Sashe 52
Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
DaÉ—i ya mamaye zuciyar Safeera, amma bata nuna ba ta ce, "Mama bama so mu takura ki ne, kuma..."
Mama Atika ta daktar da ita ta ce, "Kar ki sake faÉ—ar maganar nan, ni mai tsayawa akan lamarin ku ce a ko yaushe. Yanzu akwai abinda ku ke so?."
Safeera ta murmusa cikin jin daÉ—i ta ce, "Babu komai."
"Gobe ki shirya ki tafi aiki, in zaki tafi ki kawo min makullin gidan. Ke Rukayya in kin dawo daga makaranta ki zo ki karɓa a wajena." Ta ɗaga kai alamun to.
Baba da yake jin komai, ya fito da fara'a ya ce, "Atika ba a É—ora miki nauyi ba?."
Ta yi dariya ta ce, "babu komai. Auren Saeera za a yi nan da wani lokaci, suna buƙatar uwa a tare dasu, kuma in sha Allah zanyi iya abinda zan iya dan basu kulawar da ta kamata. Na yiwa Maimuna alƙawari, kuma zan cika in sha Allah."
Baba ya ɗaga kai cikin jin daɗi ya ce, "madallah, Allah ya ƙara zumunci." Ta amsa da amin. Baba ya fita cikin jin daɗin kalamanta.
Safeera ma ta ji daɗi sosai, lokaci ɗaya ta sake dan sun saba da Atika ƙawar Umma ce.
Safeera ta ji daÉ—in karamcinta, hakan ya rage mata nauyin da take ji a ranta. Daman dangin Umman sun ce ko zasu koma Katsina, itace daman bata so kuma ga mafita an samu hakan ya yi mata daÉ—i sosai.
••••••••
Islaha suna tsaye a gaban dining table yana zuba abincin dinner, sai da ya gama ya fara ci a nutse sannan yankalle su ya ce, "you made this?."
Islaha ta É—aga kai alamun itace, ya girgiza kai ya ce, "perfect." Ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta shi kuma yana cigaba da cin abincinsa.
Sai da ya kama kaf suka kwashe kayan suka wanke, Islaha ta ɗan ci abincin dan kayan ƙhamshinsu ba wani daɗi suke yi mata sosai ba. Bayan sun kammala ta shiga ɗaki ta yi wanka ta canja kaya zuwa mofty ta zauna tana tunanin Saheer.
Waya ta ɗauko ta buɗe saƙon Mama, ta buɗe voice note ɗin ta ji ta ce, "an samu waje ko waya baki yi min ba, ke haka za a yi dake? Haka za a yi dake tun ba a yi cikin ba harza a haihu?."
Kafin ta ba ta amsa kiran ta ya shigo kamar jira suke su ganta online.
Tana ɗauka Mama ta fara masifa tana faɗin, "dan wulaƙanci baza ki iya kirana ki faɗa min a inda ku sauka ba, haka za a yi dake kenan ko? Kin je kin fara shan laban kina cin kaji kin manta yadda tsarin yake ko?."
"Mama ina yini."
"Da ban yini ba ai da ban kira ki ba."
"Ki yi haƙuri, aikin ne da yawa shiyasa sai an yi a hankali."
"Wannan ke ta shafa bani ba, kuÉ—i ne in ki ka samu sai an raba an bani nawa, duk abinda zai biyo baya keki ka jiyo."
"Ki yi haƙuri." Mama ta ja tsaki ta kashe wayar.
Islaha bata damu ba ta kira Saherr, ta kasa jurewa sai an kwana biyu kamar yadda tace sannan zata kira sa, hakan ya saka ta kira ko zata É—auka.
Har ta gama ringing bai ɗauka ba, ta buɗe saƙonsa tana karantawa ƙirjinta yana bugawa cikin tsananin kewarsa. A hankalinta danna vn ta ce, "Hammana ka yini lafiya, ya aiki?. Ka yi haƙuri Hamma, na san na yi kuskure, ka bani dama na wanke laifina."
Tana turawa ta ga ya yi blue alamun har ya buÉ—e, ta tsaya tana jiran amsa amma shiru bai ce komai ba kuma ta tabbatar ya ji.
Ta sake yi masa wani ya sake buɗewa, daga ƙarshe sai ta ga dp ya koma fari saɓanin hoton addu'a da yake kai, in ta tura saƙon sai ya yi tick ɗaya alamun an yi blocking number.
Hankalin Islaha ya tashi, ta gigice ta rasa yadda zata yi. Daga ƙarshe ta zauna ta ci kuka son ranta, ta share hawaye ta kwanta tana jan numfashi cikin rashin mafita.
  Ball suke bugawa a babban wajen ball ɗin da aka tanada a gidan Rehaan, Rehaan yana tsaye sanye da complete set ɗin kayan barcelona, ya tufke gashinsa a tsakiyar kansa.
Yadda suke ball ɗin da jikinsu da ƙarfinsu sai ka ɗauka turanwan gaske ne, ko kuma biyansu ake yi.
Lokacin da suka gama Rehaan yana riƙe da ruwa yana sha, suka taho suna hira har suka ƙaraso tsakiyar compound ɗin gidan Rehaan.
Duk suka yi masa sallama, ya rage daga shi sai Ubaid da ya cika sa da uban surutu.
Rehaan ya ce, "ina ta so na tambaye ka sai na manta, har fita nayi zan shiga wajen Maleek na dawo. Kana da extra maid? I want it for my chef."
Ubaid ya shafa gemu ya ce, "yes i have it. She's from Nigeria, Yarinyar ta haÉ—u sosai, zaka ji daÉ—in ta."
Rehaan ya kalle sa sai ya ja tsaki bai ce komai baz Ubaid ya ce, "Riyar dubu ɗaya ta raba ka da ita, zaka mori lokacin ka yadda ka ke so. Kuma ta iya soyayya sosai Rehaan, zata shagwaɓa ka. Zan iya ara maka ita na lokaci ɗaya ta zo ku kwana tare. Wallahi ta yi, ga skin ɗinta very soft and smooth."
Rehaan ya ja tsaki ya ce, "ka bar su bana so."
Ubaid ya yi dariya ce, "i'm telling you, Æ´an Nigeria sun fi arab zama too hot, komai so sweet."
Reehan bai kuma ce masa komai ba ya koma ciki zuciyarsa cike da takaici. Allah ya sani baya son wannan ɗabi'a, yana kishin ƴan ƙasar sa sosai, yana so a martaba ƴan ƙasarsa, amma duk sun gantalar da ƙimar ta bi rariya. Cikin takaici ya shiga ɗaki, ya yi wanka ya shirya ya tafi asibiti.
Islaha ta ɗan sake, ta saba da wasu abubuwan sosai. Ta fahimci Maleek yana da kirki sosai, bai taɓa ƙoƙarin yi mata wani abu ba, sai dai a gaisa daga nan ba ya cewa komai zai fita. Damuwar ta bai wuce Hamma ba, ya ƙi ya yi unblocing ɗinta, gabaɗaya ta damu, har sim card na ƙasar suka je ta yi register amma da kira shi sai ya ƙi ɗauka, ƙarshe ma sai ya kashe wayar.
Ta yi ajiyar zuciya ta fito falon, a nan suka haÉ—u da Maleek zai fita, suka gaisa ya kalle ta ya ce, "Are you able to work as a chef in another house as well, or would that be too much for you?."
Islaha ta É—an yi jim bata amsa ba, sai kuma ya É—aga kai alamun zata iya.
Ya girgiza kai ya ce, "The house in the middle close to us, gidan abokina ne. He's looking for someone to cook and make tea for him. If you're willing, you can also work there, he pays well and he's very kind.
Islaha ta ce, "yeah i can."
"Okay. Let's go, I'll show you the house."
Islaha ta koma ciki ta É—auko hijjab ta fito ya fita itama ta bi bayansa. Tunda kuÉ—i take nema, dole ta haÉ—a da gidan tunda ya ce yana biya dakyau.
A wannan lokacin ta ga Labiba ta fito saka shara a babban trash É—in da yake wajan, suka haÉ—a ido Labiba ta É—auke kai ta koma ciki itama ta É—auke kanta.
Tunda suka nufi gate É—in gidan gabanta ya yanke ya faÉ—i, ta dinga addu'a ranta, bata san dalilin da ya saka take jin faÉ—uwar gaba ba, gashi bata san mai gidan ba balle tace tsoron aikin take yi, haka kawai tana cike da fargaba.
Bayan sun shiga compound É—in gidan ya juyo ya kalle ta ya ce, "Shima É—an nigeria ne kamar ki, amma yana kiwon damisa."
Islaha ta É—an buÉ—e ido cikin mamaki, Maleek ya murmusa ya ce, "yeah." Bata tanka ba suka cigaba da tafiya.
Gidan shiru babu sautin komai sai na tsuntsaye kaÉ—an kaÉ—an, sai kallon gidan take yi tana girmama girmansa, duk yadda take ganin kyaun na Maleek sai taga wannan yafi sa komai, ya tsaru sosai, ya sha adon flowers a ko ina.
Suna zuwa wajen babban ƙofar ta ga Maleek ya saka card ya buɗe ƙofar falon, ya kalle ta ya ce, "ki shiga, akwai kitchen ki yi abinda ya kamata. Ki yi komai kamar yadda ki ke yi min, na yarda dake shiyasa na zaɓe ki. Note, ba ya son milk tea or milk coffee, baya shan madara" ya faɗa yana miƙa mata katin, ta karɓa ya juya ya barta a wajan.
Gaban Islaha ya faɗi, ta taka ta ƙarasa cikin falon a hankali ƙhamshi yana dukan hancinta.
Falon da duhu sosai, hakan ya saka ta nemi switch ta kunna take haske ya gauraye ko ina. Ta bi falon da kallo ganin yadda ya tsaru, komai a tsaftacce, komai yana mahallinsa.
Laptop ce a ajjiye akan table ɗin, bayan ita babu komai a wajen. Ta kalli sama ta ga upstairs ɗin wanda yake sama zai iya gano na ƙasa, irin mai balcony ɗin nan ne saman, na saman in yana tsaye tsaf zaku yi hira.
Islaha ta É—aga kai ta fara tafiya dan neman kitchen ta yi abinda zata yi ba kallon falo ba.
Ƙofar farko da ta buɗe ta ga kitchen ɗin ne, mai mahaukacin girma da tsari, ta kunna haskensa tana sake kallon ko ina cikin mamakin girmansa.
Gashi babu wasu tarkace, gas stove, sai oven da microwive, sai mixer da blander kawai ajjiye a wajan.
Ita dai a tsorace ta ke kallon ko ina, kafin ta ƙarasa ta buɗe drawer a nan ta ga glass tea pot mai madaidaicin girma, ta ɗauka ta ƙarasa gaban sink ta ɗauraye sannan ta dawo ta ɗora akan gas ɗin.
Hijjab ɗin ta cire, ta sake ɗauka ta zuba ruwa madaidaici ta dawo ta ɗora ba tare da ta kunna ba. Buɗe buɗe take yi amma bata ga komai na kayan tea ba, ta ɗan yi tsaki kamar ance ta kalli gefe, a nan ta ga wani carbinet na glass, ta ƙarasa ta buɗe ta ga da kayan tea kamar hauka. Tea leaves ma sun fi kala talatin. Black, green, red duk akwai.