← Book details Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 133

Sashe 83

Ragayar Dutse Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali take jan numfashin yana sauka a hankali, a hankali nunfashinta ya dawo daidai, ta saka hannu ta kwance roll É—in kanta ta bar mayafin a kanta bai cire gabaÉ—aya ba.

Ya bata ruwa ya ce, "karɓi ki sha." Ta karɓa a hankali ta sha, ta jingina da bango kujera tana lumshe ido cikin wani irin yanayi mara daɗi.

Sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya ce, "kina da asthma ne?."

Ta É—an sauke nunafshi tana É—aga kai alamun tana da ita, ya ce, "ban sani ba, da ban baki aikin da zai saka ki sanu attack ba."

Ta É—an sauke numfashi ta ce, "ina yin aiki sosai, yau an samu incidence ne kawai."

"Sannu. Ina inhaler É—in ki? Meyasa bakya yawo dashi?."

"Na manta shi."

"Meyasa?."

"Ba a tabbtaar da akwai asthma É—in ba sai few days back, a nigeria an ce babu, amma a nan ance akwai itama babu yawa, tana first stage. Ban saba da yawo dashi ba, shiyasa ban É—auko ba."

Ya ɗan girgiza kai yana kallon ta, ita kuma ta miƙe ta ce, "zan ƙarasa."

Ya dakatar da ita ya ce, "A'a ki bar shi, na gode." Bata zauna ba tana tsaye, ya kalle ta ya ce, "Dawo ki zauna." Ta zauna a hankali tana sunkuyar da kanta.

Ya sauke numfashi ya ce, "zan iya tambayar ki?."

Ta É—aga kai alamun eh za iya, Jazy ya ce, "kuma za ki faÉ—a min gaskiya?."

Nan ma ta ɗaga kai alamun eh. Ya ɗan girgiza kai yana kallon ta kafin ya ce, "Wanne irin aiki ne ya kawo ki ƙasar nan?."

Ta É—ago suka haÉ—a ido sannan ta ce, "ga shi nazo gidan nan ina yi."

"Dalilin zuwan naki nake so na ji. Na bibiyi contents ɗinki daga shekaran jiya zuwa yau, na bibiyi na dah dana yanzu, kuma na ga har tattaunawa kin taɓa yi akan disadvantges na aiko yara aiki wata ƙasa. Yanayin kalaman ki yana nuni da bai kamata a dinga tura yaran ba aiki irin wannan ba, hakan sai ya tabbatar min da ba ƙaramin dalili ne ya kawo ki nan ba. Miss Islaha Ina so na san dalilin ki na fara aiki a nan."

Ta É—aga kai ta kalle sa tana gyara mayafinta da yake son zamewa, ta É—an sauke numfashi ta ce, "ni dai na san ban zo saboda bibiyar abokin ka ba, dan ban san zan haÉ—u dashi a nan ba, na zo da niyar na samu kuÉ—i kawai, ban san yana zuwa Jeddah ba balle na san gidan nan."

Ya gyaɗa kai ya ce, "na san ba ki san shi ba, na ji kin ce silar zuwan ki yana da alaƙa dashi ne, shiyasa nake so na sani."

Ta sauke numfashi ta ce, "in na faÉ—a maka babu lallai ka yarda."

Ya ɗan yi murmushi ya ce, "Na yi bincike a kan ki, na san komai na ki Islaha. Halayen ki, da wanda za ki aura, ƙawar ki, wajen aikin ki, inda ki ka taso, da komai na sani. Zan yarda da duk abinda za ki faɗa min, in bazan yarda dake ba bazan ce ki faɗa ba."

"Meyasa baka bincika ka san dalilin zuwana nan É—in ba? Yadda ka san komai a kaina shima ya kamata ka nemo ka sani, Mr Jafar."

"Ina so na ji daga bakin ki, ki faÉ—a min Miss Islaha."

Ta ɗan yi shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta ce, "Na faɗa maka ya sace ni daman, a lokacin da ya sace ni ni kuma mahaifina yana Nadira hospital da yake Yola, za a yi nasa dashen ƙoda, ana neman kuɗin har miliyan goma sha biyu, ban da ƙananun abubuwa da aka kashe a asibitin. Ana tsaka da neman kuɗin aikin Baffa sai ya sace ni, ya kaini aka ajjiye ni a wani gida, sai dai a buɗe ni a bani abinci a rufe. Da na ga ji sai na nemi ganinsa, muka haɗu na nemi ya ƙyale ni sai yake nuna kamar sai na basa haƙuri."

Ta dakata tana turo baki tana kallon Jazy ta ce, "Haka kawai ban yi masa laifi ba haƙurin me zan ba shi?."

Ya ɗan girgiza kai bai ce komai ba yana kallon ta. Ta ce, "Ni kuma na ƙi ba da haƙuri, daga ƙarshe da na dinga mafarkin Baffa ya mutu na haƙura na bashi haƙuri, amma ba akan laifin da ya yi min ba, sai dan dalilin Baffa. Rana tsaka ya aiko wanda yake bani abinci ya ce za a kai ni gida. Ni kuma a lokacin ina falon sa, ina ta tunanin kuɗin aikin Baffa da nake mafarki har Baffa ya mutu saboda rashin kuɗin. Kawai sai na ga kuɗi akan sofa a ajjiye, kuɗi ne masu yawa har rafar dala guda biyu....."

Sai ta dakata bata cigaba ba dan bata san ya zai ɗauki maganar ba. Jazy yadda take naganar dariya take bashi sosai, a nutse take maganar amma cikin shagwaɓa da nuna zallar gaskiya akan maganar.

Ganin ta yi shiru sai ya ce, "ina jin ki."

"Ni kuma a lokacin ban san me ya shiga kaina ba, rashin mafita ya ja ni, tunanin halin da Baffa yake ciki ya rufe min ido, na kasa tunanin abinda zan yi ba daidai bane, kawai na É—auki rafa É—aya...."

Jazy ya wani ya zaro ido, sai ta yi sauri girgiza hannu ta ce, "wallahi ba sata na yi ba, bashi na É—auka, kuma na ce zan biya sa."

Jazy ya murmusa ganin yadda ta ruɗe wai ba sata ta yi ba, Islaha ta ce, "har camera falon na kalla na faɗa masa ni ban saci kuɗinsa ba, rashin mafita ne ya saka na ɗauka saboda na biya kuɗin aikin Babana. A lokacin ban san me ya shiga kaina ba, amma wallahi ban taɓa ɗaukar abin wani ba, shima ban san meyasa na yi ba a wannan lokacin. Tunda na ɗauki kuɗinsa na je aka biya kuɗin aikin sai na kasa nutsuwa, da ina da burin na kai ƙarar sa gaban hukuma, saboda a bi min haƙƙina na sace ni da ya yi ban yi masa komai ba, amma saboda kuɗinsa ya saka na fasa" ta ƙarasa faɗa tana wani karyar da murya.

"Ina ji"

Jazy ya faÉ—a yana murmushi dan shi wallahi dariya take bashi.

Islaha ta ce, "tun daga ranar sai na fara mafarki akan kuɗinsa, ko yaushe in na kwanta sai na ga yana cewa na biya sa kuɗinsa. Ƙawata ta ce min sata na yi ba bashi bane, hankalina sai ya tashi, na fara neman hanyar da zan biya bashin. Na yi tunanin shiga film ta hana ni, sai kawai na yanke shawarar zuwa nan, dan kawai na tara kuɗi na biya sa bashin da na ɗauko. Bayan wannan ni babu wani abu a raina wallahi, ko sunansa ban sani ba."

Ya sauke numfashi yana wani irin murmushi ya ce, "Miss Islaha."

Ta É—aga kai ta kalle sa suka haÉ—a ido, ya É—an girgiza kai ya ce, "You are so funny."

"Ba wasa nake yi maka ba, da gaske ne abinda na faÉ—a."

"Na san da gaske ki ke, kin bani dariya ne kawai."

Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "ban san tsautsayin da ya sake haɗa ni dashi a nan ba, dan ni mugun haushinsa nake ji sosai wallahi. Ina zama a nan ne dan na tara kuɗi na biyasa, daga nan na kai ƙarar sa a bi min haƙƙina, dan bazan bar case ɗin sace ni ya sha ruwa ba."

Ya yi dariya mai sauti, dan wallahi ƙyalƙyala dariya yake so ya yi, kawai ba ya son zubar da ajinsa ne.

Ya ce, "Miss Islaha yanzu kin fara tara masa kuÉ—in na sa?."

Ta É—aga kai ta ce, "na fara."

"Nawa ki ka tara?."

Ta É—ago tana kallonsa, sai kuma ta chunkushe fuska ta ce, "basu da yawa, riyal dubu takwas ne, dubu bakwai a ciki....." sai ta dakata tana jin haushin abinda zata ce. Sai kuma ta sake kallonsa ta ce, "dubu bakwai a ciki, shine ya bani."

Jazy ya ƙyalƙyale da dariyar da take damunsa, yadda ta yi maganar ya bashi dariya matuƙa, ya yi dariya son ransa yana kallon ta ganin ta sake haɗe rai.

Ya dakata ya ce, "i'm sorry Miss, abin ne ya bani dariya sosai. Ya sace ki, kuma ki ka saci...."

Ta dakatar dashi ta ce, "bashi ne, ni ba sata na yi ba."

"Oh Sorry, kin ci bashin sa, kuma shine yake ba li kuÉ—in da zaki fara biyansa?."

Ta kawar da kai ta ce, "ai ba kyauta ya bani ba, aiki na yi masa ya biya ni kuÉ—in aikina."

Har lokacin murmushi yake yi yana kallonta, ya É—an girgiza kai ya ce, "Kina da sa'a Miss."

Ta É—ago ido tana kallon Jazy ta ce, "dan ya bani kuÉ—in?."

Ya girgiza kai ya ce, "haÉ—uwa dashi gabaÉ—aya sa a ce."

"Rashinta dai, ni a wajena rashin sa'a ne. Na faÉ—a maka gaskiya Mr Jafar? Wallahi babu wanda nake jin haushinsa kamar sa."

Ya É—an yi clapping hannunsa yana gyaÉ—a kai ya ce, "So ya batun interview ki da Mr Rehaan Yola?....." ya faÉ—a yana kallom ta yana so ya ji me zata ce.

Nana Haleema.
[7/16, 12:11 PM] KRBBK: RDB2P60
Nana Haleema.

Islaha ta kalle sa tana girgiza kai ta ce, "wannan yana hannunka, kai ka yi alƙawari akan hakan."

Jafar ya ce, "To ai yanzu ai kina Jeddah, bakya Yola."

"Zan koma, in sha Allah."

Ya gyaɗa kai ya ce, "ai yanzu kema kin san shi, bakya buƙatar taimakona. Kina da damar da za ki bashi invitation ke da shi."

Da mamaki take kallonsa ta ce, "A ina na san shi ɗin? Ni fa ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba har yanzu."

Ya É—an yi murmushi kaÉ—an yana girgiza kai cike da mamaki ya ce, "Unbelievable!."

Ya sake kallon ta sannan ya ce, "Wanda ku ka haÉ—u a diamond hotel, ku ka haÉ—u a asibiti, ya sace ki, ki ka ranci kuÉ—insa, ya yiwa babanki tiyata, ki fara aiki a gidan sa..." ya É—aga kai yana kallon Rehaan da yake tsaye a upstairs yana amsa waya.
Chapter 83 · 0% Book details