← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 133

Sashe 38

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha cikin rauni ta ce, "Ki yi haƙuri Safeera."

"Islaha Baba ya saki Umma!."

Gaban Islaha ya yanke ya faɗi, ta dafe ƙirji cikin kiɗima da tashin hankali ta ce, "Saki Safeera!."

Ta ɗaga kai ta ce, "Daman ya ce mata indai zata bar ƙasar nan to babu aurensa a kanta, a gaban idanuna Baba ya cewa Umma ya sake ta. Islaha ji nake kamar ana gasa zuciyata wallahi, me Umma ta nema ta rasa a duniyar nan, me zai kai Umma wata ƙasar aiki don Allah!?."

Islaha ta shafa bayanta ta ce, "ki yi haƙuri, babu amfanin ɓacin ran tunda ta riga ta aikata. Ki kwantar da hankalin ki, kar damuwar ta saka miki ciwo."

Safeera ta ce, "ni kaɗai na san me nake ji Islaha. Yanzu in Umma ta tafi ya zanyi?. Bakyan nan itama bata nan, ina zan saka raina naji daɗi? Wajen wa zan dinga kai damuwata? Babu ke babu ita, ina zan saka raina....." ta kasa ƙarasawa saboda kuka, muryar ta tana rawa ta cigaba da cewa,

"Waye zai dinga yiwa Baba abinci, waye zai dinga kula da Baba in na tafi wajan aiki?."

Hawaye ya sakko daga idanun Islaha, cikin raunin murya ta ce, "shiyasa nake cewa ki yi haƙuri, in ki ka cigaba da damuwa ke zaki samu matsala."

"Sai da ta ga lokaci ya ƙure, babu damar na faɗawa danginta, dan tasan kafin su zo ta tafi. Na kira Abban Katsinan na faɗa masa, amma na san wallahi Umma bazata saurare sa ba. Mama Atika ƙawarta ce take zugata, duk abinda take yi wallahi itace take saka ta. Kuma da ba haks Msma Atika take ba, tana da kirki, ban ssn me ya canjata haka ba.”

Islaha dai bata ce komai ba, Safeera ta riƙe hannunta ta ce, "zan zama marainiya ta ƙarfi ta yaji, babu Umma, kema babu ke, babu inda zan saka raina na ji daɗi....." hawaye ya sakko mata ta ce, "da na san haka zai faru dana amince na rarrashi Baba ya amince nima naje, da Umma tana gida, sai tafi nida ke."

Islaha ta share mata hawaye ta ce, "ki yi haƙuri, nima kin san ba a son raina zan je ba, kin fi kowa sanin dalilina na tafiya."

"Islaha ga Ummata nan, na bar amanar ta a hannunki...."sai ta kasa magana sai kuka.

Islaha ma ta ɗora kanta a bayan Safeera tana kuka mai taɓa zuciya. Cikin kuka Safeera ta ce, "Don Allah ki kula da ita, in kin ga zata kauce hanya ki dawo da ita madaidaiciya. Ki ba wa Umma kulawa don Allah, ki dinga bata shawara kina nuna mata abinda ya kamata. Kin san dai ya ake faɗar aikin nan, don Allah ki kula min da uwata, kar ki bari ta aikata wani abun da zai zamar mana tabo har ƙarshen rayuwarmu!."

Islaha gyaÉ—a kai kawai take yi tana kuka ta ce, "zan yi Safeera, zan yi iya abinda zan yi. Ki daina kuka, ki taya mu da addu'a Allah ya sa mu faÉ—a hannu na gari."

Safeera taja numfashi irin na wacce ta yi kuka ta ce, "bani da kowa yanzu, kin tafi, Umma ma ta tafi, zan zama marainiya. Allah ya kiyaye ku, Allag ya nisanta ku da haram, ya kusanta ku da halal."

"Amin Safeera. Zan dawo, zan dawo mu cigaba da rayuwa kamar yadda muka fara. Ki ta yi mana addu'a kawai, zamu cigaba da magana a waya. Sannan zan bar amanar su Zainab a hannunki, na bar miki amanar su, don Allah ki kula da su, musamman Zainab. Tana cikin matsala, tana buƙatar mai bata shawara, tana buƙatar mai rarrashinta. Kema kin san akwai case a kanta, ki bibiyi case ɗin, duk abinda ya faru ki dinga faɗa min. Akwai abinda nake tunani kuma nake hange a kai, ki tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata, kar ki bar tabiyyar Zainab ta lalace kamar yadda Hafsa ta lalace. Don Allah ki kula min da ita, ina son Zainab kamar ƙanwata ta jini."

"Zan yi Islaha, in kina ganin zai yu zan iya yiwa Baba mu É—auko ta kawai ta dawo gidanmu da zama, in sha Allah bazan bari ta yi kukan maraicin ki ba. Sannan duk abinda zai faru zan bibiya kamar kina nan, duk abinda na samu zan dinga sanar miki in sha Allah."

Islaha ta goge hawayenta ta riƙe hannunta ta ce, "Na gode. Zan yi magana da Barr Suraj in na je, komai zai tafi kamar ina nan in sha Allah. In kina fa kayan bayarwa, ki haɗawa Zainab ɗin ki bata.”

A lokacin Mama ta shigo ta bi su da kallo ta ce, "To a taso zamu tafi, ki É—auko wannan takardar gwajin da nace ki yi. Ke Safeera zaki raka babar ki Abujan ne?."

Safeera dai bata ce komai ba, ta goge ido tana riƙe da hannun Islaha kamar yadda take riƙe da nata cikin kewar juna. A sanyaye Islaha ta miƙe ta wanke fuskarta, ta buɗe handbang ɗinta ta ɗauki sabon facemask ta saka, ta yi rolling kanta da mayafin abayar da ta saka. Safeera ta miƙe ta jawo mata jakarta, kanta yana sarawa saboda kukan da ta yi a haka suka fito falon.

Da Umma suka haɗa ido, Safeera ta bi Umma da kallo kamar yarda take kallonta. Umman ta zama wani iri, jikinta a sanyaye yake matuƙa, ta zubawa Safeera ido tana kallonta cikin wani irin yanayi mai wahala fassarawa.

Safeera ta ɗauke kai daga kallon Umma, ta riƙe hannun Islaha, itama Islahan kallon Umma take yi da take a zaune cikin shirin barin ƙasa.

Mama da take ta shige da fice ta kalli Safeera ta ce, "dake za a yi rakiya zuwa Abuja É—in ne?."

Safeera ta girgiza kai, ta kalli Islaha muryar ta a shaƙe ta ce, "Islaha zan tafi."

Tare suka fara takawa zuwa harabar gidan, Islaha ta riƙe hannun Safeera cikin rarrashi ta ce, "baki yi sallama da Umma ba."

Safeera ta goge hawaye ta ce, "babu amfanin sallama da ita Islaha, ta zaɓi duniya sama da mu, ta zaɓi aiki akan mijinta, ta zaɓi ta bar mu taje inda bata sani ba. Ta je kawai, ba sai mun yi sallama ba."

"Amma hakan ba daidai bane, ko meye ya fari kar ki manta uwace ita, ya kamata ki tuna hakan."

Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Islaha itama bata da buƙatar magana dani, da zata yi magana dani da...."

"Safeera!."

Umma ta kira ta tana daga bayan su, hakan ya dakatar da Safeera daga maganar da take yi.

Safeera ta runtse ido hawaye ya sake wanke mata fuska, ta juya ta kalli Umma da take tsaye, Umma  ta ƙaraso ta ce, "zan tafi Safeera, ki kula da kanki da ƙannen ki."

Safeera kasa magana tayi bata ce komai ba, Umma ta shafa fuskarta ta ce, "duk abinda zan yi zan yi shi ne saboda ke, zan yi ne saboda rayuwar ku keda ƙannenki. Na fi kowa sonku a duk duniya, duk wanda zai so ku a bayana yake. Zan dawo nan ba da jimawa ba, ki kula da kanki" daga haka ta juya a sanyaye ta koma.

Safeera ta yi murmushin takaici bayan Umma ta ɓace ta ce, "ki ji wai saboda mu take yi, mu mun sakata, mun ce muna buƙata ne?."

Islaha bata ce komai ba, dan ta lura in ta tanka zata iya jawowa Safeera ta faɗi wata magana wacce bata dace ba akan Umma ba, ita kuma ba haka take da buƙata ba.

A hankali suka ƙarasa bakin gate, Islaha ta rungume Safeera ta ce, "Zan yi kewar ki Bestie."

"Nima zan yi kewar ki Islaha. Allah ya kare ki a duk inda ki ke, ya yi miki abinda ki ke so. Allah ya sa tafiyar nan ta zama alkhairi a gare ki."

"Amin Ƙawata, na gode."

Safeera ta raba kanta da ita ta ce, "Allah ya sake haÉ—a fuskokin mu cikin alkhairi."

"Amin Safeera. Sai mun yi waya."

"Ki saka kati sosai, an ce ana jan kuÉ—in kiran waya."

"Zan yi."

Ta gyaÉ—a kai ta saki hannun Islaha ta fita daga gidan a sanyaye.

A haka Islaha ta koma ciki a sanyaye, ta tarar duk sun miƙe tsaye ana niyar fitowa, tana shiga Hajiya Karima ta ce, "ki ɗauko kayanki da hanzari, daga nan fa Abuja muka y, tafiya cs miƙaƙƙiya a gaban mu."

Islaha ji take kamar ta ce musu ita fasa, amma in ta tuna bashin da yake kanta sai ta daure ta kawar da komai daga ranta.

A sanyaye ta ɗauko handbag ɗinta, ta jawo trolly bag ɗin ta fito da ita, ta samu duk suna ƙofar gidan gida, ga wata mota mai ɗan girma wacce zata kwashe su gabaɗaya.

Aka saka jakar Islaha a booth, Islaha ta kalli ƙofar gidansu Safeera ta ganta a tsaye, ta ɗaga mata hannu itama ta ɗaga mata, hawaye ya sakkowa Islaha, ta share hawayen ta buɗe motar ta shiga aka ja motar suka bar unguwar.

Nana Haleema.
[6/30, 9:54 AM] KRBBK: RDB2P27
Nana Haleema.

Ikram kwance a bedroom ta zubawa hotonsa ido tana kallo cikin shauƙi da soyayya. Hoton ya yi matuƙar kyau, yana sanye cikin manyan kaya, ya saka hula, kwantaccen gashinsa ya sauka a bayan wuyansa. Ya ɗora hannunsa ɗaya akan hannun kujera, ya yi murmushi mai ƙayatarwa.

Duk wanda ya kalle sa sai ya so ya sake kallo, dan iya ganin hotonsa kaÉ—ai ma wata dama ce da ba kowa ne yake samu ba.

A bayyane Ikram ta ce, "yana da kyau, ilimi, kirki, wayewa. Ban damu da kuɗin da yake dashi ba, amma ni dai ina sonsa. Ina ƙaunar Hamma Rehaan, ina mafarkin ya zama mijina, ina so na rayu dashi har ƙarshen rayuwata.”

"Wa ki ke so?."

A bazata ta ji tambayar, hakan ya saka ta firgita ta juyo da sauri tana kallon Mummy da ta zuba mata ido tana kallon ta cikin tuhuma, Ikram ta sunkuyar da kai tana miƙewa zaune.
Chapter 38 · 0% Book details