← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 133

Sashe 35

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“A shawara ta kar a faɗawa Sadik, babu lallai ya iya riƙe maganar bai faɗawa Saheer ba. Ki bari in kin je sai su ji labari, duk da na san zasu zo su tutsiye ni akan maganar, ni kuma zan faɗa musu abinda yake faruwa kawai.”

Islaha ta ɗan yi shiru alamum tunani kafin ta ce, “To mu gwada hakan mu gani, amma ina jin tsoron ɓacin ran Hamma.”

Safeera ta ce, “dole ransa ya ɓaci, shi da yake so ayi bikinku nan da wasu kwanakin masu zuwa, amma a wayi gari kin bar ƙasar, ai dole ransa ya ɓaci.”

Ta ja numfashi mai tsaho ta ce, “babu yadda zan yi ne, ni kaina dole ce ta saka ni zan yi. Har istikhara nayi akan tafiyar, shiyasa na saka a raina in har Allah ya nufa naje to akwai alkhairi a zuwana, in kuma ban je ba babu alkhairi a zuwan, tunda na nemi zaɓin Allah kuma na san zai zaɓa min.”

“Babbar matsalar ki a rayuwa shine gaggawa, duk da in mutum yana cikin yanayi na neman mafita yana aikata duk abinda ya zo ransa ne. Amma ke tun asali haka ki ke, kawai da zuciyar ki ta ɗarsa miki abu sai ki hau kai ki zauna, ki kasa fahimtar kuskuren abun har sai kin aikata. In ba dan haka ba, meye ya kai ki ɗauko kuɗi don Allah? Sannan me ya kai ki yanke hukuncin tafiya saudia? Dan kina ganin baki da iyayen da zasu hana ki ko?.”

“Ina da Hamma, na san shima in ya ji bazai bari ba. Kamar iyayena yake, duk abinda yace na bari ina bari.”

“Dole ki rage gaggawa, duk inda gaggawa take daga shaiɗan take.”

“Ga sakamakonta ina gani Safeera, da ban yi ba da ina nan hankalina a kwance. Yanzu kuwa mafarkai nake yi marasa kyau, har mafarki nayi na kasa tsallake siraɗi. Shiyasa hankalina ya tashi, nake nemawa kaina mafita.”

Safeera ta ce, “Zainab da Hafsa fa? Case ɗin da ki ke ta bibiya fa? Kina nufin zaki tsallake ki tafi ki bar yara a cikin garari?.”

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Zan bar maganar a hannun Barr Suraj, na san zai yi komai kamar ina nan. Kuma kema kin nan, zan dinga saka ki kiyi magana dasu.”

“Amma kin san ba kamar ke ba ko? In dai ki ka bar ƙasar nan an ajjiye batun case ɗin Islaha.”

“Allah zai kawo min yadda zanyi.”

Safeera ta ce, “Allah ya kyauta. Aikin ki fa?.”

“Zan yi droping ɗinsa, in na dawo zan cigaba in sha Allah.”

“Kafin shekara ɗaya za a manta da fuskar ki, kina kan matakin ɗaukaka a yanzu, in ki ka yi ƙaura aka daina ganin zaki dakusar da kan ki.

“To ya zan yi?.”

“A ganina ki yi creating content a can, ko da video flowers ne ki dinga ɗauka ana yawan ganin fuskar ki a media. Tunda kina da followers, hakan zai saka baza a manta dake da sauri ba.”

Islaha ta ɗaga kai ta ce, “Allah ya bani iko.”

Safeera ta amsa da amin a lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo da sallama.

Suka amsa suna kallon Mama da ta shigo da babbar trolly bag ta ce, “islaha ga jakar zuba kaya nan, in anjima za a siyi ticket ɗin ku, jirgin jibi da daddare zaku hau. Ki zuba duk abinda ki ke da buƙata, ki zuba kaya masu kyau kar ki tafi da marasa kyau. Sannan zaki iya yin siyayya in kin je Jedda ki siyar ki riƙe kuɗin ki. Ana siyan goro, doya, fara, man shafawa, da sauransu. Goro dai ya fi kawo kuɗi, amma wucewa dashi tun daga nan Nigeria yana da wahala, amma da kin wuce in Allah ya taimake ki a Jedda ma ya wuce zaki yi murna.”

Islaha cikin yaƙe ta ce, “Na gode Mama, ba sai na siyi komai ba.”

Mama ta ce, “shikenan, ni zan ba da sautun da za a siyar min ki saka a jakar ki, in aka siyar ki mayar da kuɗin naira ki turo min kuɗina. Sannan akwai yaji, saboda abincin larabawa babu ɗanɗano, ina dashi na siyarwa in za ki siya.”

A sanyaye islaha ta ce, “To Mama. Hamma yana nan?.”

Mama ta ce, “ke kar ki damu da Saheer babu abinda ya isa ya yi, ba haifar ki ya yi ba, kuma ba auren ki yake yi ba. Bai isa ya hanaki abinda ki ke so ba.”

Ta langwaɓar da kai ta ce, “Don Allah Mama bana so ya sani, tunda gobe zai koma Niger don Allah kar ki faɗa masa.”

Mama ta ɗaga kai ta ce, “naji……”

Mama ta juyo ta kalli Safeera ta ce, “Ke Safeera ana ta tafiya ke baza ki je ba? Ga ƙawarki nan zata tafi ta bar ki a nan, ko da yake da babar ki za a yi tafiyar” ta faɗa tana juyawa ta fita.

Safeera ta bi bayanta da harara ta ce, “babu inda Umma zata je in Allah ya yarda. Matar nan makira ce, wato dan zaki je ki samo mata kuɗi shine harda sakar miki fuska. Ki ji kayan takaici, wai in kina son yaji ina da na siyarwa.”

Ita dai Islaha bata ce komai ba dan bata so Safeera ta ji da Umma za a yi tafiyar a bakinta.

Sai da suka yi sallah suka fito, a harabar gidan suka haÉ—u da Saheer da Sadik a tsaye suna tattaunawa akan jikin Baffa da ya warware kamar ba shi ba.

Suka ƙarasa inda suke tsaye suka gaisa, Saheer ya kalli Islaha da kana kallon ta ka san tana cikin yanayin damuwa mai yaws. Ya ɗauke kai daga kallon ta, amma sai ya kasa daurewa ya juyo ya ce, “Ya dai?.”

Ta kalle sa ta ce, “babu komai, kaina ne yake ciwo.”

Ya zuba mata ido ya ce, “me ya kawo ciwon kan? Kwana biyu kina yawan cewa kan ki yana ciwo, me yake kawo shi?.”

“Gajiya ce, ɗazu na je ɗaukar labarai ne, kuma ka ga yau anyi rana kamar ba lokacin sanyi ba.”

Ya ɗan sauke nunfashi ya ce, “kin sha magani?.”

Ta ɗaga masa kai alamun eh ta ce, “zan raka Safeera na dawo.”

“Ki dawo mu yi sallama, gobe da asuba zan wuce in sha Allah.”

Ta ɗan gyaɗa kai ta raka safeera ƙofar gida, ta dawo ta tarar suna tsaye har lokacin suna magana. Bata tsaya ba ta wuce su zuwa cikin gida Saheer ya bita da kallo har ta ɓace daga idanunsa.

Ya juyo yana kallon Sadik ya ce, “ban amince da yanayin Islaha na kwanakin nan ba, tabbas ta canja ta koma kamar ba ita ba. Zuciyata tana faɗa min akwai abinda aka yi mata a lokacin da aka sace ta, a can ta samo wannan damuwar da take ɓoyewa.”

Sadik bai ce komai ba, amma shi kansa har lokacin yana tunanin kuɗin da ta kawo masa aka biya kuɗin aikin Baffa, har lokacin zuciyarsa rawa take yi akan Islaha, tunaninsa a ina ta samu kuɗin ita da aka ce an sace ta?. (Waye y sani Malam Sadik?🤣)

Islaha sai ta ƙagu dare ya yi Saheer ya zo su yi sallama ta huta, so take kawai ya bar ƙasar ya tafi Niger ko zata fi mayar da hankali akan abinda yake gabanta.

Ta gama shirin bacci kenan ya kira wayarta ya ce ta zo harabar gidan su yi sallama. Ta saka hijjab a sanyaye ta fito, a daidai lokacin Hanan ta shigo da manyan ledoji tana wani takun isa da taƙama ta wuce su ta shiga ciki. Ya ja tsaki ya ce, “gabaɗaya Mama ta lalata yaran nan.”

Islaha bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, “na kira ki mu yi sallama, bana so na takura miki ki fito da asuba saboda sanyi. Zan tafi, amma bazan jima ba zan dawo saboda jikin Baffa.

Islaha a sanyaye tankalle shi ta ce, “Allah ya kai ka lafiya, Allah ya baka abinda ka je nema.

Ya sauke numfashi ya ce, “Amin matar Hamma. Kin san nawa bill ɗin asibitin da Baffa yake?.”

Ta girgiza kai tana kallonsa gabanta yana faɗuwa ya ce, “kuɗi ne masu yawa fa, a haka ma wai dan an biya kuɗin aikin. Asibitin yana da kyau da tsari, amma akwai kashe kuɗi sosai.”

A sanyaye ta ce, “an ce mai asibitin kamar bature yake, shiyasa tsarin asibitin ya zama na turawa. In ban da shi ban taɓa ganin asibitin da nurses ne sukw jinyar mara lafiya ba, ko national hospital Abuja nasan ba haka ake yi ba, amma wannan gashi an yi. Kuma duk tsadarsa tunda an samu biyan buƙata ai mun gode Allah. Ga Baffa ya tashi kamar ba shi ba, ga Kawu ma ya miƙe kamar ba wani abun aka rage daga jikinsa ba. Ban taɓa ganin wanda aka yiwa dashen ƙoda ya miƙe ba, sai Baffa.”

Ya yi murmushi ya ce, “haka ne kam, hausawa sun ce a wajan biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Kuma tunda an samu biyan buƙata baza a ji fitar kuɗin ba, mun gode Allah da ya bamu ikon yin komai ba tare da wani ya cutu ba.”

Islaha ta murmusa ta ce, “Gaskiya ne Hamma.”

“Amma fa an ƙarar da ƙaramin arzuƙin mijin ki kaf, abinda ya rage min bai wuce gidan da nake ginawa ba. Shima dan Allah ya taimaka mana Sadik ya yi ƙoƙari an samu kuɗin aikin ne, da yanzu an siyar dashi mun koma bamu da komai. Akwai wani fili da muka siya ni da shi da jimawa, ya ce min shi aka siyar aka ƙarasa biyan kuɗin.”

Ta yi murmushi ta ce, “kuɗin da suka ƙare a hidimar iyaye Allah zai ninka su sau babu adadi.”

Ya yi murmushi yana shafa kansa cikin jin daɗin maganar ta ya ce, “Gaskiya ne Matar Hamma. Amma da a ina zamu zauna?.”

Ta juya ta kalli ɗakinsa ta ce, “Ga ɗaki can.”

Ya yi dariya ya ce, “Haba dai! Sabuwar amaryar zan ajjiye a wannan tsohon ɗakin? Lallai ya kamata naci tarar ki, kin ƙasƙantar min da mata, kin sakko da ita daga high level zuwa low levwl.”
Chapter 35 · 0% Book details