← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 133

Sashe 68

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inda glass ɗin nan ya fashe ta ƙarasa, ta ɗauki machine ɗin falon ta kwashe glass ɗin, ta goge tea ɗin da ya zube. Har zata bar wajan sai ta dinga jiyo kukan Alma daga room ɗin da yake wajen. Har zata wuce ɗakin sai ta dawo, dan ƙofar bata rufe da kyau ba.

Islaha ta ji tana cewa, "Wata housemaid ce ta zubar da tea É—in da na saka maganin, ba laifina bane, ban san ya zube ba."

Sai Alma ta yi shiru sannna ta ce, "but in anjima kaÉ—an zan zuba masa powder, i promise, tognight he will be mine, sannan zan É—auki video komai zan tura maka."

Alma ta ce, "na gode, da dama ta ƙarshe" ta faɗa tana sauke wayar.

Jikin Islaha a sanyaye ta bar wajan a hankali ta sauka downstairs tana tunani, ta zauna a kan dining ta yi shiru tana tuna abinda Alma ta ce.

A bayyane ta ce, "video take so ta yi masa ko kuma turancin ne ban fahimta ba?."

Ta sake yin shiru kafin ta ce, "i promise, tonight he will be mine....." ta ɗan sake tafiya tunani sannan ta ce, "Kenan mai zata sake ba shi? Na ji ɗazu yana cewa bazai aure ta ba, kenan ita tana so ya aure ta shi kuma ya ƙi."

Ta ɗan daki kanta, tunawa bafa Hamma bane baturen da ya sace ta ne. Ta girgiza kai tana taɓe baki ta ce, "ina ruwana? Su kashe kansu mana, tare na gansu." Tana gama faɗa ta miƙe ta shiga kitchen, amma sai ta kasa yin komai tana tuna abinda Alma ta ce.

Gashi dai ta gama abinda zata yi amma sai ta kasa barin gidan, har aka yi sallar la'asar tana kitchen a zaune tana duba yadda video ta yake ta trending ana ta zuba likes da comments.

A hankali ta miƙe tana sauke numfashi ta ce, "Islaha ina ruwan ki ne? Duk abinda zata yi masa me ya dame ki?."

Ta sake jan numfashi ta ce, "duk fa abinda ya faru cewa za a yi ni ce, gwara na je na hana kafin a É—ora min sharri."

Da wannan tunanin ta koma upstairs ɗin, daidai lokacin da Alma ta wuce daga hanyar ɗakinsa tana murna tana cewa, "Yes ya shaƙa, zan jira wasu mintina" ta faɗa yana shiga bedroom.

Jin hakan sai gaban Islaha ya faɗi, ta buɗe ido ta ce, "na shiga uku, ba dai ta kashe shi ba, ni fa da wuri nake burin barin ƙasar nan, ban shirya zaman prison ba wallahi." Da sauri Islaha ta ƙarasa ɗakinsa, ta same sa ya dafe kai da duka hannu biyu ya rufe ido ruf.

Miƙewa ya yi ta ga yana layi kamar zai faɗi, daƙyar ya kai kansa gado ya kalli Islaha yana ganin ta guda biyu ya kasa banbance wacece, ya sake runtse iso ya ce, "Subahanallah!."

Islaha ta yi sak tana kallonsa ta ce, "ashe fa ya san Allah."

Ya kwanta da baya jin kansa yana barazanar watsewa,wani irin bacci ya ji yana fizgarsa idonsa sai rufewa yake yi, shi kuma ba ya son yin baccin amma ya kasa rinjayar maganin. A hakali idonsa ya rufe ruf dogon bacci ya É—auke sa.

Islaha ta bisa da kallo ganin baƙin gashinsa a baje a kan gadon idanunsa a rufe, ta ɗan ja baya dan bata san abinda ya kamata ta yi ba.

A lokacin Alma ta shigo, Islaha tana daga gefe bata ganta ba.Ganinsa a haka sai ta yi dariya ta ce, "I am certain this moment is mine. I will have you, my love, nothing can stop me. And I will make sure to record every second of it" ta faɗa tana fara cire rigar jikinta, ya rage daga ita sai bra, ta sai ta wayar ta ajjiye daidai inda zata ɗauki komai da komai, har da light ta kunna yadda komai zai tafi yadda ya kamata, ta girgiza gashinta tana ƙarasa inda yake tana murmushi.

Islaha da take nesa da ita gabanta ya faÉ—i, ta wara ido waje ganin ana niyar yin BF a gabanta. Ta runtse ido ta fito daga inda take, Alma da take niyar fara unbotton rigarsa ta kalli Islaha ta ce, "what are you doing here? Go out!."

Islaha bata ce mata komai ba ta ƙarasa ta ɗauki wayar da ta ajjiye, Alma ta ƙaraso a guje amma kafin ta cimmata Islaha ta goge videon da ta fara ɗauka. Alma ta zo zata ƙwace wayar Islaha ta riƙe da ƙarfi, ita kanta bata san tana da ƙarfin iya riƙe Alma ba sai a lokacin, ta haska wayar a fuskar Alma ta cire face id, ta goge videon daga deleted
recent É—in wayar.

Islaha cikin kakkausar murya ta ce, "get out, before i call the police."

Ta bi Islaha da kallo ta ce, "who are you?."

"I said get out!."

Jin an kira police ya saka Alma karɓar wayarta ta ɗauki rigarta ta fita daga ɗakin. Islaha ta dafe kai ta ce, "ban yarda da gaske ana yiwa namiji fyaɗe ba sai yau, ji wannan motsatstsiyar don Allah." Sai kuma ta kalle sa da yake kwance ido a rufe yana bacci.

Ta harare sa ta ce, "wallahi ba dan kai na yi ba, zuciyar musulunci ce ta saka na yi. Kuma ka burge ni ne, yadda ta dage akan ka ya nuna min baka sauraren ta......" sai kuma ta sake jan tsaki ta ce, "Ji sa don Allah, ya wani ba je yana bacci. Mtsw! Ragon maza kawai."

Islaha falon ta koma ta zauna, a kan idonta Alma ta sauka da jaka da sauri ita dai bata ce mata komai ba.

Islaha ta yi shiru tana tuna abinda ya faru kamar a mafarki, ta sake kallon ɗakin da yake ta ɗauke kai ta yi shiruu. Tana tana zaman jin daɗin a wajen har ta gaji, ta yi sabon content duk dan ta rage lokaci amma babu wani cigaba. Har aka yi i'sha tana gidan, sai bayan takwas ma dare sannan ta miƙe ta sauka ta fita daga gidan gabaɗaya. Ita kanta bata san me ya zaunar da ita ba, ta san dai ta zauna saboda kar Alma ta dawo, kar ta yi masa wani abun a ce itace.

      ••••••

Maman orphage ta bi zainab da kallo da take zaune kanta a sunkuye ta ce, "Zainab ni ban ga abin É—aga hankali a nan ba, matar nan tana so ki je ki É—an zauna mata kafin ki dawo, kuma kitso zaki yi mata ita da yaranta; to meyasa bakya son zuwa?."

Zainab ta kalle ta ta ce, "Mama ni bana son zuwa, na fi son zama a nan kawai."

Ta miƙe ta ƙaraso ta dafa kafaɗarta ta ce, "A nan me ki ke samu? In kin fita sana'ar me ki ke samu? Sana'ar kitson da baya wuce a baki ɗari biyu, ƙarshen kyautar a baki ɗari biyar, hajiyar gaske ce zata baki dubu ɗaya. Ta ya za ki tallafi rayuwar ki da wannan kuɗin da bai wuce na purewater ba?. Bakya ganin ƴan uwan ki yadda suke jin daɗi? Bakya sha'awar kema wata ran ace kece kamar su?. Manyan makarantu suke yi, ga wayoyi masu kyau da tsada a hannunsu. Meyasa baza ki amince kema ki samo na ki arzuƙin ba?."

"Mama in na je aikin me zan yi musu da zasu bani kuÉ—in?."

"sana'ar ki mana, da ita zaki samu arzuƙi."

"To Mama zan duba na gani."

Ta bita da kallo kamar ta tsinka mata mari, amma da yake lallaɓa ta take yi sai ta ce, "tunanin me zaki yi? Ni ce fa uwar ki, ba ki da wacce za ki yi shawara da ita kamar ni."

Zainab ta ce, "zan nemi Adda Islaha."

"Komai sai kin yi magana da Islaha? Ina ki ka ga Islahan da za ki yi shawara da ita?. Tana can ƙasar waje aiki, ta tafi ta tallafawa rayuwar ta tana can tana neman kuɗin ta, ke ta ɗora ki akan aƙidar da ba itace a ranta ba. Waccee Islaha a wajan ki? A nan gidan ku ka haɗu kawai, kuma gidan ya raba ku. Ke tana hana ki taimakom rayuwar ki ne , ita kuma tana taimakon ta ta rayuwar!." Ta faɗa a fusace tana kallon Zainab.

Zainab ta yi shiru bata ce komai ba. Mama ta ja tsaki ta ce, "jeki ciki." Zainab ta miƙe ta fita ita kuma ta da ki table ta ce, "Ban san me matar nan ta gani a tare da Zainab da ta dage a kanta haka ba. Yarinyar nan zata iya saka min ciwon kai" ta faɗa tana ɗaukar waya.

"Yarinyar nan Zainab taƙi ba da haɗin kai fa, ni tsoro nake ji kar maganar nan ta fita wallahi."

"Har yanzu?."

"yanzu ta bar nan, na ɗauka rashin Islaha zai saka ta ɗan shiga hankalinta, sai na ga sake ɓotsarewa ma take yi. Bana so maganar nan ta fita, dan haka a ƙyale zainab kawai."

"Baza a ƙyale ta ba, za a samu mafitar da zata amince ko bata so."

"Kar ta jawo mana matsala fa."

"zan san abinda zan yi."

Ta kashe wayar tana tsaki ta ce, "Wannan shegiyar Islahan ta zamar min damuwa wallahi."

Zainab tana fita daga office É—in fita ta yi ta nufi gidan su Safeera. Da sallama ta shiga tsakar gidan ta samu Safeera a zaune tana shan tea.

Nana Haleema.
[7/9, 11:24 AM] KRBBK: RDB2P48
Nana Haleema

Ganin Zainab sai ta yi murmushi ta ce, "Zainab sannun ki da zuwa."

Zainab ta yi murmushi ta ce, "Yauwa Adda Safeera, ina yini?."

Safeera ta miƙe ta ce, "mu shiga ciki sai mu gaisa."

Suka shiga falo Safeera ta ce, "É—azu Islaha take yi min maganar ki, tana cewa kin zo kuwa."

Zainab cikin damuwa da ruani ta ce, "Yaushe zata dawo Adda?."

Safeera ta ce, "wallahi ban san rana ba, amma ta kusa in sha Allah."
Chapter 68 · 0% Book details