Sashe 39
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mummy ta ƙaraso ta zauna kusa da ita, ta saka hannu ta zare wayar hannunta tana kallon fuskar wayar dan ganin wanda take kallo tana cewa tana so har haka. Ganin hoton wanda take kallo ya saka ta kalle ta, cike da mamaki da ɗaure kai, a sanyaye ta ce, "Rehaan ki ke so Ikram?."
Ikram ta shagwaɓe fuska tama ɗaga kai ta ce, "eh Mummy."
"Tun yaushe?."
"Nima ban sani ba."
Mummy tayi ajiyar zuciya cikin damuwa ta ce, "to meye na ajjiye maganar a ranki, meyasa baki faÉ—a min ba?." Ikram ta yi shiru bata ce komai ba.
Mummy ta sauke numfashi ta dafata ta ce, "Ikram Rehaan yayan ki ne, dan kin so shi ba laifi bane. Amma soyayyar da ki ke yi masa kamar bata kamace ki ba, kin san Rehaan ba wannan soyayyar yake yi miki ba, yana sonki soyayyar Æ´an uwantaka ba ta aure ba. Saka irin wannan soyayyar a ranki zai iya cutar dake, kin san bazai kalle ki a wannan matsayin ba.â€
Hawaye ya sakko mata, ta É—ago ta kallo Mamy ta ce, "Na sani Mummy, ina so na koyawa kaina hakan amma na kasa. Yana kallona kamar yadda yake kallon Riyya, yana kallona kamar Janan da Banisha, nasan bazai taÉ“a kallon a wani matsayi in ba wannan ba. Amma ni kuma ina sonsa Mummy, ina Æ™aunarsa sosai, kuma aurensa nake mafarkin yi.â€
"Kin san baya kallon ki a matsayin wacce zai aura meyasa ki ka fara yi masa irin wannan soyayyar? Ko dan kin ga yana sakar miki fuska?. Kar ki manta kaf cousins ɗinsa da ƴan gidan nan kaɗai yake shiri, kuma ki tuna in ba ke ba babu wacce in ta kira shi kai tsaye zai ɗauka. Kin san Rehaan ba ƙaramin mutum bane, yana cikin matasan da suke da kuɗi a garin nan. Anya ba ki yi gangancin fara sonsa ba?."
Ta goge idonta da suka jiƙe da hawaye ta ce, "Mummy ni ba dan kuɗinsa nake sonsa ba, ko bashi da komai zan rayu dashi."
"Na sani Ikram, soyayya da ki ka fara yi masa itace illar. Koda Rehaan zai so ki kakarsa baza ta taÉ“a yarda ya aure ki ba, kin san yadda aka sha wahala da ita kafin ta yarda da auren Jafar da Juwariyya. Inda Rehaan zai yarda dake a matsayin matarsa muna daga cikin mutane na farko da zasu so hakan, bani da matsala da Nadira, na san zata yi farin ciki sosai, mahaifinsa ma zai yi murna da hakan. Amma Kakarsa bazata taÉ“a yarda, saboda ba ita ta haifi mahaifin ki ba. Kin san kishi take yi da Æ´aÆ´an kishiyoyinta kamar me.â€
"Mummy ni duk ban damu da wannan ba, indai har zai yarda dani shikenan. Sai ya É—auke ni mu koma Uk da zama, ba lallai sai na zauna a nan ba."
"Ki dage da addu'a kawai, amma bana tunanin Rehaan zai amince ya karɓe ki matsayin matarsa."
Cikin kuka Ikram ta ce, "Mumny ki daina yi min baki, wallahi ina son Rehaan so mai yawa, in na rasa shi ban san halin da zan shiga ba.â€
Mummy ta shafa kanta ta ce, "ba baki nake yi miki ba, na san halinsa ne kawai. Kar ki ga Yayan ki zai auri Æ™anwarsa ki ji a ranki kema zai iya auren ki, kowa yana da ra'ayin sa. Rehaan bashi da ra'ayin auren Æ´an uwansa, nasan kema kin san da haka. Kafin ke an yi irin ki da yawa amma bai karÉ“a ba.â€
"Mummy ai da shima Hamma Jafar É—in haka yake faÉ—a, amma yanzu Riyya zai aura."
"Na faÉ—a miki shi daban da Rehaan, abinda zai yi Rehaan bazai yi ba. Ki cigaba da addu'a, in Allah ya amince komai zai wuce."
Ikram ta kwantar da kanta a kafadar Mummy tana kuka sosai ta ce, "Amma ina sonsa Mummy, wallahi zan iya cutuwa in ban aure sa ba."
Mummy ta shafa kanta ta ce,"shiyasa na ce ki ta addu'a."
"Mummy ki faÉ—awa Mamy, ko zata saka shi ya so ni, tunda yana son abinda Mamy take so.â€
"Ikram! Ke bakya fatan ya so ki dan kansa sai an saka shi?."
"Ni ko bazai kula ni ba, indai zan amsa sunan matar shi hakan ya yi min."
Mummy ta yi dariya tana girgiza kai cike da tausayin Ikram ta ce, "Lallai kin yi nisa. Kar ki damu komai zai wuce in sha Allah, ki tashi muje ki ci abinci."
“Mummy ki faÉ—awa Mamyn.â€
“Zan faÉ—a mata in sha Allah, zamu tattauna akan hakan.â€
Zata yi magana Mummy ta ce, "kar ki ce komai, ki tashi muje muci abinci kawai." Ta goge hawayenta suka fito tare da Mummy.
   •••••••
Basu isa Abuja ba sai bayan sallar i'sha, kai tsaye aiport aka wuce dasu basu tsaya hutawa ko wani abun ba.
Bayan sun fito daga mota, kowa a gajiye yake saboda zama, gashi babu batun hutu wani sabon zaman ne a gabansu. Mama ta kalle su ta ce, "to zamu rabu daga nan, yanzu wanda zai tafi daku zai zo. Da zarar kun isa ku kira mu a waya, ban da saɓa alƙawari."
Labiba ce ta ce, "To Mama. Anty Karima sai mun yi waya" ta faÉ—a ciki É—auki da zumuÉ—i.
Hajiya Karima ta kalli Islaha da tunda suka taso bata ce komai ba, gwara da suka tsaya a gidan Mai ta sauka ta yi sallah, daga nan bata sake cewa komai ba.
Hajiya Karima ta ce, "ba fa haka za ki je kina haÉ—e musu rai ba, tunda mu ka taho ban ji kin ce komai ba, ya kamata dai ki san irin abubuwan da zaki yi in kin je can. Aiki zaki yi musu su biya ki, dole ki saki jikin ki."
Islaha ta É—auke kai bata ce komai ba, ita sallar magrib da i'sha take so ta yi, ba wannan surutan banzan ne a gabanta ba.
Hajiya Karima ta kalli Umma da take duk ta damu kanta kamar wacce aka yiwa dole a tafiyar ta ce, "kar wani abu ya dame ki fa, mutuwar aure ai ba kan ki farau ba, kuma ba kan ki ƙarau ba. Kar ki wani damu wallahi, ki je ki haɗo kan ƴan canjin ki, ki dawo a cigaba da zama. Sai me dan ya sake ki? In ki ka samu kuɗin ki ba sai ki yi wani auren ba?."
Umma cikin rauni ta ce, "Aure kuma?."
"To wuce auren ki ka yi? Nawa ki ke?."
Mama ta ce, "mata ne da É—orawa kansu fitina walllahi, ni ban ga abin É—aga hankali dan ya sake ki ba. Kina da yarinyar da zata kula da Æ™annenta ba, shikenan an huta ba. In ni ce ita, wallahi a saudian zan É—aura aure, dan na nuna masa baya gabana. In ka nunawa namiji ka damu dan ya sake ka ba Æ™aramin raini bane, komai ace saboda Æ´aÆ´a, na rasa lokacin da mata zasu waye su daina kallo Æ´aÆ´a su kama gabansu.â€
Umma dai ta kasa magana, ɗauki da zumuɗin da take yi gabaɗaya ya kau daga zuciyarta, da tana da iko a lokacin tabbas da ta koma gidan mijinta ta cigaba da zama ita da yaranta, amma lokaci ya ƙure.
"Salamu Alaikum. Hajiya Karima da Hajiya Zulai barkan ku da zuwa."
Ganin wanda ya yi maganar sai suka washe baki, cike da girmamawa Mama ta ce, "Barka dai, mun same ku lafiya?."
Ya yi murmushi ya ce, "Lafiya lau. Ya hanya?."
"Hanya alhadu lillah."
"WaÉ—annan ne?."
Mama da Karima harda saurin haÉ—a baki wajan cewa, "Eh sune."
Ya bisu da kallo yana nuna Islaha da Labiba ya ce, "kai amma waÉ—anan sun yi, zasu yi daidai da gidajen da ake nema. Gaskiya kun yi aiki mai kyau, daga gani baza a sha wahala dasu ba wajan turanci."
Mama cikin son gwaninta ta ce, "ita fa wannan Æ´ar jarida ce, babu wanda bai santa a Yola ba. Kaima na san zaka iya saninta, tunda yanzu a waya ake sanin mutane."
Hajiya Karima ta cafke ta ce, "ai indai ɓangaren turanci ne an bar mata kayanta."
Ya yi dariya yana girgiza kai ya ce, "ƙwarai ina ganin fuskarta a waya. Irinsu ake so, wanda za a iya magana dasu da turanci. Dan gidan da za a kai ta likita ne, yana jin turanci sosai, ba lallai sai ta iya larabci ba......" ya ɗan kalli Umma ya ce, "Amma wannan zata iya kuwa?." Ya faɗa yana nuna Umma.
Hajiya Karima ta ce, "Me zai hana Oga?."
"Da gani babba ce, babu lallai a samu wani yare akan harshen ta. Kun san yanzu gidajen aikin nan basa ɗaukar waɗanda basa jin larabci ko turanci, kuma daga ganin wannan bata jin ko ɗaya. Dama dai kamar waɗannan ɗin ne, an fi buƙatarsu."
Mama ta ce, "lah itama ta iya turancin ai, kawai dai yaran sun fita ne. Amma babu abinda baza ta yi ba."
Ya gyaÉ—a kai yana kallon Umma dan shi bata yi masa ba, yafi so a kawo yara kamar su Islaha, baya so aje ta zamar masa kaya, ai ta yawo da ita ba a samu abinda ake so ba.
Ya kalle su yana É—aga kai ya ce, "Sun san komai dai ko? Sun san tsari da kason kamfani?."
Mama ta ce, "sun sani, duk mun yi musu bayani yadda ya kamata. Mun faÉ—a musu albashi za a kasa gida uku, mu É—auki biyu su É—auki É—aya. Duk na karanta musu."
Ya É—aga kai ya ce, "dakyau!. Ban da sata, gulma da komai duk kun faÉ—a musu?."
"Duk sun sani, mun tabbatar baza su yi aikata ba."
"Yanzu jirgin na su ya sauka, mu je a auna kayan kafin a fara boading. Ku yi sallama, dan baza su bar ku shiga ba. Zulai bani takardun nan.â€
Mama ta miƙa masa, kafin ta ta kalli Labiba ta rungume ta ta ce,"Saduwar alhairi ɗiya ta gari, Allah ya kiyaye ya bada nasara. Kin san gargaɗina, ban da zubar da mutunci."
Ta yi fari da ido ta ce, "zan yi kewar ki Mama."
Mama ta ce, "nima haka."
Ta kalli Islaha ta ce, "Islaha sai an dawo, Hajiya Maimuna saduwar alkhairi."