← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 133

Sashe 9

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya miƙe ya fita waje suka haɗu da masu aikin gidan suka yi sallar i'sha, sananan ya koma ciki bayan ya kira babban yaronsa a ɓangaren tsaro. Ya amince da Shams ɗari bisa ɗari, ya kan bashi aikin sirri ba tare da kowa ya sani ba. Shams babban yaronsa ne, duk inda zai je suna tare dashi a mota, in dai kaga Shams kaga Rehaan.

Ya kalle sa ya ce, "Shams where is she?."

"Sir tana middle part."

"Any update?."

"Sir, She is so funny, and she is also stubborn. Abincin da aka bata for lunch taƙi ci, haka aka kai mata dinner shima yana nan bata ci ba. But Sir, it seems like she is not feeling well "

Ya ɗago ya kalle sa yana binsa da wani irin kallon ƙasa ya ce, "ya aka yi ka san haka? Ka kai mata ziyara ne?."

Shams ya girgiza ya ce, "A'a, na shiga kai mata abinci ne."

"Babu wanda zai bata abincin....."

Sai ya dakata da maganar yana kallonsa tare da ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "sai kai?."

"Ni kaÉ—ai ka ce na dinga kula da ita, shiyasa nake shiga."

Ya É—an É—aga kai kaÉ—an bai ce komai ba. Shams ya ce, "chef ya zo Sir."

Bai ce komai ba ya yi masa alama da ya fita, ya fita shi kuma ya zubawa waje É—aya ido yana kallo ba tare da ya san tunanin me yake yi ba.

Ya jima a zaune yana tunannin da bai san dalilinsa ba, kawai ya zubawa waje É—aya ido yana kallo, bazai ce ga abinda yake tunawa ba.

A hankali ya miƙe kamar ba ya son tafiya ya nufi middle apartment ɗin slowly.

Kamar mai jin tsoro haka ya yi unlocking ƙofar ya shiga, ya ji wani irin ɗumi a falom, falon ya ɗauki ɗumi sosai kamar babu ac a ciki.

Da fasassun plates ya fara cin karo, a hankali ya kai idanunsa kan tray guda biyu na abinci har ya sauke idonsa a kanta, tana zaune ta cure waje É—aya ta haÉ—a kai da guiwa tana jan numfashi a hankali.

Mayar da ƙofar ya yi ya kulle, ya tsaya yana kallonta ba tare da ta san yana tsayen ba.

Ƙarar kulle ƙofar ya saka ta san an shigo, ba tare da ta ɗago ba ta ce, "bana son cin komai, ku barni na mutu kawai."

Jin yadda maganarta take fita sai ya yarda da maganar Shams da ya ce bata da lafiya, ko baka santa ba in ka ji voice É—inta ka san bata jin daÉ—i, balle shi da yasan yadda maganar ta take kamar parrot.

Bai ce komai ba, kuma bai motsa daga inda yake ba ita kuma bata É—ago ba dan bata san waye a tsaye ba.

A hankali ƙhamshinsa ya fara zuwa inda take, ƙhamshin da ta shaƙa ya mamaye ta lokaci ɗaya, duk da hancinta ya ɗan rufe saboda sanyi amma hakan bai hana ƙhamshin ratsa hancinta ya shiga ba.

Ta ɗan ɗago a hankali tana tunanin a ina ta taɓa jin ƙhamshin turaren nan, ta ɗago a hankali kai tsaye ta kalli inda yake, ta gan shi a tsaye yana ƙarewa falon kallo kamar mai neman wani abu.

Yana juyowa suka haɗa ido, duk da nauyin da kanta ya yi mata haka ta miƙe zunbur tana binsa da kallo, shi kuma kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai daga kanta, ya cigaba da nazarin ko ina a falon, dan bai yarda da ita ba ko kaɗan.

A hankali tako tazo gab dashi, ta buÉ—e ido sosai a kan fuskarsa tana ta tabbatarwa da kanta shi É—in ne ko wani ne daban.

Ta girgiza kai tana kallonsa, ta nuna sa da yatsa hannunta yana rawa, ta É—an dafe kanta da yake ciwo ta ce, "kaine ka saka aka kawo ni nan ko kaima É—aya daga cikin azzaluman da suka ajjiye ni a nan ne?."

Rehaan kamar bai jo ba, kallon ta yake yi kamar yadda yake yi mata in sun haÉ—u.

Ganin bai motsa ba sai ta dafe kai, tunawa da baya jin hausa, duk da bata taɓa ji ya yi magana ba, amma kana ganin sa ka san bai yi kama da wanda zai ji harshen hausa ba.

Ta buɗe baki zata yi fulatanci sai ta kalle sa ta ga sam bai yi kama da fulani ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka hango kamanni na ƴan ƙasashen waje a tare dashi.

Ta É—an rike kanta da yake juyawa, ta canja harshe zuwa turanci ta ce, "kaine ka saka a kawo ni nan?."

Bai yi magana ba sai kallonta da yake yi, yana so ya ga ƙarshen rashin kunyar yarinyar.

Ta sake kallon sa ta ce, "me nayi maka, Dan ka zuba min tea a jikina nayi magana? Ko dan ka fasa min waya na yi magana shine na cancanci wannan zaluncin?. Ban sanka ba, ban san sunanka ba, ban san waye kai ba. Dan ka yi min ba daidai ba na faÉ—a sai ya zama laifi?."

Ta ja numfashi ta sauke, ta kalle sa ta ce, "kana ji? Ka bar ni na tafi naje na ƙarasa abinda yake gabana, in na kammala sai ka sake turawa a ɗauko ni, zuwa lokacin na nutsu, amma yanzu ba a nutse nake ba."

_Wannan yarinyar bata da hankali._

Ya faÉ—a a mind É—insa yana kallonta bai É—auke ido ba kuma bai ce komai ba.

Islaha ta ja numfashi mai tsaho, ta zauna akan kujera saboda jirin da yake ɗaukarta tana sauke numfashi, dan ji take numfashinta yana sarƙewa, ga ciwon kai da ya saka mata jiri.

Ta ce, "kana jina, ko kai kurma ne?."

Kamar tana magana da rock haka Rehaan ya koma mata, yana tsaye cak bai motsa ba, babu inda yake motsawa a jikinsa ya ƙame a wajen kamar soja.

Sai kuwa ta hargitse ta firgice, cikin bala'i da masifar da take ranta ta koma hausa ta ce, "Ina faɗa ka bar ni na tafi inda aka ɗauko ni ka zuba min ido kana kallona kamar ina magana da dutse, kawai dan na yi magana a kan haƙƙina sai ka saka a ɗauko maka ni kamar wata kayan miya?."

"Ina da iyaye, suna buƙatata a kusa dasu, ina da mara lafiya da yake buƙatar kasancewata a kusa dashi. Me nayi ka ɗauko ni, Sata na yi maka ko fashi da makami? Ban yi maka komai ba ka kawo ni nan!."

Ta sake jan numfashi ta ce, "Me ka ke nema dani da ka kawo ni nan? Meye ribar ka na ajjiye ni a nan kamar wata kayan wanki?."

Sai kuma ta dafe kanta da yake harbawa, lokaci ɗaya ta daina masifar ta sanyaya murya ta ce, "ka barni in tafi, ina da mara lafiya, dashen ƙoda za a yi masa, ƴan gidanmu suna can suna nemana. Ka ƙyale ni, ni ban yi maka komai ba, laifi ka yi min, laifi ne dan na nuna hakan kenan? Laifi dan ka saɓa min na nuna maka?."

Rehaan ya É—an sunkuyar da kai ya É—ago ya kalle ta, ganin yadda take hawa da sauka abin ya tsorata shi. Yanzu tana masifa, yanzu ta canja ta sanyaya murya. Sai ya ga kamar tana da mental disorder. Bai saba da hayaniya ba, ita kuma ya ga yar hayaniya ce, hakan ya saka ya juya zai koma inda ya fito.

Ta miƙe da sauri ta ƙaraso inda yake, ta tsaya a gabansa ta ce, "baka jina ne? Kai kurman banza, baka jin me nake faɗa ne?."

Ya ɗan kalle ta ya watsar da ita, ya sake motsawa zai wuce ta. Islaha ta lumshe ido tana jin jiri yana ɗaukarta ta ce, "ina da mara lafiya, aikin ƙoda za a yi masa, ka bari in je a gama komai, in ya so sai ka saka a kawo ni....."

Muryar ta tana sarƙewa ta ce, "A lokacin daidai nake dakai, daidai nake da duk wani rashin kirkin ka. Duk abinda ka ke ji dashi wallahi na fika, ƙarƙari ka kashe ni ko? To na shirya...."

Ta ɗan lumshe ido cikin jirin da yake ɗaukar ta, hakan bai hana ta fasa magana ba, ta ce, "A yanzu kam bana cikin nutsuwata ko kaɗan!" Ya ɗan yi baya kaɗan bai kalle ta ba, sai yaga ta yi baya luuu zata kifa a ƙasa....
[6/17, 11:58 AM] KRBBK: RDB2P06
NanaHaleema.

Rehaan daman ya yi expecting zata iya faɗuwa, yana kula da yadda take jiri daga tsaye, kuma yanayinta ya nuna zata iya collapsing. Ganin zata faɗi a ƙasa ya saka ya tako ya riƙo ta, ta faɗo jikinsa a sume. Ya kalli fuskar ta da idanunta suke a rufe, ya ɗauke kai daga kallon ta yana miƙar da ita tsaye a jikinsa. Gently ya riƙo ta ya kwantar a kan kujera, ya ɗan taɓa skin wuyanta ya ji zafi sosai.

Ya ɗan shafa kansa kaɗan yana kallonta na wani lokaci, ya san stress da yunwa ne suka saka ta a haka, Shams yace bata cin abinci, kuma shima ya gani, ga kukan da take yi dole ta samu zazzaɓi. Sai kuma ya ja tsaki ya fita daga falon dan ya yi waya, dan ya saka an kashe duk service ɗin da yake wajan dole sai ya fita zai samu.

Kamar ya kira asibiti ya ce a turo masa nurse sai ya fasa, ya yi order duk abinda zai taimaka mata a wayarsa, ba jimawa rider ya kawo, ya saka aka kawo masa inda yakr ya karɓa ya koma inda take.

Ya ɗan kalle ta ya ɗauke kai, ya ɗan yi baya kaɗan ya ɗauko ruwa ya shafa mata a fuskar ta, ganin ta fara farfaɗowa sai ya ajjiye ruwan,  ya riƙe hannunta zai yi mata allurar da zata saukar da zazzaɓin. Da zata yi bacci, ta ci abinci, ta daina kuka da kansa zai sauka, to ya san ba zata daina ba, gwara ya yi mata kafin ta gama nutsuwa ta fara yi masa shirme.
Chapter 9 · 0% Book details