare da ko sisi ba, kuma da alamun nasara in sha Allah."

Mama ta ce, "Sadik ni ban yarda da wanann maganar ba, kawai a samu kuÉ—in nan a basu."

Baffa ya kalle ta ya ce, "kina dasu ne?."

Sai ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya kalle sa ya ce, "Kana ganin hakan zai yu?."

Sadik ya ce, "In Allah ya amince, a cigaba da addu'a kawai. In sha Allah Saheer zai dawo gida ba tare da ko sisi ba."

Baffa ya yi masa addu'a sannan Sadik ya tafi, da a gajiye yake sosai, yana so ya je ya huta.

A take Baffa ya kira Islaha ya bata labari mai daÉ—i, bata nuna masa ta sani ba, sai ta nuna ta ji daÉ—in maganar yadda zai yi tunanin da gaske take, a haka kowa ya kwanta, duk mutanen gidan babu wanda yake cikin walwala da jin daÉ—i.

Washe gari
Friday.

Jazy yana ta shirin É—aurin aure, ya saka lafiyayyar luxury shadda fara mai kyau da É—aukar ido, yana tsaye a gaban mirror yana É—aura agogon hannunsa, sannan ya É—auki hula ya saka a kansa yana kallon kansa. Ya yi murmushi dan shi kansa ya san ya yi kyau, ya kalli Ray da tunda ya saka kayan ya koma ya zauna ko magana bai sake yi ba.

Jazy ya kalli agogo sannan ya kalle sa ya ce, "Ray lokaci yana tafiya, tun É—azu ka zauna ba ka tashi ka gama shiryawa ba."

Rehaan ya kalli Jazy kamar mai tunani, suka haɗa ido ya ga Jazy ɗin ya yi kyau sosai, sai miƙe tsaye yana ajjiye wayar hannunsa.

A tsakiyar kansa ya naÉ—e gashinsa, ya É—auki hula ya saka ya rufe gashin gabaÉ—aya babu ta inda ya fito, ya saka agogo yana kallon babbar rigar da Jazy ya saka aka É—inka masa, ya É—auka ya saka yana kallon kansa.

Ray ya murmusa dan ba sai ance ya yi kyau ba, shi kansa ya san ya yi kyau, bazai iya tuna rabon da ya saka babbar riga a rayuwarsa ba. Ko bikinsu Sameer bai saka ba, ya saka dai manyan kaya amma bai saka babbar riga ba. Kayansu iri ɗaya ne sak da Jazy, hatta takalmin ƙafarsu iri ɗaya ne, sai banbancin hula da agogo da lins.

Jazy ya ce, "Ma sha Allah! Angon Islaha, ka yi kyau sosai."

Rehaan ya haÉ—e rai, murmushin da yake yi ya gushe daga kan fuskarsa, ya É—an harari Jazy amma bai ce komai ba.

Jazy ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Wallahi kyaunka na yau na daban ne dana kullum, ka yi kyau sosai ba tsokanar ka na ke yi ba. Dole na yi mana selfie, na yi posting ko zan samu likes da comments, ka san yin hoto da irinka sai mai sa'a" ya faɗa yana ɗauko wayarsa.

Ray ya matsa daga wajean alamun bazai yi hoton ba, Jazy ya riƙo shi ya ce, "Dallah ka kalla, tarihi ne fa."

Bai ƙi ba ya kalli camerar Jazy ya ce, "ka yi dariya mana, Yayan matata."

Sai ya yi murmushi jin sunan da ya kira shi dashi, Jazy ya É—auke su hoton duk sun yi murmushi kuma ya yi kyau sosai, kowa annuri da kyaunsa ya bayyana a cikin hoton.

Rehaan camly ya ce, "ba ka da tarbiyya, Yayan matar ta ka ka raina haka."

Jazy ya yi dariya ya ce, "my billionaire."

A lokacin wayar Jazy ta fara ringing, da ya duba sai ya ga sunan Abba ne hakan ya saka shi ya É—auka.

Yana sakawa a kunne Abba ya ce, "Jaafar kuna tare da Rehaan ne?."

Jazy ya ce, "Eh Abba."

"Kuna cikin gida?."

"A'a muna guest house."

"Ku yi hanzari ku zo nan kafin ku je masallaci, kuna zuwa gidan ku shigo main palour ba sai kun shiga ciki ba. Ku yi sauri." Jazy ya amsa ya kashe wayar.

Jazy ya ce, "mu je in ji Abba, ya ce mu je yanzun nan." Ray bai ce komai ba ya É—auki wayarsa suka fito daga É—akin.

A harabar gidan ya tsaya yana amsa waya, security guard ɗinsa suka ƙaraso suna yi masa barka da fitowa. A lokacin Mansur driver Rehaan ya fito da tsaddiyar sabuwar motar Rolls Royce 2026, aka ajjiye ta a wajen ana jira ya gama wayar ya shiga su tafi. Jazy ne ya ƙarasa kusa da motar yana yiwa Ray magana, aka buɗe musu sabuwar motar suka shiga baya suka tafi gidan.

Kamar yadda Abban ya ce a main falo É—in suka shiga da sallama, mutanen ciki suka amsa suna kallonsu, su kuma suka shiga ciki suka zauna.

Sameer ne da Zayyad da Baba, sai Alhaji Rufa'i, Daddy, Abie, Baffa, da Kawun Saheer da malamin da yake É—aura auren Æ´an gidansu. GabaÉ—aya mutanen falon basu fi su goma ba, sai goro alewa da suke a ajjiye a wajen.

Sai Ray da Jazy suka zauna sannan Abba ya ce, "Yauwa, za mu fara É—aura auren Rehaan a wajan nan kafin mu tafi masallaci."

Zayyad cikin mamaki ya kalli Abba ya ce, "Abba ba a masallaci za a É—aura ba?."

Abba ya ce, "a nan za a É—aura na Rehaan, na Jafar ne za a yi a masallaci. "

Rehaan dai tunda ya sauke kai ƙasa bai ɗago ba, yana ji ana hidimar ɗaura aurensa bai ce komai ba, yana ji ko wanne ɓangare yana gabatar da kansa a matsayin wakili, yana ji ana zancen sadaki ana tambayar shaidu sun shaida. Yana ji yana gani aka ɗaura aurensa da Islaha akan sadaki naira miliyan ɗaya, aka bawa Baffa sadakin Islaha. Ji yake jinin jikinsa kamar ya daskare ya daina zagawa, ya kasa ɗago kai saboda yadda yake jin jikinsa ya yi sanyi sosai. In ya tuna aurensa aka ɗaura da Islaha sai ya ji kamar a tashi duniyar, sai ya ji kamar kowa ya mutu a bar duniyar babu kowa.

Bayan an ɗaura auren Abba ya kalli Baffa yana  murmushi ya ce, "Alhaji Mustapha mun gode, Allah ya saka da alkhairi."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "Amin. Allah ya tabbatar da alkhairi a cikin auren, Allah ya sa ya zama silar farin cikin kowa."

"Amin ya Allah."

Abba ya kalli su Jafar ya ce, "Zayyad ku je masallacin gamu nan, an bar mutane suna ta jira." Duk suka miƙe suka fita, aka bar Rehaan da Daddy a zaune.

Abba ya ce, "Alhaji Mustapha ga Rehaan...."

Abba juyo ya kalli Rehaan ya ce, "Rehaan ga mai riƙon matar ka, kuma uba a gare ta. Ka yi masa godiya akan karamci da haliccin da ya nuna mana. Ba tare da ya san mu ba ya ɗauki ƴarsa ya bamu, bai san kai ne za ka auri ƴarsa ba, amma ya amince da zuciya ɗaya. Ka yi masa godiya."

Rehaan ya ɗago ido a hankali ya kalli wanda aka muna masa, ya rasa me zai ce, dan shi bai ga abin godiya a auren Islaha ba. Amma sai ya daure ya ce, "an gode" ya faɗa a taƙaice dan babu yadda zai yi.

Baffa ya yi murmushi ya ce, "Babu komai, Allah ya sanya albarka a cikin auren, Allah ya É—orar da zaman har aljanna."

Duk aka amsa da amin ban da Rehaan da ya ja bakinsa ya yi shiru.

Baffa ya ce, "Na san ka san marainiya ce, a gidan marayu ta girma, bata san kowa na ta ba. Islaha yarinyar kirki ce, yarinya ce ta gari mai tarbiyya da sanin ya kamata. Yadda take yin ɗawainiya dani ko ƴaƴan dana haifa basa yi, yadda take yi min biyayya ko ƴaƴana basa yi min. A ko yaushe ina ji a raina ina ma ni na haifi Islaha, ina jinta kamar jinina, ina ji kamar ɗaya daga cikin yaran da Allah ya bani. Ka riƙe ta hannu biyu, na tabbatar da baza ka taɓa danasanin aurenta ba, sai dai ka yi alfahari."

Daddy ce, "Duk mun shaida, tarbiyyarta ce ta saka Daada ta ganta, ta burge ta har mu ka zo wannan matakin. In sha Allah Æ´arku ba zata yi danasani ba, baza ta yi hawaye ba, baza ta yi maraici ba. Zata rayu cikin farin ciki da walwala, za a maye mata gurbin ku da zata baro ta dawo nan."

Baffa ya ce, "Allah ya tabbatar mana da haka."

Duk suka amsa da amin kafin Abba ya kalli Ray ya ce, "ka je masallaci, ga mu nan." Ya miƙe a hankali ya fita ya bar su.

Bayan sallar juma'a aka É—aura auren Riyya da Jafar, bayan an É—aura auren anata hotuna kafin a tafi reception, Ray dai yana killace dan ba hayaniya yake so ba, duk inda ya yi masu tsaron lafiyarsa suna bin bayansa. A haka aka watse daga reception, ya wuce guest house dan Jazy ba dawowa zai yi ba.

Nana Haleema.
[7/30, 11:15 AM] KRBBK: RDB2P97
Nana Haleema.

Baffa bayan ya koma gida ya shiga har falon Mama ya samu Mama ta ita kaÉ—ai a zaune ya ce, "Ina Islaha?."

A daidai lokacin Islaha ta shigo da sallama, kafin su ji sallamar ta ta Mama ta ce, "Ta tafi yawon ta zubar, ko ta ɓatan Saheer ba ta yi, sai ƙaryar Hamma."

Islaha ta ce, "Gani Baffa."

Baffa ya juya yana kallon ta yana murmushin jin daɗi, ji yake kamar ya sauke nauyin da Allah ya ɗora masa, ji yake ya sauke haƙƙin da Allah ya ɗora masa a matsayin uba.

Islaha ta durƙusa a gabansa Baffa ya ce, "Kina da sa'a Islaha, ke mai sa'a ce gaba da baya. Duk mai nufin ki da sharri ko waye shi sai dai ya koma kansa, Allah ya yi miki abinda babu wanda ya isa ya ƙwace sa daga hannunki, alkhairin da ki ke nema ya ba ki, da ya tashi ba ki sai ya ninka ya kuma ninkawa. Karɓi nan" ya faɗa yana miƙa mata.
Chapter 128 · 0% Book details